Showing 30001 words to 33000 words out of 36313 words

Chapter 11 - RANA DAYA BOOK3 COMPLETE

11 Nov 2026

9

wani Kanin su Alhaji da ya rasu, ubansu daya, Aminu.

Shatima ya bada duk abin da ya san zai bada duk da za su zo suna shi da Nafisa, ita ma Hajiya tayi kayan barka kamar yanda ta yi ma sauran.

Salma ta yi nasarar zama daya daga cikin daliban da suka samu gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, Shatima ya yi tsayin daka don ganin Salma ta zama daga cikin sahun farko na daliban da za su fara karatu. Ta so ya barta ta zauna Zaria ya c?, ya yarda kullum a kai ta a dawo da ita.

Ya ce, nan gaba in ta yi hankali sai ya koya mata mota take zuwa da kanta. Hakan ya Kara kunna Nafisa ta bijir? da zancen nata karatun a karshe dai ta yarda ya sa ta makarantar koyon dinkin da ta je ta ga irin aikin da suke yi.

Safwan yana karya kwanar ya ce a ranshi,

Wannan ai layin su Anty Momiyo ne"

"Yana gangarawa sai ko ga gidan. Ya kalli gidan da murmushi, a fili ya ce, "Bari in dawo Anty zan shiga mu gaisa Kiran abokinshi ya sake shigowa, ya ce,Na shigo layin yanzun, ai na san layin, domin layin su Antyna ne, ga ma gidansu nan%???. kai wane gidan ne naka din?"Ya ce,

"Nine na karshe a layin, don layin baya fita"Safwan yace

"Fito waje to".Nan kuwa ya samu abokin nashi, aure abokin ya yi lokacin Safwan yana Chaina shine ya zo ganin amarya.

Sun shiga ya ganta sun gaisa, ya dai sha ruwan da aka kawo, amma bai ci kayan garar ba, ya, yi wa amarya alheri ya taso. A gurin motar da abokin ya raka shi, ya ce, "Ga gidan Antyna can, zan shiga mu gaisa

Abokin ya ce,To bari na je mu gaisa tunda makota muke"Bai shiga da motar ba a waje ya aje, suka kwankwasa. Aisha ce ta zo ta bude, cike da murna tace,

'"'Oyoyo Yaya Safwan"Ya ce,

"'Anty tana ciki?"Ta ce,

"Ku shigo Ta shiga tana kiran,

*Mama ki fito ga Yaya Safwan"

Sun zauna a falo Anty Momiyo ta fito daga kicin tana fadin, ??Batan hanya ka yi ko Safwan"?"Ya yi

*yar dariya, "Anty dai ba ni da ta cewa, don ba zan tuna rana ta karshe da na z0 gidan nan ba

'Ta ce,Yau ma na san ba na musamman kazo ba Ya dubi abokin, *Ga wanda ya jawo ni,abokina ne ya yi aure ya tare a layin nan, ba na kasar aka yi bikin shine na zo ganin amarya, yana min kwatance ina shigowa sai naga layinku Ta ce, "Ko da na ji, na san dai kazo ziyara. musamman da wahala Ta dubi abokin,Allah ya sanya alkhairi. Ko shine aka yi wancan satin yara sun ce an kawo amarya?"Ya ce, "Shine kuwa, amin na gode"

Aisha ta aje musu abinci da ruwa, Safwan yace, 'Dauki abincin n?vn, yanzu za mu tafi",.

Suna cikin hira wayar Aisha ta yi ringin,wayar tana kusa da Safwan ya dauko tare da fadin,Wayar wane ne?"

Sai kira??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n ya yanke Yana kallon wayar gabanshi ya fadi, hoton Aisha ne da yarinyar da yake ta nema. Ya sake kallon fuskar wayar tare da fadin,

"Wannan wayar ta wane ne?"Aisha ta ce, "Tawa ce

Ya shiga gurin hotunan yana kallo. Ya bude tashi wayar ya tura hotunan Salma, sannan ya mika mata wayarta. Ya kalli Anty Momiyo,

'"'Anty bari mu tafi Ta ce, "Da wuri haka?"Yace;

"Zan zo na musamman

Ya. kalli Aisha, "Bari in ba kuna siyan kati". Ya ciro yan dubu-dubu ya mika mata, sannan ya mike, Anty tana taya ta godiya.

Suna fita ya sauke abokinshi, sannan ya dauki hanya. Sai da ya yi nisa sannan ya tsaya ya ciro wayarsa ya fiddo hotunan da ya tura na Salma, ya tsura musu ido. Tunda ya rasa Badi'atu sai wannan karon ne ya sake ganin yarinyar da yake matukar so, ya yi kwatancen duniya wa Mustapha bai gane yarinyar da yake nufi ba. Haka dai ya yi ta neman wanda zai taya shi gano yarinyar ya rasa har mahaifiyarshi ya yinwa zancen yarinyar, da kuma kwatancenta amma ba a gane ba. Cikin murna ya ce,

"Yau ga ta na ganta a sama, wa zan tambaya ne labarin yarinyar nan? Ina ganin bari dai in kira Anty


Momiyo Sai kuma ya fasa ya tada mota ya nufi hanyar gidanshi, zai bi a hankali har ya gano ta. Sa'ida Kanwar Safwan tana kallon hotunan da ya ce ta duba na wasu takalma da ya yi Oder , yace ta zabi kala biyu. Ta ci karo da hotunan su Aisha, tace

Yaya Satwan ina ka samu hoton Aisha da matar Yaya Shatima?" Da sauri ya ce, "Me kika ce Sa'ida?"Tanuna mishi tare da cewa,

"Wannan hotunan da bikin Anty Badi'atu ne Ya ce, "Ki ka ce wace ce dayar?"

Tace

"Salma ce fa matar Yaya Shatima,

amaryarshi"Ya amshi wayar, "Ita ce wannan?"

"Eh Ita ce"Safwan ya fasa shiga bandakin da zai shiga, ya zauna bakin kujera yana kallon Sa'ida. Ya sake kallon hoton Salma zuciyarsa ta ce, Sa'idar da ba ta shiga cikin jama a ina ta santa?

Ya dube ta, "Ke da ba ki shiga mutane, ina ki ka santa?"Ta yi dariya, "Allah yaya ita ce, sau nawa ina ganinta a gidan Hajiya?"

Ya ce,To je ki, wanka ma zan yi"Ta ce,

"Yaya ban zabi takalmin ba Na turo ta wayarki ki zaba, yanzu sauri nike yi"Ta Ce,

??Yaya kai din fa sabga ta yi maka
yawa, kafin ka samu damar turo min.

Ya ce, "Ki je dai".

Page 28

Wankan da bai yi ba kenan ya dauki makullin mota ya fita, dole ya tabbatar da wannan zancen. Ya kalli agogon hannunsa, karfe nawa yanzu Biyu da rabi, yace

-Ina da lokaci"

Layin Shatima ya kira, "Kana gari kuwa?" Ya tambaya bayan sun gaisa.

Shatima ya ce, "Karfe uku dai zan taso zuwa Kaduna yace Dama gorin da ka ke min ne zan wanke laifina Bros"

Shatima yace Ni fa da na ga kiranka sai da na yi mamaki, har na yi zaton ko wani ka je kira wayar ta danno sunana'

Tare suka sa dariya, ya ce,

"Da yanzun na so da zuwa, amma bari na jira in shigo gobe"

Safwan dai ranar bai samu barci ba, yana ta tufka da warwara. Bai san ya zai yi ba in har ta tabba matar Shatima ce. Salma ta kalli Shatima, Yaya ina zan samu caf? a nan unguwar ne?"

Ya ce.Me za ki yi a gurin? Ta ce,

"Akwai wasu takardu da za mu yi kwafinsu, sannan akwai wasu tambayoyi da zan duba a yanar gizo

Na so siyan miki waya yau, abubuwa ne suna da yawa. Amma bari mu ga zuwa gobe" Wayar Shatima ta sake yin ruri, ya kalla,

"Safwan ka iso?' Yace

"Ga ni a gate"

Shatima ya mike, "Koma tukunna in Safwan zai fita ma hada hanya sai in kai ki

Shatima ya fita suka shigo da Salwan, dakin Amna ya kai shi da ma ranar ya hana ta fita, ya ce tunda zai yi bako daga Zaria, Aliya batq nan, Nafisa tana Abuja. Salma tana kwashe shanya ta hangi bakon a fili ta ce, Wannan ai wanda na fasa ma waya ne

Ta dan makale har suka shige zuwa gurin Amna, Shatima da Safwan suka gaisa, sannan suka soma hira. Amna ta zo suka gaiva, Shatima ya bi ta daki, ya ce ta kawo masa abinci mana. Ta ce, bari tasa masu aiki su kai.

Ya ce, "A'a bari". Ya kira Salma

Tamkar kada ta fito, amma ba ta da damar gaddama. Ta saka mayafi sannan ta nufi dakin. Ta rusuna ta gaida shi, ya amsa jiki babu kwari, domin gaskiya ya kamu da tsananin son Salma. Shatima ya dube ta,

"Shiga kicin ki kawo masa abinci

Salma ta nufi kicin, Safwan ya bi ta da kallo.

Sai da ta bace, sannan ya maido kanshi ga Shatima, wanda shi kuma yake kallon Safwan din. Ya ce, Wai wannan ma matarka ce?"Shatima ya yi dan murmushi,

"Ita Ce karamarsu Safwan yace

"Sauran ba su nan kenan?" Shatima yace

Daya tana Abuja, daya ta haihu tana Zaria

Salwan yace Kana KoKari, na yi zaton kafin shekara biyu za su tsular da kai da matsalolinsu, sai naga har yanzu kana nan a gayenka Suka sa dariya, Shatima ya mike don kunna talabijin, lokacin Salma ta fito da tiren abinci ta aje.

Taje ta tur?? teburin da ake dora abinci in ba a bukatar hawa teburin. Ta Dora masa a kai, sannan ta koma kawo abin sha.

"Amna ta fito tana cewa Shatima,

Jafar bari in Dauko shi a islamiyya.

Shatima yace

"Kada ki jima Tace

*Yanzu zan dawo Salma tana gama jerawa za ta fita, Shatima yaCe Wai ke da Allah yaushe za ki daina tsoron mutane? Dawo to in gabatar miki da shi, ba bako bane, dan gida ne, zumunci ne ba shi da shi. Kinsan

"gidan Alhajin G.R.A?

Ta ce, "Ba mun jeba, gidan su Sa' ida ko?"

Shatima ya ce, Yauwa, to shine babban yayan su Sa"ida. Da babanshi da Hajiyarmu uwarsu daya ubansu daya, shine babbansu Shatima ya kalli Salwan,

"Don Allah ka yi aure

Ya kalli Salma wadda ta zuba ma talabijin ido.

Shatima ya ce Kin ganshi tare aka yi goyonmu, amma ina da yara hudu shi har yanzun ya ki aure' Salma ta kalli Satwan suka hada ido, gabanta ya fad?w, tayi saurin dauke kai saboda wani irin kallo da ta ga ya yi mata.

Muryar Safwan ta ji yana cewa. "Lokacina ne baiyi ba. kuma mu ture batun wasa bana sa'a ne akwai masu sona da yawa, amma na lura suna son abin hannuna ne. Su kuma wadanda nike son sai a samu matsala Shatima yace

"Ban da Badi'atu wa ka so?'

Safwan ya tsiyaya ruwa a kofi ido ya kurba,

"Yanzu haka akwai wadda nike tsananin so, amma ina zaton ita ma na makaro Shatima ya dube shi, "A ina take?

Safwan yace

"A nan Salma ta kalle shi da sauri, daidai lokacin da Shatima ya ke cewa, "Nan Kaduna?"

Safwan ya ce, "Eh"

Shatima yace Yar gidan waye?"Safwa- ya girgiza kai,

"Ban san mahaifinta ba" Salma ta dubi Shatima a sanyaye ta ce,

"Yaya wayarka tana ringin tun dazu.

Ya mike ya nufi cikin dakin Amna, tare da fadin,Ina jin ringin din tun dazu. Ki zuba mana abincin Salma ta mike ta nufi gaban teburin ta tsuguna tana zuba musu dafa-dukan taliya da dankalin turawa. Safwan ya ce, "Na zone ki biya ni wayata Ta zaro ido,

"Don Allah kada ka fada ma yaya

"To fada min lambar wayarki"

-Ya dauko wayarshi yana dannawa, kanta na Kasa ta ce! "Ba ni da waya

Ta mike da sauri cikin mamaki ta koma kan kujera, me kuma zai yi da lambarta?

' Shatima ya dawo ya zauna tare da fadin,

".Ashraf ne wai ya matsa wa Mamansa sai ta kira masa ni Safwan ya ce, "Mu ma dai bari mu zo mu aje yaran nan Salma ta kalli Shatima, Yaya zanJe islamiyya

Yace

"To ki je in mun fita da wuri zan sai miki wayar*

'Ta ce, "Caf? din kuma fa?"

Shatima ya dan yi shiru, yana son ya ga ya ya ma zai mata, Safwan ya katse masa tunani da cewa,Ba ka da computer a gida?"Yace,

"Ta amfanina dai akwai, amma ai ba zan bata ta bata ba, ko ta goge min abubuwa Safwan ya yi yar dariya,

"Sai ka ce wata mara wayo, ko kuma wadda ba ta san computer din ba?"

Page 29

Shatima yace,

Yarinyar da ba ta taba rike babbar waya ba bare computer?"

Safwan yace Wannan duk laifinka ne, in mun fita yanzun muje a sai mata waya da laptop Shatima yace

-To kin ji".Salma ta ce,Na gode"

Shatima ya ce,Ki masa dai godiya, shi zai sai miki Salma ta cube shi, "Yaya na gode sosai Safwan yace Kar ki wani damu"

' Salma ta yi murna sosai da ganin wayarta dankareriya da laptop, Shatima ya ce,

"Ko dai in miki canji ne don wannan laptop din ta fi tawa kyau da tsada Salma tace To ka dauka mana"

Yace Wasa nike, ga shi ya kashe mik kudi duka fa kin ga rasist din

Ya bude ledar wayar ya ciro su duka biyun.dubu dari shidda da talatin. Salma ta zaro ido tana kallon Shatima;

*Yaya ya aka yi ka bari har ya kashe irin wanna kudin?"

Yace Gurin Safwan wannan karamin kudi

Ne Ta ce,

"To na gode, don Allah Yaya ka yi masa godiya".Ya ce,

"Bari in kira miki shi ki masa, ni tuni na yi masa-godiya

Safwan ya daya wayar Shatima tare da fadin,

"Na yi nisa, amma ban kai gida ba

Yaa ce, "Na kawo sako tace nayi maka godiya. Ya ce, "Haba babu damuwa

Salma ta amsa tayi sallama, ya amsa tare da cewa, " Sun yi miki ko? Tace

"Sosai ma, na gode sosai Yaya, Allah ya kara arziki" Yace

"Zan iya yi miki komai Salma, a cikin ledar laptop din nan za ki ga sakona, sai na ji kiranki"Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Salma ta kalli Shatima sai tana ganin kamar ya ji abin da Safwan din ya fada.

Ya ce, "Mu je duk ki hada su

Ta saka layinta a waya, randadau gwanin shi'awa, Shatima ya ciro laptop din yana kunnawa. Salma ta duba cikin ledar katin Safwan din ta gani,ta dubi Shatima, hankalinsa yana kan laptop din dayake dubawa. Ta dubi katin an rubuta, Safwan EL Nasir, ga lambobinshi nan. Ta juya bayan katin ya rubuta, "Ina jiran kiranki Salma ta yi saurin maida katin tare da tambayar kanta abin da Safwan yake nufi. Sai ta ji duk ta tsani wannan kayan, tana fa da aure ya sani, to ita abin duniya ba zai rude ta ba. Shatima yana nuna mata yanda Za ta sarrafa computer, amma yaga duk ranta a jagule ya ce,

"Ya ya ba kya murna ne?"Tace Ina murna mana, kaina ne ya kama ciwo

Yace To bari na aje gobe na nuna miki"

Ta ce,To

". Yana fita ta shiga tunani. "Bari dai kada ta yanke masa hukunci har sai in ya bayyana nufinsa, kuma babu damar ta dada ma Shatima don ba za ta zama sanadin lalacewar zumuncinsu ba.Har sati ya zagayo ba ta kira ba, kuma bata da niyya, illa dai ta yi wa katin boyo na gaske. Salma

Dankasa an shiga KASU university ta Kaduna. Ita dai English take karantawa, sabanin Salma da ke karantar Mass Communication. Burin Salma jarida, amma in ba ta samu ba komai ta samu za ta yi, sai gashi ta samu tana ganin za ta iya cinma burinta. Tana girki ta jiyo kukan wayarta, tana zuwa ta ga bakuwar lamba. Ta dan yi shiru tana son tuna ko ta taba ganin lambar, kiran yana daf da tsinkewa ta daga da sauri, yar siririyar murya ta ji an ce, "Salma?"kafin mu yi nisa wacece don Allah?"

Ta ce, "Ni ce Sa'ida daga G.R.A"

Salma tace

"Ah Sa'ida abin mamaki, ina ki ka samu lambata?"Ta ce,

"A gurin wata yarinya Saddika S. Tata

Tace min department dinku ta ke"

Salma ta ce,

"Na santa, muna shiri sosai, S.

Tata yar G.R.A ce ita ma?"

Sa'ida ta ce,

"Nima ai nan nike, amma ni Hausa nike karantawa Salma ta ce,

"Wuuu a languges ki ke, sannu fa da kokari, kuna shanta Sa'ida ta ce, '

"Kuma da yake ina son Hausar bana ganin wuyarta Salma ta ce,

"Haka ne"

Suka dan yi hira, sannan suka yi sallama da alkawarin sai sun hadu a makaranta, ta yi kamar tace ta gaida mata Safwan, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan.

Aliya an yi arba"in an dawo, kuma an koma bakin aiki. Sai dai ita ma ta sa Shatima ya daukar mata mai aiki, dawainiyar gidan Shatima ta yi yawa har ta sa albashinsa yana neman ya gagari rike gidan.

Ko da ya yi batun da Aliya, sai ta ce, to tunda haka ne kawai ya rage abin da yake kashe musu. Ya yi batun da Nafisa don so yake ya ji ta bakin kowa. Sai ta ce, tunda Aliya tana aiki ta dauki nauyin wani abin nata, ni ma tunda na fara yin kayan yaran nan da zannuwan gado kuma suna tafiya a Zaria sai na rage maka wani nauyin. Amna ma haka, ita ko Salma saita dakata da karatu

Ya samu Amna da zancen, ta ce,

"Ni dama ban dora maka nauyina dari bisa dari ba, don haka wannan ba zancena ba ne"

Kamar kada ya yi batun da Salma, don yana ganin har yanzdqn ba wai tana da hankali bane. sai Kuma ya ga ya dace ya ba ta hakkinta ita ma. Tana karatunta ya shigo har uwar dakinta, ba za ta tuna rana

Ta karshe da Shatima ya shigo dakin baccinta ba. Har a ranta tana cewa, in dai har Yaya hakkinshi ya kawo shi dakina, to yau kuwa zan sauke wa kaina nauyi Ya zauna bakin gado, "Kina karatu ne?" Tace

"Eh Yaya, ya gajiyar hanya? Ina su Ashraf?"Ya ce,

"Suna lafiya. Salma' ina son za mu yi magana, amma ban sani ba ko za ki fahimta?"

Ta ce,Yaya mai zai hana ni fahimta in dai Ka fahimtar da ni?"

Ya yi dan murmushi tare da fadin, "Haka ne.wato Salma abin da ke faruwa dawainiyar yau da kullum din nan ne yanzu haka bana iya samun rara a cikin asusuna wannan watan har sai da mai kayan abinci ya bi ni bashi fa" Salma ta ce,"To yaya a rage abubuwa Kamar me?"TaCe,

"Farko ni maimakon direba ana biyanshi a wata, kullum dubu daya zai isa in je makaranta in dawo nawa ne Zaria? Dari uku ne, ko Ka koya min kamar yanda ka ce, ka ga an samu sauki. Nama da sauran abin da bai zama dole ba sai a rago, sannan da za ka yarda Yaya ka hada da

Page 30

Kasuwanci mana. Na tabbata in ka samu irin su Yaya Safwan zai ba ka shawara tunda shi din dan kasuwa ne

Shatima ya zuba ma Salma ido, zancen kasuwancin ya ratsa shi. Ya ce,

"Amma ke ba kya ganin kasuwa sai da jari?"

Ta ce, Wannan ko su Hajiya da Alhaji za su Iya juya maka Ya ce,

"Kice gobe in tafi Zaria kenan. ZanJe inyi shawara da su Hajiya Salma da Sa'ida da kuma Saddika S. Tata suna tafe zuwa gurin motar Sa'ida, duk suka jingina jikin motar hirar dai ta karatu ce. Salma ta ce,

"Jikina ni har ya soma sabawa da suntirin Kaduna zuwa Zaria din nan kullum, ga shi duk na rame Saddika ta ce,

"Humm, ai karatu fa babu sauki"

Sa'ida tace

"Bari in tafi dama na zo na duba kune Har ta shiga mota, ta ce,Au? Na manta,

Salma Yaya Safwan ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login