Showing 6001 words to 6574 words out of 6574 words
yace "aa Bashir miye haka, sakeshi nace. Yafaɗa akame. "Affuwan Yaa Sheikh, yafaɗa tareda sakin yaa khamal ɗin. "Miyafaru ne kataremin hanya bawan Allah? Yatambaya cikin kamala. "Cikin rawar murya yaa khamal yace "yaa Sheikh kadubi girman Allah dazatinsa, kayiwa soyayyar fiyayyen halitta kaceci rayuwar ƙanwata dan Allah doctor. Ai wani irin runtse ido Sheikh yayi da ƙarfi yanajin yadda zuciyarshi ke lugude, domin khamal yaɗaureshi da jijiyoyin jikinshi. Kafin yayi wani dogon motsi yaga nasir abdul, mudassir sameen, mufeeda, balkusa, abida, duk sun zube agabanshi suna ruƙonshi suna kuka. Ai cikin tashin hankali yace "innalillahi wani'inna ilaihirajiun. Pls kutashi dan Allah, yafaɗa kamar zeyi kuka, aiko cikin sauri duk suka miƙe sedai dukkansu hawaye sukeyi. Ajiyar zuciya ya ɗauke kafin yace "kun haɗani da Allah akan abinda idan nayishi saɓawane agunshi, kun haɗani da Allah akan abinda bazan iyaba, sedai banida zaɓi akan wannan lamari domin duk wanda yace Allah yagama zance, sedai inaso kusani bazan iya taɓa wannan yarinyar ba domin ita ɗin ba muharramata bace, banida muhurin taɓata har agurin Allah, sedai zan Nemo wadda zata dubata yanzu in sha Allah dan Allah ku kwantar da hankalinku... dukkansu shiru sukayi jin yana kan ra'ayinshi, shiko abba tunanin dayakeyi daban, cikin dattako ya kalli Sheikh Faisal yace "haƙiƙa kafimu gaskiya Sheikh domin duk wanda yasan dokokin Allah baze yadda yatakasuba se wanda shedan keyiwa huɗuba, sabida hakan nake roƙar wata alfarma awurinka, kuma Allah zakayiwa baniba domin kaceto rayuwar Ayatullah, dan Allah ka auri Ayat ayanzu idan ka amince wlh zan ɗaura muku aure...ai wani irin waro ido Sheikh yayi gabanshi na tsananta faɗuwa cikin tashin hankali yake kallon abba da tsananin mamaki. Shiko Abba bedamuba yacigaba cewa " kaga tazama muharramarka seka dubata, idan Allah yabata lafiya seka sahale mata amma dan Allah kayimin wannan alfarmar kaceci rayuwarta dan Allah. Yaƙarasa zance yana haɗe hannayenshi wuri ɗaya. Aiko duk su yaa Abdul duka dasu baba, su Dr yaƙub duk sukayi na'am dakalaman abba, suna cewa "wannan gaskiya ne idan akayi haka ansamu mafita in sha Allah. Kafin yayi wata maganar sega Dr salis yafito dagudu yana faɗar "pls Yaa Sheikh help, waccan yarinyar jini take zubarwar sosai sabida allurar da doctor Musa yayi mata dan Allah mizamuyi akai? Ƙarjininta ya ƙare. Ihu ƴanmatan suka ɗauka da kuka lokaci ɗaya, su kuma mazan suna kiran Allah. Ido Sheikh ya runtse da ƙarfi kafin ya kalli ɗaya daga cikin excort ɗinshi yace "bani ɗaya cer key dake hannunka. Babu musu yamiƙamai, miƙawa abba yayi cikin kamewarshi yace "ga sadakinta idan yayi muku banada kuɗi ne ajikina yanzu, idan kuma zaku jira na ɗauko kuɗin semuje a ɗauko, yafaɗa cikin kamewa. "Yayi yayi wlh kuma munbaka kawai a ɗaura, duk suka faɗa atare, anan cikin doguwar barandar duk suka tsugunna aka ɗaura auren Ayatullah da Sheikh Faisal, inda family ta da excort ɗinshi, harda su doctor yaƙub suka zama shedu, cikin ƙanƙanen lokaci aka ɗaura auren da babu shiri balle tsammani, ana shafa fatiha yamiƙe cikin kamalarshi yanufi room ɗin da aka ajiyeta, sukuwa ajiyar zuciya suka shiga saukewa suna fatar Allah yabata lafiya.....!
END
Free page yaƙare 🙏
Duk wadda ke buƙatar wannan cigaban wannan book zata iya biyan kuɗinta.
AHALIN HARIJAI Paid book ne kibiya kuɗinki abaki, 1k kacal 👌
9112799371 moneypiont sha'awanatu kasim,ƴan Niger na zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉+2347037092176 My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 07037092176 on WhatsApp 🙏
Autar alheri✍️