Showing 12001 words to 15000 words out of 58120 words
/>
a shi da wani yakaita inda za ayi mata passpord, sabida ya biya mata aikin Hajji, da ni da twins. Y
aya Ridwan ya ji da
ɗ
i sosai da sosai, kuma ya yi masa godiya. Twins tun da na kaisu
ɗ
akinsu na wasa suka zauna, mussaman da suka ga
ɗ
akin cike da hotonansu, sabida yaran suna da matuƙar wayo sai suka sake har Yaya Ridwan ya zo tafiya, ya shiga yaga yanda
suke ta wasa hankalinsu a kwance ya tafi ya barsu.
Yana tafiya muka shiga
ɗ
akin ni da Turaki, muka fara wasa da su suma suna wasa damu, sai na ji duka duniya ta yi min daidai, farin ciki ya mamayeni fiye da ko yaushe, haka shima Turaki kana ganinsa yan
a cikin fara’a, haka har dare twims ba su ne mi iyayensu ba, dan sun ce.
“Mamma.”
Zan ce.
“Na’am.”
Sai su yi shiru, ko idan suka ce.
“Papa.”
Nanma Turaki ya ce.
“Na’am.”
Wani abin da
ɗ
in ma sun yi cin abinci, da muka zo cin abincin
dare suna ta wasa jikin Turaki kowa aka bashi na shi, da kansu suke shan custard din, amma suna
ɓ
ata jikinsu, sai wajen tara suka yi bacci, kowacce aka kaita gadonta sannan muma muka kwanta, Turaki ya ce.
“Habibty, yau kina cikin farin ciki ko? Nima hak
a.”
“Eyy Habiby, daman haka yara suke da da
ɗ
i?”
“Haka suke mana, gashin yanzu kin samu ko? Allah Yasa ƙarshen damuwarki kenan.”
“Amin Habiby, na gode da ƙwarin gwiwarka.”
“Babu komai Habibty, ki sani ni Abubakar Turaki ina matuƙar ƙaunarki, wal
lahi Habibty ba ni da bakin da zan iya bayyana miki adadin son da nake miki, ina jinki cikin kowanne numfashi na, ina wajen aiki ke, ina tare dake ke, ina bacci ke, Habibty ban ta
ɓ
a jin kin isheni ba ko na minti
ɗ
aya, a kullum muradin zuciyata ke ce, ina s
onki, ina ƙaunarki wallahi Habibty, rayuwata idan bake mutuwa ce.”
“Nima haka, ina son ka Habiby, ina ƙaunarka, Allah Ya barmin kai har abada.”
“Amin Habibty.”
Ya fa
ɗ
a tare da janyoni jikinsa. Washe gari da safe ƙarfe takwas masu decoration suka z
o, ta wajen bayan part
ɗ
in mu zaayi, inda ba za a ta
ɓ
a
ɓ
angaren su Sardauna ba, sai da suka share wajen ya yi kyau sannan
suka hau decoration suna gyara wajen, ni kuma na shiga na tashu Twins. A tare muka yi musu wanka da Turaki, muka shirya su, suka koma
ɗ
akinsu suka hau wasa, muma muka je muka shirya. Wajen ƙarfe goma da rabi masu decoration suka gama komai suka tafi, wajen ya yi kyau sosai da sosai.
Wajen ƙarfe sha biyu Yaya Radiya ta zo ita da yaranta, sun yu kyau sun canja abinsu, ina yabon yanda s
uka canja, itama tana yabon yanda na canja.
“Nana dole mu sake godewa Allah, burin mu duk sun cika, aure dai gashi kinyi, kina rayuwa cikin jinda
ɗ
i.”
“Wallahi Yaya, a yanzu dukkanmu hankalinmu a kwance, Allah Ya amsa addu’ar Alhaji.”
“Hakane Nana,
ni dai dan Allah ki ci gaba da yin biyayya ga Turaki, ji yanda yake son komai kike so, yanzu ji
ɗ
akin yaran nan, ji abinda yake musu kamar shi ya haifesu, ga Ridwan ya ce min, wai Ya biyawa Hajiya dake da twins, aikin Hajji “
“Wallahi Yaya.”
“Allah
Ya ƙara masa arziƙi.”
“Amin Ya Allah, shi Umarar azumi zai je, muku babbar sallah.”
“Ai abun kamar yau ne Nana, Allah dai ya saka.”
“Amin amin.”
Muna zauna Yaya Rumaisa ta zo, tare da matar Ra’is na ce.
“Wai Ra’is dai bazai zo gida na ba.”
Ta yi dariya sannan ta ce.
“Zuwa na mussaman zai yi ya ce.”
“Uhm.”
Na fa
ɗ
a, muna nan zaune event planner yazo, suka fara tsara wajen da yanda komai zai tafi a tsari a wajen, can kuma mutane suka fara zuwa, mai kwalliya ma tazo ta tsantsaramin kw
alliya, har da su Twins.
04:30pm
Harabar gidanmu ta cika ta batse da mutane, ‘yan uwa da abokan arziƙi ta ko ina, wajen ya tsaru yanda event planner
ɗ
in suka yi ƙoƙari akan haka, ko ina na wulga ‘yan uwana ne, da ‘yan uwan Turaki, ƙawayena da abokan
sa. Ni da shi muna zaune sai twins suma a zaune, abokan Turaki sai ku
ɗ
i suke zubawa, wannan ya fito ya ce ya bawa Twins 2million, wannan ya ce 5million, har da wanda ya basu 15Million shine yafi kowa, sai kuma masu basu gold, haka aka yi ta abu, tun ina li
ssafa miliyoyi har na gaji na daina, abinci anci, an sha, Twins sun ga sabuwar rayuwa kowanne su sai farin ciki yake. Haka ka aka tashi daga taro kowa ya watsa muka zauna ni da Turaki muka fara tattaunawa akan abinda abokansa su ka yi, na ce.
“Habiby, a
bokanka haka suke daman?”
“Ai Habibty mun saba, duk wanda aka yiwa haihuwa haka muke yi, yanzu ko wasu aka ƙara haifa haka zaayi musu, amma na farko sunfi mora.”
Na girgiza kai na ce.
“Cha
ɓ
.”
“Habibty yanzu ku
ɗ
in ya kusa 60million, ina tunanin
ko asiya musu filaye na 20/20 million, ragowar kuma abawa Yaya Ridwan.”
“Ai ba zai amsa ba, zai ga kamar mun nuna ba ‘ya’yanmu ba ne.”
“To Habibty me za mu yi da su? Idan muka cire musu 40M a ciki, ai yawadatar.”
“To Habiby ko za a biya musu Umar
ar azumi shi da matarsa, ace da ku
ɗ
in da aka samu ne.”
Legendspen
08129553971
SARTSE BOOK 3
Sayyid.
(7).
Cikin kwana biyu Turaki ya siyawa Twins manya manyan filaye guda biyu na kimanin miliyan 20 kowacce
ɗ
ayansu, sannan kuma ya fara ƙoƙarin bi
yawa Yaya Ridwan da matarsa Umarar azumi, Twins basu bamu wahala ba wajen zama damu, sun saba da mu cikin ƙanƙanin lokaci, sun kuma shiga ran mu duka. Suna kirana da Maamah, suna kiran Turaki da Papah, ranar da naje dasu gidansu Turaki basu sami wata tsang
wama ba, kowa ya kar
ɓ
e su hannu biyu, kuma na ji da
ɗ
in hakan sosai.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka sama musu mai kula da su, inda aike kai su gidan idan zan fita, idan na dawo kuma na biya na
ɗ
auko su.
Mun fara shimfi
ɗ
a rayuwa cikin farin ciki, hankali kwanc
e. A
ɓ
angaren Sardauna dai Islaha ba ta dawo ba, sabida Hajiya Falmata ta dage kan Islaha baza ta dawo ba, har sai Sardauna ya
ɗ
au mataki akan Bilkisu, abinda ya gagare shi kenan, a yanzu maganar ma ta mutu har wajen su Big Daddy, a raina na ce. ‘Idan Bilk
isu ba ta yi haka ba ai ba ta cika mai bin malamai ba.’ Shiru magana kowa ya manta da ita, ta ci gaba da rayuwa da Sardauna cikin fa
ɗ
a, kullum cikin tashin hankali gashi yawo ta ci gaba ba zama, abun nata ma ya fara gaba dan sai ta kwana acan ma inda ta ta
fi yawon, ta mayar da Sardauna sallau, ba abinda ya isa ya yi mata, sai dai mita su yi ta
ɗ
aga murya. Nikam na mai da hankali kan kula da ‘ya’yana da kuma aikina, shine abinda ke gabana yanzu, sai kuma kula da Turaki.
Lokacin da aka sanar da Yaya Ridwa
n da matarsa zancen tafiyar Umarar azumi har da ƙwallarsu ta jin da
ɗ
i, haka ma Hajiya sai a lokacin aka sanar da ita zuwan mu aikin Hajji, in sha Allah. Cikin ikon Allah watan azumi ya gabato, Turaki zai tafi goma ga azumi ya dawo biyu ga Sallah, su Yaya R
idwan kuma zasu tafi farkon azumi ne. Shirye shiryen azumi sun yi nisa, na roƙi Turaki akan ya barni na sami masu aiki da zasu dinga min kunu da ƙosai na sadaka, idan anyi sai a
ɗ
auka a fita da shi can ayi sadaka, ba tare da ya yi wani musu ba ya amince, h
ar ya bada wasu ku
ɗ
a
ɗ
en shima a matsayin na shi gudumawar, nasa aka sama min masu aiki mutum uku.
Cikin ikon Allah aka fara azumi ranar talata, a ranar mu ka yi abincin sadakar mu aka fita da shi ya ƙare tas, washe gari mu ka ƙara yawan shi sabida matar
ta ce min akwai mutane marasa ƙarfi da yawa daga wajen unguwar. Ranar azumi na hu
ɗ
u Yaya Ridwan da matarsa suka ta shi, ranar azumi na shida Yaya Rumaisa ma da mijinta suka ta shi, wannan shekara sai ta zama shekara mafi farin ciki ga ‘yan gidanmu, har mu
tum biyu sun tafi saudiyya kuma ana saka ran nida Hajiya zamuje aikin Hajji.
Ranar da aka yi azumi na goma Turaki ya tashi, gida ya zama daga ni sai Twins, har da kukansu da muka dawo, aka ci gaba da abin sadaka har azumi ya ƙare aka yi sallah Turaki y
a dawo, tun tafiyar Turaki na yi ƙoƙari wajen
ɗ
auke kai daga al’amarin Sardauna da Bilkisu, kamar basa gidan haka na mayar da su, kuma suma sun rage abinda suke yi, dan shima Sardauna ya tafi saudiyya ƙarshen azumi.
Haka aka yi bikin sallah cikin fari
n ciki, a lokacin bikin sallah matar Ra’is ta sauka inda ta sami
ɗ
a namiji, an sha taron suna anyi farin ciki, inda aka yi wa Alhaji takwara aka sanyawa babyn sunan Alhaji, ranar suna na a gajiye tilas na dawo, ga Turaku ya maida hankali akan gina sabon gi
dan da zamu koma, wajen ƙarfe tara na dare na dawo gidan, ina sauka a mota na ga ‘yan sanda a harabar gidan namu, da sauri na tura su Twins cikin part
ɗ
in mu, ‘yan sanda suka ƙaraso inda nake.
“Ranki ya da
ɗ
e barka da dawowa.”
“Barka dai, wa kuke nem
a haka?”
Na fa
ɗ
a fuskata da alamar tsoro, danni a rayuwata ma magana bata ta
ɓ
a ha
ɗ
amu da ‘yan sanda ba.
“Muna neman matar gidan nan ne?”
“Ni ce matar dake zuane a wannan part
ɗ
in.”
Na fa
ɗ
a ina nuna part
ɗ
inmu, sanna na ce.
“Matar dake zaune
a wancan part
ɗ
in kuma, tana ciki ko bata nan ni ban sani ba, wacce kuke nema?”
“Bilkisu.”
Na nuna musu part
ɗ
in na ce.
“Ita ce me nan, ni sunana Nana.”
“Ai mun buga tun
ɗ
azu ba a bu
ɗ
e ba.”
“Eyh da yake ba zama take yi ba, babu tabbacin ta
nan, sai dai kujirata tun da ba kwana take a can ba.”
“A’a idan ba ta zo ba zamu tafi dake.”
Na yi musu wani kallo, sannan na ce.
“Akan wane dsalili kenan?”
“Akan dalilin neman ta dake ayi, kun
ɓ
oye me laifi.”
“Ina ba a gidan na zo na sameku
ba? Ta ina zan
ɓ
oye ta to? Ku jira ko ita ko mijinta wani na zuwa.”
“Mu DSS ne, muna bincike ne akanta, sabida an zargin ta da harkar dillanci ƙwaya.”
“Dillancin ƙwaya kuma?”
Nai maimaita a tsorace, sannan na ce.
“Ita Bilkisun? Lallai.”
“Ey
h ita, to kinga wannan case din babbane. Idan babu ita za a iya tafiya dake?”
“Malam ni a wa? Kishiyata ce ko me? Nifa bani da wata akaƙa da ita, mijina da mijinta ke da alaƙa, dan haka ni bani da wani alaƙa da ita.”
“Duk haka, kinsan inda za a same
ta.”
“Tare muke yawon ko me? Ni zan shiga ciki, kuna nan tsaye mijinta zai shigo, zaku ganshi wani ja kamar ƙosai.”
Ina fa
ɗ
in haka na shige ciki, ina mamakin yanda mutanen nan suke neman shafa min kashi awaki, ina shiga na kira Turaki a waya, yana
ɗ
a
gawa na ce.
“Habiby da matsala gida.”
“Me ya faru Habibty?”
“Jami’an DSS ne a gidanmu, wai zasu tafi dani sabida suna neman Bilkisu basu ganta ba.”
“To ke awa? Kar su kuskura, ki fa
ɗ
a musu na ce idan suka tafi dake duk sai na yi shari’a da su,
gani nan zuwa.”
Daidai lokacin na ji ana buga min ƙofa, aikuwa na yi kamar ba na ji naƙi bu
ɗ
ewa, suna tsaka da bugun na ji Turaki yana ce musu.
“Bayin Allah lafiya?”
Sai a lokacin na taso na bu
ɗ
e ƙofar, ina ganin shi na ce.
“Sai bugu suke min,
na nuna musu part
ɗ
in Bilkisu amma sunki haƙura.”
“Ina tambayar ku lafiya, kunzo kuna tayarwa da matata hankali kuma kunyi shiru.”
“Mu jami’an DSS ne, munzo ne muna neman Bilkisu.”
“Ga can, nan ne part
ɗ
inta, mijinta da ita duk basa nan, dan hak
a kar ku zo nan ku
ɗ
aga mana hankali.”
“A tsarin ƙa’idar aiki idan akan wannan case
ɗ
in ne ana kama wa
ɗ
an da ke kusa da mai laifi.”
“Wanda ke kusa da ita ai bai wuce iyayenta ba ko mijinta, mu da zama ya ha
ɗ
a mu kuma mene a tsakanin mu?”
“Ka yi h
aƙuri yalla
ɓ
ai, amma dole zamu tafi da wani cikinku.”
“Babu wanda zaku tafi da shi, nina jami’i ne.”
Turaki ya fa
ɗ
a yana
ɗ
auko musu id card
ɗ
insa, sannan ya ce.
“Akan wannan abun zan iya shigar da ƙarar ku, bama ku ka
ɗ
ai ba, har da hukumar ku.”
Shiru suka yi, a daidai lokacin kuma Sardauna ya dawo, Turaki ya ce.
“Ga mijinta nan.”
Yana fa
ɗ
in haka ya kama hannuna muka shige, muna shiga ya ce.
“Wane lefe ne ta yi?”
“Wai dilal ƙwaya ce.”
“Ƙwaya kuma? Ita Bilkisun?”
Na gya
ɗ
a kai, sa
nnan na ce.
“Ita fa, ni na rasa gane kan matar nan, mugayen ayyukunta sunyi yawa, mene ha
ɗ
in ta da dillanci ƙawaya tana mace, tana matar aure dan Allah?”
“Sardauna idan baiyi wasa ba, Bilkisu sai ta ja masa rayuwa a gidan yari,”
Bugu ƙofar mu aka
fara yi, hakan ya sa Turaki ya fita ni kuma na bi bayansa.
“Turaku ka ji wai tafiya zasuyi da ni, ka yi musu magana dan Allah.”
Sai da Turaki ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce.
“Ba shine kuke nema ba, matarsa ce.”
“Mun sani, a
mma ai taƙi dawowa.”
“Shima ta gagare shi, bai isa ya sa ta ko yahana ta ba, amma ku yi haƙuri ku ƙyaleshi, idan ta dawo zai kawo ta.”
“To, amma muna so ya bi mu can ya sa hannu.”
“Kuje zan kawo shi yanzu.”
Turaki ya fa
ɗ
a, sannan ya kalle ni y
a ce.
“Habibty, miƙomin key
ɗ
ina.”
Na shiga ciki na bashi key
ɗ
in, sai da notarsu ta fita daga gidan sannan na koma ciki, sai dai ba afi minti uku da fitar su ba, motar Bilkisu ta shigo gidan, ko a lokacin goma na dare ta kusa, wayata na
ɗ
auka na yi
wa Turaki text na ce. ‘Ga Bilkisu ta dawo.’ Ya yi min reply da okay.
Kasancewar basu yi nisa ba ya sa suka dawo, dan ta zarar ba tafi minti biyar ba suka fara hon, ina tsaye bakin taga na ga sun fito dasu da ma’aikatan, abinda yake bureni da Turaki ya
nda baya
ɗ
aukan al’amarin mutane, yana fitowa daga mota ya nufo part
ɗ
in mu, maimakojn ya je can ya ga ƙwal uwar daka, amma ya za
ɓ
i ya dawo nan ba ruwansa, ina ganin zai shigo na koma kan kujera na zauna, yana shigowa na miƙe na ce.
“Kun same ta?”
“N
i bansani ba, na dai dawo kawai.”
Na bu
ɗ
e baki zanyi magana, muka jiyo muryar Bilkisu tana fa
ɗ
in.
“Me na yi da zaku kamani? Kai Sardauna kaine ka kai ƙara ta ko me? To wallahi ba inda zani.”
Ɗ
ayan cikin ma’aikatan ya ce.
“Mu jami’an DSS ne, da
n haka bincike ne ya biyo ta kanki, an sami sunan a cikin gidan da ake dillanci ƙwaya, kuma akwai tabbaccin cewa kullum kina zuwa gidan.”
“A’a malam kar ka yi min sharri, abinda ke kaini gidan ai daban ne, dan haka ban san ana wani dillanci ƙawaya ba,
dan haka ka rabu da ni kawai, babu inda zani, ko ita Hajiya Zinariyar wallahi ba ta isa ta yi min sharri ba.”
“Idan anje can sai ki yi bayani, amma anan kam babu abinda zamu fahimta, dan haka kizo mu wuce, kuma kaima ka biyo mu.”
Kallon Turaki na yi
na ce.
“Amma yakamata kaima ka je fa, babu wanda zai kar
ɓ
i uzirinka tin da kana gidan, ace an tafi da
ɗ
an uwanka kuma baka yi komai akai ba, alhalin kuna zaune a gida
ɗ
aya.”
“Abinda nake tunani kenan, amma bana son shiga lamarim Sardauna, mussaman a
yanzu da nagane babu wata alaƙa a tsakanina da shi, daman can ina haƙuri da shi ne, sabida ina kallonsa a matsayin
ɗ
an uwana, am
ɓ
a yanzu duk na ji komai ya fita a kaina dana gane gsky.”
“Duk da haka Habiby, ba a ta
ɓ
a canjawa tuwo suna, alaƙar ka kai da
Sardauna tana nan a matsayinta, babu yanda za ayi, Sardauna naku ne har abada.”
“Shikenan Habibty zo muje tare.”
“Twins fa?”
“Ai basa tashin dare, kawai muje.”
Mayafina na shiga na
ɗ
auka na fito, muka tafi a mota
ɗ
aya ni da Turaki da Sardauna,
karo na farko a rayuwa kenan, su biyu suna gaba ni kuma ina baya a haka