Showing 27001 words to 30000 words out of 58120 words
Habibtyna, ina so a koda yaushe ki yi ta sona, karki daina dan Allah.”
“Me zai sa na daina
ni kuwa? Ai mutu ka raba.”
Muna tafe muna shan hirarmu ta ƙauna har muka isa gidan, muna zuwa ya yi horn aka bu
ɗ
e mana, daidai lokacin na duba wayata na ga ƙarfe tara da rabi daidai na dare, muna yi parking na bu
ɗ
e na fito, shima ya fito ya fara sauko m
ana da kayanmu, ina fara taka ƙafata na ji zuciya tana wani irin bugu da ƙarfi, har sai da na runtse idona a daidai lokacin da nasa ƙafata a bakin ƙofar shiga falon, idona na kai kan wancan ƙofar da bama zama naga wajen da haske, na juyo na kalleshi na ce.
“Naga haske?”
“Aina?”
Ya fa
ɗ
a, yana shiga da jakar ciki.
“Wancan part
ɗ
in mana.”
“Eyh.”
Ya sake fa
ɗ
a yana fita, ina tsaye na kasa gaba na kasa baya ya gama shiga da jakun kunan kayan nawa, sai da ya gama ya ce.
“Ki shigo mana.”
“Ha
biby ina maka magana ka yi min banza.”
“Da yaushe? Me kika ce? Kuma anan zaki min maganar?”
Hanyar part
ɗ
in na ƙarasa na fara ƙoƙarin bu
ɗ
ewa.
“Habibty mene haka kike yi ne wai? Ki nutsu mana.”
Banza na yi da shi na fara murmur
ɗ
a ƙofar, ina fata
n Allah Yasa ba abinds she
ɗ
an ke ƙoƙarin raya min ba.
“Wai me kike nema anan?”
“Hasken mene a wajen?”
“Hasken wuta mana, ko baki gani ba?”
“Nagani, shi ya sa nake tambayarka me ya sa aka kunna haske a wajen.”
“Shine na ce ki je na yi miki b
ayani.”
Cika ƙofar na yi na nufi part
ɗ
ina, ina shiga na zauna akan kujera na ha
ɗ
e rai ina jiran shi, yana shigowa ya zauna a kujerar da nake kai ya ce.
“Habibty wai mene haka duk kika
ɗ
aga hankalinki? Kinje kina ta buga can?”
“Habiby waye acan
ɗ
i
n, ni jikina ya bani mutum ne a wajen.”
“Eyh Habibty mutum ce a wajen.”
Na miƙe tsaye a tsorace.
“Mutum? Wace?”
“Habibty dan Allah ki fahimce ni.”
“Wace kalal fahimta, wace irin fahimta kake so na yi maka?”
“Kina ji, wallahil azim na rasa
ta yanda zan fa
ɗ
a miki tun kina nan, Habibty tun muna wancan gidan namu, Big Daddy ya
ɗ
aura min aure.”
Ji maganar na yi kamar an buga min guduma a akaina, wai an
ɗ
aura masa aure, shine dalilin da yasa ya kaini aikin Hajji kenan, ni da mahaifiyata da ‘y
a’yana? Ya kaini aikin hajji sabida na basu dama su ci amarci shi da matarsa? Shine zai siya ni da da
ɗ
in baki, me ya sa duk maza suke haka ne? Wai ni Nana yaushe zan ji da
ɗ
in rayuwa? Yaushe wahala zata yanke mini ne? Wan irin abu ne wanna Turaki ya yi min,
ace ya tura ni aikin Hajji kawai ina dawo na tarar da shi da wata matar, to tukwicin aikin Hajji ne ƙarin auren? Ko kuma tukwicin ƙarin auren ne aikin Hajjin, ni bangane ba.
“Habibty! Habibty!”
Na ji muryarshi tana shiga kunnuwa na, sama sama.
“
Habibty dan Allah ki sauareni, ki ji me zance miki mana.”
Na fara zubar da hawaye, ina jin wani
ɗ
aci a raina, nama kasa magana sabida wani irin bugu da naji zuciyata na yi da wani irin ƙarfi, wanda zai iya cutar da lafiyata, da sauri na sami waje na zau
na, na ha
ɗ
a
kai da gwiwa na fara janyo kuka, amma ina ya gagara zuwa, sai wani yaji yaji da nake a cikin idona, wani ra
ɗ
a
ɗ
i da zafi, ga zazzafan bugu da zuciyata take yi.
Hannuna ya fara shafawa yana fa
ɗ
in.
“Habibty, Nana, kina jina.”
Kamar wacca
aka tsikara na miƙe tsaye na ƙwace hannuna, sai da na kalli Turaki na kusa mintuna goma, kawai na juya na kalli ƙofar fita, na yi waje a guje, ba shiri ya biyo ni yana fa
ɗ
in.
“Habiby ki tsaya dan Allah, Habibty ina zaki?”
Waje na nufa na fara ƙoƙarin
bu
ɗ
e ƙofa zan fita, Turaki ya yi saurin kama hannuna.
“Habibty ina zaki a daren nan?”
“Ka cika ni, ko ina nema wallahi gwanda naje, amma Turaki ba zan zauna a gidanka ba, bazan sake zama da kai ba, sabida kai macucine, kai mugu ne, ka zalunce ni, wa
llahi ban yafe maka ba.”
“Hasbunallahu wani’imal wakil, Nana dan Allah ki fahimce ni, ki ji me zance miki dan girman Allah.”
“Me zaka ce? Raina min hankalin zaka ci gaba da yi? Ka ce min Big Daddy ne ya yi maka aure, ko me? Ka yaudareni ka yi min ƙar
ya, a ko dayaushe ina tambayarka, amma sai ka ce zaka iya zama da a haka, ashe duk ƙarya ce, duk yaudara ce? Tun farko kasan bana haihuwa amma kazo ka yi min da
ɗ
in bakin cewa ka rayu da ni a haka, zaka aure ni a haka, amma kaje ka yi aure da wacca kake so,
wacca kake tunanin zata haihu ta tara ma zuri’a, to ni zan tafi zan haƙura da rayuwa da kai, zan je na yi wata sabuwar rayuwa, ko da babu farin ciki a ciki.”
“Nana dan girman Allah ki yi min kyakyawar fahimta, ƙarin aurena ba shi da nasaba ko wata alaƙ
a da rashin haihuwrki wallahi, ga yarinyar nan ki shiga ki ganta, ta fa
ɗ
a miki gaskiyya.”
“Har abada bana fatan Allah Ya ha
ɗ
a idona da na ta, kai kanka Turaki wallahi bana son nasake ganim fuskarka, idan kana da haƙƙi akaina Allah Ya saka maka, idan ni
nake da shi akanka na yafe maka, amma ka rabu dani, ka rabu da rayuwata, aure idan katashi ka auri goma su haifa ma ‘ya’ya dubu.”
Na fa
ɗ
a ina bu
ɗ
e ƙofar, ya yi sauri ya riƙe ni ya yi baya da ni, yasa key ya kulle ƙofar.
“Nana ba kya ganin dare ne?”
“Ko menene tafiyata yafi min.”
“Dan Allah ki yi haƙuri, ki bani dama na yi miki bayani.”
“Bana son bayaninka, ka riƙe bazai amfane ni ba, ka rabu da ni dan Allah.”
Na fa
ɗ
a ina jingina da jikin gate
ɗ
in, ba yanda Turaki bai yi ba na shiga ciki am
ma naƙi, na ce wallahi anan zan kwana asuba na yi na tafi gidanmu, sabida wani irin zafi da nake ji a cikin zuciyata, ko ganin Turaki bana son yi kwata kwata, babu abinda yake yawo a zuciyata sai zallan rashin mutunci da Turaki ya yi min, wai ya tura ni ai
kim Hajji sabida ya ci amarci, duk akan bana haihuwa, Allah Sarki ni, Allah ya kawo min mafita, amma tabbas nasha wahalal rayuwa, baya ga abubuwan da na fuskanta a rayuwata da Sardauna, yanzu ina fatan nasamu nustuwa da farin ciki, ina ganin kamar rayuwar
wahala ta zata ƙare, kamar labarin zai shu
ɗ
e ashe yanzu ya fara, shikenan wahala da wahala ni Nana, cikin murya kuka na ce.
“Allah na tuba Ya Allah, Allah karka maimaita min wahalal rayuwa da na shiga abaya Ya Allah, Allah na tuba Ya Ubangiji, Allah ka
bani ƙarfin da zan fuskanci wannan rayuwar.”
Haka na yi ta faman kuka, babu yanda Turaki bai yi ba, amma na yi banza dashi ko waigowa ma banyi ba, kawai so nake garin Allah Ya waye na tafi gidanmu, na je na yi kuka na gode Allah, Burina kawai Turaki ya
sake ni, na yi iddah nagama na shiga wata rayuwar, amma tabbas har abada har gaba da abada ma babu ni babu wani auren.
Legendspen
08129553971
SARTSE BOOK 3
Sayyid.
(15).
Da me zanji, Sardauna ya cuceni, wannan rashim haihuwar bazai barni na za
una a ko ina ba, daman ya fa
ɗ
a ya ce bazai ta
ɓ
a barina na aure wani ba, ga kalamansa sai tabbata suke, duk da yana halin jinya, amma Sardauna ya shuka mumunnan irin mai zafi a rayuwata, ya yi min SARTSE mai ra
ɗ
a
ɗ
i cikin rayuwata, ya gana min azaba, ya cuta
r da ni, ina tsaye anan dare ya yi nisa, yanda nake tsaye haka Turaki yake tsaye
yana kallona, ni kam nama juya masa baya, bayan wasu awowi ya matsu ya ce da ni.
“Habibty dan Allah ki shiga ciki mu yi magana, ki tuna kin fa ce zaki yi min uziri akan kom
ai, kar ki manta da kanki kika shaida irin son da nake miki, da kanki kika ce zaki rayu da ni duk tsanani da wuya, kin ce bazaki ta
ɓ
a barina ba, sabida kin tabbatar da irin ƙaunar da nake miki, dan Allah ki sauƙaƙa zuciyarki, ku sanyaya ta karki yi min SAR
TSE a zuciyata. Habibty rashinki zazzafan SARTSE ne ga rayuwata dan Allah dan Annabi Habibty.”
Maimakon sanyi, sai na ji wani zafi a maganganunsa, na maka masa wata uwar harara na juya baya, na sake rusa wani ihun ina fa
ɗ
in.
“Wallahi Turaki ka rabu d
a ni, ka ƙyaleni duk wasu maganganunka yaudara ne a ciki, ka ƙyale ni dan Allah.”
“Babu ƙarya, babu yaudara, babu algus a dukkan maganata Nana, wallahi sonki nake kinsani, kim yarda, dan Allah ki bani dama na fa
ɗ
a miki gaskiyya, na yi miki bayanin komai
.”
“Mitchewwww.”
Na ja wani dogon tsaki, a raina na ce. ‘Dan ya mayar da ni sabuwar shashsha shine zai ce wai ya yi min bayani, da ya samu ya yi min kalamai shikenan zanji sanyi, su maza da sunga mace na son su shikenan sai su yi duk abinda suke so,
sun san suna zuwa su yi mata da
ɗ
in baki shikenan, da raunin mu suke amafani wajen zaluntrarmu.’
Abu kamar wasa har aka fars kiraye kirayen sallah asuba, sai dai a yanzu na tsgunna daga jikin gate din, shima Turaki ya zauna daga gefe, har aka yi sallah
muna nan, gari yanayin haske na fara bubbuga gate
ɗ
in, Turaki ya fito bayan ya shiga yin sallah ya ce.
“Habibty ki tsaya na sauke ki a da kain.”
“Turaki wallahi ba zan shiga motar ka ba, ka rabh da ni dan Allah, ka bu
ɗ
e min na tafi ko na haura ta sam
a wallahi.”
“To ka taki motar nan dan Allah ki hau.”
“Na bar maka kayarka, ai daman da ku
ɗ
inka ka siya, to bana so.”
Na fa
ɗ
a ina ƙoƙarin fara
ɗ
ane gate
ɗ
in na haura, ganin ina ƙoƙarin hawa gate
ɗ
in ya sa Turaki ya ce.
“Bari na bu
ɗ
e miki, amma d
an Allah ki kar
ɓ
i wannan ki yi na mota.”
“Mitchewwww.”
Na sake jan wani tsaki, sannan na matsa gefe ya bu
ɗ
e, yana bu
ɗ
ewa na fita na fara tafiya, tin kafin naje bakin titi ma fara gajiya amma haka na daure na ci gaba da tafiya, ni da na fito kafin bak
wai amma har tara ban ƙarasa gida ba, duk na gaji na fita hayyacina, fuskata ta yi ja tana fitar da wani gumin wahala, ina tafe ina hutawa, har na ƙaraso cikin unguwarmu, nasa mayafina na rufe fuska ta yanda babu wanda zai ganni ya gane ni, a haka har na s
higa gidanmu, wanda yake cike da mutane masu shigawar Hajiya, kasamcewar jiya saukar dare ce, ina shiga ko sallama banyi ba na fa
ɗ
a
ɗ
akim gadom Hajiya, inda naga twins a kwance suna bacci, fa
ɗ
awa na yi kan gadon daga gefe na fara kuka, ina jin Hajiya tana
cewa.
“Waye ya shigo? Waye.”
Amma ta ji shiru, muryar Maman Amir na ji tana cewa.
“Anya kuwa Hajiya wani ya shigo, da an shigo ai nan za ayu.”
Hajiya ta ce.
“Wallahi kamar sautin tafiya na ji.”
“Gaskiyya ba kowa, amma bari a duba.”
In
a jinta ta gama leƙe leƙen ta tsakar gida, taje ta tura ƙofar waje ta dawo, ni kam kuka na ke yi ƙasa ƙasa, idona yanayin min zafi ma rashin bacci ga kuma uwar gajiya, ga gajiyar zama a jirgi, ga rabin kwana a tsaye, ga kuma uwar tafiya da na yi a ƙasa. Ba
jimawa wani wahalallen bacci marar da
ɗ
i ya
ɗ
aukeni, wanda banyi shi cikin da
ɗ
in rai ba, ina cikin baccin na ji ana cewa.
“Maamah! Maamah.”
Na bu
ɗ
e idona naga twins ne, na maka musu uwar harara na ce.
“Ku fita ku tafi wajen Hajiya.”
Ba musu su
ka sauka suka yi wajen Hajiya suna kuka, a loakacin na ji muryar Yaya Rumaisa tana cewa.
“Daman suna nan?”
“Eyh nan muka yo da su, jarabar uwarsu wazai iya.”
“Aifa ana can ana tashin hankali, ni na rasa me ya sa Turaki yake tsoron Nana wallahi, id
an suka jera sai ki gansu kamar ‘ya da uba, amma idan kika ga yanda yake rawar jiki idan ta yi masa magana sai ya baki takaici.”
Hajiya ta ce.
“Aini bana ma iya kallon shiriritarsu, yanzu dai suna can suna fama, tun muna can yarinyar nan ta fuskanci
wani abu ya faru, ta bi ta
ɗ
aga hankalinta, kai kishi masifa ne.”
“Babba ba ƙarama ba Hajiya, amma ita nata da iskanci.”
Wani abu na ji ya tokaremin maƙoshi, wato duk sun san da zancen auren na shi, shine ko a jikinsu lallai mutanen nan, to wallahi d
ani suke zancen Turaki ne ko shine autan maza na haƙura da shi, aure kam na yi abinda zan iya Allah Ya bada lada, amma tabbas na gama, na zauna na yi rayuwata na kula da tarbiyar twins, na sama musu farin ciki, shine kawai.
Ji na yi jikina yanayi min wa
ni irin tsami, ba shiri na tashi ma fito zan shiga kicin na
ɗ
aura ruwa, na ji salatin Hajiya, sai da ta gama ranga
ɗ
a salati sannan ta ce.
“Ke yaushe kika shigo gidan nan?”
Na yi mata wani kallo, na ce.
“Tun safe.”
“Me kike yi to anan? Ina gidan
naki?”
“Ya sake ni.”
Na fa
ɗ
a ima fara juyewa ruwan zafin da nasamu akam tukunya, cikin bawon wanka.
“Innullahi wa’inna illahir raji’un, Rumaisa fito kiji wani mugun zanci.”
Ɗ
aukan ruwa na yi, na nufi bakin famfon na kuna masa ruwa sanyi ya far
a zuba, Yaya Rumaisa ta ce.
“Nana kin cuci kanki, akam kishin banza kin rasa mijinki, miji mai sonki, nagartacce.”
“Na rasa
ɗ
in, ke kije ki aure shi.”
Na fa
ɗ
a ina ƙoƙarim shiga toilet.
“Sai kinci gidanku, kuma ki yi duk abinda kika ga dama, in
Allah Ya yarda bazan sake sa baki a lamarinki ba.”
“Kar ki sa
ɗ
in.”
Na fa
ɗ
a tare da shigewa ban
ɗ
aki, a yanda nake jin zuciyata cikkn gidanmu Hajiya kawai banza iya tsyaawa mu yi musayar yawo ba, amma duk kansu a wuya nake da su, wai sun san Turaki z
ai yi aure, amma ko a jikinsu suna jin da
ɗ
i anyi min kishiya, rashim haihuwata duk bai dame su ba. Haka na yi wa kaina ruwan zafi sosai, sannan na watsa ma fito, cikin jakar kayan Hajiya na duba doguwar riga na
ɗ
auka na sanya, na dawo na zauna, dole naje g
idan Turaki na
ɗ
auko kayana, da waya ta da duk wani abu nawa, kuma babu wani a gidan nan da zan sanya dan duk basu da gaskiyya, ina cikin
ɗ
akin na ji zuwan Yaya Radiya, tana zama Hajiya ta ce da ita.
“Kinji yarinyr nan ta kashe auren, wai ya sake ta.”
“Kai innullahi, yanzu tana ina?”
“Tana ciki, amma karki fara zuwa wajenta, yanzu zata zage ki kamar yanda ta yi min.”
Yaya Rumaisa ta fa
ɗ
a, Yaya Radiya ta ce.
“Zagi kuma?”
“Ga Hajiya nan ki tambayeta, har da ce min naje na auri Turakin, tsaba
r ta raina ni.”
“Lallai Nana, to ta ci kanta ita ta sani, babu wanda zai mata magana, ita ta yi asarar miji ba wani ba, har ta manta wahalal da tasha wajen Sardauna, tazo nan ta sami gata amma ina, shine akan ya ƙara aure take wannan abun.”
Ni haushi
n Yaya Radiya ma nasake ji da ta gama wannan maganar, na miƙe tsaye na ce.
“Ni Nana na gama shan wahala a rayuwa, zan tsaya na yi rayuwa cikin farin ciki ko da kuwa babu taimakon kowa a ciki.”
Ina fa
ɗ
in haka na fito daga
ɗ
akin, na shiga
ɗ
akin da suke
ciki, Yaya Radiya ta ce.
“Sannunki Nana, kin kyauta kin kashe aurenki.”
“Hhhhmmm, yanzu ku abinda kuka yi kyautawa ne? Akan bana haihuwa shine kuka bada gudummawar ayi min kishiya? Bance baya ƙoƙarin zama dani ba, amma a zaman ba dole sa ya ji bazai
iya ba sai ya sake ni, yafi min sauƙi akan yaje ya yi min kishiya, rashin haihuwa ai na Allah ne, wallahi kun ban mamaki kuma kun ban kunya, ina matsayin ƙanwarku jini
ɗ
aya, amma akan abin duniya koka goyi bayan ayi min kishiya.”
“Ke Nana kama bakinki?
Kina tunanin akwai wani abun duniya da zai sa ‘yan uwanki su cutar da ke?”
“To Hajiya mene? Duk sun sa za ayi min kishiya sabida bana haihuwa, amma babu wanda ya sanar dani.”
“Wai waye ya ce miki akan rashin haihuwa aka yi miki kishiya? Da alama bak
i samu zama da mijinki ba, kawai kina ganin mace a gidan kika takura ya sake ki kenan?”
Legendspen
08129553971
SARTSE BOOK 3
Sayyid.
(16).
“Nifa Hajiya ban ta kura shi