Showing 24001 words to 27000 words out of 27449 words
k'asan da yarorinta Zarah da Doctor (sunan da ake
kiran Dr Khalid tun yina qarami)
Tunda ta sauka ta ke wurga idanu ko taga zuwan diyanah, har dai ta qare ta tambaya mamansu
Shiru tayi don harga Allah takan manta da watannan halittar
"Sarah waike meye hadinki da yarinyar nan ? Sam kurace batason jama'a ni har mantawa
nikeyi da tsiruwanta"
"Haba dai,anya mama ,er mutane an Barta a sashensu ,tareda watannan makiran"
"Ke saratu banson hadin fituna ,karkizo ki nemi raba masa kan mata kawai kawai,tace maki
suna cutar da ita ne?"
"A'ah shikenan ,bara in kirata"
"Hello Anty"
"Diyanah kina lpy"
"Lpy Nike Anty ina yara "
"Gamu munxo ko kizo kiyi mana oyoyo,barorinki basu Fada maki bane"
Shiru tayi ,ni ina wani naga barori ai duk suna dakin isashiya me cikakken iko
"Kinyi shiru amaryanmu,da Matsala ne?"
"Laa ina tunanine,yanda duk suka watse suka barni ina barci ,Ashe sunzo gurinkune ganinan
qarasowa cikin gidan"
°°°
Tafkeken mayafi ta saka aka Riga da zani na atamfa mai ratsin ja ,super dinkin yayi fitting dinta
hakan ya fiddo matashin cikita na kusan Wata biyar.
Haka ta kullo dakinta ta ringa takawa a hankali tana tafe mayafin na Jan kasa tsabagen
girma,irin na qosassun hajiyoyin nan.
Da sallamarta ta shiga duk suna zaune suna cin abinci a tafkeken darduman tsakar makeken
falon
Aikuwa dagudu Khalid ya taso ya rungumeta "oyoyo antyna ,nayi kewarki"
Ya matso mararta...yamutsa fuska nayi saboda murdan da cikina yayi saboda azaba.
"Washhh" Ta Fada tana cije le6en qasa
Da sauri ta taso "yaya dai amaryanmu?"
Murmishi ta danyi me kamada na yaqe "bakomai" a hankali ta dogare hannunta a qasa kafin
takai kasan ta zauna a hankali ,irin dai zaman masu ciki
Tunda tako zauna maman take kallonta,dagowar da zatayi suka hade ido taga yanda take mata
kallon tausayawa ,tabbas tana kyautata hasashenta akan Diyanah
"Barka da rana hajiya"
"Sannu 'yannan ,meke damunkine Nene?"
"Laa bakomai wallh"
"Hajiya kin rigani maganane,ta dashe da yawa amma tayi fari kamar me shigar ciki,amma yaya
ya sani?"
"Anti bafani da komai"
Saidai bata rufe bakiba taji bul wani abu ya gilma mata a ciki, ranar farko da dan cikinta ya fara
motsi, dafe kwankwasonta ta baya tayi ,tareda rumtse ido da cewa " wash " ta wani yi zillo.
Dariya Sarah ta saki "hajiya mashallh da ya nuna kansa a dangi,lallai diya zurfin cikinki yayi
,hajiya wallahi motsi cikin yayi"
Gaddama ta kafe masu dashi batada komai, aiko Sarah ta tasheta suka tafi asibiti,ai ba'a kaiga
test ba likitan ya kwantar da ita saiga da a daidai wajen cibiyarta .kenan watan ciki hudu da
rabi,s take ya yi scan hakan ne dai ,ga yaro nan yina motsi,lafiyayye dashi...aikuwa tuni labari
ya watsu a dangi diyanah Nada ciki,a gididdiga ranar shigar Ango daki kwanakin ciki. Murna kam kowa keyi,saidai yarima ko a jikinsa bai damuba,itakuwa zulaikha kamar ta mutu
don baqin ciki yanda taga kowa ya koma da diyanah saidai gogan ko a jikinsa tamkar ba shine
mai Neman haihuwarba ruwa a jallo ba
Diyanah a maimakon ta samu farinciki sai qarin zullumi da damuwa ,kuka sin zamar mata jiki
kullum tana cikin yinsa,tayi nadamar wannan qaddararren auren ,tayaya zata kawo yaro gidan
da ubansa bai damu da uwarsa ba bareshi?
Sarah kam da ta fahimci tana cikin damuwa ne ta sameta ta titsiyeta saita Fada mata
damuwarta
Nan ta zayyane mata komai, wato rabonda tasa mijinta a ido tun ranar da ta bar garin bayan
biki
Tsoro abun ya bata "karki cemun bayan first night Baki qara saka yaya a ido ba" jinjina mata kai
tayi fuskarta da da murmushi
"Aiko da damuwa wannan aikin watancan baqar daganne ,kuma ni nan na isheta" ta fice a dakin
tana korafi,batareda tabi takan ,diyanah ba.
Sai kuma can ta dawo mata da turaren bintu Sudan ,madaran tace ta yi maza tai wanka ta
shafa ta samesu a Fadan cikin gida ,kuma in tazo ta tunkari inda yariman yike zaune ta
zauna,sauran bayanin saisun hadu
Kar6a tayi ,sannan tayi abunda tace,daganan ta nufi fadan saiga shegun barorinta na Binta ,a
yau ,bata kulasuba suka rankaya har can
Tana ratsowa ya wani kafeta da ido ,qamshinta tunda ya dokesa yaji Wata muguwar shaawarta
ya bijiro masa ,a take jikinsa ya kama rawa,shi tunani ma yike yaushe ne diyanah tazo gidan?
Sarah lanqwashe kai tayi ta labartawa sarki duk abunda yake faruwa da duk jama'ar gidan,
itakam zulaikha idonta na kan yarima tana lura da halin da ya shiga, don haka ko jin
zanturtukan Sarah batayiba ,saidai tsinkayen salatin mai martaba tayi
"Allahu Akbar,ka bata ajiyar qwanka amma kake cuzguna mata da cikinka,to yau ba sai gobeba
ina umurtanka da ka aikomun da takardan ta ,ni yarinyatace ina kishin inga an wulaqantamun
surukai"
Bakinsa rawa ya fara yi "Ciki fa kace baba? Wai diyanan ne keda ciki?"
Duk maganan da akeyi sarki bai daure raiba sai da yaji tambayarsa ,a take ransa yayi mugun
6aci "kar ka maidamu qananun mutane anan kaji...ciki rashin ciki inajiran takardan sakinta kafin
dare
Kuka ya fashe dashi ya gofana gwuiwiyinsa a qasa.
" ka gafarceni nabi Allah nabika baba ,wallahi ni ban ta6a ganin diyanah a gidan nan ba sai
yau,duk yanda akayi makaru akai mana don a rabamu amma ni inason matata...bazan iya
rabuwa da itaba" kawai saiya tsinke da kuka
Mamaki ya ishi kowa lallai akwai lauje cikin nadi ,hakury aka shiga ba sarki daqyar ya haqura da
sharadin in ya sake zslutar diyanah bai yafeba
Murna kamar mene a wajensa,haka suka rankayo zuwa gidan su ,kobi takan zulaikha baiyiba
Wannan abu ya soketa,don haka tana shiga ta dokawa boka kira,ta labarta masa komai
"Kyalesu yanzunnan zan tura masu d'an babule mai aman wuta" godiya tayi masa ta kashe
wayar.
Cikin farinciki ya tallafota har dakinsa ,komai a sauya ba kamar sanda ta shigo ba kafin biki ya
qara kyau da tsaruwa ,a kan kujera ya ajeta ya zauna yina kallonta duk ta qudindune a mayafi
"Me zan Baki tukwuicin shirin bani qaruwa da zakiyi?".
Murmushi tayi " komai ka bani ina maraba dashi".
"Na Baki soyayya ta"." Ngd ranka ya dade".
Hannunta ya kamo ya manna mata sumba a bayan hannu
Dasakin sumban da murdewan ciikinta da sauri ta duke ta kwalla qara ,bulllll jini ya kece ta
qasanta harda guda guda.
Rud'ewa yayi iya rudewa ,he can't control himself ya kasa aiwatar da komai,sai sakin Baki yayi
yina "aa'aah aaa'aah diyanah karkiyi mun haka plz" bai aune ba saidai ya ganta tana
shivering.... Qwalla qara yayi ya sunkuceta,ya fito harabar gidan da gudu yina ihun kiran
mutane, ga jini na binsu kamar an yanka dan akuya,da kan sa ya sata a back seat driver ya fita
gidan, kwarar idonta ya tale qasan yaga yayi fari ,kawai sai ya hau ihun driver
"Titin bayan babanka ne da kake shafashi a hankali? Wlh in matana ta mutu saina kasheka
kaima" haka yayi ta sumbatu da suke out of mind.
Suna shiga asibitin nurses suka kar6eta da sauri zuwa A&E
Daidai suma su Sarah suma suka qaraso ,fitowa yayi zai bisu da gudu Gaban rigarsa jam6ar da
jini ,da sauri Sarah ta qanqamesa ,ta janyesa
"No yaya ,ba girmanka bane roaming within,with dix nasty looking cloth"
"Oh Ashe?
Saboda bake bace zakiyi loosing mata da hoped baby ba ko?"
A cikin A&E anyi nasaran fitarda retain product din,don suna shiga yaron na fad'owa ,haka akayi
mata wankin ciki suka Samata drip a hannu daya dayan hannun jini.
°°°
Wannan shine ya cigaba da kasancewa da rayuwar diyah a cikin gidan, ta samu lafiya itada miji
Wata sa'in,Wata sa'in kuma kashi ya fita muqami,ta samu ciki amma bai Wata biyu ya
6are,Sarah duk wasu sirrin kundin gidan sarautan da ta sandasu na tsari da dafa'i bankawa
diyanah takeyi ,wannan shi yike sama take samun sassauci da tuni kila ta Dade bata gidan.
A lokacin da tayi 6ari na bakwai yina zubewane ,likitoci sukayi ittifaqin mahaifarta ta samu
matsala da qyar zata iya samun ciki by her capacitation ,kota samu a lokacin cleavage zai zube
kafi n ya shiga mahaifa, saidai ko a hada kwayoyin halittar su a saka mata a mahaifan ta
cigaba da rainonsa shima in aka yi missing chance sau biyu toh bazata ta6a haihuwaba
Hankalin yarima ya tashi, ya kasa fadawa kowa damuwarsa sai Sarah,itakuwa tana tashi taje
har dakin zulaikha ta yi mata kuturun wulakanci ,ta shaida mata haqanta ya cimma ruwa
diyanah bazata iya kar6an cikiba,ita mai duwawun haihuwa saita haifawa yarima,su yanzu ta
lafiyarta sukeji a samu ta rayu.
Bayan ta warkene ,Khalid ya tubure a gidan zai zauna wannan shine karo na biyu a wancan
karon ya zauna hannun zulaikha ta azabtar dashi shine uwarsa ta gaji da kawaici ta d'auke
danta, a wannan karon sai ya sauka a wajen nanne dinsa (tun yina yaro bai iya cewa Anty,sai
nanne) ...Khalid xamansa wajen diyanah ya rage mata radadin kadaici,ta samu saukin damuwa
ta riqesa tamkar danta .
Kwatsam saiga zulaikha da ciki kidifiA wannan karon ansan gidan anyi ciki,haka taringa
shaqan nauyayan kudade da sunan siyayya,ammafa suna account ko tuntun hulan baby bata
siyaba,ciki na girma lalata na qaruwa
Saida ciki yakai Wata shidda kowa ya gama saka rai ta sa jakadiyarta ta nemo mata jinin masu
haihuwa a asibiti ta shashafa wai cikin ya 6are,Ashe karyan ciki tayi don hankulan mutanen
gidan su dawo kanta su so ta ,amma kwarya take sakawa.
A lokacin da zatayi 6arin saida ta tabbatar yarima sun tafi India duba lafiyar diyanah,shine tayi
amfani da damar cewa ciki ya 6are
Shikuwa ta 6angren yarima ya yanke shawaran kai diyanah ne ai mata dashen dan a cikin
,alabarshi ta zauna har sai cikin yayi qwari ta dawo,saboda yina jin kunyarta da irin wuyar da
tasha ace zulaikha tazo ta bashi da safely.
Saida cikin diyanah ya shiga Wata na bakwai sannan suka dawo qasr da tsireren ciki,ba wanda
yasan plan dinsu sai Sarah itama takanje time to time har suka dawo,wannan abu ya caki
zuciyar zulaikha da kuka ta koma wajen boka ya shaida mata yarinyar itace magajiyar wannan
masarautar bazaa iya zubarwa ba.
Dole ta chanja dubara,itace kawo mata jiko Wanda in tasha er zata iya mutuwa,amma tar
diyanah ke kallonta,saidai ta kar6a tayi kamar xata sha taje tayi pushing dinsa a toilet.
Lokacin da cikinta ya shiga Wata Tara ,shine aka wuce kasar Egypt don ta haihu acan kuma a
lokacin ne ,gimbiya zulaikha tayi nufin qaddamar da nufinta na kashe su'adah saidai zakaran da
Allah ya nufa da cara dole yayi,daganan abubuwan da suka faru suka faru
°°°
CIGABAN LABARI
Oum Aphnan✍️
[7/27, 5:31 PM] Bamalli✌️: 81 - 85
*Jinin Sarauta*
Cikeda Murna gimbiya khalesat ta nufi sashenta ,barorinta suna rirriqe mata da rigarta dake
sharan qasa,Dole tayi murnan tafiya don ita dama bamaison zaman waje d'aya bane,gwara ta
bi baba saratu ,tasan zata hadu da er uwanta Zarah ,suyita flexing a can gidansu.
Suna shiga parlour nata ta umurci kuyanga zubaida mai kulada suturunta da ta harhada mata
kaya a madaidaicin Akwatine kurum
Tana wucewa saudah ta taso daga kujeran da take tazo nata kujeran ,tawani dunkule hannu
"Hutawarki lafiya,er sarki jikan sarki " buge bakinta tayi da hannu
"Kam kam kam wallahi saina rama "
Gwale tai mata ta dirko akan kujeran suka fara zagaye kujerun falon
"Wallahi zaki rame anmata", Aikuwa ta suri throw pillow tana Dad'a k'ara qaimi wajen
gudunta....sunyi kewaye na uku ya shigo dakin da gudu taje ruqunqumesa
" wayyo yaya na ka 6oyeni "
Jawota yayi ya fiddota ta gabansa ,itama ya kamo hannun Saudah ,tsugunawa yayi daidai
fuskarsu "Qawa da qawa mun gansu a Rana... Jiki kamar ba yanxun nan kika bada umurni aka
kora mana muguwar mu ba,saigaki kina aikin En yara "
Fincike hannunta Gimbiya khalisah tayi ta rungume Saudah "Hhh to dai na wasa ne,En
baqinciki saidai Ku mutu"
Suka ko kwashe da dariya suka tafa hannuwansu.
Janyo hannunsu yayi yina dariya ya shiga ya zauna a 3seater ya zauna da kowacce a 6ari
6arinsa.
"Princess ynx bin su mommah zakiyi kibar nanne da yayanki?"
"Iyyeh lallai ne,sosai ma gobe ishaallah mun bar garin nan,kamar yanda kaima zaku wuce kaida
aminiyata kowa ya koma ya banni ina fama da kewa "
"In natafi zakiyi kewata khalisah? "
"Sosai ma,ko ynx innadade ban ganka ba ji na nake kamar zanyi kuka...ina sonka yayana"
Tafada tana Dora kanta a kan cinyarsa
Saka hannu yayi yina shafa sumarta A hankali ya furta "Nima ina tsananin son ki er qanwata"
°°°
Rayuwa mai juyi juyi ,yanzu duk hanyoyin da faridah ke samun kudi ya toshe dama alhj bilyane
jigo kuma an tsiyace,ga her excellency ta kirata wai karta qara zuwa mata gida mijinta ya fara
zargin halaqarsu,ga PA Sam ya ma sa masu gadi a daina Barinta ta shigo masa gida ,gidansu
itama kanta bazata iya zuwaba,yanzu ta dogara ga Allah ne ta dogara da aikinta ,don
hakanema ta nema gidan ma'aikata na cikin asibitin ta koma da zama
Sam yanxu iskanci da biye biyen mata da maza sun fice mata a rai,yanzu ita soyayyar su'adha
ne ya dawo mata sabo fil, tun sanda aka tabbatar mata da mahaifarta ta lalace kuma bazata
ta6a haihuwaba ,tayi la'asar ta zama na Allah ,kullum ka ganta da cazbi da hijabi ,sai ko ka
ganta tana kuka ko addu'a Sam duniyar ta fice mata a rai ,kullum tana ganin kukan marasa
iyaye da En uwa in sun mutu a asibiti , tambayar ta shine ita in ta mutu wa zai yi kukan
mutuwarta ?
Kamar kullum yauma Asabar zaune take tun da tayi sallar subahi akan darduman sallanta,kiran
wayarta ne ya katseta ,da kamar bazata daukaba ,ganin ba number qasar nan bane
Sai kuma Wata zuciyar tace dauka fareda kila PA ne ya yafe maki
"Assalamu alaikum" shiru akayi ba a tankaba
Kamar zata kashe sai taji ance "Hello faridat ce kuwa?"
"Eh nice dawa Nike magana ?"
Dariyar ashararanci ya saki"Hhhh mata kenan masu duniya ,wato baki dauki muryanba ko?
Karki damu alhj bilya ne,naji abun Asshan da ya faru dake a bakin qawarki na tausaya
maki,saidai na barkine ki horu ki gane sata bai da riba, amma yanzu tunda naji labarin kin nafa'a
kin rabu da qananun En iskan nan ,to kizo ga ticket din jirginan ki biyo ni Algeria... "
Wasu siraran hawayene suka sirnano mata
"Alhj bilya Nagode da jajenka a gareni ,saidai ina maka kyakyawar albishir ,tun ranar da na Bar
ka ban kuma aikata wani abu da addini da al'adata ya hanani ba,kuma ka sani ina farinciki da
wannan sabuwar rayuwar da Nike ciki a yanzu ,ina fata Allah ya kar6i tubana ,sannan in riski
Allah ina mai imani,so kaima ina gayyatarka da ka shigo motar nadamar da na shiga ko ka
samu rabauta duniya da lahira ,don yanzu dai ka manyanta ya kamata ka fadaku kasan annabi
ya faku"
Wani muguwar dariyar rainin hankali ya saki "Lallai igiyar talauci tagama nadeki tayi maki cik!
Ba laifinki bane ,rashi ya kawo hakan amma still zan Baki dama ,yau zan taso daga Korea zuwa
Algeria ,so daga yau zuwa dare duk abunda kika yanke zaki iya sanar dani,sai ki iskeni a can
Algeria din"
"Hmmm ai shi kyakyawar aiki shine Wanda aka dawwama anayi ba'a fasaba ,shikuwa kauda
aikin sa6o shine kaucema aikatata ,alhj bilya Nagode inamaka fatan shiriya ,kuma tunda ka ta
soni a gaba,to zan karya layin nan ynx ,yanda bazama ka sake samuna ba ,bare kasa tubana
yayi girgid'i"
Kirit ta kashe wayar.
°°°
Bayan sati guda da faruwar Abun
Farida na zaune a falon ta bayan sallr magriba tana laziminta ,tana jiran sallar isha,TV dinta da
ta kamo tashar Aljazeera ne ta sauya zuwa CNN sannan ta rage qarar, ta cigaba da Jan
carbinta in a dimly light room, tun tana lazimin tana tuno rayuwarsu na baya da mijinta da
su'adah har ta fara shesheqar kuka tana add'ar mafita,yau gata kowa ya gujeta ,saboda mugun
halinta da sa6on Allahnta
Kuka sosai takeyi ,a daidainan taga an hasko qonannen jirgin da yayi hatsari a yammacin yau
wanda da ya taso daga Algeria zuwa Nigeria ,kafin aka fara nuno Manyan mutanen da ke cikin
jirgin da suka rigamu gidan gaskiya ciki kuwa harda Hoton alhaji bilya da shahida.
Kuka ta fashe da shi ,kafin ta wuce suuu ta tafi sujudah"Allah Nagode maka ,da ban bisuba ,da
yanzu na sameka cikin hanyar sa6onka ,ko yanzu nagode"
°°°
Gimbiya zulaikha kuwa daga gidan basu ajeta ba sai a bayan gari ,sannan suka juyo, ana fitar
da ita kuwa ,kuka ta fashe dashi ,tanata lisafe lissafen yanda zata samu kudin zuwa wajen
bokanta,don tasan kota koma gidansu raina mata wayo zasuyi gwara taje aimata maganin
kowa,taje ta zauna a gidansu kamar na sati 1 kafin a tunzuro mai martaba yazo ya maidata....to
amma ina zata samu kudin ? Bayan ba'a Barta ta dauki ko tsinke
Zinaren jikinta tagani ,a take murmushi ya su6uce mata ,anan take ta zazzaresu duka ta Tara a
qaramar jakan hannunta ,mai daukeda ATM da sauran tarkacenta dasu keys din sashenta,sai
kudi bai wuce 10k ba,napep ta Tara ta shiga ,kasuwa zaka kaini"
Kallonta yayi ,kallon tsaf ,ya San hajiya ce "To hajiya drop ko?"
Jinjina masa kai tayi
Tunda suka fara tafiya take masa masifa ,musamman in