Showing 210001 words to 213000 words out of 217599 words
annashuwa a tare da su babyn tana ta bacci babu halin d'aukarta domin dai likitanta ya bada umarni hakan kada a yawaita jagwalgwala mata jiki sai dai ido kawai Fati take tambayata da wane suna za a dinga kiranta tunda wai Sukairaju ya gaya musu sunan Hajja ne da ita na ce Mufida haka babanta ya ce a kira ta.
Yini muka yi tare da su har yaran suka dawo daga makaranta ganina a gidan ya sanya su shiga tsananin murna hankalinsu gabad'aya nakan babyn sai sun d'auketa Minal har da kuka sai da na kira Mairo tukkuna na ce ta ja ta su fita domin wani irin ciwon kai nake yi kukan da take yi kuma yana sa'bata da yanayin yadda duk na gansu cikin damuwa mussaman Khalil duk jikinsa ya yi sanyi na kasa gane shin akan menene ba ni tsammanin ubansa ya gaya masa ya saki uwarsa sai dai idan ita za ta gaya masa kuma ba na tsammanin ta tafi tana gidanta tunda na ji lokacin da yake magana da Mairo yana gaya mata sakon Ladidi tunda k'awarta ce idan Hauwan ta aikota sukan dan jima suna hira akwai wani k'aramin gari a cikin bauchi mai suna giayade anan cibiyar iyayensu take duk da ba su had'a wata dangantaka ba hirar yau da gobe ta sanya suka fahimci garinsu daya.
Washe garin ranar da muka fito Hajja da yayarsa suka dira dama ya gaya mini shine ya dakatar da su tunda ko sun zo muna asibiti ganin hakan ya sanya ni ma na hana anti Yagana zuwa tukkuna can gidanmu ma haka na gayawa Babanmu a waya cewa su bari sai mun fito Sahura kuwa kusan kullum sai mun yi waya.
Sai dare tukkuna muka samu ke'bewa Hajja fadi take yi Hauwa abinda ta yi muku Amina Allah Ya yi mata ba zan yi mata baki ba ba kuma zan nunawa duniya Tajo ne nawa ba amma da wahala ta sake yin katari da namiji da abokiyar zama kamarki zahiri kin yi iyakacin bakin kokarinki wurin ganin kin kawo daidaito a tsakaninku kin yi bajinta kwarai kuma kin yi da jiki da aljihunki a tarihi ban ta'ba ganin kishiya irinki ba Allah ya biya ki da aljanna Ubangiji Allah Ya dubi rayuwarki. Wad'annan yara kuma ina yi miki addu'a akan Allah Ya ba ki wuyan d'auka Allah Ya raya mana su.
Na dinga amsawa da Amin Amin amma bayan haka ban iya furta komai ba akan abinda suke tattaunawa Hajiya Saratu tana ta fad'a akan zaman da take yi tunda an yi ta ta kare babu wata sauran igiya zaman me take yi kuma har tana fad'in da safe za ta je gidan ta ji dalili babu sauran wani mutunci da zumunci a tsakaninsu tunda har ta iya rufe idonta ta yi wa dan uwanta wannan cin fuskarsa. Gaskiya ne a wannan ga'bar takai-takai kawai ake yi kowa nasa ya sani domin kuwa abinda ita Inna Uwanin ta nuna kenan. Wannan karon Hajja ta saki ragamar hannun yaranta ai kuma magana ta 'kare babu sauran gyara babu amfanin zamanta a gidan ta kama hanya ta tafi yara kuma ta bar su a gidan ubansu.
Da wannan suka rufe maganar ni dai magana akan Hauwa ta k'are a bakina domin ban san abinda zan ce ba ta gama goge mini hadda ta tilawa.
Aikuwa kamar yadda ta kwana da al'amarin garin Allah Yana waye wa ko karyawa ba ta yi ba ta nufi gidan Hauwa. Ni dai Ina d'aki da yake kofar a bud'e take saboda yaran sun shigo mini kafin su tafi skull na ji fad'anta a falo har ina tsinkayar muryar maigidan. Fadi take yi zaman nata ai bashi da wani amfani ban kuma yarda da abinda ta fad'a ba wai juna biyu gareta ko za ta tafi sai a bari ta haihu tukkuna shin kai ka san cikin ne da ita. Cikin rashin karfin sauti na ji maganarsa amma ban ji abinda yake cewa ba. Na yi zuru ina mamaki cikin da take ta ha'kilo a kansa shin tasan dama tana dashi ta yi wannan rashin mutuncin ko kuma dai karya take yi don kada ta tafi ne. Wani sashi na zuciyata ya dinga gaya mini karya take yi da tana da ciki da kowa ya sani tunda abinda take nema ne kenan kuma ba zata zafafa bakincikinta ba.
Can wajan minti ashirin da biyar a tsakani na dinga jin kuka kasa k'asa da maganganu suna tashi sai da na kasa kunne tukkuna na gane muryar Hauwan ce take wani irin kuka mai cin rai Hajja tana ta yi mata magana akan ta yi shiru amma sai kara karfin kukan take yi. Cikin babban sauti na ji muryar Hajiya Saratu tana cewa kan ki kika tonawa asiri Hauwa ba mu za'bi Amina ba saboda muna 'kin ki. Mun za'bi kyawawan halayenta ne da kuma biyayya amma tunda yanzu magana ta kare babu buk'atar a yi ta maimaitawa sai dai addu'ar Allah Ya fitar da sakamako da gaggawa a tsakaninku wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa ba mu da wata hanyar gyara kuma babu wata mazahaba da za a bi saki ukun ai ba a lokacin daya ya yi miki su ba an yi daya da farko ya zo ya maimaita miki biyu saboda haka baki fara yin nadama ba Hauwa kuma muna nan ba za mu fasa addu'a ba idan shi ya cutar dake kamar yadda kike yawaita fadi Allah Ya saka miki.
Saboda irin bud'e wutar da Hajiya Saratu ta yi a gidan sanya kowa jikinsa ya yi sanyi masu aiki kaf ba su fito ba domin sun jima a falon suna musayar yawu tana ta jaddada mata 15m din da take tunanin maigidan ne ya bata to ba shi ba ne ni ce hakan ya kara tsananta kukanta ina daga d'aki ina Jin gurnaninta cikin tashin hankali kamar wadda ke shirin tayar da sarkin aljannu.
Shi gabad'aya ma bai sauko ba balle ya tanka takaici da b'akinciki ya na ta nukurkusarsa. Babu arziki Hauwa ta kama hanyar garinsu jin zafafan kalamai raddi masu kauri da jefa zuciya cikin rud'ani
da bala'in yanayin da ba zai misaltu ba dama aka ce duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba tabbas ta shi ko d'umi ba za ta yi ba.
Washe gari Nusaiba ta zo mini da yaranta kaf muka yini tare su kuma su Fati suna jiran zuwan anti Yagana tukkuna don ba su kai ga tafiya ba.
Kwana biyu a tsakani ta iso da yamma kuma matan gidanmu gabad'ayansu har da Babanmu da Baba Sule suka kwana da yamma suka yi shirin tafiya gabad'aya amma ban da anti Yagana saboda na ce ta bari tukkuna sai nan da sati d'aya
Yaran shop's dina har da securities din dake gadi a wajan Lawan ya jagorancesu a daran da su Fati suka tafi muka jima da suma muna tattauna cigaban da ake samu koyaushe.
Haka na dinga samun baki daga wannan sun tafi wasu za su zo Sahura ita kadai ta zo mini wannan karon Yusura ta sake samun ciki sai kawai na ganta da yarinya jale-jale tana koyar tafiya yarinyar Idiris ce uwarta ta cire ta daga nono lokacinta bai cika ba ta yi aure a cewarta baya kawo kudin abincinta iyayanta suka ce ta cire ta daga nono a kai masa 'yarsa suka kawota suka dire babu Imani uwar ta tafi ta yi aure. Mai shegen k'iwa da rashin yarda saboda tsabar bala'i lallai Sahurar ba zata huta ba ko uban da ya haifeta bata yarda dashi balle danginsa ta ma'kale mata na dinga mamakin wannan lamari kwatankwancin abinda Minal take yi mini yanzu ko wurin aiki da ita take zuwa Hajja kuwa sai 'kara mata karfin gwiwa take yi tana fad'in kada ki sare kada ki gaji wata'kila zata ji kan ki da d'a da dukiya ba a yi musu mugunta.
Muna tare da su tsayin kwanaki uku babu irin batutuwan da ba mu tattauna ba abinda Hauwa kuwa ta aikata ya yi bala'in ba su mamaki amma jin irin hukuncin da maigidan ya yanke a kanta ya sanya zuciyoyinsu suka yi sanyi.
A ranar da suka shirya tafiya wasu bakin suka dira Hamusu da Usaini kowanne da iyalinsa sai kuma Yusi da Saminu. Hajja kuwa ta samu 'kawa 'yar gidan Usaini mai sunana kenan itama suna kiranta da Minal ta dinga tsokanarta da faratu haske ne da ita kau har ta so ta fi ubanta haske Hajiya Saratu na tsokanar Hajara kamar ba goyonta ba, ita yarinyar ashe mahaifiyar Ummansu Saminu ta d'auko domin duka hasken fatar ta gada musu duk da ta tsufa amma tana nan kar kar da ita Fulani ne na asali.
Kwana biyu da zuwansu Yusi yake gaya mini Kamalu daf yake da dawowa gida domin sun yi magana da shi a cikin satin da ya wuce na ce bai gaya mini ba duk da kuma mun yi magana da shi kwana hud'u da suka wuce ya dai tabbatar mini da cewa daf yake da ya kammala abinda ya kai shi amma bai fada mini ranar da zai dawo ba, amma ba na mamakin kan cewa ya sanar da maigidan tunda kusan ya fi sakewa da shi fiye da ni.
Kwanaki biyu a tsakani suka tafi Hajiya Saratu ma ta riga Hajja yin gaba domin ta ce ita zata zauna ta kwana biyu tukkuna har na ji Yusi yana tsokanarta wai sai ta taso sun tafi haka yake janta da tsokana irin wadda ma bai yi wa Gwaggo irinta ba tsakanin Yusi da Hajja akwai amana da kuma 'kaunar juna har da rantsuwa wai gidan babu dad'i idan bata nan ta ce masa ba wasu kwanaki za ta yi da masu yawa ba. Shi kam babu halin zama makaranta ga kasuwa ba ma shi da ishashen lokaci na kansa.
Hajja ta sake sosai da jikokinta tana jan su a jiki da wasa da dariya har dai suka sake tunda sun gano cewar kakarsu ce wadda ta haifi Babansu idan suna gidan karad'insu kad'ai ake ji a falo tana ta biye musu Baba Tabawa na yi musu dariya. Minal ce take ma'kale da ni da Mufida suna dawowa daga makaranta a wasu lukutan ko uniform ba ta zuwa ta cire za ta same ni a d'aki ta'ba nan ta'ba can ta yi ta han'koro ita lallai sai na bata k'anwarta. Cikinsu har khalil babu wanda ya taba daukarta sai dai gani daga nesa Babansu ya ce ko za a ba su sai ta kara wayo tunda ga abinda likita ya ce kuma alhamdulillahi ta yi lafiya tana shan nono sosai ta yi baccinta na rana da dare babu kuka mai zaburarwa sai dai tak'aitacce dalili duk wasu sharad'ai ina bi yadda muka yanke ni dashi rainonta yana hannuna duk rintsi babu buk'atar taimakon masu aiki gudun yin abinda zai sa'ba da lafiyarta.
Yau kwananmu talatin da tara ya kama saura kwana daya kacal mu yi arba'in ina toilet na din ga jin kukanta a gaggauce na fito da sauri na riski Minal kane-kane saman gado tana ta cakumarta da wannan rawar kan nata. Tsawa na yi mata irin wadda ban ta'ba yi mata irinta ba ta kuwa zabura da sauri ta juyo tana kallona wanda ya yi daidai da shigowar Khalil na cigaba da Fadin." Ba ki jin magana ko, na ce ki bari zan baki ita ba yanzu ba tukkuna."
Ta cire hannunta da sauri daga kan towel din Khalil da sauri ya dube ni yana fad'in." Mama me ta yi mata?"
Shiru na yi ban ce masa komai saboda kwanaki ya daketa akan haka alokacin da ta taba yun'kurin aikata abinda ta yi a yanzu. Na nufi yarinyar da sauri na dauketa aka ci sa'a kuwa ta yi shiru tana lumshe idonta baccin za ta koma.
Ita kuma ta sauka daga gadon tana ra'be-ra'be tana kallon Yayan nasu na kalleshi ina fad'in kada ka daket....ban kai ga rufe bakina ba ya kwada mata wani mari ta kwallara kara a ki'dime ta yo wajena. Na rufe shi da fada sosai. Ya fara fadin." Mama yarinyar nan sai ana dukanta fa wallahi rawar kanta ya yi yawa haka ta ga 'yan uwanta na yi tuntuni ake fad'in magana d'aya amma ta'ki ji ta zo ta cakumeta alhalin ba ta da lafiya."
Na sassauta sosai ina fadin." To na ji amma dukan da ka yi mata ya yi yawa kada ka sake ka ji ko?"
Ya gyad'a kansa yana sauke numfashi ita kuma dadi take yi." Mama ki yi hakuri." Na ce na ha'kura ai amma kada ki sake."
Ta daga mini kanta tana jan hanci. Da gaske ta sangarce shekara tara fa yanzu ya kamata ace ta rage lalata shi kuma yanzu jin sa yake yi babba a cikinsu duk wadda ta yi shirme zare idonsa yake yi bai dai ta'ba dukan su Hassana ba sai dai muzurai da tsawa idan ya ga sun yi abinda bai da ce ba.
Ya nuna mata hanyar fita da hannu ta gane abinda yake nufi aikuwa sumi sumi ta fita. Na ce Kai ba ka jin tsoro ta gayawa babanku kasan 'yar gaban goshi ce. Ya d'an yi murmushi yana fad'in ai Mufida ta ture mata fada yanzu itace akan karagar mulki."
Takaitaciyyar dariya kawai na yi na cigaba da jijjiga yarinyar a hannuna.
kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ya zauna kusa da ni a nutse zamansa ya sanya ni nazarinsa sosai yana da damuwa tuntuni na fahimta kawai shiru na yi.
Ya ce." Mama ko zan iya sanin abinda ya shiga tsakin Mamanmu da Baba don Allah ki gaya mini da na tambayi Hajja ta ce mini babu sauran zama a tsakaninsu ma'ana babu damar da za a gyara ta dawo, ki yi hakuri don Allah ki sanar da ni rufe mini bashi da amfani mahaifiyata ce na yarda amma k'wakwalwata ba zata manta da abubuwan da suka dinga faruwa ba tun da k'ananun shekaruna na gane dabi'unta ba su da kyau na yi iyakacin bakin kokarina wajan ganin ta gyara an zauna lafiya amma hakan bai samu ba.
Jikina ne ya mutu da jin abinda yaron ya zo mini da shi. Yaro karami da tunanin manya idan yana manyance abin har mamaki yake ba ni wallahi sai na yi saurin yin kasa da kaina
To na ce masa me in banda abin Khalil Hajja ta sakaye masa saboda abu ne mai muni a ce ya ji abinda uwarsa ta aikata. Amsar ai tana wajan Babansu tunda shi ya aikata ba ni da abinda zan ce.
Ya gaji da magiyarsa ya tashi ya tafi domin abinda nake nanata masa shine ni ma ban san komai ba.
BAYAN WATA UKU
Bauci
"To tunda kina ganin akwai yiwuwar haka sai ki jarraba ki gani ni dai ba ni da wata dama yanzu Hauwa gabad'aya ma cikin nadama nake a halin yanzu dalili ban san da wace fuska zan kalli yar uwata ba abinda ki ka aikata bai yi mini dadi ba ko kad'an gashi saboda ke sakarai ce kin dawo gida hannu rabbana in banda wannan kudin da ya baki wattanin baya ina takardar kamfanin da kike ta masifa akan ba kya so kun rabu rabuwa ta har abada babu kome kamfani kuma yana hannunsa har yanzu tunda dai bai baki shedar mallaka ba kin yi a banza sakarai shashasha duk shawarwarin da k'awaye da abokan arziki suke ba ki kin watsar kowa ya gaya miki ta wannan hanyar ake ya'kin kwatar 'yanci a gidan miji shikkenan ai sai mu zauna ni dake ai mu tsotsi tsamiya kin raba da ni da 'yar uwata
Hauwa gashi abinda duk muke han'koro bamu samu ba idan kun yi auran kisan wuta kin biya wanda za ku kulla yarjejeniyar shin kina da tabbacin zai sake ki, ki koma gidan Tajo. Shi din ai ba mahaukaciya ce ta haife shi ba, ta wace hanyar za mu bi koda hakan ta kasance muga bu'katarmu ta biya?" Inna Uwani ta kai k'arshen maganarta cike da damuwa mai tsananin gaske.
Ta nisa yayin da take ko'karin korar damuwa da wasi-wasin zuciyarta ta ce ." Zai yiwu Inna don mun gama magana da Yaya Naziru mijin Sadiya na ce zan bashi miliyan uku idan mun yi aure wata biyu zuwa uku sai mu rabu. Maganar komawa dakina ai mai sau'ki ne in sha Allahu zan koma kuma zan yi kokarin ganin na gyara na zauna lafiya da ita da shi don yanzu gabad'aya hankalina na gidan da yarana shikkenan Amina ta zama ita kad'ai yaran ma sun zama nata saboda na riga nasan na yi sallama da yarana Inna kamar fa ba ni na haifesu ba."
Sai hawaye shaaaa! suka fara kasa tsare a kumatunta. Ta takure jikinta sosai ta jingina bayanta jikin wata tsohuwar kujera dake falon nasu tana kuka mai tsuma zuciya.
Ta ce." Hauwa ba ki da kunya da ta ido yanzu Nazirun za ki aura da wane idon za ki dubi Sadiya duk abinda za ki yi fa ki yi tunani akai shima Nazirun kwad'ayin me yake yi ne, ki je ki nemi wani a waje wanda babu dangantaka mana.
Ta dago kanta tana kallonta kafin ta ce." Shine kawai nake ganin zai cika alkawari Inna tunda ai rashin ba shi goyon baya ne a wancan lokacin ya sanya ya nemi auran Sadiya Inna kada ki manta fa tsohon saurayina ne. Kuma ya gaya mini kudin nan da zan bashi zai dora akan kasuwancinsa da ya yi rauni tunda zahiri yanzu Sadiya ta fi shi samu tana aiki tana kuma business ni kaina na sha yin order a wajanta.
Ta ce." Saboda baki da wayo ko, ba ki tunanin d'adin baki ya yi miki domin ya rama abinda ki ka yi masa a baya wane irin cin kashi ne ba ki yi masa ba da k'yamata saboda ba shi da kud'i, ki yi nazari sosai akan hakan."
Shiru ta yi na d'an wani lokaci kafin ta ce." Inna ki daina wannan tunanin don Allah shi kansa fa dana gaya masa kudirina goyon baya ya ba ni ya ce yana da kyau