Showing 147001 words to 150000 words out of 265549 words

Chapter 50 - ABOKIN RAYUWA COMPLETE

15 Sep 2026

190

zauna kusa da Aliyu. Cikin murna da farinciki take kallon Aliyu.

"M

adallah Aliyu ne a gidan na mu yau?"

"Ni ne Ammy ya jikin na ki"

"Jiki Alhamdulillah Aliyu ina samun sauki, ashe ka samu shigowa"

"Eh kin san daman na ce zan shigo na duba ki, sai gashi kuma wani uzurin ya taso aka yi daidai, a airport na hadu da Turhan

ai sai muka zo tare"

"Maa Shaa Allah, haka fa ka fada min zaka zo ai ka huta baka tsaba alkawari uwarka ta yi farar haihuwa Aliyu"

Ammy ta fada har lokacin bata kalli inda Turhan yake ba. Turhan ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, Aliyu ma ya ji babu

dadi domin Ammy tana kokarin muzanta abokinsa ne a gabansa which it's not fair.

"Amman dai jikin da sauki sosai ko Ammy?"

"Na samu sauki Alhamdulillah, ai na ma fadawa abokinka ba sai ya zo ba, kawai be ji magana ta ba ne daman be saba ji ba"

"Haba Amm

y taya baki da lafiya kuma ki ce kar ya zo? Ai ba zai yiyuwa ba, ke fa mahaifiyarsa ce Ammy ki rika duba wannan"

"Zuwansa ba zai rage ni da komai ba balle ya kara ni, rabin ciwon nan ba shi ne silarsa ba? idan ya zo ai ba da lafiya zai zo min ba, kuma ina

da masu kula da ni nan yayan yan'uwa sun ce wadatar, idan za amin allura kullum sai Nurse ta zo, Likita kuma kullum yana zuwa duba ni, saboda na fada masa ni bana son asibiti ko da mutuwa ce a bar ni na mutu a gida, kaga shi kenan abokinka ya huta ba sai

ya sake zuwa kasar nan ba sai yayi zamansa a can daman haka ubansa yake so"

Turhan ya kalleta felling hopeless cikin murya mai rauni ya ce.

"Wani dan kirki ne zai yi fatan mahaifiyarsa ta mutu ya huta? Ammy ya kike magana haka kamar mai magana da makiyi

nta? Danki ne fa ni jininki, na rasa ya zan yi na kawar da wannan bakin shatin dake a tsakaninmu, Ammy kina tunanin all this while abun nan dade yake min? Ko tafiya kika yi kika bar ni wannan abun ba zai barni na samu salama ba, Ammy ni ma ina cikin damuwa

gaba daya yanzu bana jindadin rayuwar da nake, abun da a aikata kuskure ne kuma ni dan'adam ne aziji"

Ammy ta girgiza kai.

"Aa abun da ka aikata ganganci ne ba kuskure ba, da gangan ka aikata, saboda baka kallo da daraja irin ta uwa, kuma abun da ka yi

min ai ka kyauta tun da ka samu tukuici, Allah ya maka albarka Turhan na gode"

Aliyu ya ce.

"Ammy ki yi hakuri dan Allah ki yafe masa abun nan ya wuce"

"Na yafe masa, amman wucewar wannan abun? Sai na koma ga Ubangijina, ni kadai na san me nake ji, yaro

n nan shi kadai Allah ya ba ni, idan kai ka manta mahaifiyarka ba zata manta ba Aliyu, irin fadi tashin da na yi akan na samu ganin yaron nan, na wahala a gidan mahaifinsa kuma na wahala kamin a bar shi ya zo gurina, na dauki yar mutane na aura masa da tun

anin hakan zai saka na samu dana da zuri'arsa a kusa da ni, amman ya watsar ya karyata duk wata halayya tasa dana fadawa yarinyar nan, marainiya ba uwa ba uba, yanzu Allah kadai ya san halin da take ciki idan ma tana raye, bata da kowa sai Allah bata da wa

ni wanda zai nemi ya san halin da take ciki tun da bata da dangi, yarinyar nan ta yarda da ni amman Turhan ya rusa duk wannan ya nuna ba ni da muhimmanci a garesa kamar yadda ubansa ya nuna min"

Ammy tana maganar hawaye ya sauko idonta, Turhan yayi kasa d

a kansa ya saka hannunsa ya rike goshinsa idonsa suka cika da hawaye, ba na tausayin Emily ba na bakinciki daya saka mahaifiyarsa har ta zubar da hawaye akansa gaban abokinsa.

"Wane irin muhimmanci Aisha take da shi a gurinki har haka Ammy? Da har zaki zu

bar da hawaye akan abun da ya faru?"

"Irin muhimmanci da baka da shi"

Ta amsa masa kai tsaye da kakkaurar murya.

"Indai saboda ni ka zo, toh ka hada kayanka ka koma bana bukata, ka bari idan na mutu sai ka zo jana'iza"

"Subhanallahi Subhanallahi"

Ya m

aimaita har sau uku sai Aliyu ya dafa shi.

"Turhan fita waje ka jira ni"

Ya tashi cikin wani irin yanayi na bakinciki da ya fice falon, sai da ya fita sannan Aliyu ya ce da Ammy.

"Ammy bana son na tunatar da ke abun da kika riga kika sani, na san kin so

Emily da Turhan kin tsara zamansu, amman haka be samu ba baki tunanin wata su din ba alheri ba ne ga junansu? Kuma haka Allah ya tsara shi da ita babu dogon zama, kuma Ammy karki manta duk yadda zaki so Emily Turhan danki ne, na san be kyauta ba amman fus

hinki a kanki da damuwarki zai iya janyo masa matsala a rayuwa ko ba yanzu ba a nan gaba, kuma Ammy Turhan yayi nadama sosai yanzu haka zancen da yake min yana son ya saka kudi mai kauri akan nemo Emily, abun ya dame shi ma, ki yi hakuri Ammy"

Ammy ta yi

murmushi.

"Allah ya maka albarka Aliyu, ka san muhimmanci uwa shiyasa ka fadi haka, tafi ka tafi na gode"

"Shi kenan Ammy Allah ya kara sauki ya baki lafiya"

"Ameen Allah ya maka barka"

Ya mata sallama ya fito falon a jikin motar da suka shigo ya samu

Turhan ya jingina fuskarsa dauke da damuwa. Aliyu ya saka hannayensa aljihu yana sauke ajiyar zuciya ta dayan bangaren abokinsa ya ba shi tausayi, sai dai kuma idan ya tuna labarin da Emily ta ba shi sai ya ji kamar be tausaya masa ba.

"Turhan am sorry i

yaye sai lallabawa"

"Haka take fada min maganganu marasa dadi a duk lokacin da na zo, kuma ta sani na yi iya kokarina gurin neman yarinyar nan, ban same ta ba toh ya zan yi? Kana jin tana fadin bata san halin da Aisha take ciki ba, ni kuma da nake cikin w

annan halin bata jin tausayina na rasa ya zan yi"

"Da sannu komai zai zama daidai In Shaa Allah, wai taya ka yi Aisha ta subuce maka.?"

Madadin ya amsawa abokinsa sai ya ce

"Ita ma fa yarinyar ta jefa ni a matsala, miyasa ta amince da auren nan tun fark

o fisabilillahi"

"Allah ya kawo sauki, ni zan wuce abun da zan fada maka shi ne ka yi hakuri da mahaifiyarka kuma ka yi ta addu'a"

"In Shaa Allahu, ma gode Aliyu, bari na yi ma direban magana sai ya kaika gida"

Aliyu ya shiga motar Direban yaja shi zuwa

gidansa, a mota Aliyu ya gwada kiran Number Emily ya jita a kashe sai ya aika mata sako.

"Are you okay?"

Domin ya san ya kamata ace ta kira shi bayan riskar sakonsa, and maganar Ammy ta taba shi na cewa bata da wanda zai damu ya san halin da take ciki t

un da bata da kowa. Bayan direban ya aje shi ya juya shi kuma ya shiga gidan da yayi datti yana mamakin taya haka ta faru domin yana da mai gyara masa gidan every week. A falo ya samu Fatima na ta bachi har lokaci akan kujera hannu ya kai ya taba jikinta y

ana mamakin wane irin bachi ne take haka, sai ya ji shi da dan zafi kadan. Mai kula da harabar gidan ya shigo yana masa sannu da zuwa Aliyu ya amsa yana tambayar ina mai gyara gidan.

"Tun da ta tafi bata dawo ba, bata fada maka komai ba tace dai zata je g

anin gida ta bada keys a aje maka"

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bawa Aliyu da hannu biyu. Aliyu ya mika masa Atm dinsa ya fada masa code sannan ya fada masa inda zai tafi ya samo musu abinci mai kyau...

Sorry ku yi hak'uri gobe zan yi l

ong page in Shaa Allahu.

[7/2, 6:50 PM]

𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮



𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆

:

🍒

ABOKIN RAYUWA

🍒

*



*© Khadeeja Candy*

Page 4

️

⃣

5

️

⃣

Kamin yaron daya aika ya dawo Aliyu ya shiga ciki yayi wanka ya canja tufafi sannan ya dauki wayarsa ya kira Mama B

arakat ya tambaya ko tana gida.

"Eh ina gida Aliyu ko ka shigo garin ne?"

"Eh na shigo kuma yau nake son na shigo gurinki saboda ina son komawa gobe kin san aikin na mu babu daga kafa"

"Haka ne to sai ka shigo"

Ya sauke kiran sannan ya fito falo yayi s

allah yana sallamewa aka yi knocking, knocking din da ya tashi Fatima ta farka idonta har sun yi ja tsabar bachi, Aliyu ya karba ya rufe kofar.

"Yaushe muka zo nan?"

"Kina bachi little princess"

Ta yi mika

"Kai ka dauko ni?"

Ya risina inda take zaune

yana kallonta da murmushi a fuskarsa.

"Eh kin tashi lafiya?"

Ta kalli falon.

"Nan gidanka ne?"

Ya daga mata kai.

"Ashe kana da wani gida Vito ma gida biyu yake da shi"

"Good taso ki wanke baki ki yi wanka sai ki ci abinci ki yi sallah"

Ta kalli sha

ddar dake jikinsa.

"Kai ka yi?"

"Eh"

Ya kama hannunta suka sauka tana fada masa kanta na ciwo, ya shiga da ita dakinsa ya nuna mata bandaki da yadda zata yi komai sannan ya fito ya dawo falon ya zauna yana taba wayarsa, har a lokacin sai da ya gwada kir

an Number Emily ya ji ta a kashe. Yana ta nazarin abun da zai saka ta kashe wayarta kuma ta dauki lokaci har haka bata kira ba bayan sakon da ya tura mata, duniyar tunani ta dauko shi daga can bangaren Emily zuwa na Turhan idan ya ce be ji tausayin abokins

a ba yayi karya, ya san da zarar Emily ta bayyana a rayuwarsa komai zai zame masa daidai, sai dai kalamansa na dazun cewar da laifin Emily na amincewa ta aure shi ya sanyaya masa guiwa, jikinsa kuma yana ba shi cewar Emily ta yi gaskiya ko Ammy ta san da F

atima a matsayin jikarta abu ne mai wahala ta bar mata ita balle kuma Turhan, hakan ya saka shi ya ji lallai ya kamata ya bar garin Kaduna gobe gudun kar makamancin abun da ya faru a Airport ya sake faruwa, gashi kuma yana son ya san halin da Emily take ci

ki domin rashin samun wayarta da kuma maido masa da amsar sakonta ya saka shi a damuwa.

A tare suka ci abincin da Fatima tana ta fada masa mafarkin da ta yi, ya rigata koshi a dole ya jira sai da ta koshi ita ma sannan ya kwashe kayan ta bishi Kitchen tan

a kallo komai ta gani sai ta taba ta tambaya, ko ta fadi Momy na irinsa.

"Fatima Zaki iya zama a gidan nan ke kadai naje wani guri na dawo?"

Ta lake kafada

"Aa ba zan zauna nan ba, sai dai mu tafi tare"

"Ba zan dade ba kuma zan iya bar miki wayata ki y

i game ki yi kallo"

"Duka na kalli komai na cikin wayar ni bana son zama"

Ya rasa ta ina zai fara rarrashinta ta zauna domin baya son tafiya da ita gidansu Kameela, na farko dai yana ganin hakan kamar cin fuska ne ga Kameela na biyu kuma iyayenta ma ba l

allai su fahimce shi ba domin ko kowa be gane yar waye ba Kameela zata gane kuma karamin aikinta ne ta fallasa shi a gabansu.

Ya mika mata dayar wayar da ita ya fi aiki da ita ya dauki wanda ya bata dazun ya saka aljihunsa.

"Wannan baki san me ke ciki ba,

na kunna data zaki iya duba duk abun da kike so a YouTube ki kalli cartoon kuma ki sauke duk game da kike so, Momy ki na na san zata kira ta wannan wayar idan ta kira sai ku yi magana kamin na dawo?"

Ya karba ba dan ranta ya so ba, can ta kalli hotonsa d

ana Kameela dake makalle a falon.

"Waye wannan?"

"Matata ce"

Aiko take ta hade girar kasa da ta sama ya nukokoce kai.

"Ba zan zauna ba, so you have a wife"

"Yes Baby"

"I hate you"

Yayi murmushi

"I know I'm sorry, Bari na tafi na siyo miki chocolate

da ice cream kinji?"

Sam ta ki yarda gaba daya mood dinta ya canja daya fada mata yana da mata, ita a tunaninta idan suka saba da shi zata iya dawowa gidansa ita da Emily su bar gidan Vito, amman tun da har yana da mata ai ba wannan damar.

"She's ugly"

"No she's not"

Ya amsa yana dariya.

"I want my momy"

"Bari na tafi na dawo sai na kaiki gurinta"

Daker ya samu ta yarda ta zauna sannan ya dauki dayan key din motarsa ya fice, daga gidan be zame ko'ina sai family house din su Kameela, a bangaren Mama

Barakat ya faka ya fito yana tunanin ya kamata ace ya riko musu wani abu, gashi babu enough cash a aljihunsa, sai dai kuma babu yadda ya iya domin ya riga ya zo dama ace be zo ba ne sai ya tsaya ya nema.

Haka dai ya aje komai ya shiga bangaren da sallama,

yaranta suka amsa masa suka gaishe shi sannan suka kawo masa drink da abincin, suka fice daga falon cike da tarbiya, babu jimawa Mama Barakat ta sauko sanye da wani lace mai tsada irin na su na yarbawa domin zama a cikin hausawa da kuma auren bahaushe be

saka ta jefar da al'adarta ba, yaranta ma yawanci da yaren yarbanci take musu magana shiyasa duk sun iya yaren.

"Maraba maraba da Aliyu"

Ya sauka daga kan kujera ya zauna kasa saboda ta zauna akan kujerar.

"Haba zaunawarka mana"

"Aa nan ma ya wadatar,

na same ku lafiya"

"Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya hanya"

"Alhamdulillah"

"Maa Shaa Allah baka ci komai ba?"

"Already sai da na ci abinci na fito"

"Tohm, ina godiya dai Aliyu daka saurare ni kuma ka ni umarnina a matsayina na step mother din Kameela,

hakan ya nuna kai yaro ne mai jin magana mai biyayya kuma mai tarbiya, na jidadi sosai Allah ya maka albarka"

"Ameen"

"ka shiga bangaren na su ne?"

"Aa na fara zuwa nan ne tukuna"

"To yayi kyau, da har jiya nake cewa ina son na sake kiranka, domin Kame

ela gaba daya ta fara fita hayyacinta abincin kirki bata iya ci, yarinyar nan tana sonka kai ma kuma na san kana son matarka, ni ban san me yake shiga tsakaninku kuke ta samun matsala ba"

"Kameela ta cika kishi ne, da abun da ya kai da wanda be kai ba duk

na kishi ne a gurinta, bata tsayawa ta saurara kuma bata amfani da tunani kamin ta aikata abu, amman dai In Shaa Allahu ba za a sake jin kam mu ba"

"Hakan yayi kyau domin na tabbatar ita ma kanta a yanzu ta dauki darasi kuma zata gyara"

"Allah yasa"

"A

meen"

Mama Barakat ta ji kamar ta masa maganar Emily sai kuma ta ji rashin dacewar hakan, domin be kamata ta shiga tsabgar rayuwarsa ba, bayan kuma ta fada masa Kameela bata fada musu komai ba, sai kawai ta sauke numfashi ta ce.

"Tashi ka tafi, ka yi hak

uri da duk abun da zaka ji ko ka gani gurin Hajiya, kasan ita uwa dole ta nuna bacin rai idan aka taba mata ya, balle ma Kameela bata fada mana dalilin dawowarta gida ba, amman dai duk yadda zaka yi ka yi iya kokarinka ka tafi da matarka, Allah ya kawar da

fitina a tsakaninku"

"Ameen na gode Mama, tafiyar ta zama ta gaggawa ban riko komai ba, sai dai idan na koma In Shaa Allahu"

"Haba ina ce ai an zama daya, idan zaka zo gida sai ace dole sai ka riko wani abu? Yanzu ai mun zama iyayenka ba surukai ba, sau

rarena da kai yi kawai ka bi shawarata Wallahi ya fi duk wani abu da zaka ba ni na gode"

Yayi mata sallama ya tashi ya fice ta bishi ta kallon burgewa tana jin ina ma ace daya daga cikin yayanta yake aure yadda yake da biyayya da jin magana haka. Motarsa

ya shiga ya yi mata key yayi reverse ya shiga bangaren mahaifiyar Kameela yana faka motarsa tana fitowa tare da kanwar Kameela cikin shirinta da alama fita zata yi, Aliyu ya fito mota ya nufo inda suke sai Hajiya ta yi kamar bata ga Aliyu, sallamar da yay

i ma kanwar ce ta amsa masa shi ma cikin rainin wayo domin basa kallonsa da daraja gaba daya, ya mika mata gaisuwa bata amsa ba sai kokarin shiga mota take.

"Hajiya Gurinki na zo"

Ya dago ta kalleshi a wulakantacce kai kace ba shi da gata ko kuma dan t

alakawa ne.

"Ina jinka?"

Ya danna tafarfasar da zuciyarsa ke yi.

"Na zo ne akan maganar Kameela"

"Ina jinka bani da lokacin batawa fa fita zan yi, kuma saboda kai ka san ba zan fasa fitar da zan yi ba"

Ya hade yawu zuciyarsa na bugawa da karfi.

"Ina son na dauke ta mu koma ne"

"Kam uban nan"

Kanwar ta fada Hajiya kuma sai ta fito motar

"Ka dauke ta ku koma saboda a titi ka aureta? Ko kuma an fada maka bata da kowa? Ai ko baranta muka yi aka ba mu ita sadaka ba zaka shigo haka nan kawai ka d

auke ta ku tafi ba, kuma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login