Showing 216001 words to 219000 words out of 265549 words
ya aureta, kawai dai kai suke son gasawa aya, shi da yake da matarsa ma, dole shiryawa za su yi, idan ka yi hakuri kana nan Aish
a zata nemeka, ni na san Ummi ba zata yarda Aliyu ya auri wannan yarinyar ba, ita hauka ce take dibanta"
"Ammy saboda kina mace ne, ba zaki gane ba, Aisha ta kai duk inda mace ta kai babu wanda zai ganta be ji yana sonta ba"
"Tohm sai ka gwada naka kokar
i, ni dai daga bakin nan na cire hannuna"
Turhan ya ji babu dadi.
"Wani abu Aisha ta fada miki ne Ammy? Kamata yayi ki goya min baya, duba yadda Ummi tana bin bayan danta duk kuwa da cin amanar da yayi, na tabbatar da ni ce ba zaki yarda na dauko Kameela
matar Aliyu na aje a nan ba"
"To me zai saka ka yi haka? Ka nemi wata ka aura idan har kana son auren ne"
"Aa Aisha dai, idan ba ita ba..."
Yayi shiru takaici ya saka Ammy tashi ta bar masa falon.
"Aifa sai dai a mutu, amman ba zan taba yarda Aliyu y
ayi min wannan cin kashin ba, bayan ya gama da ni ya rabi matata Allah kadai ya san abun da ya faru kuma yanzu yace wai zai aureta saboda kawai bakar kiyayya ba tare da na masa komai ba"
Ta juya fuska.
"Ita ma dai wani lokacin da matsalarta da gaskiyar
Ammy, ni ban ce ta raga min ba, amman ta daina sake jiki mana da wannan katon kwarton, ji yadda ta kyau dan Allah haka zai sakata gaba yayi ta kallo, macuci"
Ya hade yawu da karfi, ya saka hannunsa yana karawa rigar wuyansa fadi kokarin yagata take, yan
a jin kamar numfashinsa na danne, bani irin kishin Emily yake ji har na bala'i
EMILY POV.
Misalin karfe 9pm tana zaune falo Ummi na kara mata wasu darussan na rayuwa, Aliyu ya sauko Fatima na janye da hannunsa. Da suka kawo kasa sai Fatima ta sake sh
i ta nufi Emily ta kama gashinta tana yaryadawa a bayanata.
"Momy Dady yace in dinga rufe miki jiki"
Emily ta juyo ta kalleta, Ummi ta yi murmushi bata ce komai ba, Aliyu kuma ya kalli Emily kadan ya dauke kai.
"Uncle Aliyu yace zai koma gidansa gobe
, Momy zaki je? Zamu koma can ne kuma? Miyasa ba zamu zauna gidan Dady ba, Ammy tana sonki da Dady sai mu koma can har Uncle Aliyu ko?"
Ummi ta kalli Aliyu dake gefenta.
"Ina zaka koma"
"Gidana dake nan Ummi, zan fi jindadi, kuma yana da kyau mu kiyay
e dokokin ubangiji"
"Hankalina zai fi kwanciya ka zauna a nan, kwantarka ake ne zaka koma can? Ina jin nan da sati biyu ma za mu koma Abuja gaba daya"
"Aa Ummi indai kika ce zaki sama min masu tsoro zan yarda shi ma saboda ki zamu kwanciyar hankali ne
, amman Addu'a ta ashe ni, zan koma can In Shaa Allahu"
Emily ma ta kalleshi tana jin babu dadi ganin take kamar idan baya cikin gidan ba zata sake sosai ba, yanayin ya sauya har ta kasa boyewa ta cire gashinta dake hannun Fatima ta mike tsaye ta bar fal
on.
ONE WEEK...
Ba banza aka bar Aliyu ba, daman fa yarbawa sun iya mugun abu, idan ba haka ba taya Aliyu zai sake ta, daga kawai ta kai yarinya gurin Babanta, gashi har ya fadawa Ummi ta saka guba a abinci, ko Ummi bata nuna mata bata son zuwanta gi
dan ba ta san ba zata sake aminta da ita ba, gashi yanzu ko zuwa gidan bata son ta yi.
"Kai gaskiya ba banza ba, kalli ko Bakar Barakar nan dan ba zan ce Mama ba ni bata haife ni ba, kamata yayi abbah ya koreta gaba daya daga gidan nan kamar kare, amman
be yi ba sai saki daya yayi mata har da cewa wani wai baya son kowa ya fitar da maganar ta yi zaman yayanta, yana nufin zai maida ita kenan, shiyasa take ta shige min tana kiran Aliyu tana wani bani shawarar munafukai, ashe ta san Emily yarta ce shi take h
angowa"
Magana take da kanta tana ta safa da marwa tana dora hannu a kai tana saukewa, ita a yanzu babu tashin hankalinta kamar yadda Aliyu ya juya mata baya, sakonta be reply ya bi yayi blocking din number ta ma, Ummi ma bata amsa mata idan ta kira kuma
bata maida mata da amsar sako, gashi yanzu Aliyu gida daya suke rayuwa da Emily.
"Wai to shi wannan Turhan din in ban da sakarai ne shi haka zai zuba ido wani ya karbe masa mata? Ayi mutum kamar dusa, wannan bakin ciki ina zan kai shi? Wallahi Aliyu be m
a dace da yarinyar nan ba, ga kafirci ga shi bata hanyar aure aka aureta ba"
Ta fashe da kuka ta sauke hannu ta sake dorawa, haka take kowace rana ta saka wannan ta kwance waccan ita kadai domin yan'uwanta babu mai tayata gaba daya ma basa son zancen Ali
yu, su sun ji dadin haka daman ba sa son aurenta da Aliyu gashi yanzu an rabu kuma sanadin haka Abbah ta saki Mama Baraka, Hajiya sai shiga da ita take na balmar baka tana son mijinta ya kori Mama Baraka daga gidan gaba daya.
Kuka Kameela ta ci sosai ta
rasa ina zata saka kanta, ko ba Emily ba ba zata so Aliyu ya so wata ba balle kuma Emily, mace da ita kadai ce ta hana ta walwala ta kuma rabata da mijinta, kuma sanadinta ta sakawa mijinta guba gashi yanzu shi ne silar komai, ba dan haka ba da duk abubuwa
n da suka faru ta san Aliyu zai iya yafe mata su zauna domin tana son mijinta, amman yadda Ummi ta dauki zafi ta san zata sha wahala kamin ta samu kanta. Balle kuma Emily tana gidan ta dauke masa hankali da kyaunta ta san ba zai tsaya tunaninta ba, daman t
un farko kyaun ne ya dauki hankalinsa ba komai ba.
"Ni ban san ma san miyasa wannan Mama Baraka ta hadu da bature ba har aka haifo wannan yarinyar, kuma abu ya zo ya zama kamar na gida ni na shiga uku, shiyasa na ki ya rabu da ita, ashe ita wannan Mama B
arkatar tana nan tana shirya masa soyayyar Emily ni aka maida mahaukaci"
Ta kwanta ta tashi ta rasa ma wane irin tunani zata yi, kuma ta san idan ta yi sake bata hankara ba zata ji an daura musu aure domin ba a banza aka bar mijinta ba, kamar yadda aka y
i ma Babansu.
Ta zauna tana ta cizon baki, babu wanda ta fado mata a rai a yanzu kamar Tasmia zuciyarta ta raya mata babu inda zata samu mafita sai a gurinta. Ta janyo wayarta ta duba sai ta tuna bata da number Tasmia ta goge tun a wacan lokacin da suka s
amu matsala. Sai dai abu mai sauki ta can gidansu, bata da tabbacin zata iya samunta a gidan amman saboda neman mafita ta dauki key din sabuwar motar da Momynta ta siya mata ya fita ba tare da sanin kowa ba ta dauki kafa zuwa gidansu Tasmia.
Ta isa gidan
tana ta sake sake kuma tana dan jin kunya da nauyin Tasmia na abun da ya faru tsakaninsu, be ma kamata ace ta je neman taimakon Tasmia ba amman saboda bata da wata mafita sai wannan ya saka ta aje komai a gefe ta faka harabar gidan na masu rufin asibiti b
ayan mai gadi ya bude mata gate.
Ta rufe motarta ta nufi cikin gidan tana rike da key ta a hannu da green din hijab dinta idan ka ganta ba saka yi zaton zata yi fitina ba.
Ta shiga da sallama a tsakar gidansu Tasmia jikokin da suka nan suka amsa mata su
na wasa da ruwa. Su ta tambaya ko tasmiya na ciki suka ce mata tana cik sai ta nufi kofar falon ta shiga da sallama. Suka amsa mata da mamaki domin Tasmia ta fada musu sun samu matsala da Kameela sai dai bata labarta musu gaskiya maganar ba kawai ta ce sab
oda Kameela tana da zafin kishi ne. Mamasu ta amsa mata da far'a kanen kam sai kallonta suke.
Ta kai har kasa ta gaishe da mamansu sannan ta tambaya Tasmia ko tana ciki, maman ta tambaya ko lafiya ta amsa da babu komai tana dariya. Sai aka nuna mata daki
n da Tasmia take, ta nufi dakin ta shiga da sallama tana yaye labule. Ita kanta Tasmia ta yi mamakin ganinta har tana tsoro domin bata san da me ta zo mata ba.
"Yan bautar kasa wato kun gama babu ko labari babu ziyara?"
"Ke da wacce kika zo? Ni da ke f
a kai ta san kar ne"
Tasmia ta fada sannan ta tashi zaune da kyau kar a shammace ta. Kameela ta tabe baki.
"Ni da alheri na zo miki, ba sheri ba"
"Koma da wacce kika zo ni daidai nake da ke"
Kameela ta zauna ba tare da an mata tayin zaman ba.
"Ke
dan Allah ki bar abin da ya wuce ya wuce mana, ni ma yanzu ina cikin tawa matsalar mafita nake nema shiyasa na rugo a guje na zo gurinki"
Tasmia dai kallonta kawai take.
"Dan Allah ki ba ni aron hankalinki kuma ki natsu sannan kuma ki fahimce ne"
"I
na jinki"
Kameela ta yi shiru na lokaci can kuma sai ta ce.
"Emily ce matsalar, amman ba zan fada miki komai ba sai idan zaki taimaki kanki ki taimake ni"
"Zan taimake ki ba tare da sanin me ya kawo ki? Hajiya ki fada min damuwarki kawai ba wani noke
noke"
Kameela ta rage murya ta marairaice ta fara karanta mata damuwarta sannan ta koro da labarin Emily. Tasmia dai sai saurarenta take har ta kai aya. Kameela ta juya makullin motar dake hannunta tana kallon Tasmiya bayan ta gama bata duk labarin Emil
y da kuma abun da ya faru.
"Tohm yanzu ni miye nawa a ciki? Har kike ba ni wannan labarin?"
"Tasmiya aurena fa ya mutu?"
"Na san aurenki ya mutu mana, abun duniya ai baya boyuwa na ji tun kamin na dawo garin nan kuma yanzu gashi kin kara fada min, dalil
in da zai kawo ni cikin matsalar ne ban sani ba"
"So nake ki taimaka min, ni biyanki ne ma zan yi Wallahi, na san da can kina son Aliyu ai ki yi duk yadda zaki iya ki dauke hankalinsa daga gurin kafirar nan, ni da ta aure shi Wallahi gara ke ki aure shi"
Tasmia ta yi dariya
"Wato Kameela kin dauke ni marar hankali marar wayo ko? Ke ce mai wayo? Bayan duk abubuwan da suka faru yanzu ni kike son na zame miki tsanin hawa? Miyasa ke ba zaki yi yakin da kanki ba?"
"ba zaki gane ba ne, gaba daya baya saurar
e ni yanzu ya juya min baya kamar ba Aliyuna ba, daukar yarinyar da na yi na kaita gurin Turhan har Aliyu ya sake ni ni sai nake ganin kamar ba banza aka bar ni ba, Wallahi idan Aliyu ya auri kafirar nan an gama da ni gaba daya, uwarta ta yi kishi da uwata
ni kuma na yi kishi da ita? Da dai ita ta aure shi kara ke"
Tasmia ta tabe baki.
"Ni yanzu ina da wanda zan aura masa Kameela, kuma mijinki mai wuyar sha'ani da shegen wayon tsiya"
"Ai mataki zamu dauka ko ta halin yaya, idan kika ba ni hadin kai ma
har acit sai mu watsa mata fuskar ta lalace daman ai kyau ne yake jansa"
Tasmia ta yi murmushi a nan ta gane Kameela so take ta jefata a matsala.
"Ki yi kishi da ita taya? Ai ke ba Aliyu kike aure ba, kuma tun da kika ga ya sake ki saboda ita ya nuna
miki ta fiki muhimmanci kenan, haka ya buga min warning lokacin da muke can fa saboda ita, kin san mijinki dan duniya ne duk inda aka juya sai ya gane mutum, dama kin hakura domin yadda kika cika idda abu ne mai wahala ya maida ke, balle kuma kin ce har ma
haifiyarsa bata sonki a yanzu, yo daman Kameela uban waye zai so ki? Kin ga yanzu ni dake ai mun zama daya, wai ke uwar gori kin ce ban da aure ko? To yanzu ni da ke waye shegen? Ni Wallahi Emily ma tausayi ta ba ni da kika ba ni labarinta, daman tun da na
ganta ganin farko na fahimci tana cikin damuwa, kuma na kulla abota da ita, sai gashi son zuciya ya dauke ni na so cutar da ita ashe da na shiga uku, ni yanzu na bibiye mijinki kamar wata karuwa? Ko an fada miki karuwanci naje can ba bautar kasa ba? Kuma
ni yanzu na samu wanda zan aura, kuma idan ba ki bi a hankali ba duk abun da kika fada min sai na fadawa Emily da Aliyu"
Kameela ta fusata.
"Tasmia idan ke ba karuwa ba ce wacece ke? Dan ubanki nan kika bar garin nan kika tafi har Ph bautar kasa da kika
je kuma kika kama hanyar gida baki zauna inda kowa ke zama ba, kika dinga bibiyar mijina wai saboda kin yi kwantain, yanzu saboda kin samu damata na zo har shegen gidanku neman shawara zaki fada min magana, kutumar ubanki Tasmia, idan kin fasa tausayin Em
ily ko fada mata abun da na fada Allah ya tsine miki albarka"
Tasmia ta yi mata sowa da baki....
"Oohhhhhhhhh an dai ji kunya, ke da kika takama kin fi karfin mijinki yau ke ce namiji ya gagareki, kike raba ni saboda ki samu shiga, ke yanzu dan Allah ba
ki ji haushin kanki ba ma? Kim san kina Aliyun uban waye ya saka ki hauka? Kanki farau kishi mahaukaciya yar marasa tarbiya.."
"Ubanki ne shegiya mai warin talauci, kuma muna nan dake zaki gan ni da Aliyu, ni da shi mutu ka raba ne takalmin kaza dan ubaki
Zubairu"
Tasmia ta rufeta da duka suka fara kaiwa juna naushi sai da kanen Tasmia da mamansu ta shigo aka raba su.
"Lafiya"
"Mama ki bar ni na ci uban yarinyar can, ganin take saboda suna da kudi zata iya taka kowa? Muma na ao muna da rufin asiri ya
r iska, daman ina rike da ita a zuciyata, idan ba ke wawuya ba yaushe zaki yi fada ni kuma yanzu ki wanko kafa ki zo wai na taimaka miki ke dakikiya ko.? Kara da Aliyun ya sake ki ai, kuma da yardar Allah sai ya auri Emily ke kishiya uwarki kishiya"
"Ke
ce yar iska marar tarbiya, mai bibiyar mazajen mutane, ko yanzu wa san mijin wa kika kwato? Muna nan da ke Aliyu ba zai auri Kafira ba, haka kuma ba zai auri yar iska irinki ba"
Mama ta rufe baki.
"Aa ahhhhh kin ga wannan.... Amm... Kameela kike da sun
a ko? dan Allah kama hanya ki tafi bana son fitina, ba alfahari ba ni dai yarana ba su da abokin fada, kuma ba zan su ki yi abun da zai saka mu da ke mu yi ta nadama ba, dan Allah yafi kin ga karfi ma ba daya ba, daman tun farko na ganki na san ba lafiya b
a"
Ta dauki makullin ta dake can karshen kofa ta fice tana ya huci sai zagi take jefowa Tasmia idan ta yi yunkurin ramawa Allah Mamanta ta hana. Kameela ta fito rai a bace ta shiga motarta ta juya kamin mai gadin ya bude mata gate ya daga masa hankali da
horn kamar zata tashi gidan.
[8/8, 9:58 PM]
𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮
𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆
: *
🍒
ABOKIN RAYUWA
🍒
*
*© Khadeeja Candy*
Page 6
️
⃣
5
️
⃣
"Idan Hajiya Baraka ta yarda mun tafi dake kuma Ammy ta amince toh wannan makarantar ya kamata a sakata, dama
n ina jin ana fadar suna karatu sosai"
Emily ta yi murmushi kadan.
"Na manta ban tambaye ki ba, ko kina zuwa coci a lokacin da kike can? Kar ya zama mun tauye ki a nan ki kasa mana magana"
Emily ta kalli Ummi ta mamaki.
"Aa bana zuwa coci ko a can"
"O
kay, tohm yayi kyau, idan kin gama kallon sai ki shiga Kitchen ki wanke kayan da muka ci abinci da su, zan shiga na kwanta"
Ummi ta mike tsaye ta nufi hanyar Stairs, Emily ta bita da kallo tana murmushi, sosai take jindadin yadda Ummi take daukarka kamar
wata wanda ta dade a gidan ba bakuwa ba, akwai mai aiki da Ummi zata iya sakawa ta yi wanke amman ta zabi ta sakata haka ya faranta mata rai, haka take mata idan za a jera abinci ko a kwashe kayan ita da Nafeesa suke kwashe, su kai Kitchen. Ummi na haurawa
sama Emily ta tashi ta shiga kitchen ta fara hada kayan ta daurayewa kamin ta saka kumfa.
Tana tsaka da wanke wanken ta ji muryar Aliyu ya shigo falon da sallama, duk yadda take zumudi da marmarin ganinsa bata aje ta fita falon ba, har sai da ya leko Ki
tchen din yana zaton Ummi ce a ciki, don ya san halin Ummi ba girkin kowa take ci ba, haka kuma bata yarda kowa yayi ma mijinta girki ba sai ita.
Ta juyo ta kalleshi suka hada ido, sai suka sakarwar juna silent