Showing 27001 words to 30000 words out of 129444 words

Chapter 10 - BAKAN GIZO COMPLETE

kuma idan har hakan ta kasance da gaske kai kayiwa Amrah cikin WALLAHI sai mun durk'usa da kai agaban kuliya."

Aunty tace. "Bayani zakiyi domin musan inda zamu dosa"

Zuwaira tana kuka tace, "Me

zan fad'a maki bayan wanda Amrah ta fad'a yanzu? abu d'aya ne nasani wanda naji bata fad'a ba shine tabbas Nazir yana sonta tun tana 'yar k'arama, sannan yayi ta burgar cewa wai ita d'in matarsa ce,

to yaya ta zamo matar bayan nida mahaifinta duk bamu sani

ba?haka nashi uwayen ba wanda yasan da wannan zance, ita kanta ma bata da masaniya akan hakan, to taya zamu yarda da renin Hankalinshi?."

Ruguntsumi

πŸ€”

Akafta

πŸ‘ŒπŸ»

D/Auta ce

πŸ‘πŸ»

*

🌈🌈

BAKAN GIZO

🌈🌈

*

*NA HADIZA D/AUTA*

htt

ps://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*

⭐⭐⭐

TAURARI WRITERS ASSOCIATION

⭐⭐⭐

*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)

*PAGE 19*

**********************

Aunty Asabe jikinta yayi sanyi k'alau sannan tayi

jarumtar fad'in, " anya ko Nazir Mutum ne kuwa? Nifa wannan lamarin ya rikice man kwakwalwa."

Zuwaira ta sauke ajiyar zuciya sannan tace, "Mutum ne kamar kowa nasan Mamarshi da babanshi da kanwarshi duk, saboda munyi makotaka dasu haka ma

munyi zaman lafiya dasu kafin rashin jituwa ta kunno kai tsakanimmu"

Aunty tayi saurin fad'in "Rashin jituwa kamar yaya? Fad'a kuka yi dasu halan?"

Zuwaira tace, "Ba wani fad'a kawai dai rashin fahimta ce ta shiga shiyasa mutanen unguwar su

ka sako ni agaba, sai gashi ALLAH ya kawo muna Salis ya bamu wannan gidan muka dawo, tun daga lokacin ban koma jin labarinsu ba, saboda ban koma zuwa unguwar ba sai ranar da muka je dake"

Aunty ta kalli Amrah tace, "To ke kina nufin duk zaman da kuka

yi dashi baki san yana sonki ba?"

Amrah tana sharar hawaye tace. "Nidai WALLAHI bai tab'a cewa dani yana sona ba, sai dai kullum yayita fad'a da samarina, yana cewa wai ni matarshi ce"

Suna cikin firar ne sai ga Abba k'anen Amrah ya shigo yace

ga Malam Nura cen k'ofar gida, nan take Zuwaira tayi kicin kucin da rai tareda mik'ewa tsaye ta bar masu d'akin, Aunty Asabe tace, "ka shigo dashi" ya fice d'an lokaci tsakani sai gashi ya shigo tareda Malam d'in, kai tsaye d'akin Amrah ya shiga su

ka fara gaisawa da Aunty tareda tambayar jikin Amrah, sannan Aunty ta fice ta barsu Malam ya kalli Amrah fuska ba walwala yace,

"Nazo ne domin inji abunda yake tsakaninki da wanda ya baki jini, saboda ni gaskiya bana lamuntar abunda ake so ayiman, k

e matata ce aurenki nike banga abunda zai had'aki huld'a da wani mijin da kika fito gidanshi ba, wannan ya zama na farko ya zama na k'arshe idan hakan ta koma faruwa gaskiya zan d'auki mataki."

Amrah tun lokacin da ya fara magana ta fara kuka, saboda

daman cen Kukan a kusa yake shiyasa yana kai k'arshen zancenshi ta fashe da wani kuka mai sauti tana fad'in,

"ALLAH ka amshi raina in huta nagaji da wannan bak'in ciki da kullum safiya da sabon salon da yake zo man" aiko sai ga Zuwaira tsidik kamar

an jefota jikinta yana rawa ta kalli Malam tace, "Kayi gaggawar bata takardar sakinta don WALLAHI kaji na rantse bazata koma gidanka ba."

Ta k'are maganar a cikin d'aga murya Aunty ta shigo d'akin ranta a b'ace tace

"Haba Aunty Zuwaira wannan fa

ba shine maslaha ba, ki bari abi abun a hankali har aga wannan matsalar ta kau, don wannan k'alubale da muke ciki har yanzu babu wanda yasan matsayin auren, har sai komi ya bayyana gaskiya ta fito sannan ne za'a san matakin da za'a d'auka, don haka kima b

ar zancen wani saki don ba shine agabanmu ba yanzu" Zuwaira tana hararar Malam tace,

"Nidai yanzu shine agabana idan ya sauwak'e mata zanfi jin dad'in tunkarar matsalar dake gabanmu." Malam ya mik'e ranshi a b'ace ya fito d'akin, Aunty tace

dashi "Kayi hak'uri don ALLAH kayiwa Amrah Uzuri saboda ita kanta bata san komi akai ba, don haka mu ajiye komi zuwa lokacin da ta sauka, insha ALLAH komi zai fito kuma gaskiya zata yi halinta"

Dak'yar ya bud'a baki yace, " Bakomi ta zauna gidan h

ar zuwa lokacin da zata haihun" yana k'are maganar ya saka kai ya fice, Zuwaira ta bishi da cewa. "Ko k'arshen rayuwarta kace ta zauna ai gidansu ne kuma mallakinta, huta da hurar hanci ba uban da zaisa ta koma wannan tsinannen gidan naka." ciki

n b'acin rai Aunty tace

"Gaskiya abunda kikeyi kwatakwata bakya kyautawa Aunty Zuwaira, haba ina laifinshi WALLAHI Malam ya ma yi k'ok'ari da ya tsaya iya haka, wanda na tabbata son da yake yiwa Amrah'r ne yasa bai d'auki wani kwakkwaran mataki akan ha

kan ba, saboda ba kowa ne zai iya jurar wannan kayan takaicin ba, yanzu abu d'aya ya rage mu gano inda Nazir d'in yake koda ta hanyar abokansh ne."

Zuwaira tana kallonta tana mere har ta k'are maganar sannan tace

"Don ALLAH kice yayi mata saki dubu i

n anayi." Aunty Asabe ta janyo hijabinta ta saka sannan tace da Amrah, "Ni zan tafi sai kuma na koma dawowa, duk abunda kikaji kina sha'awa ki kirani a waya ki sanar dani, koda banzo ba zan aiko maki ALLAH ya baki lafiya."

Amrah tace AmeeΓ± cikin z

uciya saboda kukan da take yi, Aunty taje ta had'o kan kulolinta ta jibga a wata k'atuwar leda sannan tace da Zuwaira, "Ni na tafi sai kuma na sake juyowa" har ta kai k'ofa sannan Zuwaira tace, "Sauka lafiya" ba tareda tace da ita k'anzil b

a ta fice zuciyarta cike da haushin Zuwaira, a gefe d'aya kuma tausayin Amrah da Malam tareda d'an tayin cikinta da zai fad'o duniya cikin ruguntsumin rayuwa.

Bayan fitar Aunty Zuwaira inda take shiga ba anan take fita ba, sai ruwan bala'i take saukewa

Malam da Aurenshi, Amrah dai sai sharb'ar hawaye take yi saboda izuwa lokacin zuciyarta har ta saba da bak'in ciki.

Bayan kwana uku da wannan rikici Aunty ta bazama neman Nazir ruwa k'ok'o, koda ALLAH zaisa ta sami wanda zai san inda zata sameshi, d

on ko gidan Dattijuwar nan mai kosai tayi maya biyu, domin kawai taji wani information game da Nazir amma ba wata nasara, dole ta hak'ura ta zubawa sarautar ALLAH ido, saboda Numbar ma da ya kira Amrah da ita tayi ta kira kullum magana d'aya ce ake cewa

waton a kashe take.

Watan cikin Amrah tara cikin na goma ta fara nak'uda, ba shiri Zuwaira ta kinkimeta zuwa Asibiti, tasha wuya sosai kafin ta sanbalo yaronta k'atoto fari jajir masha ALLAH, son kowa k'in wanda ya rasa mai kama da Amrah sak, Zuwaira

duk da bata son Malam amman wannan yaron taji k'aunarshi har cikin ranta, Aunty ko hana kowa ya d'auke shi tayi tana nanuke dashi, Amrah kam duk da taji dad'in ganin yaron, amman kasanceawar ruguntsumin da rayuwarta take a ciki yasa bata wani farin ciki.

Kasancewar haihuwar dare ce tayi akace sai da safe za'a sallameta saboda ta jigatu sosai kafin ta haihu, Aunty Asabe tayi gida Zuwaira ta kwana da Amrah, cikin dare yaron yana ta kuka likitoci suka ce Amrah ta bashi Nono, tana kukan bak'in cikin shayar

da yaron da ba'a san wanene tantagaryar ubanshi ba, ta ciro nono ta fara bashi aiko ya karb'e kamar daman cen ya saba sha, zumui zumui yana tsotsa Amrah da zugin bak'in ciki ke ratsa zuciyarta, ta fashe da kuka tareda janye nonon aiko yaro ya k'ara fasa k

'ara, Zuwaira ta rufeta da fad'a dole ta maida masa yayi ta tsotso har yayi bacci, sannan aka ajiye mata shi akan gadon, itama ta kwanta, sannan ne kowa hankalinshi ya kwanta Zuwaira ma ta d'an kishingida akan kujera, Amrah kam daman wani masifaffen kwana

ne a idonta tana kwantawa sai bacci.

Da misalin k'arfe hud'u na asuba kukan jaririn ya tayar dasu, a firgice dukansu suka falka tareda waigen ta ina kukan jaririn yake fita, abun mamaki ashe wani jaririn ne da ke kusa da gadonsu, wanda shima sabuwar h

aihuwa ne amman basu ga nasu jaririn ba, cikin fad'uwar gaba Amrah tace

"Mama ina yaron?"

Zuwaira ta zabura da k'arfi cikin tsananin gigita tace, "Nan fa yake kwance kusa dake, kina bacci ma ya falko NA bashi ruwa ya koma baccin, sannan nim

a na k'ara gincirawa, kodai Nurses sun tafi dashi suyi masa allura ko wani abun?"

Ba shiri Amrah ta fashe da KUKA jikinta yana tsuma saboda tashin hankali tace.

"WALLAHI d'aukesa aka YI Mama daman yace ranar da na haifu a ranar zai karb'i danshi

."

To fa wata sabuwa

😱

Akafta

πŸ˜†

D/Auta ce

🀝🏻

*

🌈🌈

BAKAN GIZO

🌈🌈

*

*NA HADIZA D/AUTA*

https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*

⭐⭐⭐

TAURARI WRITERS ASSOCIATION

⭐⭐⭐

*

(We entertain and educate acco

rding to our religion and ethnics)

*Kuyi hkr dani don ALLAH WALLAHI nayi busy da yawa kwanan nan am very sorry my fan's

πŸ™πŸ»

*

*PAGE 20*

**********************

A cikin fad'uwar gaba Zuwaira tace, "Wanene?" Amrah ta k'ara fashewa da wani

kukan tace, "Wanda yace cikin nasa ne."

Ta k'are maganar cikin tsananin kuka, a zabure Zuwaira ta fito d'akin tana kururuwar an sace mata jika, kafin kace me asibitin gaba d'aya ta d'auka anyi satar jariri sabuwar Haifuwa, aka bazama bincike lung

u da sak'on na asibiti amman ba wani alamu da zai nuna ma akwai wani mara gaskiya a cikin asibitin balle asami b'arawon jarirai.

Ganin yanda hankulan Amrah da Zuwaira ya tashi yasa wata mata da itama haihuwar tayi, ta zo jikin gadon Amrah cike da tau

sayi tace, "WALLAHI ni naga fuskar wanda ya d'auki yaronnan da idanuwana, saboda lokacin kwanciyata kenan bayan na k'are baiwa jaririyata nono, sai gashi ya shigo d'akin ganin mutum a gadonki yasa na dallare masa fitilar dake hannuna a fuska, bai damu

da hasken fitilar ba haka ma bai fasa d'aukar yaron ba, na yunk'uro da k'arfi da nufin in zo in hanashi d'aukar yaron ne tawa jaririyar ta falko tana ta kuka, dole na d'aukota sannan na nufo shi yana gaf da fita d'akin rungume da jaririn, na ciyo kwalars

hi ta baya ba shiri ya k'wace daga rik'on da nayi masa, sannan ya juyo muna kallon juna ido cikin ido yace dani, kada in koma yin gangancin tab'a shi ko inyi kuwwa, don zai iya halakar dani da 'yar jinjirata akan a hanashi d'aukar danshi,na bishi da kallo

cike da tsoro tareda k'ara mak'ale 'yata a jikina, har yasa kai zai fita sannan ya juyo yace dani idan an tambayi ina yaron ince daku Babanshi ne yazo ya tafi dashi, idan kun tambayi sunanshi in ce maku NAZIR."

Ba shiri Amrah ta cakumo matar cikin zafi

n nama, ta d'aga murya kamar wata zararra tace, "WALLAHI sai kin biyani yarona, kije ki karb'o man yarona."

Dak'yar aka b'anb'ari hannun Amrah daga shak'ar da tayiwa matar, ta haukace mata sosai akan sai ta nemo mata yaronta,

tana maganar cikin k'

araji sannan ta zube k'asa a some, da gudu likitoci suka yo kanta zuciyoyinsu cike da tausayinta, tareda fargabar kada ace zuciyarta ta buga saboda bak'in cikin rasa yaronta, don daman cen bincikensu ya gano zuciyar tana gaf da bugawa, saboda jininta ya h

aye sosai da sosai komai zai iya faruwa da ita matuk'ar ba'a daina b'ata mata rai ba.

Da gudu aka fara bata taimakon gaggawa Zuwaira kam tana cen ana bulayin neman jariri, bata ma san abunda yake faruwa ba saboda an baza 'yan sanda a asibitin sai binci

ke ake yi, dak'yar aka yi nasarar dawo da numfashinta dake tafiya da sauri da sauri, sannan likitocin suka rage fargaban da suke yi don rayuwarta tana cikin k'ila wa Kala, bayan anyi mata alluran bacci ne sannan likitocin suka watse, sai wanda ke kula da k

omi nata ne ya tsaya yana k'are mata kallo cike da tausayi, saboda ganin yarinya k'arama da ita ta shiga gararin rayuwa irin haka, yana k'ok'arin barin wajen ne yaga wata farar takarda a k'asa ya duk'a ya d'auko tareda bud'ewa a lokaci d'aya, aikuwa sai ga

shi yaga abunda ya shalle tunaninshi, domin kuwa abunda ke cikin takardar ya nuna lalle wanda ya d'auki yaron na gida ne, domin kuwa ga abunda ya fad'a,

_"Na d'auki yarona idan har kuna son na maido shi taci gaba da shayar dashi sai in kun bani

matata, kun walwale aure kan auren da kuka yi mata ko don ragewa kanku girman zunubin da kuke d'aukarwa kanku."_

_NAZIR_

Cikin d'aurewar kai likitan ya k'ara jujjuya takaradar kamar wanda yake neman wani k'arin bayani daga takardar, cikin

sanyin jiki ya saka takardar aljihu sannan yakai kallonshi ga kyakkyawar fuskarta, da ta rame tayi fari fayau saboda ciyo damuwa ga kuma fargaba tareda jigatuwar haihuwa, haka kawai yaji yana buk'atar jin ainahin labarinta da abunda ke faruwa ga rayuwart

a, cike da tausayinta ya fito d'akin ya nufi Office d'inshi, sai maimaita zancen dake cikin takardar yake yi a ranshi.

Zuwaira kam har gari yayi haske tana cen tareda 'yan sandan suna bincike, sai ga Likitan nan yazo ya jawo wani d'an sanda d'aya tared

a yi masa bayanin cewa case d'in na gida ne, saboda uban yaron ne ya d'auki danshi za'a bi abun a hankali a karb'o yaron, amman idan har hakan bata samu ba dole ne a nemo su su shigo cikin lamarin, sannan suka tafi ya juyo kan Zuwaira ya fara bata hak'uri

saboda yanda yaga duk ta firgice kamar wata sabuwar Mahaukaciya saboda b'atan jikanta.

Zuwaira kam bata ma gane abunda yake fad'a saboda firgicin da take ciki, don Zuciyarta tana ta canki in cankar waye wanda yayi wannan k'arfin halin raba yaro da mam

anshi?.

Dak'yar ya shawo kanta ta hak'ura ta koma inda Amrah'r take domin taga a wane hali take, aiko ganinta kwance sambal tareda oxygen d'in dake taimakonta wajen zuko numfashi, ba shiri ta fashe da kukan tausayin 'yarta mutane sai lallashinta suke

yi suna bata hak'uri.

K'arfe takwas dam Aunty ta shigo d'akin fuskarta cike da fara'a ganin halin da ta tarar da Amrah a ciki yasa tayi turus, sannan ga Zuwaira zaune a gefenta tanata kuka gwanin ban tausayi, Aunty takarasa wurinsu jiki ba kuzari tace

, "Ina yaron?"

Zuwaira tana ganin Auntyn taji wani sabon kuka yazo mata cikin muryar kuka tace, "Asabe an sace jaririn." ba shiri Aunty gabanta ya k'ire ya fad'i jiki ba kuzari ta dafa k'arfen gadon tace, "Ta yaya hakan ta faru?"

Daga nan Zuwairar ta fara yimata bayani cikin kuka,tana cikin fad'a mata sai ga likitan ya shigo d'akin yace dasu su zo akwai maganar da zai yi da su, suka biyo bayanshi har office d'inshi suka zazzauna, sannan ya kalli Aunty yace

"Wanene Nazir?"

Duk

ansu suka zaro ido cike da mamaki suka had'a baki wajen fad'in "kasan shi ne?" yayi d'an murmushi don rage masu firgicin da ya gani kwance ga fuskokinsu sannan yace, "bansanshi ba hasali ma ni tambayarku ce nike yi saboda yaronku yana hannunshi, ga

ba d'aya suka zabura Zuwaira tayi hanyar fita office d'in kamar wata mahaukaciya, Likitan yayi saurin shawo gabanta yace, "Banso shiga cikin lamarin ba amman duba da yanda yarinyar rayuwarta take cikin had'ari, sannan ku gaku hankalinku yayi tsananin ta

shi shiyasa na shiga, da zummar ALLAH yasa shiga ta cikin lamarin koda za'a sami sassaucin matsalolin

da yarinyar take fuskanta." Zuwaira jikinta sai tsuma yake akan ta fita taje ta d'ebowa Nazir 'yan sanda akawo mata jikanta, Aunty tayi k'arfin halin ri

k'ota a rikice tareda tambayar Likitan ya aka yi yasan shine ya d'auke yaron?, kai tsaye ya fiddo takardar ya mik'a mata sannan yayi masu bayanin yanda aka yi ya sameta, jikinta yana rawa ta karb'a ta karanta sannan ta d'ago cikin tsananin firgici ta kall

i likitan tace, "Ko zaka iya gane wanda yazo ka d'ibi jininshi ka saka mata watannin baya har yace ita d'in matarshi ce?" Likitan yayi shiru na d'an lokaci sannan yace a gaskiya idan har na ganshi zan gane shi, sai dai kai tsaye bazan kawo fuskar

shi ba, waton dai a takaice shine Nazir kenan?"

Aunty tace "Eh shine don ALLAH taimako d'aya muke so kayi muna" likitan yace "kamar me fa?"

Tace "ka kula muna da Amrah mu zamu je mu binciko duk inda Nazir d'in yake" yayi saurin fad'in "k

ada ki damu wannan ba damuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login