Showing 114001 words to 117000 words out of 237218 words
su anan ki zauna."
"Menene da nan din?"
Bai kai ga magana ba attishawa ta tare shi ya dinga yi har sai da na tashi na nemo masa tissue ya dinga fyace majinar data tsinke. Ya tara tissue din a wuri d'aya na kwashe na je na zuba ashara na dawo na same shi har yanzu yana ta attishawar dai.
Kada ki karanta littafin nan ba tare da kin biya ni hakkina ba. Littafin gudun aure na kudi ne.
Lallai a yau na sake tabbatar da cewa mura tana daya daga cikin manyan laluran da suke galabaitar da jikin dan adam, daga jiya zuwa yau gabad'aya kamminsa sun canza fuskarsa har ta dan kumbura ga dukkan alamu ma dai yana da matsalar sanyi a jikinsa shiyasa da aka motsa shi ya tashi gabad'aya.
Fita na sake yi daga d'akin na samu Yusura tana soya indomi da kwai na ce ta miko mini fulas din shayin da yake gefanta ta had'o mini da kofuna biyu masu dan girma na gilas.
Na sake komawa d'akin yana kashingide attishawar ta lafa.
Ya bi ni da kallo a lokacin da na kàrasa wurin da yake har na tsiyaya masa shayin da yake ta tiriri da k'amshin kayan shayi bai d'auke idonsa daga kaina ba. Ni ma ban ce masa komai ba na fara motsa masa shayin har sai da ya yi daidai yadda zai yi dadi sha. Na mika masa babu jayayya ya kar'ba har da godiya.
Gefe na zauna ina d'an sauke ajiyar zuciya. Na ji yana cewa." Har yanzu ban gayawa Hajja kina garin nan ba, haka zalika ma na gargadi Yusuf akan kada ya sanar mata Ina so ni dake mu gama magana yanzu da daddare na d'auke ki a mota domin ki duba gidan da za ki zauna."
Ba tare da na kalleshi ba na ce.'' Wai me yasa ba ka so Hajja ta san abinda ya shafe mu ne, kada fa ka manta mahaifiyarka ce, baka da hurumin boye mata abinda yake faruwa da rayuwarka."
"Wannan ai ba abin alheri ba ne shiyasa nake lullube mata."
Na ce.'' Yanzu ka amince kana kuskure ko?"
Ya d'aga mini kai alamar E.
Girgiza kaina kawai na yi ban kuma yi mamakinsa ba domin duk abinda yake yi mini a yanzu yana yi domin ya samu kaina, shiyasa duk abinda na ce ya yi kai tsaye yake amsawa babu ja'inja, a ganina kuma hakan ba zai hana shi watarana idan na ha'kura ya sake kuntuka mini ba."
"Na ji dadin shayin nan sosai na gode miki."
Maganarsa ta dawo ni da hayyacina. Na dube shi sai na ga yana kallona shima kafin a hankali ya ce." Kin kasa samun nutsuwa ballantana ni ma na samu nutsuwar da zamu cigaba da gudanar da rayuwarmu, akwai abinda nake so na gaya miki wanda ya shafe mu ne gabad'aya da duk wani makusancina amma ina fargabar ki juya mini magana ko ki ji kamar da gayya na gaya miki."
A tsanake na ce." Ni babu irin wannan gilin a zuciyata me zai sanya ka sanar da ni alheri kuma na ji b'akinciki idan ba ka sanya ni daya daga cikin masoyanka ba to na tabbatar zan zo a ta biyu don haka ina yi maka fatan alheri akan duk abinda ya sami rayuwarka."
"Na gode sosai, Allah Ya yi miki albarka."
D'akin ya yi shiru ni ina ta jiran na ji ya gaya mini abin alheri ya yi shiru yana ta kurbar shayin yana lumshe ido da gaske ya yi masa dadi. Na ce.'' Idan bai isheka ba akwai sai na tsiyaya maka."
"A a, ya isa wannan din an jima dai kafin na tafi zan kara shan wani."
Na kar'bi kofin daga hannunsa na ajiye sai na ji ya ce." Kin cire key din motata cikin aljihun rigata ko?"
Ban ce komai na janyo handbag d'ita na d'auko masa mukkulin .
"Ina Hamusu ba shi ya bude motar ya debo mini wayoyinsa.
Rufe bakinsa ke da wuya Hamusu ya shigo gidan na tashi da sauri na fita na same shi suna magana da Yusura hannunsa ri'ke da ledar magungunan na kar'ba tare da mika masa key din motar na ce." Yallabai ya ce ka debo masa wayoyinsa a mota."
Ya kar'ba ya fita da sauri
Allah Ya sa jiya da ya yi mini sayayya ya sayo rowan roba swan na d'auki daya na sake komawa d'akin.
Na ce." Ga magunguñan wayoyin kuma yanzu zai kawo."
Ya kar'bi ruwan da maganin Ina daga tsaye duk Ina kallonsa ya 'balli maganin ya sha. Na ce." Ko na dan dafa maka wani abu mai dan nauyi kafin ka tashi nasan maganin mura da kashe jiki wata'kila ma bacci ya d'auke ka yanzu."
Ya ce." Da kuwa kin kyauta amma towo na garin dawa, miyar kuka kuma."
Na ji shigowar Hamusu a karo na biyu muryarsa a falo yana fad'in." Anti ga wayoyin." Fita na yi da sauri na amso masa shi kuma ya juya zai fita na ce." Akwai abin kari Yusura ta yi Hamusu ka zauna ka karya zata had'a maka komai sannan don Allah idan ka shiga cikin gari ka hado mini kayan towon dawa."
Ya ce." In sha Allahu anti."
K'aramar wayar a kashe take babbar ce a kunne na mik'a masa ya kar'ba cikin nutsuwa ya fara dubawa, ganin haka sai na juya zan fita hankalinsa na kan wayar ya ce." Ina za ki je kuma ke da ki ke jinya."
Dawowa na yi na zauna ban ce komai ba.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN👎*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky
*TALLAH!*
*Albishirinku mata ƴan ƙwalisa matan da suka amsa sunansu mata, waɗanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaɗar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na ƙawa da ƙawa ɗaya tamkar da dubu, sha ƙundum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo ķano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haɗa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ƴar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari ƙasa_ƙasa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da buƙata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari ƙawar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar ɗakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ƴar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuɗi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da ƙwarewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaɗan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*👇🏻
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse melaƙabin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da ƴa mace duk ramarta, da ƙanjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daɗi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ƙari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456
*46*
Ya d'an duba abinda zai duba kafin ya dube ni a nutse ba tare da nuna nishad'i ba ban dai sani ba ko b'oyewa ya yi ya furta." Kin san da cewa Hauwa tana da juna biyu?"
Gabana ne ya buga da karfi sakamakon jin maganar da ta yi tsalle ta fito daga bakinsa ban kuma tsammaceta anan kusa ba.
Sai da na yi namijin ko'karin daidaita kaina don gudun kada ya gane kid'imewata na kar'bi maganar da ya dumfare ni da ita da annashuwar da ban shirya yinta ba na ce." Kai ma sha Allah ko shine dama abinda ka ke cewa za ka gaya mini?"
Ya gyada kansa da kwarin gwiwa ya furta." Kwarai kuwa na so na gaya miki tun kwanakin da suka shige to ban san yadda za ki ji a ranki ba, sai kuma wannan rikicin ya b'alle a tsakanimu zan fi so ki samu nutsuwa mu daidaita a tsakaninmu ke ma ki samu na ki cikin zan ji dad'i na ga kuna yi mini jereran haihuwa."
Na danne abinda yake yun'kuro mini na tsantsar kishi da tausayin kaina na furta." Na taya ku murna sosai, Ubangiji Allah Ya raba lafiya ya kuma raya abinda za a samu. Maganar na samu ciki na haihu ina ga abu ne mai wahala domin ba abin wasa ba ne d'aukar ciki da rainonsa balle a zo kan k'adami na haihuwa. Tunda har jininmu bai hadu ba ina ganin mu ha'kura kawai da haihuwar nan Yallabai ai kai baka da matsala ni ce ma abin tausayi."
Na kare maganata idona a tsakiyar nasa idon.
"Ina ce wannan maganar mun rufe babinta tun wattanin da suka gabata dalilin da ya sanya fa kenan nake jin shakkun gaya miki saboda na fi kowa sanin halin rigimarki."
Na ce." Me ka mayar da ni mara son zaman lafiya ko me? ko duk wannan addu'ar da fatan alherin da na yi muku baka gamsu ba har sai ka jefe mini magana idan ka boye mini cikin matarka ai ba zaka 'boye mini haihuwar ba tunda ba zata ta'ba dawwama dashi a jikinta ba."
Shiru ya yi mini bai tanka mini ba.
Hakan ya kara dagula mini raina. Gabad'aya ma sai nake ganin yana so ne ya raina mini wayo ne ya muna tsaka da rikici ya wulakanta ni har da tukwicin saki ban yi masa komai ba kuma ya zo ya ce mini na taya shi murna akan wane dalili. Haushinsa da nake ji sai ya dawo sabo dal, na ji kamar na ce ya bar mini gidana amma babu halin hakan.
Ya kwanta tare da rufe idonsa yana jina ina ta sakin maganganu bai tanka mini ba. Na goge hawayen da ya d'an zubo mini a kumatu na tashi na fita.
Hauwa tana da ciki wannan ya nuna cewa daga zarar ta fara haihuwa zata kar'bi gidan. Ni kuma saboda son zuciyarsa na d'auki ciki na yi wahalar rainonsa da nakud'a na haihu daga baya abinda na haifa ya mutu. Ita Hauwa itace mai rayayyun 'ya'ya kenan.
Kishi ya rufe mini ido gabad'aya tunanina ya kulle har sai da muka yi waya da Anti Yagana ta sake mayar da ni hanya tukkuna na dan samu sasaauci tabbas Allah ne mai yi kuma shi ne mai kashewa da rayawa. Idan ya so duka yaran da Hauwa zata haifa su zama rayayyu idan ya so kuma ya d'auki ransu ba kuma tare da wata lalura ba. Tabbas akwai wannan ciwon kuma kisa yake yi bayan ya gama galabaitarwa amma hakan ba zai zama hujjar da za a ce ba za a haihu ba domin yana iya canza komai hakan ba abu ne mai wahala ba a wurinsa. Da wannan tauhidin nata muka yi sallama jikina duka babu karsashi da sukuni na sake yin tubus a lokacin da na tuna irin rantsuwar da ta dinga yi akan yadda ta tabbatar da cewa yana sona domin idan babu soyayya ba zai ta'ba zama irin yadda nake so ba har ya kwana a k'ukutance gida irin wannan da babu tsaro a cikinsa.
Haka na wanzu cikin nazari da tunanin rayuwar da zan fuskanta a gaba.
Dutsan guga na ce Yusura ta kar'bo mini a shago, tunda ko babu wuta babban gen suke kunnawa da kaina na goge masa kayan tsaf na ajiye masa a gefansa bacci yake yi sosai wanda na tabbatar da cewa maganin da ya sha ne yake tasiri a jikinsa.
Ni da yarinyar dai muka yi akin towon har da man shanu ya sayo na kuwa soya shi da albasa mai yawa. Na ce idan zai tafi asibiti sai ya zo ya tafi dana Gwaggo domin zai yi mata dad'i a baki.
Na had'a masa komai cikin babban tire har zobo na yi masa wanda ya ji citta duk don saboda ya samu sau'kin kirjinsa.
Biyu saura na koma d'akin har yanzu dai bai motsa ba ga lokacin sallah.
A hankali na dan bubbigi gefan katifar bashi da nauyin bacci dama can ya bude ido yana kallona na ce." Lokacin sallah ya yi.".
Ya yun'kura ya tashi zaune yana fad'in." Ina buk'atar ruwan zafi wanka zan yi tukkuna."
Na ce." Da ka ha'kura da wankan nan tunda ba ka jin dadin jikinka."
Girgiza kansa ya yi. "A a ki sama mini ruwan d'umi kawai.
Na tashi na fita ban sake cewa komai ba. A babbar tunkuya na d'ora masa ruwan sai da ya tafasa tukkuna na juye a bokiti na surka da d'umi sosai na kai masa bandakin d'akin.
Ya tashi jikinsa da kwari sosai ya shiga bandaki na bi shi da kallo jikina a d'an sanyaye ni kuma shine kaddarata jiyyarsa tsakanin jiya da daddare da yau jikina ya nuna ya na yi muguwar gajiya saboda kai kawo.
Maganarsa na ji daga bandakin wai na mika masa kayansa.
Ya zuro hannunsa na bashi kayan gabad'aya har singilitin da wandon ciki.
Kada ki karanta wannan littafin ba tare da kin biya ni hakkina ba. Gudun aure na kudi ne
Na je na d'auko tiren dana shirya masa abinci na ajiye masa a gefan daddumar dana shimfida masa.
Bandakin tsakargida na yi wanka na koma cikin d'akin na same shi ya idar da sallah yana waya da Hajja har yana cewa da ita ta bashi Yusi. Ban ce komai na fara had'a masa abincin a maidaidaicin filat na ajiye a gabansa gefe da yajin daddawa da man shanu.
Na tsiyaya masa zobon a kofi.
Ga mamakina na ji ya fara dariya harda kyakyatawa ina jiyo muryar Yusi kad'an-kad'an ko me yake ce masa oho, na ji yana fad'in." Idan na kasa juyo da hankalinta kai ma sai ka zo ka gwada taka sa'ar don wannan Maman naka ta fini rigima."
Na ji maganarsa Yana fad'in." Dukana za ta yi wallahi ni tsoronta nake ji Baba."
Yana dai dariyar ya ce masa "idan ta dake ka sai na rama maka ai."
Jin haka na san da ni suke lallai ma Yusi ashe na zama abin zolaya a wurinsa, ban yi tsammanin akwai ranar da za ta zo yaron nan ya manta da ni ba.
Suna gama wayar ya dube ni yana fad'in." Kin ji ni da Yusuf ko? shi ya ba ni shawara na zo na baki hakuri, da na ce ya zo mu je tare ya ce a a dukansa ki ke yi.''
Murmushin takaici na yi na ce." Ai na ji abinda kuka shirya kai kuma ka rasa wanda zai baka shawara sai wannan mashiriricin."
Ya d'an janyo filat din da nasa masa towon ya tallafe da hannunsa yana fad'in." To menene ai yaronki ne ya rayu dake zai fiye da ni zai fi kowa sanin halinki."
Gyada kaina na yi a hankali na ce.'' Kun kyauta kai dashi ai."
Ya yi bismillah yana cewa." Towon nan tun kafin na yi loma guda yawuna ya tsinke wallahi."
Yadda ya tallafe filat din a hannunsa shine abinda ya ba ni dariya na tashi ina fad'in." Ka dai ci a nutse kada ka 'kware."
Bai ce mini komai ba ya cigaba da cin abinsa na zauna gefan katifa a nutse na janyo akwatin kayana na shiga duba kayan da zan sanya na yi wankan tun d'azu amma ban samu sukunin canza kayan ba ballantana na yi sallah. Na ji dai dadin ganin yadda jikin nasa ya yi sau'ki gashi nan har ya zage yana cin abinci.
Cikin rashin sukuni na gama shiryawa domin a jikina na ji cewa kallona yake yi. Ina juyowa kuwa muka yi ido hud'u da filat din towon a hannunsa yana ci yana kuma kallona kamar wanda ya samu tibi. Na d'an zumbura baki can k'asa-kasa na ce." Ni kam wane irin kallo ne wannan?"
"Me ki ka ce?"
Shiru na yi ban ce komai. Sai ya cigaba da cewa." Kin ce idan ni maye ne na ci kaina ko?"
Da sauri na dube shi da mamaki a tare da ni." Haka na fad'a?" Na ce cikin sigar tuhumarsa. Sai kuwa ya daga kansa." Eh mana haka ki ka ce ai na ji, yanzu kuwa zan zo na cinye ki, ai kin ba ni magani na yi ras da ni, sannan kin ba ni towo da tantakwashi me ki ke tsammanin zai faru?"
Dariya maganarsa ta ba ni, na ce." Kana nufin ka warware kenan, muryarka fa har yanzu bata fita sosai."
Yana sud'e yatsun hannunsa ya ce." Za ki tabbatar da haka idan ki ka ji ni a jikinki."
Na ce." Ai ba ka fara ba, domin kuwa gidan nan bashi da wani tsaro kai ka san kanka ni ma nasan wanene kai ."
Ya yi shiru bai tanka mini yana cigaba da sud'e hannunsa na ce." Wai miyar ce ta yi dadi