Showing 24001 words to 27000 words out of 36313 words

Chapter 9 - RANA DAYA BOOK3 COMPLETE

11 Nov 2026

19

sa lokacin Shatima ba ya gida, goma saura ya shigo sasan Salma. Tuni ta cire kayanta tayi sallar isha tare da shirin bacci ya juya ya fita.

Bikin Badiatu ya kusanto, Aliya kuma an shiga watan haihuwa, in tana tafe ta dafe kugu, Salma takan sha dariya domin dai tana ganin masu ciki kala-kala, amma ba ta ga mai gwadare irin na Aliya ba. Ko su Amna dai iyayen son jiki ba ta ga tana irin wannan yatsinar ba. Salma dai ta yi sabbin dinkuna ban da wanda Shatima ya yi musu, kudinta da ta ke dan makalewa ta ba Salma Dankasa ta sai mata ya diddika irin nata masu kyau ta bada aka dinko mata su, sun yi kyau sosai kayan. Salma ta zaci Shatima zai barta tun ana saura sati daya bikin, sai ya daure fuska ya ce, ba ya son shirme. Da kyar da rokon da Badi'atu ta yi ta masa ya barta ana sauran kwana uku biki, cikin kawaye Salma ta saje suka sha lalle ana ta shirye-shirye. Bikinsu uku ya tara mutane sosai, Salma ta yi aron kudi dubu goma gurin Yaya Hadiza da ta kwashi adashe za ta canza gado, Salma ta ce,

"Don Allah ta ara mata ta yi wa Badi'atu gudunmuwa ta kashe kudinta duka ne, amma da zarar an gama bikin za ta tara ta biya ta. Wani saitin agogo ta sai mata mai guda uku dubu goma sha daya. Sun yi kyau sosai kowa ya gani sai ya yaba, Nafisa da Salma dama rana daya suka zo. Amna cewa, ta yi ita sai ranar biki. Aliya kuma shida kansh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ya ce ta bari sai ranar biki. Salma gidan Hajiya Kaka ta sauka gidan Kaka don za ta fi sakewa, can jama'a tayi yawa,Amna gidan Anty Momiyo suke da Badi'atun da kuma kawayenta.

Duk shagulgula tare aka hada da nasu

Hamida kamar kamu, sisters day da sauransu. Dinner ce wadda abokan ango suka shirya ita ce ta

Badi"atun kadai, wadda aka yi ana gobe daurin aure da zasu wuce zuwa Katsina inda mijin Badi'atu yake aiki, domin Costom ne babba.

Amarya ta yi kyau har ta gaji a gurin Dinner,su Salma an sha gayu babu yanda za a yi ka ce tana da miji. Sai faman kashe hotuna suke yi da sauran kawaye da 'yan uwansu Shatima sa'anninta, lokacin da aka zo soma rawa su Salma mazari nan suka shige tare da amarya ana ta rawa,

"yan uwa da abokan arziki suna ta yi wa amarya liki. Kallo sai ya koma sama lokacin da wani ya zo yana yi wa amarya ruwan "yan dubu-dubu. Gurin ya Dauki ihu, Salma ta tsura masa ido cikin mamakin ko wane ne wannan,ga shi ita kadai yake wa likin ban da ango. Da ya gama kuma ta ga ya nufi kujerar da su Anty Momiyo suke zaune, Salma ta taba Aishan Anty Momiyo tace,

*Wai wane ne wannan?"

Aisha ta ce, "Yaran yayansu mamanmu ne. ya so Anty Badi' atu sosai ta ki yarda".

Salma ta ce,

"Shi ma yana da mata?"

Aisha ta ce,

*A'a, ita dai ya so ya aura, ga shi yana da kudi sosai, kasuwanci yake yi komai suna yi irin su shinkafa, taliya da dai sauransu'
8/22/22, 17:00 - Ummi Tandama???i: ??Nd3??_/Q

Page 22


Salma tace

"Kash! Da ma ta yarda ga shi mai kyau. Wannan ko ga shi har da mata da yara biyu"

Aisha ta ce,

"Ai kowa ya ji haushinta bare Hajiya. Babanshi shine babba a dakin su Hajiyan fa,kuma ya rungume su kamar me, komai shi yake musu don shi ma dan kasuwa ne. yana da kudi, da dan ne ya taso sai ya fi uban kudi" Salma ta ce,Allah ya yi wannan ne mijin nata Aisha ta ce,

'Kuma haka ne, Allah ya ba su zaman lafiya Sunanta da ta ji Imran ya kira ne ya sa Salmawaiwayawa da sauri. Imran Kanin Aisha ne, ya ce,Anty Salma wai ki zo Ta ce, 'In ji wa?"Ya ce,

'Ke dai ki zo"

Ta bi shi ta gun su ta fit?? waje. Tana mamaki sosai ko su wane ne? dan Yaya Hadiza da Inna su ne za su zo mata, amma sai gobe gidan daurin aure. Har Kosawa ta yi sukai ta ga ko wanene. mamaki ya kamata ganin Yusuf. Da sauri ta isa gurinsu tana fadin,

"Na shiga uku, wa ya ce ku zonan? Me ya kawo ku?"

Tana yi tana waige-waige. Duk ta firgice.

Ya ce,Kwantar da hankalinki mana, mene ne don na zo miki biki? Salma kawarki ita ce ta bani katin bikin yayarki, Tun yamma muka zo ni ma ina da yan uwa a Kaura, can muka sauka shine na ce bari mu zo Dinner, gobe mu je miki Daurin aure daga nan ma sai ki gabatar da ni"

Salma tace

"Yusuf ka taimake ni., wallahi ni matar aure ce, ina da mijina fa"

Ya ce.Salma sai dai kawai in ba ki sona kawai ki fada min, amma Salma kawarki ta tabbatar min cewa ba ki da wani miji":

Salma ta ce,

"Ai ba ta sani ba ne. to na ji din ma bana sonka, don Allah ka tafi mijina yana nan gurin auren kanwarsa ake yi fa"

Ya ce, "Ni dai ban yarda da zantukanki ba, ki kai ni kawai yanzun gurin danginki".

Abokinsa da suka zo tare kuma ya ce,

In kina jin kunya ko tsoro fada mana gurin wanda zamu, sai mu je da kanmu. In kuma sun fi son ganin magabatanmu sai su zo"

Ganin mutane sun fara fitowa daga dakin taron sai Salma ta yi baya da gudu, jikinta yana bari ta nufi cikin dakin taron. Karo ta ji sun zabga da wani, a rude take fadin,

"Subhanallahi?y

" Domin wanda suka yi karon yana kokarin fitowa ne, yana yin waya. Wayar ta fad?w kasa, cikin sauri ita da shi suka kai hannu da nufin dauka. Salma ta riga shi kai hannu ta dauki wayar kirar Samsug ce wadda ake yayi, karshen tsada a wannan lokacin. Ta juya wayar a hannunta bayan wayar ya yi kwatsa-kwatsa dai shi ma bayan gilashi ne. da sauri ta dago ta kalli mai wayar da nufi ba shi hakuri, sai ta kasa ganin wanda ya yi wa Anty Badi'atu ruwan kudi ne. ga shi ya zuba mata ido yana kallonta, bakinta yana rawa tace

"Don Allah ka yi hakuri. Bai ce Kala ba sai kallon Salma yake yi

Ta mike da sauri ta nufi ciki tana yi tana waiwayenshi, shi yana tsaye yana kallonta mamakin barnar da ta mishi ne yake yi mata irin wann)?n kallon, ko kuwa mene ne dalili? Gurin da su Aisha suke ta nufa, ta ce,Ina mayafin kuma?"

Ta taba kafadarta,

"A'a ina to mayafin?"

Ta soma waige-waige, ta kalli Aishan,

"Bana baki ba? Tace,

"A ina ki ka ba ni??y

Salma ta ce,

"'Tun da za mu yi hoto"

Aisha ta ce,

"Kuma da aka zo kiranki bakin karba ba"

Salma ta ce,

"Allah dai ya sa ban yar ba

Ta soma dube-dube, ba ta ganshi ba ta soma duban inda za ta hango Shatima. Ta kasa tashi daga inda take zaune duk ta tsani taron ta kosa a tashi. Ta mike tare da fadin,

"Bari dai in duba gurin can da na buge ma mutumin nan waya"

Ba ta ga mayafin ba sai su Shatima da ta hango shi da wannan da suka yi karo suna magana a gurin motocinsu,

Muryar Yusuf ta ji yana kiran Salma. Da sauri ta dubi gurin su Shatima don ta tabbatar bai ji kiran sunanta da aka yi ba, kuma cikin sa'a Shatima ya ji kiran tunda tsakaninsu babu nisa, domin ta ga ya kai dubanshi gurin Yusuf din, sai ta yi sauri ta juya cikin addu' ar Allah yasa Shatiman bai ganta ba. Bayan an tashi ta bi ayarin amarya zuwa cikin motoci suka nufi gida ranar dai gidan Anty Momiyo ita ma ta kwana

Tun Karte goman safe suka dawo gidan

Hajiya kaka domin nan za a daura aure, duk amaren ma nan suka hadu. Ana ta wanka da kwalliya.

Salma ta makale ana gama yi wa amare kwalliya ita ma aka rangada mata, suka sha ankon daurin aure ana ta hotuna. Aliya da Amna sai ga su, Salma tace

"Da ma Yaya a daren nan ya koma Kaduna kenan!"

Sai ta ji Aliya tana fada ma Nafisa wai

Mustapha ya je ya dauko su. Salma ta dauki Jafar yaran Amna tare da fadin.

"Zo mu yi hoto"

Ko don ganin mutane ne ya san Amna fadin wannan katon za ki dauka? Salma da ma sau daya ta taba daukarshi lokacin da suka dawo ta je ta yi musu barka. Salma ta amshi wayar Aisha tana yi musu hoto, Aisha ta ce,

"Ke dai don Allah Anty Salma kisa Kawu Shatima ya sai miki waya, wayar kowa cike da hotunanki

Salma ta Ce,

"Kuma don Allah kar ki goge min ko daya anjima duk zan tura su a wayar yaya Aliya ta kalle ta,

"Shi kuma sai ya ba ki wayarsa babba ki masa wasa"

Salma ta Ce,

"Ai ba wasa zan masa ba, in ya hana kuma sai in amshi ta Anty Badi atu in nayi Waya sai ta turo min ko ta whatsapp ne

Su Inna da Hadiza sun zo ta kawo su gurin Kaka suka yi mata murna. Sun ci waina sannan suka bari su je can gurin Hajiya da kuma gidan su Nafisa su yi ma mama murna ita ma.

Bayan an gama daurin aure Shatima ya shigo yana neman daya daga cikin matansa, Amna ya iya samu a waya, ya ce, suna son abinci shi da abokansa.

Ta ce,

"Ni ina zan je nemo abinci?"

Aliya kuma tana Zaune turus tana son gwaninta ga ciki ya yi nauyi, ta ce,

"'Amna ta yi wa Anty Momiyo magana"

Amna tace

"Ni fa gaskiya ban iya surutun abinci ba Salma ta gama saka dayan yadinta, ta yi kyau sosai riga da siket an sha Dauri ta fito kenan

Mustapha ya shigo, ya ce,

"Kai su Anty na an sha kyau. Yaya na son abinci shi da abokansa'

Salma kuwa ta je har dakin abinci ta debo kaloli, tuwo, waina, shinkafa dafa duka da nama da abin sha, tire biyu.

Mustapha ya dau daya, ita ta dauki daya.

Shatima ya amshe ta tareda fadin,

"Sannu Tace

"Yaya ina wayarka?"Ya dube ta,

"Me za ki yi da ita?"

Page 23


Ta ce, Zan tura abina ne daga wayar Aisha ka aje min. bai san dalilin da ya kasa hana taba, illa dai ya ce.

"Kar ki yi min wasa da way??. Tun kafin ta nemo Aishar ta soma daukar sabbin hotuna da wayar ta Shatima ta sake zuwa ta Dauki Jafar suka yi wasu. Aliya ta sha mamaki ganin wayar Shatima a hannun

Salma, ta tura duk hotunan da ta yi a wayoyin jama'a sannan ta je ta kai masa. Lokacin saura su 'uku a cikin dakin da suka ci abinci. Ta mika mishi tare da godiya, sannan tace Yaya ni ma fa zan je kai Anty Badi' atu".

Ya ce,Ina?"

Ta yi shiru don jin yanda ya amsa da karfi.

Munnir yace

"'Katsina mana

Shatima ya hade rai,

*Koma ciki malama babu inda za ki je Za ta yi magana ya ce,

"Bana son jin komai"

Salma jiki babu Karfi ta fita ta koma cikin gida. Dakin Hajiya Kaka ta shige ta takure a bakin

~ gado. Hajiya Kaka da take zaune kan sallaya suna hira da wasu

*yan uwansu ta kalli gadon tare da tambayar wane ne nan ya yi rijib a gado?

Salma cikin damuwa tace

"Nice

Hajiya Kaka tace

"Salamatu ce?'

Salma ta ce. "Ni ce Kaka'

Ta ce.A'a na ga kin saka kaya kin fita yanzu?"

Salma cikin shagwaba ta ce,

*Yaya Shatima ne wai ba zan je raka Anty Badiatu ba, kuma Kaka yadace a ce shi yana babba ya mu hudu matansa ace babu wanda ya je rakiyar Kanwarsa gidan miji?" Kaka tace

*Zance yake yi, dole kuwa a samu mai zuwa a cikinku. Ina Shatima, a kira min shi"Salma ta ce,

"Sal dai in sa a kira shi kar ya ce Karansa na kawo

Hajiya Kaka ta ce,

*Kira min Saude ta sa a yi min magana da shi"

Salma ta fita cikin murna ta bar Hajiya Kaka tana fadawa wadanda suke zaune tare, kirki da hangen nesa irin na Salma.

Tace

"Yarinyar nan ga ta karama amma lissafi gare ta irin na manya, ga ta da kokarin kyauta ga girmama mutane

Saude ta shigo tana fadin,

"Ga ni kaka, ina shiryawa ne za mu kawo amare ki musu fada a kai su
gurin iyayensu a zo a tafi, don Badi' atu tuni Alhaji ke waya su zo tafiya da nisa"

Kaka ta ce,

"To ku kokarta ko a tafi. Yanzu, ban da shirme irin na Shatima a ce ko daya cikin matansa babu mai zuwa?" Anty Saude ta ce Ai ba zai yiwu ba, tunda ita babbar cikinta ya girma ita karamar mu je tare ko kuma Maman Jafar tunda Nafisa babu hali ita wanna ga tsohon ciki' Kaka ta ce,

"Kira min shi an ce yana dakin

%?H?akina Salma tana jiyo muryar Shatima yana gaisawa da mutane a falo ta shige bandakin Hajiya Kaka. Tana jin lokacin da yace

"Kaka ga ni, an ce kina nemana ruwa a jallo Ta ce.

"Zauna dan nan ka fada min in ji ko gaske ne. wai babu wanda zai je a cikin matanka Yace

'Me za su je kuma su yi kaka?"

Tace Ka ji zancen banza, kai ne fa babba a cikin gidanku, matanka hudu amma babu wadda zata raka kanwarta, ai ko dai da ka ji haushi. Babu wadda fa ta je jere cikinsu'

Shatima ya ce,

"To wa za shi cikinsu, Nafisa suma cikin hidima suke, Aliya ta yi nauyi, ita ko Amna ba son shiga jama"a take yi ba'

Salma ta bude Kofar bandakin ta fito daidai lokacin da Kaka ke fadin, "To ai ga Salamatu"

Ya kalli Salma,

"Kin zone kin kawo karata?"

*Yan dakin suka sa baki da cewa,

*Gaskiya matanka ya dace su wakilceka a wanna tafiya' Jin baki ya yi yawa ya ce,

"To shi kenan Kaka su je duk wadda za ta"

Ya dubi Salma, "Ki same ni a dakin baqi

Kaka ta ce,

"Kada in ji ka yi mata fada, ba Kara ta kawo ba"Ya ce,

"Kar ki damu Kaka kudin shan ruwa a hanya zan ba ta Salma ta kalle shi don ta, ya sakar mata harara. A tsorace tabi bayansh, motarshi ya shiga ita ma ta bude ta shiga. Ya rufe ta da fada, ta sunkuyar da kai yana fadin,

"Ke shegen yawo ki kasa a ranki shi ya sa har ki ka kai Karata, ina ta lura da rawar kanki da ki ka kama yanzu. Jiya ina kallonki Salma ta yi saurin dubanshi tare da fadin,

"Mene?'Ya ce,

"Mayafi ma aje shi ki ka yi ki ka kama
yawo haka jiki duk a matse, kina manta cewa kina da aure ma ko?"

Salma ta sauke ajiyar zuciya ta godw ma Allah da ya sa iya rashin mayafin ya gani. Ta girgiza kai tare da fadin,

"Bana mantawa Allah kuwa

Ya ce,

"Kuma tunda kin matsa sai kin je ki je
din, amma ki sani duk wani motsinki zan sani, sannan kuma ko naira ba zan ba ki ba

Ta saki fara'a,

"Babu abin da zan yi ma, babu komai in b?? ka da kudi

Yace, "Ina da shi, ba zan bada babe

Salma ta ce,

"Yaya in har kana ga zuwana din ba ka so Allah a barshi. Da ma dai rashin dacewar aCe mu ba mu je bane kana kai babba shi ya sa har nayi magana Yace

"In kin zauna ma me za ki yi min? kije kawai abinki"Ta ce,

"To na gode, bari inje in shirya"

Har ta fita, yace

"Amsa Dubu biyu ya ba ta, ta sa hannu biyu ta karba,

ta ce, "Na gode

A Katsina gidan amarya ya yi kyau, duk da cewa kowa da barinsa. Ita da kishiyarta amma gida daya suke, irin tarbar da suka samu daga dangin mijin su ne suka saka ran cewa ta karbu gurinsu.

kishiyar ce dai sai dai a ce Allah ya kade fitina,domin kanta tsaye washegari bayan an yi budar uwargidan don a hada su, tace

"Kar ku ce min amana, don ba a bada amanar kishiya

Anty Saude ta ce,

"To, mu dai fatanmu a zauna lafiya, zama na amana"

Ta ce,Idan ta so haka za a zauna

Duk suka sha mamaki, don haka da suka dawo dakin Badi'atu suka yi ta mata nasiha, tare da jaddada mata hakuri. Da za su taho Badi'atu ta sha
kuka, haka ma Salma.

A Zaria kuwa bayan tafiyar'yan kai amaryaKatsina, Shatima ya samu su Aliya ya ce su shirya su koma don gobe zai wuce Abuja. Amna dama a takure take, nan suka koma gidan Hajiyan Shatima don shiryawa. Aliya kuma ta ce, bari ta je gidansu su gaisa tunda ba taje ba. Har ta ce da zai barta zuwa gobe. Yace a' a, su gama komai zuwa bayan magariba. Ya dauki mota ya nufi gidan su Nafisa lokacin motocin daukar amare sun fita da suke nan an kuma kwashi jama' a. Har,zai juya don ya san kila

Page 24


Nafisa tana cikin yan kai amare, sai dai ya ce yasan gidan ya ragu da jama'a bari ya shiga ya yi sallama da su Mama ta sun yi waya. Cikin sa a da ita ya fara cin karo a falo, tace

"A'a Baban Ashrat?'Ya ce,

"Na'am, kin gama shiri ko?

Tace Wane shiri kuma?"

Ya ce To mu je inda babu mutane mu yi magana Nafisa cikin mamaki tace Shigo nan

Ta tura akin su Hamida. Wasu yara ne a ciki, ta ce, "Kuje falo

Ta kakkabe mishi bakin gado tare da fadin, Zauna Ya zauna yana cewa,

"Ina yaran?"Ta ce,

"Ashraf ya makale wa Babata tun da muka zo. Babanmu kuma yana bayan Mama

Shatima ya yi murmushi, "Ai dole ya makale ma takwaransa?Ta dub+s shi, *Ina yini?"Yace Lafiya lau,tunda an kai amare ai biki ya Kare saimu tafi ko, don gaskiya gobe da ke za mu nafisa ta yi yar dariya, "tace gobe fa za,a yi budar kai, ka ga ya dace in tafi?"

Yace an gama budar kai tunda an kai amar+s dakinsu, kuyi musu addu,ar zaman lafiya-kawai"Tace yaya gaskiyal ba zai-yiwu ba, kannai na har biyu na kasa halartar budar kan kansu Ya ce,

"To na ji, zan jira ki goben ki taho da wuri na fada miki Abuja za mu wuce, jibi office

Ta ce,Wai ni Yaya me ya sa ba ka min adalci? Ni kadai ce matarka? Ga Salma ai tana htun ba makaranta take zuwa ba, kuma ga Amna in ma Aliya tana da ciki. Amma ko yaushe sai a kace dani zakaje Abuja, kuma ni anki saka ni makaranta,Fisabilillahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login