Showing 6001 words to 8429 words out of 8429 words
na gefe tana kallonsu cikin shauƙin abin itama kafin tamiƙe ashiga sha'ani da ita. humm wa'iyazu billah. Wannan abin da Hajiya Rukayya keyi ayanzu shine Ahaji dikko yakamata tanayi agidanshi wanda yayi sanadiyyar kwanciyarshi jinya har ila yau.
Nigeria
Tun ranarda yah fawan yasamu nasarar kasancewa da humaira tun a wannan ranar suka buɗe sabon babin soyayya me ban sha'awa domin wani irin sonta yakeji da ƙaunarta acikin ranshi wanda yamantar masa da maisoon sam acikin rayuwarshi,,,,wata irin kulawa yake bawa amaryarshi wadda sam ba'ayi zatoba balle tsammani,,,,,itama hakan tazage tana farantawa mijin nata iya iyawarta domin kuwa sosai take tafiyardashi yadda yakeso...afannin Aisha da yah muhseen ma abin ba'a magana sedai muce Allah yaƙara danƙon soyayya...tsakanin zamanta da humaira kuwa masha allah domin kamar wasu ƙawayen junan hakan suke mu'amalarsu, cikin soyayyar junansu.
Zaune suke akan dining a pert ɗin humaira suna cin abinci, yah fawan yashigo gidan da sallah ɗauke abakinshi...dasauri humaira tazo ta rungumeshi tana faɗar "sannu da zuwa hubbi na kadawo lafiya? Kiss ya manna mata a kumatu, tareda kashe mata ido ɗaya yace "'lpy qalau my princses se kewarki kawai, yasake manna mata kiss agoshi, yana ƙoƙarin matseta ajikinshi...dasauri Aisha tamiƙe tana faɗar "yah fawan sannu dazuwa. Firgigit yaɗago yana kallonta kafin yace "au dama kina nan wai? Sa'idone ya zaunar dakeko? Bro yakoya miki saka ido ko? aiko zanyi maganinki...ido tawaro cikin ɗan tsoro tace "ni kuma yah fawan minayi? Zakisan abinda kikayi ai..."ba abinda tayi kuma ba wanda zata sani yawwa garama kasani karka kuskura kataɓa min mata kayimin ɓarna malam, yah muhseen yafaɗa yana ƙoƙarin shigowa parlor.
Ido yah fawan yawaro cikin mamaki yace "kai haba 😳 mikake nufi bro banganeba? Cewar yah fawan cikin mamaki... murmushi yah muhseen yayi tareda kashe mai ido ɗaya yana murmushi kana yajanyo Aisha jikinshi yarungumeta cikin tsokana yace "ƙanwata kina tsaye za'ataɓamin mata daga zuwa miki firako? "Narkewa humaira tayi jikin yah fawan cikin shagwaɓarta tace "Allah yaya bahaka bane shima faɗa ne kawai yayi ko hubbi na? "Kai kawai yah fawan ya iya ɗaga mata yana sakar mata murmushi, domin jira kawai yakeyi yah muhseen yafita yaɗauke abarshi suje sufaran tawa juna...yah muhseen kuwa kamar ya harbo jirginshi hakan yasa ya doka mishi harara afili yace namamajo kawai kana ya ɗauke matarshi suka fice,,,, fitarsu keda wuya shima yaɗauki tashi suka wuce bedroom ɗinsu, yana faɗar "wayyoo my hume kibani abin daɗi plesse kinji se neman fasamin wando takeyi. Murmushi humaira tayi tareda kai hannu tariƙo hajiyar datayi tsaye kamar rodi, kafin tayi magana yah fawan yace "washhh allahh naahh kinjiko daɗi takeso wlh yafaɗa dede lokacinda suka ƙarasa bedroom ɗin.
Saudia
Afannin maisoon da sheikh sudais ma hakan abin yake kullun cikin ƙara ruruwa wutar soyayyar su keyi wani irin so da ƙaunar haɗi da kulawa suke bawa junansu,,,,hakan kwanaki sukaja sosai,,,kullun se maisoon taje gun gimbiya zaitun safe da yamma domin ta gaidata, ayanzu hakan tahanawa bayi kulada bedroom ɗin gimbiya zaitun da kuma abinda zataci, domin itace da kanta ke girka abincinta aciki take kaiwa gimbiya zaitun da memartaba sarki hassan,, gimbiya zaitun tabata hadimai kusan huɗu masu yimata hidima sedai tamaidasu acewarta biyu sun isheta suma sabida sutayata wasu aiyukanne...afannin gimbiya saudat da yarta kuwa har yau basu ƙara haɗuwa da maisoon ba domin sun bazama neman miyagun malaman tsibbo kuma sunyi nasarar samun biyan buƙarsu domin kuwa sun je gun wani hatsabibin boka wanda yabasu wani garin magani yace ita kursum ce dakanta zata zubawa sheikh sudais shi acikin duk abinda zesha kana ta tabbatar yasha idan tayi wannan kuma washe garin ranarda tayi hakan setaje tayi wanka da ɗaya maganin tasaka sihirtaccen turaren daya bata kana taje tahaɗu da sheikh sudais, duk yadda ijen aljani baya riskarsa tabbas idan tayi aiki da abinda yabata bata kuskure ba to wannan tsafin zekamashi, baze ƙara kallon mata mace matsayin maceba se ita hakama ze tsani maisoon mummunar tsana kana memartaba ze koreta daga masarautar,,, wannan abin yayi musu daɗi ba kaɗan ba, suka juyemai maƙodan kuɗadenshi kana suka dawo masauratar cikeda farin ciki.
Da yamma liss bayan maisoon da hadimanta sun kammala abincin dinner, tacewa hadima fuwa takai akan dining itakuwa tashiga bedroom ɗinta domin tayi wanka...bayan hadima fuwa takai kayan abincin kamar yadda maisoon ta umurceta seta dawo tashiga gyara kitchen ɗin domin hadima juwaira taje pert ɗin gimbiya zaitun takai mata nasu itada memartaba.
Cikin sanɗa kursum tashigo parlor kamar wata ɓarau niya kallo ɗaya zaka mata kasan cewar batada gaskiya, ganin bakowa a parlor yasa taji wani irin daɗi aranta, cikin sauri taƙarasa gun dining ɗin tareda buɗe wani juck dataga duk yafi kyau da ɗaukar hankali, murmushi tayi ganin da faffen ruwan black Tea ne aciki domin tasan shine abinda gimbiya zaitun kefara sakawa akai mishi ko lokacinda beyi aureba, cikin zumuɗi tabuɗe ledar hannunta jikina rawa tajuye maganin datazo dashi, kana tamotsashi cikin sauri tarufe tareda juyawa tabar parlor zuciyarta fyas hakan tanufi ɗakin uwarta cikeda murmushin samun nasara, hakan suka rungume juna cikin jin daɗin ganin aikinsu yafara tafiya yadda sukeso.
Bayan fitar kursum dakamar minti 15 yarima basam da yarima junaid suka shigo parlor shigowarsu yayi dede da fitowar maisoon, tayi ado irinna ƴaƴan Hausawa inda tasaka riga da zane na atanfa gliter me ruwan ash calor da browon acikinta, gaskiya ba ƙarya tayi kyau sosai gwanin sha'awa gawani irin sheƙi da fatarta keyi kamar ka kwanta jinin yafito, hakama jikinta ko ina yaƙara cika domin ita kanta dataje fitowa taji muryar su yarima junaid seda takoma ɗauko ɗan ƙaramin mayafi ganin yadda breast ɗinta sukayi kamar zasu fasa rigar sufito,,,da murmushi ɗauke akan kyakkyawar fuskarta taƙaraso cikin parlor. "Anty gimbiya barka da yamma, cewar yarima basam. "Yawwa ɗan ƙanena mejiran gadon Saudia, tayi maganar cikin tsokana domin ahakan suke barkwanci suda ita. "Humm gimbiyar alaramma sheikh sudais sarkin Dubai na gobe, barkanki dai da hutawa. "Harara tadokawa junaid domin dama hakan suke shida ita..cikin murmushi yawaro duka idanuwanshi kana yace "nashiga ukku gimbiyar yah sheikh irin wannan harara haka, kai gaskiya dai nikam karnayi mafarkin wannan idanuwan..dariya kawai maisoon tayi har haƙoranta suka bayyana kana tace "Allah ya shiryeka junaid...ameen shirin jigida wanda baya kwancewa. Duka yarima basam yakai mishi yana gocewa cikin dariya yace "Allah idan ka karyani kaida Ammi na...shidai yarima basam bece mishi komaiba domin damacan shiba meyawan magana bane....abinci suka buɗe kowannensu yazuba abinda yakeso yaci kana suka fara cin abinsu cikin nishaɗi. Junaid ne yajanyo juck ɗin data zubawa sheikh sudais black Tea ciki ze ɗiba, cikin sauri ta karɓe tana faɗar "wannan kam na manyanka ne yaro, tareda zabga mai harara....yarima basam ne ya kalle kana yace....!
Autar alheri ✍️
🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘
Book 4
Page 77 & 78
"Yace anty gimbiya zansha plesse... murmushi tayi kawai tabuɗe juck ɗin domin tazuba mishi, sekuma ta tunada abinda tasakawa sheikh sudais aciki, ido taɗan waro sa'annan tace "i'm sorry my ƙane barana haɗa ma wani wannan na yah sheikh ne banaso na wahalarda ƙanena. Shima murmushin yaƙarayi kanshi aƙasa yace "ngd anty domin yagane nufinta. Harta juya zata shiga kitchen sekuma tatsaya tunawa da wani kamshin dataji lokacinda tabuɗe juck ɗin, hakan yasa tadawo taƙara buɗewa tareda kai hancinta, tabbas kamshin shi yasauya, cup taɗauka ta zubo Tea ɗin cikin mamaki takebinshi da kallo domin koda yake baƙi kslarshi tacanja sosai yakoma kamar dack blue sosai ɗinnan, wani irin abune yazo mata azuciya yatsaya atake idonta suka fara ƙanƙacewa, cikin ɗaga murya tadokawa hadima fuwa kira kamar zata tsaga parlor.
Dukkansu kallonta sukayi acikin mamakin sauyawarta lokaci ɗaya,,,itakuwa hadima fuwa dasauri tafito daga kitchen ɗin tana amsa kiran da maisoon tayi mata. Wani mugun kallo ta watsa mata kafin tace "fuwa waye yataɓa abincinnan bayan nabar kitchen? Ta tambaya idonta ƙuri akanta. Cikin mamaki da tsoro hadima fuwa tace "bawanda yataɓa ranki yadaɗe nice kawai na ɗauko nakawosu nan Allah dai yasa ba laifi nayiba? Shiru maisoon tayi tanabinta da ido ko ƙiftawa babu kafin tanisa tace "waye yashigo kafin su basam? Kuma ina hadima juwaira? Tasake jefa mata tambayar. "Bawanda yashigo ranki yadaɗe kuma juwaira tunda taɗauki abincin memartaba bata dawoba...kai kawai maisoon yajikinta kana tace "kin tabbata? "Eh ranki yadaɗe. Shikenan jeka. "Godiya nake Allah yaƙara miki lafiya, cewar hadima fuwa tana barin wurin hartakusan shiga kitchen sekuma tadawo dasauri tana faɗar "tuba nakeyi uwar gijiyata tabbas aɗazu ina kitchen naji motsi a parlor sedai koda nafito bayan gimbiya kursum kawai nagani tafita daga parlor, taƙarasa zancen kanta aƙasa. Ido suka zaro atare, ita kuwa maisoon kafeta kawai tayi da ido kafin tayi saurin riƙe Hannun junaid dayaje saka abincin abakinshi. Cikin faɗuwar gaba suke kallonta, ita kuwa cikin bada umurni tace kowa yadakatarda cin abincin nan, kana tajuya zuwa ƙofar fita parlor cikin sauri kamar zata tashi sama,,,,dukkansu da kallon mamaki suka bita amma ba wanda yayi yunƙurin binta.
Tana fita bata zarce ko inaba se pert ɗin gimbiya zaitun, tareda nufar bedroom ɗin gimbiya kursum kaitsaye sedai tun kafin taƙarasa ciki sukaci karo da ita abakin ƙofar, kallon kallo aka tsayayi tsakaninsu kafin maisoon tace "yah sheikh yace nakiraki, tafaɗa cikin basarwa. Wani malalacin murmushi kursum tayi aranta tana faɗar "lallai aikin wannan bokan shine ake kirada yankan wuƙa. Afili kuma setace "muje tayi gaba cikin ƙarairaya hadiman dasuka rakota suna take mata baya har pert ɗin sheikh sudais, tana shiga parlor Maisoon ta dakatarda hadiman abakin ƙofa kana itama taƙarasa ciki....kursum kuwa su yarima basam takebi da kallon wulaƙanci ganin yadda suka zuba mata ido...Maisoon tana ƙarasowa wurinta tace "bisimillah zauna kafin yafito tayi maganar kamar ba komai. Seda kursum taɗan yamutsa fuska kana taja kujera tazauna tana ɗan jujjju idonta ranta wasai musamman dataga black tea ɗin da maisoon tazubo a cup setayi tunanin shine yasha yarage.
Ƙarasowa maisoon tayi wurinta kana tace "kitaɓa wani abin mana tayi maganar tana ɗauko black tea ɗin data zuba a cup taƙara wani sa'annan tamiƙawa kursum....wani ɗan iskan kallo tabita dashi na bakida hankali kafin taja tsaki cikin tsiwa tace "nayi Miki kamada wadda zataci banzan abin hannunki ne? kawai kije kisamarwa yah sheikh zuwana koni naje nasameshi dakaina, taƙarasa zancen tana bankawa maisoon harara..gira ɗaya maisoon ta ɗage mata kana tayi murmushi tace "au haba Ashe dai zaki iya samunshi? Humm to nidai duk ba wannan ba kawai ki karɓa domin shine abinda zebaki damar ganinshi, taƙarasa zancen tana ƙoƙarin kai mata cup ɗin bakinta. Cikin ɗan firgici kursum taja baya tana bankawa maisoon wata muguwar harara"wlh bazan shaba ina ruwanki dasenasha wani abu anan gidan nasani kowani mugun abin kika sakamin aciki, tayi maganar cikin firgici tana ƙoƙarin barin parlor....wata muguwar ɗamƙa maisoon tayi mata tana hiyo da Ita, kafin tahaɗe girar masa da kasa tace "ƙarbi kisha tun muna sheda juna nidake domin wlh ko sama da ƙasa zasu haɗe sekinsha wannan tea ɗin zakibar pert ɗinnan.
Wani irin tsorone yamamaye kursum lokaci ɗaya gumi yafara wanke mata fuska. Sukuwa su yarima junaid ido kawai suka zuba musu suna kallon ikon Allah domin suma a ɗarɗare suke zukatansu fal da tsoro kar Ace har abincinda suka riga sukaci akwai wani mugun abin aciki. Jabaya kursum tafarayi tana neman wurin guduwa, cikin sauri tajuya zata gudu, cikin zafin nama maisoon tasaka mata kafa tafaɗi yarab, sa'annan ta ɗauketa da wasu gigitattun matuka har biyu Seda duka parlor ya amsa, Ita kuwa kursum ta buga wata muguwar ƙara domin sosai marin yashigeta wanda ya haddasa mata ɗaukewar ji da gani lokaci ɗaya, ido yarima junaid yawaro yayinda yarima basam yasaki murmushi....ƙafa Maisoon tasaka ta danneta da guywarta kana taɗauki cup ɗin taɗora akan bakinta tareda saka hannun ɗaya ta toshe mata hanci wanda yasaka dole tabuɗe bakinta babu shiri,,,juye mata Black tea ɗin tashigayi tana haɗiyewa dole, seda tashanye ganin wani yazube ƙasa yasa Maisoon kallon yarima junaid da idonta dasuka koma red sharr tace "zubamin wani, tafaɗa cikin wata irin murya me mugun amshi...dudda cewar yarima junaid yaso kin zubomata amma yanayinta ba ƙaramin tsoro yabashiba Hakan yasa yaɗauko cikin sauri yazuba mata har seda yacika cup ɗin...Hakan taƙara juyewa kursum shi kana ta ɗagata tana banka mata wani mugun kallo, ganin tana yunƙurin ami ne yasa Maisoon yimata wata muguwar shaƙa cikin ɗaga murya tace "narantse da sarkin dake busa numfashi idan kikayimin amai anan Sena fidda miki maƙoshi waje, yafaɗa tana sauke mata wasu zafafan marukan..atake idon kursum suka firfito waje kamar zata sheƙa barzahu sekakari takeyi cikin galabaita da azaba...wasu marukan Maisoon taƙara sauke mata tana faɗar "uban waye yabaki damar shigowa parlor na? mikika zubamin a abinci? Wakikeson cutarwa? Ni MIJINA? Ko ƙanenshi? Wlh idan bakiyi maganaba Sena kasheki shigiya marar imani uban me kika zubamin nace? Tafaɗa cikin daga murya wanda yayi Dede da shigowar sheikh sudais parlor cikin kamala da sallama ɗauke a bakinshi,,,sedai abinda yagani yayi bala'in bashi tsoro da mamaki, dasauri yaƙarasa wurinsu yana faɗar "subhanallah butti Mike faruwa ne? saketa plesse, yafaɗa yana ƙoƙarin raba maisoon da kursum sedai abin yaci tura ganin yadda takafe wuri ɗaya kamar dutse, seda yayi da gaske yasamu ya ɓanɓareta daga jikinta, atake kursum tazube awurin sumammiya..betsaya komaiba kawai ya saɓa maisoon akafaɗa yanufi bedroom ɗinshi da Ita, yana watsawa su yarima basam harara ganin yadda suka zuba ido kawai suna kallon matsrshi zatayi kisan kai ga dukkan alamu suma atsorace suke. Ɗauke kansu sukayi dasauri daga kallonshi harya shige bedroom ɗin.
"Haba yah sheikh wannan hararar taka ai sedai kayi waye ze tunkari Anty gimbiya awannan yanayi tahaɗa dashi, cewar yarima junaid..shidai yarima basam bece komaiba se hadimanta dayakira wanda suke abakin kofa suna rawar ɗari babu halin shiga dudda sunajin ihunta tunda Maisoon ta hana, kuma idan suka barta zasuci abinsu agun gimbiya saudat, sunajin kiran yarima basam cikinsu ƙara durar ruwa, cikin bada umurni yace susaka mata ruwa kana sunɗauketa daga nan su kaiwa uwarta kafin me gidan tafito domin idan tagantanan ƙarasata zatayi...aiko cikin sauri suka aiwatar da abinda yace..sukuwa pert ɗinsu suka nufa suna tafe yarima junaid na faɗar"tab dijam dama Ashe Anty gimbiya Hakan take Ashe tamafi ƙarfin yadda muke tunaninta tab lallai akwai dambarwar fitina agidannan zanga ya Anty saudat zatayi...shi dai yarima basam bece mishi komaiba seda suka shiga parlor su kana yace "wannan hukuncin datayi mata shine Dede domin bamusan watayi nufin cutarwa ba kuma kila mu muringada munshiga tarkonta tunda munci abincin sedai kawai Allah yakaremu...ameem ameen amma da Anty gimbiya ta huce zanje na ɗauko abinnan nakaishi abincika ko akwai wani abu aciki, cewar yarima junaid..humm kawai yarima basam yace yana shigewa bathroom ɗinsh
Sheikh sudais kuwa yana shiga ya ajiye akan bed ɗinshi amma se wutsil wutsil takeyi nason kwacewa tafito sam taƙi yadda ta zauna..ganin taƙi yadda ta zauna ne yasa yayi saurin....!
Autar alheri ✍️