Showing 66001 words to 69000 words out of 265549 words

Chapter 23 - ABOKIN RAYUWA COMPLETE

15 Sep 2026

206

gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyar

sa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake

yi ma ginin ba.

Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har

tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita.

Tun

daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na s

auyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana c

ikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage.

Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna

ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba.

"Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos

ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa"

"Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan b

angaren ba"

"Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na d

awo Aisha"

Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka.

"Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tas

hi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?"

Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa t

a bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya s

higo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa.

"Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutan

en Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida"

Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin ma

haifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina

ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban

yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska.

"Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa"

"Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke"

"Ko kawa ba ni da a garin nan balle

na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa"

"wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne"

"ina yi saboda na samu abun da zan ci"

"Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda

da kaddara"

Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne.

"Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga

dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?"

"Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na

musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi"

Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi.

"Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki"

Ya fada, a

she kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abi

nci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa...

Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin."

***. ***. ***

Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar

kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce.

"Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin baki

nciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...!

Yawancin irin wa

ɗ

annan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi.

Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye

tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?'

Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai d

a na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ru

wan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa ha

ɗ

ari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...'

Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni ka

mar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da

Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na y

i da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa.

Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa k

arasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na kar

ba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace.

"An daura aur

ena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kaw

o amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce"

Ina daga zaune na daga kai na kalleshi.

"Ba zaki ce komai ba"

Bance masa komai ba bayan kallons

a da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu.

"To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data r

ike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba"

Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe...

D

on't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

Kuma karku manta ku yi sharing

[5/4, 6:26 PM]

𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮



𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆

: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

🍒

ABOKIN RAYUWA

🍒

*



*© Kha

deeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍

️

Page 2

️

⃣

1

️

⃣

Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na

sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku.

Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje

ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi.

Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa su

ka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace.

"Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?"

"Eh"

Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da koraf

ina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da y

ake yawan yi min.

A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban s

an mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta sai ranar. Yace da abincinta ta zo da komai nata, kuma wai bana masa biyayya abu kadan zan fara cewa ba shi da adalci ina masa ihu da Allah ya isa. Iyayensa ma suka goya masa baya mai garin ya rufe ni da fada.

"Ke mu fa irin tarbiyar da kuke a can ta arna ba ita muke a nan ba, tun da har kin yi aure kuma kin musulunta ya kamata ki watsar da wannan dabi'ar"

Mahaifiyarsa tace

"Ai matsalar auren tun farko bata san musulunci ba ko kuma bata tashi a cikinsa kenan

, su fa tarbiyar su da auratayyarsu dabam take, musulunci ma ai suna yi ne kawai a baki"

Mai gari ya fadi nasa iyayensa da shi kansa su fadi na su, na rasa ya zan yi sai kuka nake ina bashi hakuri.

Da muka dawo gida sai ya fara dukana irin dukam da be ta

ba min ba, dukan da zaka rantse dansa na kashi ko na aikata wani criminal abu, ina bashi hakuri yana duka wai abun nawa ya wuce ina fada a makota cewar yana bari na yunwa da sirrin gidansa ya kai har na dauki kararsa na kai gurin mai gari a nemi tozartashi

.

Duka yayi min ba na wasa ba, yana dukan yana min gorin wai daga ya taimaka ya tsamoni daga wuta da yanzu idan na mutu wuta zan tafi. "Iyayenki ma suna can cikin azaba, saboda sun yi shirka da Allah, kuma Allah kadai ya san ta hanyar da aka same ki, shiy

asa kike butulu, matar ma data rike ki yanzu ai gudowa kika yi kika barta, ni kuma na dauko ki na musuluntar da ke na aureki amman kina min butulci, idan ba ni ba wane namiji ne zai auri arniya ya kuma ba a kawo ta da komai ba, marar asali ma irinki"

A lo

kacin ne kalamansa suka fi yi min zafi da daci fiye da dukan da yayi min, na ji kamar ace ina da ikon da zan zare numfashi daga jikina na manta da kowa da komai. A daren na sha kuka washe gari na dora haka na kwashe kwana uku bana iya komai sai kuka. Abun

da ban sani ba be sani ba shi ne, ashe lokacin da ya doke ni ina dauke da cikin dansa, shi be sani ba saboda ba nice a gabansa ba, ni kuma tunani da tashin hankali da nake ciki be bar ni na ankara ba, daukewar da al'ada ta yi min na tsawon wata hudu ban ga

ne ba saboda hankalin ba nan yake ba, gashi kuma cikin fari ne ban san komai akan ciki ko haihuwa ba, domin a gidan marayun da muke zaune ban da karatu da sana'a ban maida hankali gurin koyon komai ba ko kuma sanin wani abu wai shi ciki da haihuwa.

Sai da

ciki ya kai wata biyar sannan na gane cewar ina da ciki shi ma Malika ce ta fada min.

"Wata nawa ne Aisha"

"Ni ban sani ba, ni na dauka ko yunwar da nake fama da shi ne ya janyo cikina yayi girma"

Ta yi dariya.

"Kai Aisha kina da wauta, ga abu har ya

fito yaushe rabon da ganin al'adarki?"

Na tsaya tunani ni kam bana ma iya tunawa. Ta bani shawarwarin yadda zan yi kuma ta fada min na tafi asibiti. Na dawo gida ina ta murna da dare da Khaleefa ya shigo na masa maganar sai yace min ai ya sani, shi mahauk

aci ne da ba zai gane ba. Na yi mamaki ya gane amman be taba min maganar ba kuma be nuna min komai ba? Da na masa maganar zuwa asibiti sai yace shi ba shi da kudi yanzu na bari sai gaba idan ya samu kudi.

Ma zan yi a lokacin idan ba hakuri ba, na san ba d

an ba shi da kudin ba, domin yana cikin shirye shiryen bude shago a kusa da gida ne, idan kuwa ba shi da kudi ba zai bude ba, nice ba ya son kashewa kudin, sai na bawa zuciyata hakuri na saka masa ido, na jidadi samun ciki domin ya dauke min damuwa sosai b

an sani ba ko dan saboda ina da son yara ne ko kuwa dai saboda ina kurciya ne, wata kila kuma saboda ina jin cewa zan samu iyali ne, ma'ana dai zan samu dan'uwa na jini daga gareni. Kusan sai ya dauke min rabin damuwa da tunanin da nake idan na ji motsins

a sai farinciki ya baibaiye ni.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login