Showing 81001 words to 84000 words out of 104433 words

Chapter 28 - DANGI DAYA COMPLETE

boye masa ba, haka Yazauna yana tunanin mafita
Nihla ya hango tareda Ilham azaune agefe, tana riqeda lil Abba a hannunta

Ahankali yataka yaje wajansu Yazauna, yadubi Nihla tareda miqa mata wayarsa yace "qanwata
temakamin da number Angon namu mana"

Murmushi tayi kadan, ta karbi wayar tasa tasaka masa number ya Yusuf aciki, sannan tabashi,
ya karba yayi godia

Wayarta ce tahau qara, tana dubawa taga ya Yusuf ne, tadauka

Ilham da Aslam suka kalleta, cikin zazzakar muryarta yace "hello ya Yusuf , yakake yagida"

"lafiya amarya ta, nashigo kano fa, zanzo naganki inaso naji shirye shiryen dakika tsara, saina
wuce daga nan"

"Ayya ya Yusuf ai bana gida, munzo asbiti ne, saide nayima kwatancen wajan saimu hadu
anan, kaga sai Muje gidama nahadama wani abin kaci"

Be tambayeta waye baida lafiya ba yace "toki turomin adress din Inda kike yanzu"

Sunan asbitin kawai tafada masa yace yana kusa, tace to zata futo waje bakin titi Inda zai ganta

Wayar ta kashe tadubi Ilham tace "zanje waje nadubo ya Yusuf "

Ilham tace "to shikkenan"

Ahankali ta miqe tafuto, Aslam ya kalli Ilham yace "kibita mana, kidan bata shawara ko zata
saurareki"

Kallan mijin nata tayi, duk yashiga damuwa, tarasa wacce irin soyaiya sukewa tsakanin su shida
ya Abba, tace "to" sannan ta biyo bayan Nihla

Daga murya tayi ta kirata, Nihla ta tsaya ta, sannan ta qaraso sukaci gaba da tafiya
Ilham tace "ya Aslam ne yace nazo naraka ki"

Nihla tace "Allah sarki, kinga salihin miji, wallahi idan ya Abba ne bazai bar matar saba"

Murmushi tayi tace "nikam Nihla nabaki shawara mana"

"inajinki" cewar Nihla

Shiru Ilham tayi, saida suka qaraso bakin titi suna jiran ya Yusuf ya qaraso sannan tace "Nihla
Dan Allah meyasa bazaki tausaya wa ya Abba ki aure shiba?"

Cikin sauri ta dago kanta ta kalli Ilham tace "aure fa kikace Ilham"

Hannunta Ilham takama hannunta ta riqe tace "eh, aure nace Nihla, to menene aciki idan kin
aure shi? Nihla wacce irin zuciya gareki?yaushe kika koma haka? Mutumin nan yayi miki laifi
kuma yabaki hakuri, babu wanda baya aikata kuskure acikin Rayuwar sa Nihla, saide na wani
yafi na wani,kidinga tunawa ya Abba dan'uwana ne da'aka bar wasiyya cewa kuyi aure, Nihla
ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi muroqeshi gafara yayafe mana, haba
Nihla, yanzu ashe bazaki iya tausayawa yaron Momy ba? Bazaki iya ceto yaron Daddy daga
halin da yake ciki ba? Nihla wannan shine sakayyar dazaki nunawa Momy kenan? matar da
tasoki Tun kina qarama kina gaban mahaifiyarki? Duk cikin yaran Momy Babu Wanda ya
qyamaceki Nihla, kowa kokari yake yaga yafaranta ranki, Momy tana qaunar ki Nihla, Inda wata
uwarce da tuni ta sauya miki, suna qaunar dansu fa, soyaiyar dasuke miki ce tasa bazasu iya
nuna miki komai ba, idan kina tuna laifin dayayi miki bazaki taba yafe masaba, kuma bashi zaki
dubaba, a a, iyayen sa zaki duba, kinji de abinda likita yace, zuciyarsa tana gab da kamuwa da
ciwo, kuma komai yana hannun ki, idan kinso zaki iya ceto Rayuwar Dan mutanan dasuke
kaunarki Kamar yarsu ta cikin su, idan kuma kinso zaki iya barin sa, amma kiyi tunani akai "
Tana gama fada mata tayi shiru tareda sakin hannunta

Zuciyarta fal da tunanin maganganun Ilham, tabbas maganar ta Babu ta yarwa aciki, Momy
uwace abar alfahri ako'ina, to amma baban ta fa? Tayaya zata iya nusar dashi? Tayaya zata
fuskanci ya Yusuf da wannan maganar? adede lokacin yaqaraso wajansu, suka gaisa cikin
kulawa, ahankali suka qarasa cikin asbitin Ya kalleta yace" yanaga jikinki yayi sanyi ne? Waye baida lafiya? "

Murmushi tayi tace" lafiya ta kalau ya Yusuf , ya Abba ne baida lafiya, dukanmu ma muna ciki,
ko zaka qarasa ku gaisa da Momy duk suma suna ciki "

Yace" why not "

Ahankali suka qaraso cikin asbitin, cikeda kulawa Yusuf ya gaisa da kowa, sosai Momy ta ware
suka gaisa dashi Kamar Babu abinda yake damunta

Suma su Daddy sun yaba da halin sa sosai, kowa dayake wajan yayaba da tarbiyarsa, babu
laifi yanada nutsuwa

Likita ne yazo yace zasu iya shiga su ganshi yanzu, gaba dayansu kuwa suka nufi dakin

Yana kwance hancinsa sanye da oxygen, ga kuma na'ura agefen kansa tana aiki, dakuma
wadda take nuna yanayin hawa da Saukar numfashin sa

Cikin sauri Momy ta qarasa wajansa, ta dora kanta agefen gadon tasaki wani irin kuka, tama
kasa magana sai kuka datake sosai

Hajiya Farida ce tazo ta janye ta tana bata baki, gaba daya dakin Babu Wanda bai tausayawa
Abba ba, ajikin hajiya Faridanma bata dena kukan ba, tari yafara Ahankali, duk hankalinsu saiya
dawo kansa, Tun yana tari Ahankali harya dawo yanayi sosai, Aliyu yayi sauri yakira likita,
likitan na zuwa yace Dan Allah su fita daga dakin, gaba dayansu suka futo
Aslam yaja Yusuf gefe suna magana, wadda Babu Wanda yasan akan me suke tattaunawa
saboda sunyi nesa da mutane


Saida suka gama magana sannan Yusuf yakira Nihla, suka tafi zata rakashi wajan motarsa, har
tana mamakin wacce iri magana ya Aslam yayi masa? Kuma menene dalilin karbar number sa
awajan ta?
Har gaban motarsa sukaje yashiga Yazauna amma bai rufe motar ba, ta kalleshi tace " banji
kace komai ba, akan maganar da mukai waya"

Memakon yabata amsa sai yace "Wancen gayen yacemin sunansa Aslam, yayi min magana
akan ki, yace ma ya karbi number ta awajan ki zai kirani kuma sai akai sa'ah nazo, yafadamin
saboda ke Abba yake rashin lafiya, kece maganin damuwar sa, yayi min bayani sosai akan
hakan, kuma na gamsu da bayanin sa, Nihla why not muhaqura ki auri Abba?"














Mutara zuwa gobe insha Allah �🏻

Sharhi please










Amnah El Yaqoub �🏻[7/12, 9:57 PM] El Yaqoub: ��DANGI 'DAYA��
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub



Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



51&52


Lokaci daya idanunta suka cicciko da qwallah, ta dubeshi muryarta na rawa tace "ya Yusuf...
Mekake fada hakane? Meyasa zaka qini saboda shi?"

"ba saboda shi nafadi wannan maganar ba Nihla, kinsani ina son ki, tunda kina qarama, Tun
bansan menene so ba nake tare dake acikin zuciyata, halin da suke ciki shida iyayen sa zaki
duba, mutanan nan sun karbeni hannu bibbiyu Babu Wanda ya nunamin komai ko akan fuska,
sunada karamci Nihla "
" yanzu me kake nufi kenan?"

" ki auri Abba Nihla"
Batare daya shiryaba hawaye yazubo masa yasaka hannu ya goge cikin sauri sannan Yarufe
motar tareda dora kansa akan sitiyarin motar yana kuka

Kallansa tayi tasaki wani irin kuka tareda juyawa ciki aguje tana kuka


Usman dake zaune gefensu Daddy yace "yanzu Daddy ai sai a fadawa su baba Ibrahim adaga
wannan aure na Nihla, mu dangin mahaifiyarta bamu shirya ba, saboda Abba bashida lafiya"

Alhaji Baqir yayi Murmushi yace "naga alama de Usman bakason wannan auren ko"

Kansa ya sosa yace "A a kawu, danaga wai hankali ba'a kwance yakeba"

Murmushi yasake yi, amma Daddy de yayi shiru baice komai ba, zuwa yanzu kam kodan ceto
Rayuwar dansa yakamata yaje su Gana shida Ibrahim Mai hakuri, yakamata su shirya suje su
sameshi


Cikin kuka tashigo wajansu, gaba daya hankalinsu yadawo kanta, Nihla kuwa bata zarce
ko'inaba sai wajan Momy, fadawa tayi jikinta tana kuka sosai, Momy tace "me yake faruwa
Nihla?keda waye?"

Shiru tayi takasa bata amsa, mezatace mata? Saboda ance na auri danki nake kuka kome?
Dan haka tayi shiru, Momy tasa hannu tafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, haka tayi shiru
amma cikin ranta wani kukan takeji tanaso tayi, Ilham tataso tace" kitashi mukoma can "

Babu musu tabi Ilham suka koma gefe sai Jan zuciya take, Ilham bata tambayeta dalilin kukan
ba, tabarta tagama hucewa tukunna

Nihla tayi shiru tana tunani, ita kuma tata qaddarar kenan, sai anzo auren ta afasa, yanzu gashi
shima yace ta auri Abba, hakan yana nufin za'a sake fasawa kenan akaro na biyu



������ ������


Washe gari Alhaji Basiru da Alhaji Baqir dakuma Daddy da Alhaji habib mijin hajiya Farida suka
shirya sassafe suka nufi Abuja
Saukarsu keda wuya Alhaji Isma'iel da baba sukayi musu masauqi acikin falon nasu, baba sai
mamaki yake irin wannan zuwan nasu

Saida suka gama gaishe gaishe sannan Daddy yadubi ma hakuri yace "Ibrahim wajan ka
mukazo gaba dayanmu nan da qoqon bararmu, haqiqa munyi maka laifi abaya, kuma muna
qara neman kuskure, ba kuma komai ne yasa nina aikata hakaba saidon kaunar yar'uwata

Aisha dakuma abinda kuka haifa, Awannan lokacin kokadan banaso nayima magana akan Zan
dauki Nihla natafi da ita, saboda nasan yanda kake jin mutuwar Aisha kaima bazaka so karabu
da yarka ba, nikuma ina qaunar yarinyar, hakanne yasa nadauke ta muka tafi, maganar aure
kuma da bamu sanar makaba wannan ma mun dauki laifin mu, amma maganar gaskiya itace
banine nayanke wannan hukuncin ba, iyayen mune, bawai ikona bane hakan, amma kayi hakuri
"

Baba yayi Murmushi yace"haba Alhaji, ai Babu komai, komai yariga yawuce, rannan ma kuwa
Shima Abubakar yazo shida Aslam"

Mamaki yakama su Daddy, ashe su Abba sunyi hankali, Alhaji Baqir mahaifin Aslam yayi
Murmushi cikin ransa yace shikkenan ma sun rage mana hanya, yadubi baba yace "ai
Abubakar dinma bashida lafiya, yana kwance a asbiti yanzu haka, zuciya ce takeson yimasa
ciwo, amma batakai ga farawar ba"
Alhaji Isma'iel yace "subhanallah... Subhnllh, kode shine yaron da Yusuf yake fadamin bashida
lafiya?"

Baba yadubi Alhaji Isma'iel yace "A a yaushe Yusuf din yaje kano?"

Alhaji Isma'iel yace "toni jiya yazo yake min kuka waishi afada maka sun hakura da aure shida
Nihla, saboda akwai wani dan'uwanta dayake rashin lafiya akanta, wai kada ya mutu a dalilin
su, toni kuma ban dauki zancen nasa serious ba, tayaya kuna tareda yarinya zakace kunfasa,
ban yarda da maganar tasaba, shiyasa ma ban yiwa mai hakuri maganar ba "
Alhaji Baqir yayi Murmushinsu na manya yace" wallahi shine, ai mungaisa dashi jiya, Yusuf
kenan, Yusufa yaron kirki "🤣

Alhaji Basiru yayi gyaran murya yace" ai jikin nasama da sauqi, har yanzu de bai farfadoba,"

Baba ya Jinjina kansa yace " inafa lafiya kana cewa yaro har yanzu bai farfado ba "🤣

Alhaji Isma'iel Yace"Allah sarki, Allah yabashi lafiya, to amma ina ganin tunda yara sun fahimci
juna harshi Yusuf din yayi jihadi, to ina ganin kawai ayi hakuri gaba daya tunda kowa ya fahimci
kowa yanzu, sai adaura musu aurensu kawai, idan Allah yabashi lafiya duk wata bidi'ah da
za'ayi suyi daga baya "
Farin ciki yakama Daddy, da kansa yasauko daga kan kujerar dasuke kai yafara yiwa Alhaji
Isma'iel godia, Alhaji Isma'iel yace

" Babu komai ai matar mutum kabarinsa "

Alhaji Baqir yace" toni ina ganin, tunda abin yazo da haka, memakon Muje musake dawowa,
kawai asiyo goro yanzu adaura, shikkenan anhuta "

Alhaji Isma'iel yace" A a akwai goro, Muje masallaci anemi liman yadaura musu auren, ni Zan
zama waliyin Nihla "

Baba yakasa magana ganin irin karamcin da Alhaji Isma'iel yayi masa, haqiqa samun irinsu a
yanzu sai antona

Gaba dayansu kuwa suka futo, kai tsaye masallacin unguwar sukaje aka kira liman, da maqocin
Alhaji Isma'iel Wato baban Nadiya, Alhaji Baqir yaje banki da kansa yaciro kudi, yace shine zaiyi
wa Abba waliyi, nan take kuwa aka daura musu aure akan sadaki nera dubu dari, aka danqawa
baban ta sadakin, kowa aka bashi goro, suka yiwa limamin ihsani, sannan suka futo kowa
zuciyarsa fes

Daga nan su Daddy sukayi wa su Alhaji Isma'iel godia, suka nufi Airport

Mamy da taji labarin abinda yafaru ta tausayawa Abba, saide wani bangaren na zuciyarta yana
jimamin rabuwarta da Nihla, taso ace danta Yusuf yasameta, amma yaya za'ayi, matar mutum
kabarinsa



������ ������




Zuwan su kenan asbitin itada Dida da Ilham, Diyana bata zoba tana fama da cikin ta, Ilham sai
fada take mata "kintashi kinsaka wa kanki damuwa ina dalili? Tunda shine yace zaiyi hakuri
yaya zakiyi dashi, amma Tun jiya kidinga kuka,Yaya zakiyi da qaddarar da Allah yadora miki,
kokuma zuwa zakiyi wajan Yusuf din kijashi ta qarfi, kuma Momy tayi miki Tambayar duniya
kinqi bata amsa, yanzu idan taji saboda Yusuf yace yafasa aurenne saboda danta ya warke kike
kuka ai ba zataji dadi ba, menene amfanin rashin mantuwa da ruqo Nihla "

Itama Dida tace"wallahi de kam, idan ma kina tunawa da lokacin da yace baya son ki ne
agaban family ai yakamata ace zuwa yanzu kisan cewa saboda ke dinne ya kwanta jinya, idan
mutane kowa da kowa yaji ya Abba yace baya sonki to yanzu kowa ya shaida ya Abba yadawo
yana sonki, kuma gashi Akwance baisan wake kansa ba saboda ke, duk cikin mu waye yasamu
irin wannan soyaiyar? Yakamata ki godewa Allah Nihla "

Nihla tayi shiru tana jin maganganun yan'uwanta, ahaka suka qaraso cikin asbitin da hannunsu
dauke da abinci, kasancewar ba'a barin kowa yashiga dakin dayake shiyasa suka nemi waje

suka zauna, sai Momy ce kawai acikin dakin nasa

Daddy ne yashigo asbitin fuskarsa dauke da farin-ciki Kamar ba dansa ne baida lafiya ba
Su Ilham suka gaida shi, sannan Nihla takira wayar Momy tafuto daga cikin dakin

Gaisawa sukai dasu Ilham suka qara yimata, yamai jiki sannan suka bata Abincin, Momy taji
dadi sosai tayi musu godia sannan sukai mata sallama suka tafi, sukabar Nihla awajan

Tazauna tana duba wayar hannunta, Momy dake gefe itada Daddy tace "Alhaji yanaga kanata
Fara'ah ne? Allah yasa lafiya"

Murmushi yayi yace "daga Abuja muke"

"Abuja kuma Alhaji, meyake faruwa"

Hannu yasa a aljihunsa yadauko goro yace "riqe wannan goron"

Momy ta karba tace "na menene Alhaji?"

Yace "goron daurin auren Takwarana ne shida yarki"

Momy ta zaro ido tare saka hannu abaki cikin mamaki, takai Kallanta wajan Nihla taga
hankalinta yanakan waya
Tace "Alhaji da gaske kake?"

"da gaske nake, ga shaida nan kingani, shikkenan Abba sai hankali ya kwanta"

Momy tasaki ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah... Allah nagode ma, to Alhaji binka zanyi mutafi
gida nayi wanka nahuta nima, tunda ga matar sa nan ita saita zauna ta dora daga ina na tsaya"

Daddy yayi Murmushi yace "to zo mutafi"

Abincin hannunta takai wa Nihla tace "Nihla riqe wannan Abincin, idan Allah yasa yau yafarka
shikkenan sai kuci, akwai kayan Tea aciki, idan kuma bai farkaba sai kici, ni natafi gida sai
munyi waya"


Mamaki yakama Nihla, tace "Momy gida kuma? Ba anan zaki kwana ba?"

Momy tace "a a, aina dena wannan zaman Nihla, yanzu kam saike" 🤣

Jikinta yayi wani iri, tayaya Momy zatace tazauna da ya Abba bayan tasan hakan bai kamata
ba? Tace "to Momy kuma...."

Cikin sauri Momy ta katseta, "Nihla bafa Zan zauna ba, yau kema ki d'ana"

Tadubi Daddy tace "Alhaji Muje"
Har sun fara tafiya Tajuyo tace "yawwa Nihla Karki Manta likita yace kullum dasafe ana goge
masa jikinsa da ruwa Mai Dan dumi, duk abinda kike buqata yana cikin dakin, idan baki ganiba
saiki kirani"


Nihla ta kalli Momy takasa cewa komai, wai me Momy take nufi ne, ya za'ayi takama taba
jikinsa bare har dasu goge jiki? 🤔

Momy kuwa bata jira amsar taba, suka tafi itada Daddy











Kuyi hakuri da wannan ba yawa

Sharhi please �











Amnah El Yaqoub �🏻
[7/14, 2:19 AM] El Yaqoub: ��DANGI 'DAYA��
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


53&54



Jiki a sanyaye tajuya cikin dakin, ahankali ta tura kofar dakin tashiga, idonta yasauka akansa,
babu oxygen din ancire masa, amma fuskarsa tayi wani irin fari, Dan qaramin lips dinsa ta kalla
duk yafara bushewa, gashin idonsa sun kwanta gwanin sha'awa

Kujerar dake gefen kansa tazauna ta ajiye Abincin, sannan tayi shiru tana tunanin irin wannan
zaman jinya, ko yaushe zai farka? 🤔

Ya Yusuf ne yafado mata, Allah sarki, tunda sukai maganar rabuwa dashi basu sake waya ba,
tana mamakin yanda lokaci daya yace zai sadaukar da soyaiyar ta ga ya Abba, bayan tasan ya
Abba da kishi idan shine ba lalle ya'iya hakura da itaba

Haka tazauna shiru ita kadai a dakin, lalle idan hakane Momy tayi kokari, amma tarasa Inda
Momy tasa gaba, tayaya zasu barta daki daya da ya Abba?

Ajiyar zuciya tayi tajuya ta kalleshi, saikuma ta dauke kanta cikin sauri Kamar tana tsoro karya
kamata



������ ������



Mutanan gida kam, kowa labari ya sameshi, saboda su Alhaji Baqir kowa daya koma gida
yafadawa iyalansa, Aslam Kamar yayi me saboda murna, Ilham kuwa bakinta Yaqi rufuwa, haka
tadinga d'aga lil Abba sama tanayi masa wasa Yaron kuwa sai dariya yake shima Kamar yasan
abinda ake
Aslam Yazauna yanemi number Yusuf domin su tattauna kuma yaqara yimasa godia amma
kiran duniya ya Yusuf bai dagaba, haka ya hakura, ya shirya da daddare domin suje asbitin
shida Ilham, Ilham tazuba musu abinci, sannan tahada wa Nihla wani maganin mata, tatafi mata
dashi, cikin ranta tana cewa gara tafara bawa qawar tata Dan abubuwan nan tanasha, tunda
auren yazo a qurarran lokaci, kuma tasan halin Nihla yanda batason ya Abba yanzu tsaf zataqi

sha, Dan haka gara tana zuwa dashi tana bata tanasha a gabanta

Zuwan su asibitin kenan suka kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login