Showing 102001 words to 105000 words out of 217599 words
ina mayar masa da kayansa. Shi kuma ya cire agogon hannunsa ya zare gilas din da hular kansa ya tashi tsaye tare da cire babbar rigar ya ajiye saman gado. Toilet ya nufa bai sake ce mini komai ba na sauka kasa da yaron na mayar dashi wajen mai rainonsa. Kicin din na nufa sun kammala komai na shirya masa abincin kamar yadda ya buk'ata da ya shigo
Na same shi yana sallar Isha'i na ajiye tiren a wurin da yake zama sai da ya jima saman daddumar yana addu'a kafin ya shafa ya taso yazo ya zauna na fara ko'karin zuba masa abincin yana ta kallona.
yana ci muna hira gidan Malam 'Daha da irin sallahun gaisuwa da godiyar da suka bashi zuwa gare ni. Nan yake yi mini bayanin abinda yake cikin leda viva da take ajiye gefe naje na daukota kayan dake ciki na fito dasu sassa'ken gargajiya ne da saiwowi gasunan kala daban daban. Ya fara yi mini bayanin yadda za a yi da ruwan rubutun dake d'aure a waya farar leda irin mai zurfin nan za a dafa maganin a tace a sha tsayin sati daya kullum karamin kofi d'aya. Babu maganar sauran asiri a tattare dashi kamar yadda malamin ya yi masa bayani matsalar dai aka samu har ta ta'ba masa lafiyarsa wannan mummunan d'aurin da aka yi masa tunda dama an yi shine akan manufofi da yawa. Idan har an dage da magani da kuma addu'a karfi da mazantakarsa zai dawo fiye ma dana baya. Sai dai ya ce kada wata mu'amula irin ta aure ta wanzu har sai an gama shan maganin tukkuna.
Ai a daran ban bari gari ya waye ba na dafa maganin na tace shi sosai na zuba cikin wani dogon jug guda biyu na kai saman nasa na ajiye kullum da safe za a sha kofi d'aya idan ya yi karin kummalo.
Da safe kafin na fita falo Sahura ta kira ni a waya cikin annashuwa da farinciki take fad'in." Amina don girman Allah ki taya ni da godiya wurin Yallabai jiya na kar'bi takardar gidan da ya yi mini alkawari zai ba ni anan hotoro wajan ma'aikatarmu gida mai kyau Amina ginin zamani gashi ya sanya an zuba mini komai tarewa kawai zan yi."
Sai ta rushe da kuka.' har sai da na ji wani iri a raina na ce." Haba Sahura menene kuma na kuka don Allah ai kin wuce haka a wajenmu don girman Allah ki daina wannan kukan ba na so."
Na ji ta tana fad'in." Ya zama dole na yi kuka Amina na dad'i ne wallahi na rasa inda zan tsoma raina ba ki ga gidan ba mai yalwa da wadatattun d'akuna ga ababen more rayuwa kuma wai gidana ne mallakina."
Na ce." To menene a ciki ai komai rabo ne, ki godewa Allah kawai."
Ta ce." Shine abin godiya a koyaushe amma dai ya zama tilas na godewa wanda ya zama sanadi."
Sallama muka yi da ita ban kuma yi kasa a guiwa ba yanzu zan je na sake jadadda masa godiyata.
na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Sai da na leka su Baba Tabawa tukkuna na duba Sultan ta yi masa wanka yana ta bacci cikin net dinsa muka gaisa sosai da su ina tambayar jikinsa ta ce ai ya warware sosai don jiya ma kwata kwata bai kwana da zazzabin ba har gari ya waye.
Na godewa Allah a cikin raina na fito saman zan nufa na samu Hauwa a kan kujera ita kadai a falo a zaune muka kalli juna na ganta a hargitse duk ta muzanta na janye idona da sauri daga kanta ai hausawa suna cewa.' Duk wanda ya hana uwarsa bacci to shi ma watarana bai zai rintsa ba kana ganinta kaga wadda take cikin tashin hankali da damuwa ashe tana son yaron ta cillar dashi ta tafi gashi yanzu 'kiri-'kiri tana kuka da nadama 'ya'yanta suna gudunta har dai mai suma saboda ta daukeshi Khalil da Minal kuwa ba na tsammanin ma suna yi mata magana domin duk gidan kamar mujiya haka ta zama.
Ina hawa saman ya ce na had'o masa shayi haka na sake sakkowa na shiga kicin na had'o kayan shayin na fito still dai tana zaune a kujera shiru ta d'an ba ni tausayi amma kadan ban kalleta ba na ji ta kira sunana na tsaya tare da dubanta.
Maganar dai jiya ta sake maimaita mini kada na gaya masa don ta d'auki sultan ya suma."
Na b'ata Raina ina fad'in." Wai me zai sanya na gaya masa ne Hauwa? me ki ka d'auke ni ne?" idan har ya san abinda ya faru to ki tabbatar babu yawuna smma ai kin san a gaban yara aka yi kuma irin wannan lamarin da wahala ya 'buya."
Ta yi shiru tana gyad'a kanta ba ta ce komai ba. Na kad'a kaina kawai na haura saman da mamakin yadda ta yi sanyi ta zama wata Saliha bana tsammanin ma jiya ta rintsa saboda yadda na hangi tashin hankali a idonta.
Sai da na bari ya kammala shan shayin tukkuna na tsiyaya masa maganin a madaidaicin Kofi da kamar minti ashirin da biyar a tsakani ya sha maganin har yana yin gyatsa yana fad'in." Na gode uwar biyu.'
Na janye kayan tea din daga gabansa ina murmushi na ce." A madadina da Sahura muna kara godiya zuwa gare ka Ubangiji Allah Ya kara suttura da rufin asiri Allah Ya sa a mizani na gode sosai Allah Ya saka maka da alheri."
A tak'aice ya furta." Ni ma na gode sosai Allah Ya saka miki da alheri Ubangiji Allah Ya sa mu rayu tare har karshen numfashina."
Amin na furta. Ina kallonsa zuciyata na d'an dokawa kan zuciyata na sa'ko mini wani lamari na ji maganarsa yana fad'in." Yau Maryam ta cika kwanaki arbarin da rasuwa ko?"
Na ce." K'warai kuwa Nusaiba sun yi abin sadaka da sassafe su Masa'udu suka fita da shi zuwa bakin titi tana can tana baccin gajiya dakinsu baba Tabawa."
Ya gyada kansa a nutse Yana fad'in." Babu wani Abu da nake buk'ata a game da dukiyar matar nan Amina amma ya zama dole mahukunta suka shiga ciki tunda duka mun gama harhad'a abubuwan da ta mallaka ni da yaronta Salim sutturanta kuma na gayawa Nabila tunda har yanzu tana gidan a zaune tare da yaran Salim da Adam na ce su raba a tsakaninsu abinda ya danganci furniture na d'akunan gidan da na'urorin dake kicin dinta yaran sun ce a bar musu a gidan abinda na gada daga ciki na bar mu su. Wad'annan manyan kadarorin nata da kudin da muka gani cikin wannan dirowar tata sune alkali zai kasafta ba ni buk'atar komai na bar musu abinda dai nasan ba zan ta'ba yafe mata ba shine ko'karin mayar da ni rago mai rauni da ta yi. Idan har lafiyata da mazantakata irin ta d'a namiji ba ta dawo daidai ba Allah Ya isa ban yafe ba wallahi."
Na yi gaggawar danne dariyar da take so ta kufce mini sosai na daidaita yanayina don ganin yadda yake magana cike da alhini da saduda da damuwa.
Na daure na ce." Maryam ba kai kadai ta cutar ba my love har da ni fa."
Ya yi saurin kallona kafin ya gyara zamansa ya riko hannuna yana murzawa ya furta." Shiyasa ai kullum idan na yi sallah nake neman sakayya a wajan Ubangiji ta cuce ni Amina idan na gaza miki ta wannan fannin zan k'wareki kawaici da hak'urinki zai k'are nasan watarana za ki nemi hanyar rabuwa da ni saboda rashin samun wani babban lamari wanda ya tasirantu da gangar jikinki."
Na ce." Haba dai ka daina yin wannan tunanin in sha Allahu rabbi zaka samu lafiya ka ma fi da k'arfi da mazantaka kamar yadda malamin nan ya fad'a kai dai mu cigaba da yin maganin sau'ki zai zo in sha Allahu."
Rungume ni ya yi sosai a jikinsa yana fad'in." Na gode sosai matata tuntuni na gama sheda cewa soyayyar gaskiya ki ke yi mini amma ba na jin dad'i a cikin raina a duk lokacin da na nemi ki na gaza kawar miki da bukatarki hankalina na tashi ina kuma tausaya miki a cikin zuciyata."
Cikin dauriya na ce." Babu komai fa kada ka tayar da hankalinka ina tare da kai duk rintsi in sha Allahu."
Ya sake matse ni tsam-tsam yana sauke ajiyar zuciya tare da sumbatar wuyana kamar dai koyaushe. Yana d'an yamutsa wasu wuraran na jikina.
Na janye a hankali Ina kallonsa yanayinsa ya canza sosai wanda yake nuna zallar buk'ata.
Ya dinga sauke nishi a hankali a hankali Ina kallonsa ya mike babu wani karsashi a tare da shi ya tafi ya je ya kwanta a gado. Yadda alamu suka nuna wannan shara'din da aka gindaya ya yi masa tsauri Allah kuma ya sanya ya iya jurewa zuwa sati dayan........✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*138*
To a daddafe dai ya iya bari wa'adin da Malam 'Daha ya gindaya ya cika. Ranar da maganin ya k'are kamar ya zuba a ruwa a k'asa ya sha saboda murna abin ya dinga ba ni da dariya da mamakin yadda gabad'aya ya manta da cewar ba ni kadai ba ce matarsa akwai wata wadda son rai da rashin hakuri ya sanya yake take mata hakkinta. Yanzu tun ina jin haushin Hauwa wallahi ta fara ba ni tausayi domin kuwa tun daga ranar da yaron nan Sultan ya suma ta yi bala'in sanyi take neman shiri da ni kuma yanzu takan fito falo ta zauna idan ta ji motsinmu da yara da masu aikin ana wasa da dariya sai ta fito ta zauna tana bin mu da kallo tana d'an murmushi har idan an yi magana ta tsoma baki amma dai duk da hakan yaran nahiyar da take zaune basa kallo balle ma su je wurinta ta dinga jan Usai kenan da wasa ita kuma tana nok'ewa tare da zum'bura baki nata yaran Khalil da Minal bata yi musu magana balle kuma Sultan da baya son ganinta ko zama ta yi idan yana wasa sai ya rarrafa ya nufi wajen uwar rainonsa abin yana yi mata ciwo sosai. Amma babu yadda za ta yi haka gobe ma idan ta ji mu da yaran za ta sake fitowa.
A yau din ne da wa'adin ya cika kwanan turaka ya dawo hannunta duk da na lura duk ranar girkinta bata hawa saman yau kuma tun safe naga tana kai wa da kawo wa a falon ta hau saman har sau biyu. Sai na ji dadin hakan a cikin raina duk dai har yanzu ina jin tsoron kaidinta amma dai zan fi so su shirya su daina zaman gaba da k'ullatar juna tunda tuntuni sun riga sun zama abu daya.
Ban sani ba ko sun sasanta bai nuna mini alamar hakan ba tunda ai namiji ne yau zai ce baya son abu gobe kuma ya canza ya ce yana so kuma itama macace tana da nata dabarun na janyo hankali.
Na so dai a ce a yau din da yake ta gand'okin yin jima'i ya jarraba a kaina domin fita daga kokwanto da samun kwanciyar hankali dan gaskiya damuwarsa ce kawai ta fito fili sai nake ganin na fi shi damuwa kawai ina dannewa ne.
Kwalliya ta yi sosai da yamma nuna tare da yaran a falo da yake Juma'a ce suna hutun makaranta ta fito ta dan zauna cikin mu na kamar minti talatin wajan biyar da arba'in ta haye saman tun daga lokacin ba ta sakko ba har da dare ya shigo na tashi na nufi d'akina domin gabatar da sallar magriba.
Na gama lazimina na dan jingina jikin gado zuciyata na d'an harbawa kad'an sai na tsinci kaina da shiga damuwa. Na sake rintse idona da k'arfi ina kiran sunan Allah ba ni so kishi ya jefa mini son rai a zuciyata idan har da adalci ya kamata a ce na bashi goyon baya wajan ganin ya yi hakuri sun sasanta junansu. kuma daidai gwargwado ta yi hakuri ta jure kuma alamu ya nuna ta zubar da makaman ya'kinta neman shiri take yi ta sigogi da yawa. Amma dai duk da haka na so a ce yau din a yi gwajin a kaina ko don samun nutsuwar zuciya.
Sai da na yi sallar Isha'i tukkuna na ci abinci. Na samu waje na kwanta da wayata a hannu Ina d'an duba What'sapp dina amma dai still can kasan zuciyata sai dokawa yake yi ina mamakin ganin bai kira ni a waya ya nemi abinci ba kamar yadda yake yi idan ya dawo daga sallar isha'i wata zuciyar ta ce mini wata'kila bai shigo ba har yanzu shiyasa. Na girgiza kai ba na tsammanin hakan domin da ya yi sallar Isha'i yake shigowa sai da babban dalili yake sake fita idan ya ci abinci yakan dan duba Loptop din shi har zuwa goma na dare ko sha daya gaskiya ya shigo.
Ko dama murnar da yake yi kenan tunda sun jima ba su had'u ba dole ya yi marmarinta ya nuna gandoki. Idan kuma na tuna irin lugwigwitar da jikina ya sha a hannunsa a tsukin kwanakin da suka kasance na shara'din sai jikina ya yi sanyi na kasa gazgata kowane sashe na zuciya.
"Na gaya miki fa Hauwa na daina kwanciya dake saboda wannan dalilin na ji dad'i dake na dare daya ki dasa mini b'akinciki na shekara goma. Ban had'a shimfida dake ba balle ki d'auki ciki ki haife mu yi fad'a ki dire mini yaro ko yarinya ki tafi gidanku wannan shine hujjata." Ya yi maganar cikin kwanciyar hankali
A raunane ta ce." To yanzu ya kake so na yi na kai geji na rantse da zatin Allah ji nake yi kamar zan yi hauka a tsananin buk'ace nake rayuwata za ta shiga matsala."
A nutse ya furta." Ba ki yarda da hujjata ba kenan. Ba fa zan yi ba na gaya miki ki tashi ki fita kina 'bata mini lokaci zan yi aiki."
"Dan girman Allah ka yi hakuri kada ka jefa rayuwata a wani hali."
Ya dubeta sosai yana fad'in." Kin ga na yi miki kama da wanda zaki karyawa rantsuwa Hauwa?"
Ta girgiza kanta cike da damuwa."
Ya ce." Ba zan yi kaffara akan ki ba, ki tashi ki ba ni waje idan kuma za ki iya yi mini fyade Bismillah."
Tana kuka sosai ta furta." Allah mai ji ne da gani, kana zalintata kana tauye mini hakkina na rayuwar yau da gobe ba zan yi maka fyade ba amma sai Allah Ya saka mini tunda ni ba mazinaciya ba ce balle na je na nemi wani kai kuma kana yi da matarka kuna gamsar da juna hakkina ba zai barku ba wallahi."
Dariya ya kama yi yana kallonta kafin ya ce." Ke ni fa ba wata lafiya na cika ba yanzu idan ma za ki daina shiga 'kunci akan ban kwanta dake ba itama Amina ha'kuri take yi Maryam ta kassara ni da asirinta.
Cikin rashin yarda da maganarsa ta furta." Wallahi ban yarda ba ai dama can haka ka ke yi mini ka jima kana zalintata sai Allah Ya saka mini."
A gajarce ya ce." Ni ma Allah Ya saka mini."
Ta tashi tare da kama hanyar fita ya bi ta da kallo ko daya bai tausaya mata ba domin ji yake yi har yanzu bai gama goge takaicin da ta cusa masa ba a baya.
Da asubahi ban kai ga tashi daga dadduma ba ya shigo da jallabiya da carbi tabbacin daga massalaci ya fito. Muka gaisa ya nemi gefan gadona ya zauna har da cire jallabiyar ya ajiye. Na ninke dadduma na ajiyeta a wajenta na zauna ina kallonsa a nutse na ce." Kwana biyu da suka wuce mun yi waya da anti Yagana tana gaya mini Dada bata da lafiya don har kwanciya ta yi a asibiti."
Da alhini ya ce." Me ya same ta?"
Na ce." Ciwon wuya ta yi amma dai da sauki an sallamota daga asibiti ina son zuwa dubata."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ban 'ki zuwan ba amma legos nake so ki shirya mu tafi cikin satin nan da zamu shiga."
Na ce." Da dai ka d'auke mini zuwa legos din nan tun da kaga a halin da nake ciki ya kamata na zauna waje d'aya na samu nutsuwa ku je da Hauwa kawai."
Ya d'an Harare ni kafin ya ce." Dake zan je Hajiya ba wani dadewa za mu yi ba in sha Allahu mu dawo cikin yaranmu mu je mu huta ni dake na wata d'aya sannan akwai ayyukan da nake so na gabatar a can din."
Shiru na yi ina kallonsa tare da raya abubuwa da yawa na yi masa maganar Hauwa yana hararata kuma bayan tare suka kwana nuna mini yake yi har yanzu ba su daidaita ba.
Ya ri'ke hannuna yana d'an janyo ni jikinsa yana cewa." Jiya me yasa ba ki zo ba?"
Na ce."Me yasa zan zo? Don girman Allah ka daina wasa da tunaninmu yanzu don ka sasanta da Hauwa shine abin yi mini boye-boye na fi kowa farincikin hakan wallahi."
Ya fara ko'karin cire mini hijabin jikina yana fad'in." Ni na gaya miki haka Amina kada ki yi mini rigima a irin wannan lokacin da nake tsananin kewa da bukatarki kada ki yi abinda zai dakusar da farinciki da karsashina my love.."
Ya fara sumbatar sasssan jikina a mutukar dimauce yana yin wani irin numfashi bakina ya mutu murus domin abinda jikina yake marari ne ya samu da na yi yun'kurin yin magana da turjiya sai na ji bakina ya yi nauyi bayan sa'kkonin soyayyar da yake aika mini ta kowace ga'ba. Bakinsa ma amayarwa yake yi tare da wata irin sheshsheka haka muka kasance cikin ru'kun'kumar juna zuciyata na ta tsalle ido a lumshe can kasan zuciyata ina ta kiran sunan Allah da ro'kon Allah wanzar da alheri akan abinda za mu yi Ubangiji maji ro'kon bayinsa wata iriyar rayuwa muka yi wadda ta ki'dimar da mu. Kuzuri da nagarta da mazantaka abin sai godiyar Allah da sake jaddada addu'a ga Malam D'aha da zuri'arsa kamar yadda ya fad'a mun ga zahiri domin kuwa