Showing 72001 words to 75000 words out of 99881 words

Chapter 25 - AMEENATOU COMPLETE

Mamuhgee   

30 Aug 2026

241

bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

[3/7, 7:04 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*

43

A cikin murya me nutsuwa Kai tsaye ya gaidasu Dad din acikin

jam'i batareda ya Bada amsar maganarda Dad Lameenu ya jefesa da ita ba ta farko.

Dayake dukkaninsu kowa da abinda yake bakinsa na maganar Dake cinsu Basu tantance sauyin muryanba Wanda Daman Shima Haroon idan jikinsa na Sanyaye muryansa a natse da sany

i take fita Dan haka Babu Wanda ya tsaya amsa gaisuwan bare tambayar ya jikinsa Kai tsaye Dad dayaji Baya iya kallansa Dan yau din cika masa ido Haroon keyi sbd kamanninsa da Jamaal sun tsananta ayau dayake ganinsa kaman Jamaal Dan haka batareda y kallesa

ba murya a daure da bacin ran abinda yayi yace

"Ko zaka bani dalilanka Daya Saka bawa project dinmu da ma'aikatan aikinsa Hutu harna kwana uku batareda sanar damu meyake faruwa ba??

Numfashi me sanyi ya sauke Yana dauke idanuwansa daga kallansu kafin

ya Tako ahankali dukkaninsu sukai saurin kallansa ganin ya tinkarosu Yana kallansu Dad Lameenu ne yayi saurin cewa

"Amsar abinda yake faruwa muke buqatan Dani sbd Haroon Banga alamar zaka cika alkawarin daka dauka ba na sakamu alfahari dakai,

Aikin Na

n fa duka duka sauran sati uku ne a time dinsa ya cika,.

Dad kallansa ya sake yi Yana Jin zuciyarsa na son shiga tinani daban daban Amma ya watsar Yana cewa

"Karka manta nutsuwanka akan aikin Nan shine tabbatan aurenka Dan Neman aure ba shine aurenba

Karka manta da Hakan Dan nakai maquran rashin nutsuwan Nan taka,

A Hakan kake Neman mutuwa sbd mace kanason kayi aure batareda kasan ciwon kanka ba bare tinanin tsayuwa ka zama abin alfahari ga iyayenka ba tayaya zaka tsayu ka zama abinda matarka ko ya

yanka zasuyi alfahi dashi....

Dakatawa Jamaal yayi daga inda yake tsaye tareda dago idanuwansa da sukai ja ya Kalli Dad din dashi ma shi ya Dan kalla Yana cewa

"Yes, Haroon haryanxu ka kasa sakani farin cikin Da kowannen Uba yake shiga akan yayansa d

a alfahari dasu,

Alkawari nayi Maka akan idan kasakani farin ciki akan wannan aikin zan nema Maka auren da kakeso Amma......

Katsesa Jamaal yayi Dan bazai iya tsayawa sauraron wainnan maganganun akan Dan uwansa ba komai zai iya faruwa Dan zai iya bayya

narda kansa Dan haka wayarsa ya daga ya kira siddeeq take siddeeq ya shigo da takardun komai dasuka gama a yau din ya karba daga hannun siddeeq ya ajiye gaban Dad din Yana kallansa yace

"Gashinan Alkawarin zan cika Maka acikin kwanakin da bazasu kai na

cikan kwanakin ba Amma Kuma a ranar da komai ya tabbata a yanda kakesonsa a ranar nakeson a daura mun auren da yarinyar....."

Daga dad har Dad Lameenu sakin Baki suke kokarin yi gurin kallansa da mamaki hankalinsu na rabuwa biyu daga abinda ya fada da K

uma karanta takardun Daya zuba a gabansu suna karantawa cikin tsananin mamakin sabuwar project din data dawo musu Da cikakkiyar damansu a hannunsu.

Dad Lameenu Daya kasa Kai karshen takardan cikin farin cikinsa Daya mantar dashi mamakin dasuka shiga yac

e

"Nayi Maka alkawarin daura Maka auren Ameenatou a washe garin ranar da Akai bikin Budewa duniya wannan aikin project dinnan Haroon idan abinda nake Gani da suna SEELAHs a jikin takardan Nan ya bayyana.

Dad ma mamakin ne yayi mugun kashesa kafin ida

nuwansa su sauka kan signature din jamaal Dake karshe wayarsa tayi ringing daga turawansu na Abujan ne Yana dauke idonsa Akai siddeeq ya matso Yana rufe file din tareda amsar masa cikin girmamawa Dan basa Daman amsa wayan wadda ta Saka Dad Lameenu washe du

kkanin bakinsa cikin tsananin farin ciki Yana sake tabbatarwa da Haroon zuwa wani sati zai tabbatarda Abdul yayo parking da familynsa sun iso Lagos din gaba Daya.

Wayar da Dad keyi ta sakashi Shima dukkanin farin cikinsa bayyana Yana washe Baki Yana way

ar cikin turanci Dan nutsuwa Yana Kuma Basu tabbacin wannan Karan Inshallah komai zai tafi daidai Nan da 3 zuwa 4 weeks komai ya zama cikin Shirin bikin qaddamarwa.

Dad na gama wayar Haroon din ya kalla cikeda farin ciki yace

"For the first time da y

au nake alfahari dakai Son"

Kalman zafafa zuciyar JAMAAL tayi Dan haka baice komaiba sai sake fuska da yayi ya amshi zancen Dan kawai da zargi.

Buga kofar Akai kafin aka Bude tareda shigowa

BB ne Wanda duk kwakwalwansa take Neman Juyewa sbd ba dar

e ba Rana a bincike da yawon garuruwa suke da kauyuka gurin Neman da haryanxu Babu me baccin arziki akansa tsakanin shi dasu Mam din.

Tinda yake a rayuwansa wannan shine aiki mafi wahalan dayakesha mara sauko ko kadan a duk shekarun Nan,

Shi kansa sbd

baqar wahalan dasuke Sha a wannan aikin yakejin bazai taba samun nutsuwa ko Kwanciyar hankali ba matiqar ba Gano abinda suke Neman sukaiba kaman yanda yasan har abada uwayen gidan nasa bazasu taba samun baccin nutsuwa da Kwanciyar hankali ba idan ba burins

u na shekarun cika yayi ba.

Cikin girmamawa yace

"Sir Haroon barka da dawowa"

Batareda Jamaal ya amsa ba Dad Lameenu ya Kalli siddeeq Wanda Shima Kai tsaye ya juya daga office din ya fice tareda Turo musu kofar.

iPad din hannunsa ya ajiye gaban

su tareda bayanan daya samo akan bincikensu ya fara da cewa

"Ranka ya Dade na samu tabbacin 'yayan matar sir Omar Daya gudu da abinda ta haifa a daren yanada nasa 'yayan guda biyu Kuma dukkaninsu Maza ne sedai Kuma matarsa an bani tabbacin kafin barinsu

gombe a wancan lokacin ta haihu Wanda nakeda tabbacin ba haihuwa tayi ba babyn sir Omar dinne"

Cikin zaquwa Dad Lameenu yace

"Bayanin inda suke shine babban abinda muke buqatan Jin idan an samo"

Hakama Menene asalin abinda aka haifa din?

Mace ne

ko namiji??

Hakurina da bugawan zuciya akan wannan lamarin ya kusa kamani BB a gaggauta samo mana inda suke sbd tashin aikinmu yau da aka samu shi kadai bazai riqe mana matsayinmu da tsagwaran dukiyar da muka rasa ba muna tsananin buqatan dukiyarmu Dake

hannun Omar.

Dad da Shima abinda yake ransa kenan ya Kalli Haroon dayake tsaye har lokacin gabansu Yana kallan fuskokinsu da bakinsu yace

"Haroon ya qara muku kudin Daya kamata banason aurensa yazo duk tsanani duk wuya batareda an samo mana inda suk

e ba,

Idan Kuma bamu samo Hakan ba to tabbas lokacin zuwansa garemu yayi Dan bazai taba yiyuwaba ayi auren 'dana dayake matsayin dansa batareda yazo ba,

Zuwansa Nigeria kuwa ba abune da zai taba yiyuwaba yazo ya tafi batareda ya kaiwa abinda ya Haifa d

a cikinsa ziyara ba Wanda shi da kansa zai kaimu ga Magajinsa batareda ya saniba.

Kallan Haroon ya sake yi Yana sake cewa

"Ka Basu duk adadin kudaden da suke buqata kaje ka fara Shirin aurenka Dan daga lokacinda Omar ya sauka a Nigeria dukkanin motsi

nsa a tafin hannunmu zai zama."

Gyara Kai Jamaal yayi Yana kallan BB dayakejin bazai iya barinsa ya sake ahakan iskan yanci ko Daya ba Amma Kuma Yana buqatan sanin abinda yake faruwa kafin komai Dan kuwa zantukansu sun Saka kansa daukan zafi.

Gyada K

ai BB yayi Yana Jin nutsuwa da farin cikin Suma wahalallen burinsu ze Kai karshe sbd a saukake ma auren Haroon din zai kawo Omar har gida Kuma zuwansa kaman bayyanar abinda yake boye ne.

Maganganun sauran ayyukansu dasu BB din keyi ne suka fara Kai tsay

e tareda tambayan huldan datake hannun BB din da yaransa ya tabbatar musu da komai Yana tafiya lafiya kalau duk da an kama wasu yaransa Amma ya tura yaronsa Daya Daya bari aka kamasa aka Saka cikinsu Sbd ya hanasu fadan komai sedai aka wayi gari sun rasu d

ukansu su biyu sai shi Dayan yaron nasa sun fito dashi Dan haka Babu matsala Tako ina.

Juyawa Jamaal yayi ya fito idanuwansa basa ganin gabansa sosai sbd Ja da tashin hankalin Daya tsinci kunnuwansa daji batareda ya tsaya jin sauran abubuwan da hankalin

sa yake Neman kasa dauka duk da ya Dade da sanin ba imani a lamarinsu Dad bare tausayi sbd abinda sukaiwa fadila da har yanzu baida sheda ko tabbacin sune sukai Amma ayau da kunnuwansa Yana Jin abubuwan da baisan tayaya ma zaace sune suke aikatawanba,

H

aroon ya San dukkanin wannan abin dayake faruwa kenan ya boye masa tinda gashi suna maganar a gabansa batareda sanin ba Haroon dinne ba.

Yana fitowa Kai tsaye mota ya nufa Yana miqawa siddeeq hannu ya basa key batareda ya Juyaba,

Kirjinsa yake Jin ya t

oshe masa Babu iska ko kadan Babu abinda yake buqatan so kaman ya fita daga Mansion din.

Siddeeq na ganin Hakan ya miqa masa key din motar Haroon Daya fito dashi Dan fitarsu idan sun gama.

Saida siddeeq ya nuna masa motar ya nufi inda take tin kafin

ya Isa ya Budeta Yana Isa shiga kawai yayi ya tayar da reverse ya fice daga Mansion din Yana saukar da duka glasses din motar sbd iska ta shigesa.

Yana ficewa siddeeq ya Ciro wayarsa Yana shakkar abinda ya faru daga cikin office din Amma dai koma Menene

Haroon Yana buqatan sani Dan dawowa sbd ansamu matsala ga dukkanin alama.

Su Dad kuwa farin ciki da zaquwan auren ne gaban Daya ya mamayesu sbd ga dukkanin alama sanadiyar auren zasu samu abubuwa da dama dasuke so suke fata,

Haroon ya fara zama abin A

lfaharin da zai sake fitar da sunan seelahs da tsayuwarsu hakama dawowan Omar dasuke fata ta sanadin auren da dole zaizo ko Dan Yan jarida dazasu yada maganar auren koina da rashin zuwansa auren 'dan farko da zaayi a Seelahs din tinda na Jamaal kaman auren

boye ne da ba kowa ya saniba Amma wannan da kansu zasu Kai masa gayyata ta musamman da matsayin zamansa wakilin ango da zai karba auren da hannunsa.

******Haroon dayake tareda mahaifiyarsa tana jinyarsa cikin tsananin so da kauna da kulawa tareda tatta

li Jin yayi zuciyarsa ta karaya Da yanda tin farko ya zabi mahaifinsa akan mahaifiyarsa,

Bata taba nuna masa banbanci tsakaninsa da Jamaal ba sedai shine Karan kansa ya zabi mahaifinsa akanta sbd sonsa dayakeji cikin ransa fiyeda komai.

#MAMUH#

*_

ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_

Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA

ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

[3/7, 7:04 PM] MG:

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

44

Mum Aleena datake Jin batason sake rabuwa da 'danta sbd halinda yake ciki na tsananin buqatan kulawansu dan sai sunyi da gaske zasu iya rabasa da depression din Daya kamasa,

Drug kuwa da suka samu a jininsa Basu sanar masa

ba itada Jamaal sbd sunason tantance shine yake Sha da kansa kokuwa sbd sun kasa yadda ko sanin tayaya zai zama Yana Shan kwayoyi irin wainnan.

Siddeeq Kuma ya tabbatar musu da Babu kwayoyi mayen ko makamancin Hakan da Haroon yake Sha Amma Kuma duba da

depression dayake ciki da tsananin matsi a Hannunsu Dad zai iya samun kansa da Shan kwayoyin Dan samun fita hayyaci ya Dena Jin komai.

Tin daga ranar da Haroon din ya taho aranar ya ringa yiwa mum din kuka kaman karamin yaro cikin ciwo da tsananin buqat

an again Dan uwansa akan bayason rasa Ameenatou kaman yanda ya rasa fadila,

Shi a yanzu ba yabon mahaifinsa yake nema ba Ameenatou kawai yakeso a rayuwarsa.

A gaban Mahaifiyarsu Jamaal ya Sakasa sukaiwa juna alkawari.

Idan Haroon yayi masa alkawarin

dawowa ga mahaifiyarsa Dan samun lafiyansa da rayuwar nutsuwa da Kwanciyar tare Kuma da cika burin Mum dinsu na ganin yayanta duka biyu a tareda ita to shi Kuma yayi alkawarin zuwa ya gyaro dukkanin abinda Haroon yakeso Dan samun yabo daga Dad dinsa da Ku

ma zama abin alfaharinsa tareda tabbatar da aurensa da yarinyar Amma ana daura auren zasu taho tare.

A daidai wanna gaban Babu abinda Haroon bazai iya yiba akan samun Ameenatou da samun nutsuwan zuciyansa data Dan uwansa da mum Dan haka ya amince da daw

owa cikinsu gaba Daya bayan auren take mum ta rungumesa cikin farin ciki da Jin dadi sosai tana Jin kaman tinda ta haifesa sai yanzu ne zata samu zaman datakeson yi da 'danta hakama zata kaman yanda ta kaunaci fadila take taji tana kaunan Ameenatou har cik

in ranta duk da Bata taba ganinta ba Amma tayi masa alkawarin inshallah da ita zaayi aurensa.

Daman ba wani zama zasuyi a Poland dinba Nigeria zasu taho sbd bikin auren Da Haroon din kwata kwata yaji Baya son a dauko lokaci ayi kawai ya tahowansa kusada

mahaifiyansa Dan haka sauki kawai sukeson ya Dan samu su taho saiga Kiran siddeeq Wanda ya sakashi shiga fargaba da tsoron abinda Jamaal yaji Dan haka shine ya dagawa mum hankalin komawansa baima jirata ba washe garin ranar ya Siya ticket dinsa ya tahowan

sa Dan bayason abinda zai janyo fushin Jamaal ya lalata masa komai adaidai lokacinda ake gap da samun abinda yakeso.

Jamaal kuwa a ranar Bai kwana a Lagos ba ya wuce Abuja tareda siddeeq ko su Dad din Basu saniba Dan idan Yana ganinsu zuciyarsa kasa riq

e koshi waye din takeyi gwara ya tafi ya Jira zuwan Haroon Daya San duk inda yake idan har baida gaskia Yana hanyar dawowa.

Kwana Daya saiga Haroon din ya diro Amma Bai yadda ya Hadu da Jamaal din ba Kai tsaye Nasarawa ya wuce sbd bayason suyi hayaniya

Kuma baisan Menene yaji bama tukuna bare yasan ta inda zai fara.

Da yamma sosai ya iso Dan haka wanka da sallah kawai yayi Bai tsaye komaiba ya wuce gidan Babbah.

Zaune suke a tsakar gidan sai lallabata dadah keyi sbd taqi Shan magani daga ciwon Kai

zazzabi ya maqale kwana biyu anata fama da ita.

Zuwansa ya Saka Abdul sakin ajiyan zuciya hakama Hafiz Babbah Baya Nan

cikin sakewan fuska da nutsuwa ya qaraso Hafiz na janyo masa kujeran zama Yana masa barka da zuwa.

Yaya Abdul ya fara bawa hannu

suka gaisa cikin tsananin kulawa Yana tambayarsa kwana biyu ko numbernta Baya shiga.

Murmushi ya sake Yana cewa aikin dayake gabansa ne ya sakashi kashe dukkanin wayoyinsa sbd aikin ya koma babba fiyeda yanda suke tsammani.

Gurin dadah ya Maida kalla

nsa Yana gaidata cikeda girmamawa da kulawa kafin idanuwansa suka koma kan Ameenatoun Dake zaune sanye da Riga da wando na bacci ko hula Babu a kanta ko inda yake Bata juyo ta kalla ba maganinta take kokarin Sha tana kasawa sbd batason magani ko kadan.

Hafiz Dayafi kowa shiga damuwan bayan Ameenatou tambayarsa siddeeq yayi suna sake shiga wata firar Amma gaba Daya hankalinsa na kan Ameenatou da yayi magana tayi masa shiru kaman Bata ji ba Kuma kowa yasan ta jisa Daman sun San sai anyi Hakan.

Dadah ce

ta Dan rarrasheta tana cewa

"Budurwa bakiji ana Miki ya jiki bane?

Duka fushin bana rashin kiransa da zuwan bane gashinan ai ya taho saiki sauko,

Yi masa hakuri kinji¿

Maganin ta daga duka ta Saka a bakinta tareda binsa da ruwa ta shanye batareda m

a tasan tayi Hakan ba sbd fushin Daya taso mata.

Tinda ta fara zazzabin ko ruwa Se ta Saka anbata ko hulan kanta Bata iya sakawa sai an Saka mata sai gashi ta miqe tsaye da kanta ta wuce dakinta tana cewa bacci zatayi.

Hafiz ne ya Bude Baki yace

"

Ke meye haka wai?

Inace Wanda ake fushi da ciwon akansa gashinan yazo,Kuma Ashe Zaki iya tashi da kanki kika ringa wahalar Dani da Dadah tin jiya ko bacci na fara saita kirani na kawo mata ruwa Ashe tsaban rashin tausayi ne to Zaki San dawa kikai."

Tan

a jinsa Bata ce komaiba saima hararan kofar datai tana Jin zafin abinda yayi mata ranar Yana dawo mata.

Dadah murmushi ta sake tana sake tambayarsa nasa jikin ya amsa mata sbd yasan halin mutuniyar sarai basai an tsaya basa hakurin abinda tayin ba,

Abd

ul ma sake tambayar jikin da aikinsa yayi kafin suka fada firar tafiyansa Lagos gobe zuwa nxt week Kuma su dadah ma zasu taho duk da ba zuwan kenan ba zadai suje suga inda Allah ya Kaisa dasu.

Duk firar dayaketa yi hankalinsa na kan kofan dakinta Amma S

am taqi yadda ko motsi tayi yaji dadi Bare fitowa.

Sallan magrib suka fita sukayo suka dawo gidan tareda Babbah daya masa ya jikin da fadan rashin Kiran tinda koyayane Daya samu ko mintina bibbiyu a wuni ya ware ya kira din zasuji dadi itama me fushin d

a bataiba.

Gashi tanata fushi da maimaita shariyan dayayi mata.

Hakuri ya bawa Babbah har suka shiga wata firar inda Babbah din ya sanar masa su Alh Lameenu sun kira akan maganar auren sukeson ta taso ayita kusa tinda dai ba amfanin jiran ko tsaiko.

Har cikin ransa yaji farin ciki Yana mamayesa sedai Kuma fushin da Ameenatou keyi me zafi akansa Yana cin zuciyarsa sbd yasan Jamaal ne yayi mata koma Menene Dan haka Shima take yaji Yana buqatan ganinsa Dan haka anan yayi sallar ishai yaci abinci suna ga

mawa harya fito Bata fito a dakinba Kuma babbah ya Hana kowa takurata fitowa saita huce da kanta taji ta hakura tukuna.

Yana fitowa da wayar hannunsa ya kira layinsa dayake hannun jamaal Amma Jamaal din yaqi dauka sbd Shima Yana sane da Haroon din ya da

wo guje masa yayi.

Kiran dayake yi Jamaal yaqi dagawa ya Sakasa dawowa hayyacinsa akan abinda yake jiransa Dan haka dole ya shirya tinda safe ya nufi Abuja.

Koda ya Isa Jamaal din Yana bacci Dan haka siddeeq na ganinsa ya saki murmushi Mai hade da sa

kewa Yana masa barka da dawowa.

Kallan hanyar stairs na Hawa sama yayi kafin ya dawo da kallansa kan siddeeq din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login