Showing 1 words to 3000 words out of 7525 words

Chapter 1 - DIJEN ƘAUYE COMPLETE

Unknown   

29 Aug 2026

3

*DIJEN ƘAUYE.*

🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕

*True Life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

*Wannan page din Nakine kyauta Sukutum nabaki shi babbar masoyiyar Dijen kauye

wanda take matuqar kokarin yin sharhinta akai dabada gudummawa tare da tayani posting ina godiya Nafi Nijar* Alherin Allah yakai miki har Nijar

👍🏼💘



👍🏼👏🏻

PG 105-110

Kwanakin da dady yadebar musu na shagalin biki da komawarsu gida yanata ta

fiya har saura kwana takwas amma dijen bata yi wani shiri ba domin har ranta bata son takoma gidan Abdallah tafi son zaman gidan dady tanajin dadin yanda momy ta maidata "yar lelenta tamkar "yar cikinta abinda zataiwa mubina shitake mata don har magungunan

matan datasaka aka kawowa mubina da tsimi itama dijen ta bata abu daya zuwa biyu ke sakata fargaba yanda inta tuno zata rabu da kawarta masoyiyarta mubina wacce zaman Aure zaikaita har garin bauchi zatayi mata nisa batason ta tuna sbd sun shaqu matuqa ba

xata taba mantawa da mubina ba domin itama ta taka rawar gani wajen ganin rayuwarta tayi kyau da haske tabar jahilci da duhu tashiga haske don har malamin islamiyyarsu mubina ke xuwa gida yana biya maa karatun qur,ani da hadisai tana godewa Allah daya nufe

ta da zama abirni tunda gashi *TA TASHI DAGA DIJEN KAUYE TADAWO DIJEN BIRNI*

tasan da cewa ma Abdulhakim shine silar faruwar komai daya hada auranta da Abdallah taji aranta hakan dayayi mata yakyauta tunda gashi tasamu ci gaba arayuwarta ta dalilin haka

n da Abdul din yai mata da tuni yanzun tanacan kauye ckn jahilci da duhun kai tunda batayi arabi ba balle boko sai a birnin

Dije tana zaune akan sallayarta ranar juma,a bayan ansauko daga masallaci tana tilawar karatu Ni,ima tana can kwance akan katif

a tana bacci saijin shigowar Abdulhakim taji yafado dakin nasu da sallama

Ta dubeshi duba na tsanaki yayi kyau fiye da kullum yasha farar shadda tazarce kansa dauke da hula tagaidashi ya amsa ckn xolaya tace dashi

'"Su ango ansha kamshi kamar andaur

a aurenma saikamshi da kyallin angwanci kakeyi.

Yayi murmushi yace "hhhmmm khadija knn kema ai amaryar ce kyallin kkyi kamar yadda nakeyi ai.

Takama baki tace "Ni!

🤔

waceni me ido ba dan ciki ba wani kyalli danakeyi

Yazauna akan stool din gado

yadubi Ni,ima yace "wannan bacci takeyine?

Dije tace "eh,tasamu yin bacci yanzun nan

"To ya jikin nata amma da sauki ko?

" da sauki sosai tana tfy ita kadai ma saidai tana dingisa kafar kuma bata dadewa tana tafiyar sbd gajiya take da wuri saita

huta takeci gaba.

Ya gyada kansa yana fadin "to da haka da haka dai saukin zaizo gaba daya Allah dai yakiyaye gaba yabata lfyr baki daya.

Tace "Amin.

Yace mata "ya banga madam dina ba tana ina?

Tagane mubina yake nufi saitayi dariya tace "tayi

tafiya au bata gaya makaba knn?

Yasan zolayarsa take saiya basar yace "ok,ok ta fada amma ai tare mukaje muka dawo dan haka yanzu dai ina tashiga inje in lalubo kayana.?

Ta kyalkyale da dariya wato bai shigaba knn dataso ta shigar dashi

Ta kark

ata kai tace "dazu suka fita da kawayenta rabon invitation.

Ya gyada kai yana fadin "to ke kuma wane shiri kikeyi don komawa gidan mijinki tunda dai kinji abinda dady yace kuma har an gama muku gyara yau saura 8 days.

Ta hade rai harda raurau da ido

ta narke masa zatayi kuka

"Nidai walh bana so inkoma gidan mugun nan walh tunda yakai hannu yadakeni nakara tsanarsa dan Allah katayani baiwa dady hkr yataimaka mini yaraba Auran nan nagaji da xama dashi.,...tafara kuka

Yaga abun nata da gaskene yah

au bata hkr yana rarrashi "kinga yi shiru abin baikai hakaba share hawayenki ingaya mk yanda za.a yi kurabu ckn sauki.

Ckn sauri tahau goge hawayen danta yarda abinda xai rabasu zai fada.

"Kinaji ko banaso kowa yasan irin tsanar da kikayi masa kinga

daga dady har momy baxasuji dadiba tunda suna sonki kuma dan sune me zaisa baxakibi abin asannu ba tunda kinga yanzun shi yadaina tsanarki yana sonki kinga inkin koma saikiyi tayi masa wayo kina dabara yakamu dayawa asonki ta yanda komai kikace yayi zaiyi

mk babu musu.

Da sauri tana fara.a tace "da gaske ?koda nace yasakenine zai saka inna ce masa??

Yagyada kai da murmushinsa yace "kwarraiii ma kuwa

Nan tahau murna tana fadin "aiko dai yaya Abdulhakim kakawo dabara walh haka za.ayi.

Yaji dadi

har ckn ransa daya kawo dabara sbd yanajinta tamkar kanwarsa dasuke uwa daya uba daya tun ada shiyasa ma baya son su rabu don bayaso takoma kauye ayanzu khadija tayi kyau tayi haduwar da dole inta shiga cikin yan kauyensu abanbanceta don tayi freash tacik

a ta goge tazama khadijan birni.

Da wannan dabarar suka rabu

Yana futa Ni,ima datayi shiru tanajinsu ta tashi zaune ahankali takalli dije tace mata "khadija sannu da kokari.

Ashe dama tun asali ba son Abdallah kikieyiba amma kika iya zama dashi

lallai na jinjina mk kinzama jaruma yakamata ace anbaki lambar girmamawa dan haka ayanzu nima zanbaki shawarata daki kama mijinki tunda hankalinsa yajuyo kanki kisoshi kamar yadda yake sonki domin kici ribar rayuwarki kada kibari kurabu domin zamanki a bir

ni shine yafi dacewa dake ba zaman kauye ba dan Allah kiyi tunani.

Dije da tayi sakato tanajinta ta kakalo murmushi tace "naji batunki na dauka yar,uwa tosaidai ke kuma awane matsayi kk agunsa ?kinga inhar na amince mas to ke kuma fa ?yazakiyi da son da

kk masa kinsan dai baxan juri inga ya wulakantakiba gara kawai komun koma innemi hanyar rabuwarmu dashi yazauna dake ke kkfi dacewa dashi kina sonshi tsakani da Allah kuma ke yar masu kudice gaki yar birni..."kema yar birnin ce khadija.cewar Ni.ima tana d

ariya.

Dije takama hannun Ni,ima tana cewa "Sister Ni,ima pls mubar wannan zancenma don wani bamai yiwuwa bane .

Ta tashi tafuta tabar Ni,ima tana murmushi da yabon kyawawan halayen ta aranta tabbas samun kishiya kamar Dije sai antona.…………

*muje zuwa*

👌🏼

*DIJEN ƘAUYE *

🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕

*True life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 110-115

Duk yadda Abdallah yaso yahadu da Dije abu

yaci tura taki bari su hadun sbd tasan nufinsa akanta gasashi kawai takeyi dataji muryarsa afalo inta taho take komawa inko tana zaune afalon daya shigo zatayi dabara taje kicin ta hado masa lemo ko ruwa saita zille tagudu dakinsu

Dayawa agidan sunyi za

ton ko itanma tana sonshine tunda akan idonsu take masa wannan kyautatawar wanda shi agunsa bakaramin dadin hakan yake jiba

Ko mubina abokiyar sha.awararta tayi zaton ko dijen ta sauko

😅

Abdulhakim ne kawai yasan komai

Sai Ni,ima datake kallon di

jen kawai a mara wayo domin ta ranfota itama kuma tana ganin rashin wayon dijen tsababa tunda Allah ne yabata dama yakamata ace ta dama lokacinta danji take inama itace dijen,ita yanzu baga yanda Allah yamaisheta ba garin neman gira ta rasa ido garin neman

soyayya ta hanyar asiri gashi abu yaja mata jangwan tazama gurguwa kuma samoshin datayi ta hanyar asiri ada yanzu ya karye babu wancan bayanin

don yanzu kam Dije ce kadai agabansa ko lowerst baiji sonta kamar yadda yakejin na Dije ba.

Andaura Auren

Mubina da Abdulhakim Anyi shagali bana wasa ba wanda aranar aka kaita gidan Abdulhakim din sukuma su Dije a washe gari Suka koma gidansu

Abdallah ne yadebesu amotarsa yakaisu gidan nasa

A wauta ta dije kin kwana tayi asashenta wai ita lallai adaki

n Ni,imar zata kwana sbd jikinta

Ni,ima tayita mata dariya tace "ho!Allah nagode maka da halin dije na sokonci kekam wai yaushe zakiyi hankali ne ?mace da mijinta tagujeshi maxa tashi ki koma bangarenki donni da kk ganni naxama cikon gida agareku nabar

mk Abdallah.

Dije tace "amma dai ko meye har yanzun kina matsayin matarsa kuma kece uwar gida tunda kin girme mini dan haka nabar masa ke yakwana asashinki kuma kidaina cewa ke cikon gida ce matar gida kk kamar kowace macen da take jin ita macen gida ce

.

Ni,ima takama baki tana kallon dije kawai mamakinta takeyi ita kokishin mijin batayi toko dan bata sonsa

Tabbas tana zargin ko dijen bata san so bane tunda kamar Abdallah ace ba.a sonsa handsome dashi kyakykyawa me faffadan kirji son kowa kamar y

adda wasu matan ke son su sami miji me irin fasalinsa lallai ta jinjinawa dije.

👍🏼

Saida dije tayi kwana biyu asashin Ni,ima tana yi mata girki sannan Abdallah yataka mata burki yace mata maza ta koma nata part din yasa me aikin momy ta dawo gun Ni,

imar.

Ranta bai soba ta koma bangaren nata amma taci alwashin saita bakanta masa rai don itakam taki jininma yayi mata magana ballan tana ma yakebe da ita tasan kuma damar hakan yakeso

Dayake ackn hutun zangon karshe suke na third term za.ai musu can

jin aji zasu shiga jss 3 kwana tayi tana nazari aranta na yanda zata tafi kauyensu domin tunda tazo birni zuwanta daya da sukaje da momy da mubina da Aunty maryam kusan shekara biyu knn tun tana jss one

Tasan inta tambayeshi zataje kauyen nasu baxai bar

ta ba Shiyasa tasamo wata dabara na tafiya batare data fada masa baki da baki ba arubuce zata bar masa sallahu kawai

Ckn dare daya dawo kai tsaye yanufi dakinta yamurda kofar yaji akulle take

Yaciji yatsa kawai yakoma dakinsa domin duk wayon kaxa sai

ansha romanya tagama guje gujenta da boye boyenta yasha alwashin saiyasa ahannunsa ya murji "yar roba.

********

Da sassafe tagama shirinta dama toilet dinta ackn dakinta yake tagama shirinta tsaf ta sanya wani swice lace da ddy yadinka musu su uku ita

,Ni,ima,Mubina me tsadar gaske ne harda gyalens kwalliyar purple ne ajikinsa dan haka ta bude akwatinta ta dauko wani takalminta plat ne da jakarsa purple sabbine tun na Auranta sai yanzun yai mata amfani sbd ada can batasan toomach ba

😅

Har gari ya

gama wayewa bata bude kofar ba abu daya ne take jinsa kudin motar da zatayi xuwa kauyensu batada isassun kudi ahannu abinda yake ahannunta baifi yakaita tasha ba

Tanajinsa yaxo yana kwankwasa mata kofa yana kiran sunanta

"Khadija bude kofar mana.

Ta taso tazo ta tsaya jikin kofar tana fadin "inna bude me zan maka?

"Sai zakiyimin wani abin ne zaki bude?nifa mijinkine khadija bai kamata kiringa min haka ba yakamata boyen kankin nan da kkyi yazo karshe inada bukatarki _plz open the door my wife_

tayi murmushi kawai domin ko me zaice bazata bude dinba duk dadin bakinsa ayau

Tace "zan bude maka kofa amma saika gaya min abinda yake tafe dakai.

"Kudin cefane nazo nabaki tunda naga bakida komai a kicin.

Taji wani sanyi aranta kudin motar zuwa

kauye yasamu.

"Ka ajiyemin akan table katafi inka dawo mahadu da dadaddare.

Yazaci da gasken take zasu hadun da daren saikawai yace mata "to zan ajiyr mk amma kiyimin alqawarin da daren bazaki kulle kofa ba.

Ckn wani salon murya da batasan tana d

a itaba ta yaudara tace "naji na amince nayi maka alqawari zanbude maka kofa harma mukawana tare.

Har ckn ransa yaji dadin kalaminta kuma ya yarda da ita.

Yajuya asanyaye ya ajiye mata dubu biyar yafice

Saida tajiyo tashin motarsa yafuta sannan ta

fito ta dauki kudin ta saka ackn jakarta ta zatgawa karenta igiya ko ni,ima bata yiwa sallamaba don batason asan ta tafin ma

Me gadi ne yaga futarta yayi mata adawo lfy

Tana zuwa tasha saura mutum daya amotar da zata hau ta zuwa kauyan nasu tuni ta

na shiga mota ta daga sai kauyen Marina..…………

*Auntyn Sayyada da Shahida ce*

👌🏼

*DIJEN ƘAUYE *

🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕

*True Life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 115-120

Addaji Tana tsakar gida saijin Sallamar Dije taji tashigo janye da akwati ahannunta

Addaji da murnarta ta tareta tana fadin "maraba maraba da yan birni on njab'b'aama b'oy.

Dije tayi murmushi tace " addaji sann

u da gida.

"Yawwa dije Gorko maa accii ma na? _Tare kike da mijin naki_?

Dije ta girgiza

_Toye Abdallah woni?_ Ina Abdallahn yake?

A sanyaye Tace" _o wurtake jam_

Addaji ta kura mata ido taga kamar akwai damuwa atattare da ita sa

ita gyara zama tace mata "Dije ko akwai damuwa ne?

Dije ta girgiza kanta tace "babu wata damuwa Addaji kawai dai nazo ganin gidane

"Da amincewar mijinki?

Addaji ta watso mata wannan tambayar.

Tayi dim!baxata fadi gaskiyaba sbd Addaji zata iya

hadata da kawunnanta su korata ba shiri itakam tana son ta huta na kwanaki don tayi kewar kauyen nan nasu.

Asanyaye dije tace "eh!dama shiyace nazo nayi kwana biyu zaizo yadaukeni.

Murmushi Addaji tayi tace "Allah sarki yakyauta ya kika baro mutan gi

dan?

"Lafiya suke Sunce agaidaki.

"Ina amsawa, tashi kikai kayan ciki kizo ga abinci can a madafi kizuba kici.

"To Addajina. Dije tafada tana mikewa da fara.a akan fuskarta

Tunda tazo take cikin Nishadi tawuni aranar tana sharar baccinta hanka

li kwance saidai mafarkin datayi yadaga mata hankali sosai ganin wai gata da Abdallah suna nitso a swimming pool yana suna wanka

daganan bayan sun gama wankan sai gasu a lambu azaune takwantar da kanta ajikinsa yana bata tufa abaki

Abin yadaure mata k

ai data farka wato ma dan shirmen mafarki har wani soyayya aka nuna mata tanayi da Abdallah ack

Taja tsaki tana fadin "Allah kaimin tsari dayin soyayya dashi.

*******

A can birni kuwa hankalin Abdallah tashi yayi matuqa ganin yadawo baiga dije agid

an ba yaduba kowane sashi harna ni,ima bata nan

Ni,ima da mai aikinta sukace yau dai kam basuji motsin taba.

Amma mai gadi yabashi tabbacin yaga futarta da akwati ahannu.

Yagarxaya gidan momy ko can ta nufa amma abin mamaki sai momy tace masa bata

zo ba

Momy ma fada tahaushi dayi "banyarda dakai ba Abdallah da alama akwai abinda kayi mata yasa tabar gidanka batare daka saniba.walh duk inda

kasan zaka samota kaje kanemota kafin ranka yabaci domin inhar dady yaji ranka ne zai baci maza kaje kanemo

"yar mutane inkuma ba hakaba mu iyayanka muje munemo ta

Hankali atashe yafuta yasuri mota yahau titi yana ta kalle kallen hanya ko Allah zaisa yaganta ahanyar

Gidan Aunty maryam ma yaje amma tace masa itama batazoba tabbas abin yadaga masa hankali

har dare yana yawwon nemanta ko da yaiwa Abdulhakim wayama ko taje gun mubina shima ce masa yayi batazo musuba

Sai dare daya dawo gidansu dady yasashi gaba da fada yace masa "Da alama ko kauye ta tafi ta gaji da abinda kake matane.Abu danake mata na tak

urawa agidana kawai saidai ko can din ta tafi abinta.

Dady yace "dolenka kayi sammako gobe katafi can kauyen kataho a ita inkayi mata lefi kuma kabata hkr cewa tace wannan sbd baka isa ka wulakanta khadija ina raye ba.

Haka yakoma gida sukuku dashi a

part din dijen yakwana yana tunaninta sai ayanzun ma yakarajin wata azababbiyar kaunar khadijan tabbas inya sami zuciyar khadija zataga soyayya tsantsa sai ya mantar da ita irin tsanar datayi masa don yasan kome tayi ayanzu laifin sane.

Ya kudurta arans

a duk rintsi duk wahala bazai yarda yarabu da khadijaba zaiyi juriya yai hkr da ita na duk abinda zata nuna masa na qiyayya har Allah yasa wataran tasoshi

Washe gari ko karyawa baiyiba yai wanka yanufi kauyen marina don taho da khadija

Yana tafe ahan

ya Abdulhakim yakirashi yake tambayarsa ya maganar khadijan anganta kuwa?

Abdallah yace "gani dai ahanyar kauyensu zanje naduba kotana can mutaho tare don dady yace kada inyarda intaho kafata kafarta.

Abdulhakim yace masa "to Allah yasa tana can din

domin nakikkira wayarta naji akashe ko matsalar network ne.

Abdallah yace "may be hakanne.plz my bros katayani addu.a Allah yasa tana can din

"To amin dan,uwa Allah yakiyaye.

"Amin. Sukai da juna sallama yakashe

Agidan gonarsu yasauka saida

yahuta da kusan awa biyu kana yanufi gidansu Dije wanda saida kwatance ma yaje gareshi don zuwansa daya bazai iya sake kai kansaba again

Yasa yaro yai masa sallama da masu gidan

Koda yaro yasanarwa Addaji bako na sallama awaje da sauri ta leka

T

ana ganinshi tahau fara.a don koda bata taba ganin saba tasan shine mijin dijen don tariga tasan Abdulhakim farin sani shine dai dama bata taba ganiba

Har kasa ya durkusa yagaidata tareda gabatar da kansa gareta

Tace "lale maraba shigo daga soro mana

.

Taje da saurinta tadauko masa tabarma ta shinfida azauren yashiga yaxauna

Takawo masa fura da nono tadamu tasha sukari

Yau saiga Abdallah dashan fura harda santi mutumin da ada yakewa Abdulhakim kallon kaxami yanashan furar yan kauye kawai don w

ulakanci bawai don yaga wata kaxanta atattare da dijenba

Yaita baxa ido yaga ta inda dijen zata bayyana

Sai can addajin ta dawo tace masa "kayi hkrfa taje gidan kawunta ne tun dazu amma nasan yanzu tana kan hanya.

Yace "ba komai inna.

Addaji ta

ce "ko akwai matsala ne?

Ya girgiza kai da sauri "a,a babu wata matsala inna kawai dai nazo mukoma ne dama kwana daya nace tayi.

Ta gyada kai sai sannan takara yarda da Dijen

Yana nan zaune harna tsahon awa guda

Yanata latse latsen wayarsa sai

jin sallamarta yayi da siririyar

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login