Showing 15001 words to 18000 words out of 38678 words

Chapter 6 - RANA DAYA BOOK1 COMPLETE

11 Nov 2026

15

ce A na uku Mama tasa hannu ta ciro wayar a kusa da filon da ta tada kai. Ta kalli wayar “Ai

Shatiman ne ma ya ke kiran ki.”

Ta tashi zaune da sauri ta amshi wayar, Mama tayi murmushi sannan ta fita. Nafisa ta daga. Ya ce, “Sweety ina ki ka shiga ina ta kira ba ki daga ba?”

Muryarta can kasa tana kuma rawa irin ta marasa lafiya. Ta ce, “Yaya ba

ni da lafiya ne.” Ya ce, “Subhanallah! Tun yaushe?”

Ta soma shesshekar kuka. “Na kwana biyu.” Ya ce, “Shi ne ba ki fada min ba? haba Sweety! Ban so ba da ki ka yi haka, me ke damunki?”

Ta ce, “Zazzabi ne.” Ya ce, “To kin je asibiti?”Ta ce, “Mama ta ce mu

je na ce a’a, ina shan

magani a gida Ya ce, “Wa ya fada miki ana

zama da ciwo? Ina Mama din. ki bata.”

Ta yunkura ta tashi ta ce, “Bari in kai mata.” “Za ki iya tafiya amma ko?” Ta ce “Bari na kokarta.” Ya ce, “Ban ji dadi ba Sweety, na kira ki muyi hi

ra sai kuma in ji kina ciwo?”

Ta ce “Ga Mama din.” Ya gaida ta, sannan ya fara korafın ya ya za’ayi a biye ma Nafisa don ta ce ba za ta asibiti ba?Mama ta ce, “Kaga Nafisa rigima ce da ita, tun daga ranar da ta ji cewa su uku ne rana daya tasa ma kanta da

muwa take wannan ciwon. Ya ce “Au! Dama wannan ne?” Ta ce, “Shi ne.” Ya ce “To shi ke nan Mama bata wayar muyi

magana. Mama ta mika mata wayar, ta nufi daki tana “Hello!” Ya ce, “Sweety kin bani mamaki, kin san ya ki ke a zuciyata kuwa?”

Dadi ya rufeta,

ta kara shagwabewa. “Ni Yaya

sai ina ganin don iyayenmu suka hada mu shi yasa

ka ke share ni, kuma ka fi son su.” Ya ce, “Ni na fi son wadda tafi sona, ke ga shi ma har yanzun ban tashi daga Yaya a gurinki ba.”

Ta ce, “To zan daina cewa, kuma Allah Yaya

duk nafi sonka.” Ya ce, “Gashi kin sake fada bayan mun yi da ke sunan da zan kira ki da shi shi ne za ki kira ni.

Cikin shagwa

ɓ

a ta ce “To zan ce.” Ya ce, “To ce ina ji.” Tayi ‘yar dariyar kissa. Ta ce “Sweety.” Ya ce, “Kai! Kin iya fada, dan kara in ji.

” Ta sake fadi. Ya ce, “To na kashe Yaya din nan ko matata?”

Ta cc, “Eh.” Ya ce, “Don Allah ki tashi daga ciwon nan kar ki zo ranar biki ba ki yi kyau ba. Ni fa kin san bana son mace ramammiya.Ta ce, “To ai ba ka kirana ne kuma baka zuwa.” Ya ce “Wannan b

a shi ne yake nuna bana sonki ba, aikina yana da yawa, kullum fa Kaduna ni ke zuwa ina dawowa, ga aiki a gida, ga ginin ku da za ku zauna. Abubuwa da yawa.”

“To amma za ka ke kirana?”

“Duk lokacin da na dan samu sarari kamar haka zan kira ki, kuma zan zo

yanzun dai kin warke?” Ya tambayeta cikin nuna kulawa.

Ta ce, “Na warke.” Ya ce, “Yauwa sweety, duk lokacin da ki ka tuno ni kiji a ranki cewa ina tare da ke dari-bisa-dari.”

Haka ya yi ta nuna mata sonsa har sai da ya

tabbatar ta gamsu, ta kuma yarda

yana yinta sosai.

Tsawon awa daya kafin yayi sallama da ita.

Washegari misalin karfe takwas ya dawo daga Masallaci ya shiga motarsa ya zauna don ya yi waya da Aliya.

Daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta an dace da zata duba kudinta, ta gama saka lam

bobi ta danna kenan kiran ya shigo, don haka ko ringing bata yi ba ya zama ta daga. Duk da taga sunan Shatimanta ne bata so haka

ba, sai ka ce tana zaman jiranshi. Amma sai ta sa a kunne cikin kissa tayi sallama ya amsa, sai ta ce, “Laa! Wai kai dinne da

gaske?” “Kina zaman jirana ne?” Ya tambayeta.

“Ina yin mamaki ne a zuciyata ne naji cewa ina danna gurin amsa kira, nasa a kunne zan ji muryarka, lallai sona da kai wani abu ne na musamman.”

Ya ce, “Nasan haka, ba ki bukatar sai kin tuna min shekaru uku

kina jiran soyayya, ba abin mamaki ba ne don kin ji a jikinki cewa kirana zai shigo.”

Ta ce, “To mu gaisa in ji lafiyarka.” Ya ce, “Ina cikin koshin lafiya, sai so da kaunarki da ke kara samun mazauni a zuciyata.”

Ta lumshe ido. “Ni ko ina nan ina tunan

in ya ya ka kare da ‘yar uwata, ko ta amince zata zauna, da mu din?” Ya ce, “Ai tunda ki ka bani wannan shawarar naje na gwada. Tayi sosai, na kara miki lambar yabo a cikin kaunarmu.” Ta ce, “Naji dadin haka.” Ya ce, “Ke kamar kya yin kishina, wasu kuma su

na cewa kishi yana daga cikin so, haka ne?”

Ta ce, “Ai kishin jahilci shi ke så wa ayi ta tashin hankali my love. Mu da muke Musulmi, gidan Manzon tsira (S.A.W) shi ne fitilarmu, kalar kishin matanshi zamu yi, kishin faranta maka tare da ba ka shawarwari

nagari.

Kuma don ina kishinka ba zan kauda kai ga abin da ka ke so ba, zan danne in so abin da ka ke so tsakani da Allah. Ina jin sauran matanka dani zamu zauna tamkar ‘yan’uwa.”

Ya ji dadin kalamanta, har yace”Ke ta daban ce a mata my love, haka a zuciy

ata.” Taji dadi matuka. Suka ci gaba da hira har ta ke tambayar shi yana ganin auransu zai dauki tsawon wane lokaci?

Ya ce, “Me yasa take tambaya?” Ta ce, “Ka san an ce me kwarmin ido da wuri yake soma kuka.” Ya ce, “Haka ne. Ni dai a tsarina sai na gama

muku wurin zama, sannan in zo kan batun biki, don bana son a sa min rana mai tsawo. Komai-da-komai dai bana son ya wuce na da wata tara.”

Ta ce, “Allah Ya nuna mana lokacin. To ammal kafin lokacin za a sa manya a ciki ko?” Ya ce, “Eh mana, da zarar sun ga

ma bincike su za su zo ga manyanku, itama awa guda suka kwashe kafin suka yi sallama,

Ita ko Amna yafi jin dadin yin waya da ita in yaje kwanciya, Don haka sai da ya gama komai na al’adarshi kafin ya kwanta sannan ya kira ta.Yau ya ci sa’a a kiran farko t

a daga, bai san ma ta dagan ba sai da ya ji ‘yar muryarta ta ce, “Hello honey.” Ya ce “My honey kina lafiya?” Ta ce, “Kamar yanda ka ke.”

Suka yi hirarsu irin ta so da kauna, bata kawo mishi batun sauran ‘yan matan ba, shima bai dauko mata ba. Tsawon awa

daya yana yada manufarshi kafin suka yi bankwana.

Bayan duk bincike sai a ka tura neman aure, babu inda aka samu matsala sai gidan su Amna, in da suka nuna a dan jira in sun gama bincike za su neme su. Bayan sati uku sannan suka ce manyan su dawo.

Alhaji

Musa Baban Nafisa shi ne zai amso auran Amna, ya zama ko ina an ba shi. – Gininshi kuma ya kammala, amma fa asusun ya yi kat! Har sai da yayi aro gurin Babanshi. shi

Gida dai ba abin da yake jira sai masu gidan. Gurin tsara sadaki aka samu bambanci. Baba

n. shi shi ne zai ba da Nafisa, ya murza gashin baki ya ce dubu dari ne sadakin ‘yarsa. Baban Nafisa mai amsar ma Shatima aure ya ce “Haba Yaya, a dai rangwanta.”

Alhaji ya ce, “In suna so su bayar, ‘yarshi tana

da ilimi. Haka Baban Nafisa yayi masa tra

nsfer ta

dubu dari a nan take, abin gwanin sha’awa.Su ko gidan su Aliya hamsin suka saka mata, sai kudin gaisuwa ashirin, saba’in kenan. Amna kuwa dukiyar aure dari, sadaki kuma hamsin. Duk haka aka ba da, sannan aka tsaida lokacin aure wata sha biyu ishi

rin ga shi a lissafi sauran wata hudu kenan.

A son Shatima kar a kai wannan lokacin amma an duba lokacin da za’a samu hutu mai tsawo kowane bangare suna cikin kasa kuma suna cikin jihar.

Kamar yanda ya tsara a wata daya yake kai musu ziyara, ran Juma’a y

aje gurin Nafisa. Sati

yaje gurin Aliya Lahadi kuma yaje gurin Amna. Haka duk karshen sati yake tura musu kati na dubu dai-dai. Haka kuma yake kiransu sau biyu a kwana goma,

Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya

dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar

Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai

mata, dama oder take yi.

Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa

lokaci_____

*

🏚

️

RANA DAYA

🏚

️

*

CHAPTER 8

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*



*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Acce

ss bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko k

u turo katin Mtn ta wannan number 09068032427*

*08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa

masu karfi da Basu da illah*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*1 Gumbar kankana da ayu*

🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*

🍀🍀

4 *Kaza mekwai*

🍀🍀

5 *Zabo me zuma*

🍀🍀

6 *Kaza me allurai

🍀🍀

sahihiyar mallaka ba boka ba malam*

🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*

🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*

🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi*

12 *Maganin hips and bobbs*

13 *

hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*





🍀🍀

🍀

🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan*

*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba k

e amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀

Mun tsaya

Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya

dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba

musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai

mata, dama oder take yi.

Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci.

Amna kuwa ba ta mantawa da tura masa sakon murna da

shiga sabon wata a duk lokacin da aka shiga. Tsarin kowaccensu ya birge shi

Shatima yana da kaifin basira, da hikimar zama

da jama’a, don haka yake ganin kamar cin tuwo ne

ko shan ruwa zama cikin mata hudu ma bare uku. Shagali ake shiryawa a kowane bang

are musamman gidan su Amna wadda ta kasance ita ce mace ta farko da za’a soma aurar wa a gurin Mahaifinta.

Itama Nafisa ana ta shiri don ita ce ‘yar fari gurin Babanta, ga kuma dangi kowa na cin buri, Aliya kuwa suma suna shiri daidai karfinsu, bata shaga

li suke yi ba su, suna ta kayan daki ne a samu a yi mata gado seti biyu, ga kuma gara tunda sun san yana da hali da kyar in ba daki biyu za’a kai ta ba. Sannan gefen kayan gyara jikin Amare ko ina suna ta yin daidai karfinsu.

Alhaji Isa Baban Shatima cew

a ya yi ba zai ba Shatima komai ba ‘yarshi zai wa kayan Gado da kayan gara. Ya fadi haka ne lokacin da Shatima ya samu Babanshi da Hajiyar su a daki Baban nashi yana tambayar wace gudunmawa zai ba shi?

Shatima ya ce, “Alhaji nima a dan duba min, Allah a

susuna babu kudin kirki, gashi ko akwatuna ban siya ba.”

Hajiya ta ce, “Amma jiya ka ce min Alhaji Murtala ya turo maka da dubu dari biyu ko? Yanzun ma nike fadawa Babanku.”

Shatima ya ce, “To duk kowace ta min magana ashobe da za su fitar, Amna ce kawai

bata min ba, itama nasan zata yi, shi ne zan raba musu wannan dari biyun.”

Alhaji ya ce, “Ai kai dan dangi ne za ka samu gudunmawa, Murtala da duk cikin ‘ya’yan Mahaifinmu yafi kowa mako, amma shi ya fara baka gudunmawa har dari biyu.”

Hajiya ta ce, “Ba

dole kowa ya motsa ba tunda Babansu zai yi aure har mata uku rana daya. Shatima ya ce, “Alhaji ka min daí wani abu koda canza min mota ne.”

Ya ce, “Au! Ka ma tuna min, Alhaji Nadabo ya

ce kaje gidan motocinsa ka zabi wadda ka ke so.”Murna ta cika Shatim

a. Ya ce, “Amma gaskiya

Baba Alhaji Nadabo ya yi min komai.” Hajiya ta ce, “Kuma fa ya ce duk ruwan da za a sha a biki na gora aje kamfaninsa na ruwa a debo. Allah ya saka mishi da alkhairi.” Suka ce

“Ameen.”Shatima ya ce, “Allah Yasa mu ma abotarmu da

Munir tayi kamar taku, shima yana da irin halin Babanshi.” Ya cc, “To ke Hajiya har yau ba ki fadi naki ba.”

Ta ce, “Kai uban masu kudi da gata ka ke, nan da wata mai kamawa asusunka sai yayi kamar zai fashe. Don haka ni yanzun ba zan yi alkawarin komai

ba sai nan gaba tukunna.”

Ya mike “Shi kenan, bari in je in shirya yau Kano zani gurin Amna.” Hajiya ta ce, “Ka fa yi ma Badi’atu alkawarin zuwa da ita tun shekaran jiya take min zancen.” Ya ce “To ta shirya har da Munnir zamu je ni na ma manta da mun yi

haka da ita.”

Karfe biyu sun isa birnin Kano sun samu tarba sosai musamman Badi’atu wadda tayi kyau cikin riga da wando da mayafinsu ‘yan Dubai.

Amna tayi murna da zuwan Badi’atu, ta hada ta da kanwarta Sumy don za su yi sa’annin juna. Tunda suka kebe ta

shagulgulan da za su shirya. soma mishi zancen

Ta ce “Mu fa tun ranar Laraba zamu fara biki.” Ta tashi ta dauko mishi katin wanda aka tsara shi da ruwan zaiba, jikinshi kuma ruwan jibi. Karamine kwarai katin sai shegen kyau kamar ka lika a jiki kayi ado.

Ya karanta a ranshi ya ce tab! In ko shi zai ba da kudin shagalin nan za a samu matsala, don ba shi da su, amma dai bari ya jira ya ji abin da zata ce. Ta dube shi.

“Katin yayi kyau kuwa?” Ya ce, “Sosai ma.” Ta ce, “Kamar guda nawa zan baka?” Ya ce “Tun

da yanzu saura kusan wata biyu har da kwanaki, ki bari sai abin ya kara matsowa, kar in zuba a wani guri in manta.Kin san kaina kullum kara daukan hayaki yake yi, mata uku fa!”

Ta taba baki, “Ni ina mantawa da cewa bani daya ba ce, ko su Mom dina ba su

fada ma kowa ba sune kawai suka sani. Zan ajiye maka amma za ka zo min dai duka ko?”

Ya ce Zan dai zo amma ba duka ba, kuma mu da abokanmu zamu shirya Dinner wadda za ku zo ku duka amma sai an kai ku.” Ta ce, “In lokacin mutane na sun watse zan je mana, a

mma in suna nan sai dai kayi hakuri don ba su sani ba.”

To babu matsala, Allah Ya kai mu.” Munnir ma da ya ga katin sai ya ce, “Ni dai bari in rike wannan yayi min kyau.”Sumayya da suka je dakin su da

Badi’atu, ta nuna mata ashobensu kala shida. Duk masu

tsada ne kowane shagali da kalar da za a sa.

Badi’atu ta ce, “Lallai ku kam har kun fitar, mu dai sai cikin watan nan da zamu shiga sannan za a

fitar, Kanwar Babanmu ce zata fitar da su.”

Sumayya ta ce “Mutum yaushe har ma an kusan gama bada wa. Yayar B

abanmu tayo odar ba saidawa ake yi ba, har kawayenta duk an basu ne tare da katin biki.”

Badi’atu ta ce “Tab! Duk wannan kuma za a ba mutum daya?” Sumayya ta ce, “Eh mana. Ita kuwa Amarya kin ga kayan da zata sa da biki? Akwati uku ne aka je Dubai aka din

ko su, na biki ne kawai har ma da irin rigar aure dinnan zata sa.Tare aka siyo da kayan da shima ango zai sa a

ranar da takalmi da komai. Badi’atu ta saki baki,

har ta soma tunani tsarata kawai Summy ke yi

Har suka soma shirin tafiya Shatima bai ji tayi

masa zancen kudin komai ba, kamar yanda Aliya da Nafisa suka mishi da ya ziyarce su a ranakun Juma’a da Asabar.

Kowace ta tambayi kudin ashobe, da kuma sauran shagulgulan tata zata yi da kawayenta Ya kalli Amna, “Ke ba za ki yi ashobe ba ne?”Ta lumishe i

do, “Ai tuni sun cire abinsu, ni ai ba zan sa ba, sun kusan gama raba shi ma.” Ya ce, “To yanzun me ki ke bukata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login