Showing 1 words to 3000 words out of 8228 words

Chapter 1 - Daga Raino complete

03 Sep 2026

2

DAGA RAINO

Episode 1

AZARE

Yara ne suka zagaye motar suna ta

ɓ

a wa nadiya guntun tsaki taja ta gyara zaman sultan da yake cinyar'ta.

Dr mansur kallon ta yayi yace '' are you okay...?''

bata ce mai komai ba ta bu

ɗ

e kofar ta fita Sultan ta saka a kafa

ɗ

a

r ta , tana jin tsanar garin na ƙara rufe ta ban da ta matsa sai ya zo ita kuma bata so su rusa mata shirin ta da ba zata ta

ɓ

a barin sa ya zo gurin mahaifar sa.

wani durkusasshen gida ne na laka.

kofar gidan almajirai ne zaune wasu na rubutu wasu na biy

a karatu.

Wani dattijo ne zaune da Kur'ani irin bugun falle falle din nan na da, a hankali ya

ɗ

ago sosai yayi mamaki yau mansur idon sa yake gane masa.

Yaron da yafi wata biyar ba kira ba aike farin glass din sa ya dauko ya saka domin a ganin sa ba daida

i idanuwansa suke gane masa ba.

Dr mansur Suleiman azare ƙara sowa yayi ya

ɗ

urkusa har ƙasa ya gaishe da Malam babba me allo kaf fadin azare kana fadan wannan suna gurin sa za'a kawo ka malami ne babba wanda ake ganin girman sa.

kan'sa a ƙasa yace, '' ma

lam ina wuni.,,

ajiye kur'ani yayi yace, '' mansur lafiya qalau yau kai kake tafe..?''

kan'sa a kasa yace, '' eh wallahi na same ku lafiya...?''

Alhamdulillah kowa lafiya qalau.

ya fa

ɗ

a yana daukar Kur'anin sa.

mansur

ɗ

ago kan'sa yayi ya kalli nadiya

da ta tsaya a can gefe da ido yayi mata alama tazo.

Ranta idan yayi dubu ya

ɓ

aci haka ta ƙara so ina wuni.

Malam cikin fara'a yace '' mun wuni lafiya ya jikan nawa...?''

Alhamdulillah lafiya qalau ta fa

ɗ

a tana kawar da kan'ta gefe hannu ya saka ya kar

bi Sultan yaron kallon sa yake yana mai dariya da yake masha Allah akwai fara'a.

tashi mansur yayi, itama tashi tayi ba ƙaramin hakuri nadiya tayi ba ganin malam ya dauki wani ruwa a kofin silver ya bawa sultan yaron ne yake ta kallon lokacin da yake basa

ruwa shi ne ya dauki ruwan ya basa.

suna shiga soran gidan ta ja tunga ta tsaya tace '' sweet gaskiya ka karbo min yaro na ko baka ga ruwan da malam ya bashi ba kar wata cutar ta kama shi...?'',

ha

ɗ

e rai yayi yace '' nadiya me kike nufi mahaifina zai ba

wa sultan abin da zai cutar dashi ne...? Me ya saka kike haka ne ...? Wannan ruwan da kike gani shi nasha na girma har kika gani kika ce kina so na na aure ki.,,

yana gama fadar haka yayi gaba takaici hana ta magana yayi,

ɗ

age abayar ta tayi tana jan kara

min tsaki.

gidan duk kwata dakyar kake samun hanyar shiga cikin gidan.

sallama yayi Dada ta take tsakar gida a zaune ta kunna Radio da sauri ta washe baki tana cewa miji na yau kai ne a gari... matar ta tuba bata rasa miji da nayi fushi har ina cewa na s

ake ka saki tara yanzu kuwa na komar da kai.

dariya yayi yace , '' dada kenan daman ni nasan ba wanda ya isa ya raba mu.,,

Hakane kishiya ta ta kike rabe rabe zo ki zauna anan ta nuna mata , tabarmar kaba.

zama tayi tana yatsuna fuska kan'ta yana ƙasa t

ace '' ina wuni.,,

Dada tace '' lafiya sumul qalau ina Sultan yake badai ya isa yaye ba...?kin baro shi a gida.,,

a'a tare da shi muka zo mansur ya bata amsa.

Dada tace '' maman taku tana daki ku shiga kwana biyu bata jin dad'i alhamdulillah yau jikin t

a yayi sauki maharazu ya siyo mata magani tana surfe turmi ya fashe ya bugar mata kafa wallahi shikkenan take ciwo.,,

tun kafin dada ta ƙara sa ta miƙe ya shiga daki jikin sa yana rawa tausayin umma ne ya kama shi umma uwa ta gari umma da take kin ci take

kin sha duk ganin yayi karatun boko da yake so yayi ta siyar da kayan dakin ta yau shine ya samu abin duniya ya bar ta a haka ina hankalin sa yake me yake damun sa anya kuwa be zalinci kan'sa ba.

ɗ

urkusawa yayi ya shiga dakin tana kwance sai numfarfashi

take domin kafar'ta ta takura mata.

dafa ta yayi yace '' umma.,,

a hankali ta

ɗ

ago kan'ta bakin ta narawa tace '' Mansur kai ne...?''

ta fa

ɗ

i haka cikin rauni da son tabbatar da abin da take gani a zahiri domin ta jima tana mafarkin ya zo lokaci

ɗ

aya su

ka dena samun sa a waya kullum sai ace musu user busy.

a hankali ta , tashi zaune ta cire mayafin da ta rufe kafar ta dashi kafar ta kumbura sosai.

Mansur ƙasa yayi da idon sa ya riƙe hannun mahaifiyar sa yace '' umma ki yafe min. ,,

dafa kan'sa tayi ta

ce '' Mansur ko sau daya ban riƙe ka a cikin zuciya ta ba kullum addu'a nake maka babban buri na ka samu ka ciyar da iyalan ka ni basai ka bani ba , nasan idan kana dashi sai inda karfin ka ya ƙare duk rintsi duk wuya karka ci abin da bana ka ba duk inda h

alak take ka neme ta domin inhar ka fara cin haram ka lalata kan'ka da zuri'ar ka wallahi dakin nan da yana magana sheda ni kullum cewa nake Ubangiji ya yafe maka ni bakai min laifi ba Allah ya yi maka albarka kai da yan uwan ka karkai sakaci da ibadah.,,

duk dakiya irin tasa sai da yaji kwalla ta , tarar mai a idon sa umma ta cika uwa ta gari duk irin abin da ya faru ita kawai babban burin ta ya bawa iyalinsa ita basai ya bata ba ajiyar zuciya ya sauke yace '' ya jikin naki...?''

da sauki yanzun nan ne m

a ta dan tayar min.

ta fa

ɗ

a tana kallon kafar tata.

Mansur yace '' umma ki dena wannan surfen da kike yi ga yaran nan nan idan ma ya zama dole kiyi balle insha Allahu ba zaku ƙara sake shiga wani hali ba Allah zai rufa asiri.,,

umma tace '' mansur kenan

zama guri

ɗ

aya ba dad'i yaran da suke da son jiki musamman ma nuratu bata son ta daga ko tsinke ne dan ma ina mata jan ido.,,

Mansur yace '' to har da nake cewa son tafiya da ita , kinga nadiya aiki take fita sai ta dinga dan temaka mata da wani abun zan

saka ta a makaranta ga rainon Sultan ita kinga aiki take tafiya....,,

Umma tari ne ya tsarke dakyar Muryar ta , take fita tace '' a'a ba zan baka nuratu ba ga jidda nan ka dauke ta shikkenan mu cika alkawarin da mukai wa shatou.,,

gaban sane ya fa

ɗ

i sh

ifa shaf ya manta da wannan maganar danne fargabar sa yayi yace , '' to shikkenan ba damuwa .,,

yauwa Allah yayi maka albarka kai da yan uwan ka yau zaka tafi ko sai gobe...?''

Mansur yace '' yau inshallahu.,,

Umma jin jina kai tayi a hakan ma taji dad'

i ganin sa da tayi.

nadiya ce ta shigo a can gefe ta zauna ta gaishe da umma amsawa tayi cikin kulawa.

tana tambayar ta ya iyayen nata alhamdulillah lafiya qalau tace musu.

umma kin ga nuratu ta hana ni daukan sultan ko, wata yarinya ba zata huce shekar

a goma sha

ɗ

aya , ba ta shigo tana fadar haka.

Ganin yaya da matar sa da sauri ta gaishe da su amsawa yayi kan'sa yana kan wayar sa jidda zama tayi tana cewa umma kice ta bani shi gata can ta , tafi gurin dada dashi.

Umma tace, '' ki kyale ta ke da riƙe

shima sai ya ishe ki tare zaku tafi.,,

da sauri ta zaro ido lokaci

ɗ

aya nadiya ta

ɗ

ago ita da gidan ta shi ne zai dauko wani be fa

ɗ

a mata ba ai ita ce me gidan tun da dai ta haifi da namiji yanzu duk rabin dukiyar mansur tata ce.

Mansur ganin yadda take

kallon sa sai yayi sauri ya rubuta mata message kamar haka nasan Sultan yana hanaki fita aiki da wuri da shirin sa shi ne nace a bani

ɗ

aya a cikin kanne na su dinga temaka miki kinsan ni bana son yan aiki ga kanne'na nan suna bukatar temako.

ajiyar zuciy

a ta sauke ta zata haka kurum yace zasu tafi da ita da yaga tashin hankali ita bata bukatar kowa daga dangin mijin ta ya rabe ta.

Jidda tashi tayi, ta fita ta zauna a kusa da, dada tace '' umma tace zanbi yaya dan Allah ki ce tayi hakuri ni wallahi bana s

on binsa .,,

Ungo dan uban ki kaf cikin ku, ki godewa Allah shi ne za kiyi mai butulci birni fa zaki tafi Abuja garin shugaban ƙasa.,,

hawaye ta share dan da gaske bata son tafiyar nan.

dada shiga daki tayi ta dauko nono me kyau fari tas dashi a cikin k

warya da ludayi fefe ta saka ta rufe nonan tace '' maza tashi ki kai mai.,,

turo baki tayi ta dauki ƙwayar ta shiga dakin ajiye mai tayi s gaban sa bata ce komai ba ta juya ta fita idon ta duk kwallah ta taru.

budewa yayi sosai yaji farin cikin kawo mai

nono da Dada ta yi daukan ludayi yayi,

bismillah yayi ya kai bakin sa.

Jidda dawo wa tayi ta ajiye wa nadiya a kusa da ita nadiya tace '' dauke alhamdulillah na koshi.,,

domin ko taba kwaryar ba zata iya ba wallahi.

to tace ta

ɗ

auka ta kai wa dada.

t

ace '' tace ta koshi.,,

Dada ta

ɗ

aga murya tace '' ke bana son ki dauke mu a matsayin surukanki ki sakata ki bararraje nan ma kamar gidan ku ne.,,

Nadiya tace '' wallahi da gaske na koshi.,,

to ai shikkenan cewar Dada.

Malam ne fa su maharazu suka shig

o kara gaisawa suka yi.

Mansur fita yayi shi da maharazu.

Nadiya ba ƙaramin takura tayi ba fitowa tsakar gida tayi kamar ance kallo hanya ganin maharazu da wasu yara da kwalayen macaroni taliya shinkafa buhu uku ta gani.

ta shiga uku shikkenan shiri

n ta ya lalace shi ya saka tayi blocking din su, suka dena samun sa innalillahi wa'inna ilaihir raji'un babban bakin cikin'ta tagan sa yayi wa yan uwansa ko mahaifan sa wani abin.

da ido ta bisu har suka ajiye su dada albarka ta dinga saka mai haka ma ,

malam da umma.

ganin lokaci yana kurewa koma gobe yana da patient da zai duba kuma yana da wanda zai musu theatre.

kallon jidda yayi yace, '' ki ha

ɗ

a kayan ki yanzu zamu huce.,,

Ihu ta saka tana buga kafar'ta nuratu minal me za su yi idan ba dariya ba d

akyar dada ta lalla

ɓ

a ta , ta shirya ta fito tana share hawaye kayan ta ta dauko da yake

ɗ

azu sukai wanki umma ta saka su, sukai ninki dan haka kayan kawai daukan su tayi a karamar Ghana most go.

Nadiya amsar sultan tayi sukai musu sallama.

har kofar

gida dada ta rako su haka su minal sai tsokanar ta suke yi.

bu

ɗ

e mata gidan baya yayi ta shiga ya miƙa mata sultan ta riƙe jakar ta a boot ya saka ta shiga mazaunin direba yayi nadiya ajiyar zuciya ta sauke ba karamin dad'i taji ba da suka fito waje ji t

ake kamar a kaya take.

a hankali suka soma tafiya Sultan kwanciya yayi a jikin jidda a hankali bacci ya sauke sa.

gyara mai ƙwanciya tayi itama ta miƙe kafar ta ta kwanta.

ba ƙaramar tafiya sukai ba nadiya kallon sa tayi tace '' gaskiya inhar ba zaka bi

ya mana kudin jirgi ba , bazan kara zuwa garin nan ba kalli awan mu nawa sai yanzu muka shigo.

be kulata ba yayi horn a wani katafaren gida.

Mai gado ya bu

ɗ

e mai a lokacin kuma kissa ta , tashi zaune shaf ta manta da sultan a jikin ta aikuwa ya fado ya z

unduna ihu.

da sauri nadiya ta juyo tana mata fa

ɗ

a daukan sa tayi tana shafa bayan sa jidda ware ido tayi ta soma kalle kalle fitowa sukai suka barta a ciki.

ganin bata da niyar fitowa mansur yace'' fito mana mun zo.,,

da sauri tace '' ban iya budewa ba

.,,

Nadiya yin gaba tayi tana jan uban tsaki zuwa azare be mata rana ba gashi ta dawo da wata bagidajiya yar kauye bude motar ma bata iya ba.

jakarta ta bu

ɗ

e ta ciro wani kati ta saka a jikin kofar.

Budewa tayi ta shiga parlour ne iya parlour duk wani

kayan jin dadin rayuwa akwai shi kujeru set uku ne a parlour.

bata tsaya a ko ina ba sai a bedroom din'ta ajiye Sultan tayi,

ta shiga toilet.

a bangaren mansur dauko kayan jidda yayi yana gaba tana bin sa a baya har suka shigo cikin parlour.

zama tayi

a ƙasa ajiye mata kayan ta yayi kusa da ita ya shiga daki ganin sultan yana zaune yana kuka da sauri ya dauke sa ya fito da shi.

miƙa wa jidda yayi.

ina tana kalle kalle bata san ya miƙo mata ba sai da yayi mata magana da sauri ta kalle sa ta amshe shi

.

shiga kitchen yayi bu

ɗ

e fanfo yayi ya wanke hannayen sa sannan ya bu

ɗ

e fridge lemo ya dauko cake a cikin wani box me kyau fitowa yayi dashi ya ajiye a lokacin kuma nadiya ta fito daure da towel ko rufe mata cinya me yi ba amsar sultan tayi tana cewa beb

tafiya nayi na watsa ruwa ga kukan da yake anya kuwa zai yarda da yarinyar nan...?''

lemo ya bu

ɗ

e ya kai baki sa sannan ya ajiye yace '' yau da gobe babu abin da bata saka wa zai yarda da ita.,,

Okay ta fa

ɗ

a tana juyawa.

Jidda kunya ce ta kama ta , tun

da take bata ta

ɓ

a ganin wannan rashin kunya haka ba ko matar yaya ado idan zata shiga bayi da hijabi take shiga ashe yar iska ce sai wani ta

ɓ

e baki take.

tana cikin wannan tunani yayi mata Magana da sauri ta

ɗ

ago tace '' na'am yaya.,,

dauki kayan ki, ki

shiga can dakin.

tashi tayi tace '' to.,,

dauka tayi ta tafi dakin da yake facing din'ta.

a hankali ta tura kofar daki ne me kyau komai akwai ajiye kayan hannun ta , tayi ta kwanta akan kujera tana sauke a jiyar zuciya da yake a kwai kujera guda daya a

kwai gado.

mamakin dukiyar yayan nasu take , a hankali bacci ya dauke ta ba zato ba tsammani taji

ɗ

ala mata duka da sauri ta miƙe tsaye jikin ta yana rawa domin sosai dukan ya shige ta.

Nadiya ce tsaye akan ta abincin hannun ta , ta

ɗ

angwarar mata a ƙas

a duk kusan rabi kantso ne kallar abincin tayi ta

ɗ

ago ta kalle ta tace '' ngd aunty.,,

harararta tayi ta ajiye mata sultan tace '' dan uban ki ba zama kika zo ba kar na ƙara ganin kin kwanta a kan kujera dan uban ki a nan kika saba kwanciya ne...? da zak

i miƙe min wannan bak'ar kafar taki...? idan kika ji yayi kuka kisan yadda za'a yi ki lallashe shi karki kawo min shi zan huta ne.,,

Jidda muryar ta na rawa tace , '' to inshallahu bazan sake kwanciya ba kiyi hakuri.,,

rankwashin ta , tayi akai ta juya t

abar dakin jidda daukan Sultan tayi tana shara kwallar ta zama tayi ta soma cin abincin da ta kawo mata da yake yunwa take ji tas ta cinye shi ruwan da ta kawo mata a cikin kofi ta sha tana kokarin ajiyewa ta shigo tana harararta tace, '' ki ajiye plate d

in da kofin a wajen ki komai da shi zaki dinga yi karki saka min cuta ni da

ɗ

ana.,,

Jidda to tace mata..

kwanciya tayi a ƙasa ta kwantar da sultan a ruwan cikin ta yaron laluban ta ya fara yi yana son ya sha nono da sauri ta

ɗ

auke hannun sa tana rarraba

ido so take takai mata shi tana tsoran tijarar ta.

mansur ne ya shigo da wando three quarter da riga armless ba ƙaramin kyau kayan sukai mai na milk da maroon kalar kayan ga wani farin glass da ta saka da laptop a hannun sa yace , '' ta kawo miki abinci..

.?''

da sauri ta tashi ta

ɗ

aga kan'ta kwallah na taruwa a idon ta so take tace mai gida take so amma babu fuska ko dama tana shakkar sa

ɓ

alle yanzu da ya ƙara zama kalar masu kudi komai nasa ya canza ya zama kato.

bece komai ba ya juya ya fita kuka ta ru

she dashi kifa kan'ta tayi a jikin gado ta fara kuka har ga Allah bata son zama a cikin gidan nan.

ta jima a haka sannan ta tashi, ta hau kan gado ajiye Sultan tayi a hankali da ya fara bacci.

saukowa tayi so take tayi fitsari ya matsai ta amma ta ƙasa f

a

ɗ

a domin bata san toilet ba ganin yana shirin kashe ta fitowa tayi bata samu kowa a parlour ba sai jin hayaniyar su tayi sama sama tafi

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login