Showing 108001 words to 111000 words out of 265549 words
me ke min dadi naji bana
son zaman gidan gashi ba ni da kowa a garin nan"
Tasmia ta bude baki.
"Ahhh lallai kuwa mahaukaciya ya dauke ki, amman kin yi hakuri nuna masa kishi da kike ai soyayya ce, shi duk be gani ba sai kora da hali? Da ni ce ke ba zan sake kwana a gidansa ba s
ai na koya masa darasi"
Kameela ta kalleta.
"Ni ba inda zan je ina son mijina Wallahi, idan na tafi ai na bawa Emily din damar ta rika magana da shi tana samun yadda take so gashi ma gurin aikinsu daya"
Tasmia ta girma mata kai.
"Kameela ke fa yar many
an mutane ce, kina da gata ina da yan'uwa da kudi, be kamata Aliyu ya wulakanta kuma ki zauna ba, ai tun da har ta kai ya furta ki koma gida idan baki koma ba ai zai cigaba da wulakanta ki ne, ai kawai ki yanki ticket gobe ki kama hanyar gidanku sai ya nem
i ki, ai ba ayi ma namiji haka, tun da har ya iya nuna wata ta fiki kara ya san darajarki"
"Akwai abun da baki sani ba Tasmia, iyayenmu ba san auren za su iya raba auren idan suka ji cewar Aliyu ya kore ni saboda na kira wata a gurin aikinsu na zageta sa
boda tana budurwarsa"
Tasmia ta daka mata tsawa.
"Ke dalla can Aliyu autan maza ne da kike ta wannan rawan jiki da tsoron rasa shi? Haba Kameela sai kace maza sun kare aduniyar nan ne"
"Tasmia Aliyu na dabam ne fa, cikin maza dari irinsa daya ake sam
u, ni na san yana hakuri da ni, yana min komai kuma be taba wulakanta ni irin haka ba sai da bakar Emilyn nan ta zo"
Tasmia ta shiru tana kara jin kalamanta cewar Aliyu na dabam.
"Toh yanzu ko number shi zaki ba ni na kira na ba shi hakuri? Domin na lu
ra baki shirya tafiya gida ba, kin shirya karbar wulakancinsa ne, daman maza ai idan suna son ka babu abun da ba za su maka ba, idan kuma suka ki ka zaka fara ganin wulakanci kala kala"
"Tasmia ko hauka nake dai ai ba zan dauki number wayar mijina da kain
a na ba ki ba, tafiya gida dai zan tafi ko dan ya gane ni ba kanwar lasa ba ce"
Tasmia ta watsa mata harara.
"Kin dauka kowa irin Emily ne? Ko mazan duniya sun kare an fada miki ni zan iya auren mijin da zai nuna ya fi son matar waje da matarsa?"
Kam
eela ta watsa mata wani kallo tana jin zafin kalaminta.
"Mijina ba manemin mata ba ne, balle ki ce ya fi son matar waje akan ta gida"
"Idan ba haka ba akan me zai fifita Emily take da suna ko Imily akan ki? Ke mai dai ki yi tunani mana"
Kameela ta nu
na ta da yatsa.
"Ke ki iya bakinki, ban zan dan bana son mijina ba, sai dan na rasa gurin da zanje a cikin daren nan, tun da na zo na fada miki damuwata sai wani zuga ni kike kina zagin mijina, an fada miki rabuwa muka yi ne? Ni fa na zo nan ne saboda n
a samu mafitar yadda zan shirya da mijina, amman sai wani zakewa kike kina ta zaginsa"
Tasmia ta yi murmushi.
"Matsala ta dake ke zahila ce, idan yabon Aliyu kike son ayi ai nan zaki zo ba, dan ni na san darajar kaina ba zan baki shawarar zama da mutum
da har yanzu baki gama sanin ba, Aliyu yana neman hanyar rabuwa da ke ne kawai shiyasa yake wulakantaki domin ba Emily ce kadai budurwarsa ba"
Tasmia ta karasa fuskarta babu alamar wasa.
"Me kike nufi?"
Har Tasmia ta daga wayar sai kuma ta fasa abun d
a ta yi niya ta dauke kai.
"Ki daina yarda da namiji dai kawai"
"Ai ke baki yi auren ba balle ki fada min kabli da bad'adin namiji"
Fadar bata yi aure Tasmia ta ji abun kamar gorin auren take mata a take zuciyarta ta haye sama san lokacin da ta maya
r mata da zazzafar amsa ba.
"Kara ni ban yi auren ba, ke da kika yi auren ai ta wuje ta fiki daraja a gurin mijinki, mijin ma da Emily kadai yake nema ba ni kaina da kansa ya saka min Number wayarsa, kuma idan kin koma ki tambaye shi sau nawa ya zo gidan
nan gurina"
"Karya kike yi Wallahi ai ko Aliyu zai kula mata ba irinki zai kula ba, domin ba ki fini da komai ba, sai idan ke kika nemi shiga gurinsa saboda an yi kwantai babu miji kuma ga bakin jini, ga kuma rashin tarbiya, idan ba rashin tarbiya ba ya
ushe mace cikakkiya rikakkiya kamar ke zata zo ta kama gidan kanta set-contain da sunan bautar kasa? Duk garin Kaduna be ishe ki zama ba sai kin tsallako kin zo garin da mijina yake saboda shi ne abun farautarki ko?"
Ta dago wayar ta kama Number Aliyu ta
kira shi na farko be daga ba sai a na biyu.
"Assalamu Alaikum"
Ya fada Tasmia bata ce komai ba ta katse kiran daman burinta Kameela ta ji muryarsa domin ta gasgata karyarta.
"Komai zaki fada ki fada ni dai na riga na gama da ke Wallahi"
Kameela ta r
ufe ta duka Tasmia ta maida himma suka fara dukan dukan gashi babu mai raba su, ta ko'ina Kameela dukan Tasmia take ba kuma dan ta fi Tasmia karfi ko jiki ba halima Tasmia ta fita cika amman ta yi mata kwance galala tana dukanta, da ta gama da ita ta koma
gurin kayan falon ta fara watse su.
"Wallahi Wallahi akan Mijina sai na kashe ki Tasmia, daga ke har Emily sai na yi maganinku"
Ta Dauki Jakarta ta fice daga gidan tana huci. Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa ta hau ta koma gida, ta
na shiga ta fadi kan kujerarta ta fashe da kuka bakinciki ya mata yawa, yanzu mayakan sun zame mata biyu kuma ba kowa ya janyo ba sai Aliyu, ta san wani abun da Tasmia ta fada gaskiya ne cewar yana neman rabuwa da ita ne shiyasa yanzu yake wulakanta ta, a
yanzu ta gano dalilinsa na yi mata alkawarin ba zai kara aure ba ashe saboda yana son ya tara mata awaje ne, gashi daga tafiyarta haihuwa komai ya canja kamar daman dagawarta kawai yake jira, a daren ta siye flight ticket daga PH to Lagos daga Lagos ta hau
jirgin Kaduna kwana ta yi tana kuka tana bakincikin da nadamar dama ace ta bar shi ya ci abincin dazun da yanzu duk bata ji wannan ba.
EMILY POV.
Kanta a sama tana kallon taurarin da suka yi ma samaniya ido, har lokacin hakoranta ba su rufu daga d
ariyar da take na wayar da ta yi da Aliyu ba, bata sauke kanta kasa ba sai da mai gadin gidanta ya bude gate motar Vito ta kunno kai a harabar gidan, tana kallonsa har yayi farkin sannan ta sauka ta karasa inda motarsa take, ya bude motar ya fito yana mata
wani irin kauna da ke kara tabbatarwar kaunarta a zuciyarsa musamman data nuna masa kulawa da tsoronta na gudun kar wani abu ya same shi.
"How are you?"
"I'm good, ba su maka komai ba"
"Ba su yi ba, kuma ba su samu komai ba"
"Taya hakan ta faru"
"Saboda cikin kasa nake aje abun da yake dole a gidan, kuma ina da yaran da suke hango abun da zai faru idan suka ga bakuwar fuska sai su shirya komai"
Ta yi murmushi.
"Na jidadi da wani abu be sameka ba"
"Daman babu abun da zai same ni ai, sai dai y
a samu wanda ya shirya hakan"
Ya wuce ya nufi Gardenta gurin da ya binne bindigarsa sai ta bi bayansa da tambaya.
"Ka gano ko waye ne"
"Ban gano ba amman zan gano, kuma idan na gane kowaye sai ya dandani kudarsa, sai ya raina kansa"
Har yayi ginar
ya ciro bindigarsa bata sake cewa komai ba, mikewa yayi tsaye ya matsa kusa da ita.
"Kin damu da ni Emily ko ba haka ba?"
Ta yi shiru bata amsa masa ba.
"Miya haka ki aurena? Mi ya rike ki daga nuna min soyayya Emily? Ba ki jin cewar lokaci yayi da y
a kamata ace mun kasance karkashin inuwa daya?"
Ta sauke idonta kasa tana shafa wuyanta.
"Kina da wani buri ne da kike son cin ma kamin ki amince min ne?"
"Vito bana son sana'arka"
"Bayan shi fa"
"Fatima-... La lall"
Bata karasa ba ya katsi hanz
arinta yayi gaba.
"Oh Okay"
Ta bi bayansa suka fito daga gurin ya nufi motarsa ya bude ya shiga har yayi mata key sai kuma ya fito ya dawo daidai inda take tsaye ya shafa fuskarta sannan ya koma motar, tana tsaye tana kallonsa har ya fice, abun da ba s
u sani ba duk abun da suke Chidimma na lekansu. Emily ta shigo falonta kenan wayar hannunta ta yi ringing data duba wayar sai ta ci karo da sunan Tasmia, babu bata lokaci ta amsa.
"Hello"
Tasmia ta fashe mata da kuka.
"Emily dan Allah ki zo ina cikin
damuwa ina cikin bakinciki, ki zo yanzu dan Allah ina da bukatar taimakonki"
"Okay gani nan zuwa"
Ta nufi staircase da sauri ta dauko key din motarta ta fito ta sauri ta nufi gurin da motar take, daga unguwar da take zuwa unguwar da Tasmia take tafiya
ce ta mintuna Arbanin amman cikin minti ashirin da biyar ta isa gidan Tasmia hankali a tashe saboda ta ji muryarta tana kuka kuma gashi ta fada mata da bakinta cewar tana cikin tashin hankali.
Tana faka motar ta bude ta fita ya fara kwankwasa kofar Tasmi
a kamin ta tura ta shiga, yanayin yadda ta ga falon a hargice ta san ba lafiya ba, ta zauna kusa da Tasmia dake rusar kuka tana tambayarta abun da ya faru.
"Ni ma ban san miya faru ba, matar nan tana shigowa ta rufe ni da duka wai mijinta yana zuwa gidan
nan nemanki, gaba daya Kameela bata da hankali, akan Aliyu zata iya komai Wallahi kara ma ki rabu da mijinta, ni din ta yi min haka ina ga ke kuma"
"Ba soyayya nake da mijinta ba, kuma waya fada mata yana zuwa nan nemana? Yaushe rabon da na zo gidan nan
ma"
"Waya sani wata kila bincike tayi har ta gane ko kuma shi ya fada mata ai maza ba su da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba"
"Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu"
"Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti"
"Okay tashi mu tafi"
Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye
"B
an san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki"
Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake
aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan t
a sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling.
"Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiran
sa"
Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta.
"Okay mu tafi asibitin"
"Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba"
"Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya"
"Okay"
Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai
tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta.
ALIYU POV.
"D
aman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda
kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta"
Shi ne sakon
da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce.
Amman me zai
saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibit
i ta kwana.
"Ahhh Ahhh"
Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka.
"Me ya faru?"
"Baka ga sakona ba"
"Na gani, garin ya ta miki duka?"
"Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gi
dana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka"
"Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na"
"Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sa
i yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana
son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya"
Bata jira abun da zai
fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily.
Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma
aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa.
"Hello"
"Emily"
"Na'am"
"Kina ina? Me kike yi a yanzu"
Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne
sai washe gari ta dawo.
"Ina gidana"
"Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?"
"Aa"
"Tasmia fa?"
"Meyasa ka tambaya?"
"Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?"
A take ran Emily ya bace
"Matarka bata da hank
ali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?"
"Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata mag
ana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani"
"Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta"
"Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni d
an iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai"
Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a han
yarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B