Showing 6001 words to 9000 words out of 38678 words

Chapter 3 - RANA DAYA BOOK1 COMPLETE

11 Nov 2026

5

cire ta.”

Ya kalli Mahaifin nashi wanda bai ce kala ba tun da suka soma magana.

Ya ce, “Alhaji ba ka ce komai ba?” Ya ce, “Ba ni da ta cewa Shatima, duk abin da yafi alkhairi Allah Ya zaba, tunda ka samu daurin gindin Tsohuwa a ta gefena ka kai makura.

Shatima ya yi murmushin nasara a ta wannan gefen. Hajiyar ta ce, “Ka je kayi tunan

i nan da jibi.” Shatima ya mike cikin rangaji tare da fadin “Badi atu ta kawo min abinci Hajiya.”

**

Tunda Kaka taji sallama tare da kamshin kalolin abinci ta tabbatar cewa Hajiya Halima ta diro gidan, domin wannan ita ce shaidar farko da take fara ala

mta mata cewa Surukar arziki ta shigo gidan.

Ta fito daga cikin dakinta tana dogara ‘yar sandarta mai kyau, wadda ta ke taimaka ma kafafunta wadanda suka yi rauni.

Ta amsa sallamar cikin murna, ta zo ta zauna kan kujera. Hajiya Halima ta zauna kasa kan k

afet. Badi’a da Maryama suka shiga jere kulolin da Hajiya Halimar ta zo da su.

Suka sake fita suka shigo da sauran. Kaka ta ce, “Ba ki gajiya Hajiya Halima, kowane lokacin in za’a zo duba ni sai an zo min da abin tabawa. Allah Ubangiji yasa ke ma ‘ya’yank

i suyi miki. Ga jarumin namiji nan Shatima, cikin matansa Allah zai sa wata ta miki fiye da abin da ki ke min.

Hajiya Halima tayi murmushi bata amsa ba don nuna kara ga uwar mijin tata.

Bayan sun gaisa ne suka shiga hirar duniya, Badi’atu autar Hajiya Ha

lima, da Maryam yar gidan Hajiya Saude kanwar Baban su Shatima wadda ke gaban Kaka, sun kule a daki suna tasu hirar.

Hajiya Halima ta kalli Kaka ta ce, “Hajiya sai kuma wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake

yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi

daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun

ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce,

“Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.”

Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min

faten sai ki

sa farfesun kafar Sa din a ciki.”_____

*

🏚

️

RANA DAYA

🏚

️

*

CHAPTER 4

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427*

*08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*

*Ka

yan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*1 Gumbar kankana da ayu*

🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*

🍀🍀

4 *Kaza mekwai*

🍀🍀

5 *Zabo me zuma*

🍀

🍀

6 *Kaza me allurai

🍀🍀

sahihiyar mallaka ba boka ba malam*

🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*

🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*

🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa

indai matsalar sanyice gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi*

12 *Maganin hips and bobbs*

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da maz

ajensu Kevin Mata*

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*





🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan*

*takawomuku

hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀



Mun tsaya

wannan mashirmancin ya zo da zancen zai

auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi

daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun

ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba

, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.”

Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “

To fa! Duk a cikina? To zubo min

faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.”



zubo mata ta bata sannan ta kwala ma Badi’atu kira, suka fito. Ta ce, “Ku je ku kawo ma Hajiya ruwa, sannan

ku zo ku kwashe kulolin nan zuwa kicin.” Suka ce, “To.”

Sai

da Kaka tayi nak! Ta koshi, sannan ta kalli Hajiya Halima.

“Zancen Shatima, ina son ki cire rashin yardarki da kin amincewarki, ki aje su a gefe. Ki bi da ido, sannan ki hada da addu’a.

Shatima gwarzo ne ba irin mazanku ba, mutum ya zauna da mace daya k

amar fasto.” Ta gyara zama sannan ta ci gaba, “Yanzu bari in yi miki wani lissafi, mata nawa Maigidanmu ya aura? Nasan kin samu labari mu hudu ne ko?”

Hajiya Halima ta daga kai alamun “Eh.” Ta ci gaba da cewa, “Kowace mace ta haifi ‘ya’ya da yawa, babbarm

u tana da goma sha daya, mai bin ta na da takwas, wadda ni ke bi tana da goma, cikinmu ni ce kadai me ‘ya’ya hudu.

Babban

ṣ

u ya kwanta ya mutu shekara biyu kenan, matarsa na nan a Kaduna da ‘ya’ya biyar. Ke naki mijin ‘ya’yanku uku daga shi Shatima sai Mu

stapha, sai ko Badi’atu, sai dan uwansa Baban Nafisa.

Suma su uku ‘ya’yansu duka mata, Nafisa da

kannenta biyu. Saude ce ma me ‘ya’ya shida har

na samu aka bani Maryama. Tattara ki kirga min

jikokin nawa duk guda nawa ne?

Ta dafa kirjinta tare da fadi

n “Ni fa nan da ki

ka ganni yanda Allah Ya halicce ni ina son zuri’a,

naso a ce cikin ‘ya’ya mazan nan guda uku da

Allah Ya bani naso in samu wanda zai gaji

Babansu a ‘ya’ya, don sai da ya bar talatin da

uku a duniya.

Kuma Alhamdulillahi kin dai

san komai ba sai

na fada miki ba, cikin ‘ya’yan nan babu mai irin

mukamin da babu. Akwai Soja, akwai Dansanda,

ga yan kasuwa, ga Malamai na duka bangare

biyun boko da Islamiya.

Ga Sarakuna duk da dai wannan gado ne, don

haka ina son ki bi Shatima da

addu’a don ina ga

shi ne zai zama magajin Kakanshi, dama sunansu

daya. Ina so ki sa masa albarka a cikin duk

lamuranki.”

Ba ta da zabin da ya wuce mika wuya don

tasan ma babu wani abu da zata fada har ya yi

tasiri. Don haka ta ce “To Hajiya, Allah Y

a shi

albarka, ya zaba abin da yafi zama alkairi.

Kaka ta ce, “Yauwa hali dubu rubutun dutse,

dama ni nasan ke komai naki cikin sauki ne da

fahimta, Allah Yayi miki albarka.

Hajiya Halima ta ce, “Amin. To amma Hajiya

an bincika sauran da ya ke son an

ji ya’yan asali

ne ko? Ta ce, “Ke dai ki kwantar da hankalinki,

komai na jan namiji daban ne, burinmu dai ki bishi da

addu a.Nafisa tana zaune a cikin lambun gidansu kan

kujera irin mai lilon nan, sanyi da kamshin lambun

yana kara ma zuciyarta nishad

i.

Ta lumshe ido tana kallon surar Shatima a

idonta, cikin shiga ta kasaita da kamshi. Gaskiya

tana matukar son Shatima har ma ba za ta iya

misalta son ba.

Tasa hannu ta dauki wayarta da ke kan cinyarta

ta bankado hotonsa wanda tasa Badi’atu ta tur

o

mata. Zuciyarta tana dadi in ta kalli fuskarshi.

Lallai za ta tura mishi sakon gaisuwar Juma’a

yanzun nan tun da yau take babbar rana. Message

ta shiga ta soma tura masa sako kamar haka:

Ya Allah Ya tsareka, Allah Ya tsare gabanka

da bayanka, ya da

ukaki rayuwarka. Ya sa ka

Cimma duk abin da ka ke nema.

Allah tsare idonka, da kunnenka, da ji da ganin

haram. Allah Yasa Aljanna ce makomarka.

Barka da Juma ‘a.

Ta karanta ya kai sau goma kafin ta runtse ido,

gabanta kuma yana faduwa ta tura masa.

A fili ta ce, “Allah kasa kar in yi da na sanin

tura sakon nan. Abin da ya bata mamaki kuma

bata yi tsammani ba shi ne, jin karar sako ya shigo

wayarta.

Bata ba tunaninta wahala ba, kawai ta yanke

hukunci cewa sakon daga shi ne Cikin nutsuwa ta

duba

ga abin da ya ce:

Zan shigo misalin karfe biyar ni da Aminina,

zan kasance cikin farin ciki in na same ki a gida.

Sannan abincin gidan Babana shi ne zai zama

abincin rana na a yau.

Ki húta lafiya.

Tayi ta maimaita karanta rubutun. Ta dai

fahimci yan

a nufin zai zo yau shi da abokinshi,

amma ba ta gane batun cin abinci ba. Ta ce a fili,

Bari in je gun Mama tayi min fassara.”

Uwar ta gama karanta sakon sannan ta saki

murmushi.

To in ba ki gane ba yau a nan gidan zai ci

abincin rana, nan ba gidan B

abanshi ba ne? Nafisa ta ce, Har nayi tunanin haka, sai kuma

na ce kila in yaci abincin rana a gidansu sannan

zai zo. To Mama yanzun me za’ayi masa kenan?

Ta ce, Ki binciko irin abincin da ya fi so mana

koda gurin Badi’atu ne.” Da sauri ta dauki wayart

a

ta nufi dakinta. Badi’atu ta kira tana tambayarta

irin abincin da Yaya Shatima yafi so. Kusan duk

abincin gargajiya yana so, amma babu kamar

burabisko.

Sosai tayi kwalliya ta fesa kalolin turaruka, ta

kame tana yawaita kallon agogo. Tsinken agogon

ya sauka kan digon da ke nunas biyar daidai,

kararrawar kofar falo tana bugawa.

Cikin dakinta ta shige da sauri kar ya soma

karo da kwalliyarta, ba birgewa ba ne. Hamida ta

ce, Yaya Nafisa in ba su ba nefa ki ka boye?

Ta ce, “Ke dai kije ki gani. Kun

nenta na gurin

taji Hamida na fadin “Sannun ku da zuwa. Sai da

Suka gaisa da Mama sannan ta ce Hamida ta kai su

lambu inda aka yi musu shimfida.

Ta ce, “Mami zo ki cema Yayarku ga su

Yayanku sun iso, sai ki je ki taimaka ma Hamida

ku kai musu abinci

.Cikin shadda doguwar riga mai ruwan goro ta nufi inda aka sauki bakinta. Tayi musu sallama

suka amsa, ita da shi suka kalli juna cikin ido. Tayi

murmushi tare da jan dan mayafinta ta rufe

fuskarta alamun kunya Sannan ta zauna a kusa da dayan tuntun wa

nda

ba a jingina da shi ba. tuntu uku aka saka a kan

kafet din da aka shimfida. Cikin girmamawa ta gaishe su. Ya ce, “Sunana

Muhammad Jafar Isa, lakabina Shatima. Wannan

abokina ne sunanshi Munnir Khamis, dukkanmu

muna aiki ne a karkashin Gwamnati. Na

zo gurinki

ne don ina son ki zama daya daga cikin matana. Da sauri ta dago ta dube shi, suka hada ido ya

sakar mata murmushi. Bakinki da magana amma ki fara gabatar

mana da kanki tukunna. Cikin’ son taja ra’ayinsa

da muryarta ta ce, “Sunana Nafisa Musa

Shátima

kuma ni daliba ce a Jami ar Ahmadu Bello da ke

nan Zariya.Ina cikin shekarata ta biyu. Sai dai abin da ban

fahimta ba shi ne, ka ce zan zama daya daga cikin

matanka, shin kana da wasu matan ne ko ko ya ya

abin yake?

Sallamar su Hamida ce ta

sa shi yin shiru. Suka

Aje kuloli da kofuna. Hamida ta dauki plate biyu

ta soma zuba musu burabisko.

Yace, Kanwata sa plate daya wa abokina, ni

matata ce zata sa min in gani ko ta san cikin

mijinta.

Nafisa ta amsa ta zuba mishi komai ta jere a

gaban

shi. Bayan tafiyar su Hamida ne, Shatima

suka soma cin abinci.

Matso ki ci tare da ni. Ya fada cikin

murmushi. Ta ce, “Ni naci tun lokacin da aka

gama. Ya ce, “Ba ke ki ka girka ba ke nan? Ta

ce, “Ni nayi, bai yi dadi ba ko?

Ya ce, Bari in gama tunda

babu kyau magana

in ana cin abinci.” Ta dafa hannuwanta “Bari in

tashi ku gama. Ya ce, “A’a zauna ina son ina cin

abinci ina kallonki.” Ta zauna tare da jan mayafi ta

dan rufe gefen fuska.

Sai da suka gama ci da sha, sannan suka koma

hira.

Ya ce. M

eki ka ce dazu? ta ce, “Batun

matanka da ka ce zan zama daya daga ciki.” Ya

ce, “Eh gaskiya ke ce ta uku.

Ta zata zolayarta yake yi, don haka bata ji

Komai ba sai ma ta ce, Ban san lokacin da ka auri

Biyun ba, ko kuma mu ne ba a gayyata ba.

Ai rana d

aya za’a daura da naki, kuma ina

zaton ma hudu za’a daura duk da ban san wace ce

dayar ba.”

Ta ce, “Zan fi son mu aje batun wasa, ni da kai

muyi zance na gaskiya.” Ya ce, Ai ke ce ki ke

ganin wasa ne, amma babu wasa cikin zancena.

Fuskar Nafisa ta ca

nza launi daga fara’a zuwa

kalar damuwa, shi kan shi ya lura da haka amma

bai bi ta kan haka ba, sai ma ya mika mata

karamar wayarsa.

Ban yi saving din lambar ki ba da na amsa a

hannun Badi’atu, ki saka sunan da ya dace, don da

shi zan kira ki a gaba

n kowa.

Ta amsa ta saka tayi saving da (Sweety). Ya

kalla sannan ya dube ta. “Sweety! Har a gaban

Mama da Hajiya, da Kaka, da su Baba?

Tayi dan murmushi “Eh. Ya ce “To kema

hakan za ki kira ni.

Sun dauki lokaci suna dan tattaunawa, kafin a

kira Mag

riba. Suka mike da zummar tafiya. Ya aje

mata kudi ‘yan dubu dai-dai guda goma.

Ki sai omo ki wanke kwanuka, abinci ya yi

dadi.” Ta dube shi, “Haba dai, ka bar shi kawai.”

Ya ce, “Ai ba ki tambaye ni ba. Tayi musu rakiya

har gurin mota.

Bayan tafiyar

su tazo a rude gurin Mama. Ta

ce, “Mama Yaya Shatima ya yi min wata magana

da ta sa naji komai na duniya ya ishe ni, wai mu

uku zai aura rana daya!

Mama tayi ‘yar dariya, “Ina ga ba ki san

tsokana ba ko? Wasa ya ke miki.” Hawaye suka

soma zubowa dag

a idanunta.

“Wallahi Mama babu alamun wasa a tare da shi

sam-sam! Ta ce, “To bari Babanku ya shigo mu

Ji, in dai zai auri wasu ai shi ne waliyyin shi.

Yana Yana daga kwance ya kalli agogon wayarshi,

sha daya ta gota. Ya danna lambar Amna, sai da

tayi

ruri ta katsee. Yayi murmushi, ya san kadan

daga cikin jan ajin Amna.

Ya sake kira, can ta daga muryarta can kasa ta

ce, “Hello!” Ya ce, “Ba ki yi bacci ba Amna?” Ta

cc, “Eh, ban yi ba tukunna, sai yau ka ke kirana?

“Kiyi hakuri zan shigo gobe.”

Ta

ce, “Sai kuma ka daga zuwan, don gobe

duka gidan ba mu nan.” Ya ce, To fa? Ina za ku

haka har da ba za ku amshi bakuncina ba?”

“Ni dai Umra zamu je da Mom, da Dad sai

Sisters dina guda biyu. Amaryar Dad da sauran

yara za su je (London) hutu.

Ya sauke

ajiyar zuciya, “Sai yaushe za. ku

dawo? Ta ce, “Sati biyu zamu yi, ba dadewa

zamu yi ba.” Ya ce, “Shi kenan. Don Allah ki sani

cikin addu’arki.”

Insha Allahu, amma dai zamu yi waya in mun

sauka ko?

Dole na, ina son wannan muryar taki sosai

Amna. Ya

fada cikin murmushi.

Muryata kawai ka ke so ban da ni?

Ke ma kin san fada bata baki, ina matukar

sonki.

Nima ina sonka da yawa, sai dai ina ja baya ne

don ina ganin kamar ba ka damu da ni ba.

Ya ce, Me yasa ki ke ganin kamar ban damu

da ke ba?”

T

ayi yar dariya tare da sake matse wayar a

kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar

da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni,

sai yau ka samu sukuni din?

Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa

dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna b

ata

magana da karfi ko. kuma ba ta

son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar

birge Shatima.

Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa

da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan?_____

*

🏚

️

RANA DAYA

🏚

️

*

CHAPTER 5

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan nu

mber 09028485925```

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login