Showing 93001 words to 96000 words out of 129444 words
Itace ta haifesu, Zuwaira cikin fad'uwar gaba tace
"Kan Ub
an cen lalle ko gidannan za'ayi yak'in Basasa na biyu muddin aka ce kune Yan hayan da Zamu zauna daku"
D'aya daga cikin yanmatan wadda da alamu tafi zama tsagera tace
"Kece sabuwa a fagen yak'in mu ai mun riga da munci dubu sai ceto, don haka ki iya
bakinki WALLAHI tun kafin mu lakad'a maki shegen duka a yanzunnan don mu Fara sanar dake mu d'in ko su waye ne mu"
Amrah dake d'aki tana kuka jin sautin maganganunsu na rashin mutunci ga Mamarta yasa ta fito rik'e da k'ugu tana kallonsu d'aya bayan d'ay
a tace,
"Ku haka ake yi daga zuwa sai tashin hankali? To Bari kuji arzikinmu ne kuka zo kuci gidan don haka Babu Yar iskar da ta isa ta d'aga muna dan yatsa bamu karya shi ba"
Yanmatan biyu suka kalli juna suka fashe da dariya dayar ta k'araso gaban
Amrah ta tsaya tana nunata da D'an yatsa tace
"Ke karamar k'waranya a cikin kayan miya wacece ke Kuma miye Matsayinki?"
Ta maida kallonta ga dayar tace
"Wai Aunty Zulfi ko itace ma yarinyar da aka ce tayi shari'a da Mijin da Mahaifinta ya aura mat
a tun tana Yar shekara Tara?"
Wadda aka Kira da suna Zulfi tace
"Kin canka adaidai ko Hafsa don kuwa ita d'in ce dai a gabanki ALLAH dai ya rabamu da irin wannan bak'in halin Mai cike da abun kunya"
Wadda aka Kira Hafsa ta rufe Baki tana k'unshe d
ariya tace
"Sannu kinji ALLAH ya baki ladar abunda kika aikata don Wannan shi ake kira da rashin sanin darajar Mahaifi, in wasu suna Biyayya bayan rai ga saurayi to ke rashin Biyayya bayan Rai kika yiwa Mahaifinki tirr WALLAHI kinsha haush...."
Kafi
n ta Kai k'arshen maganarta ne Zuwaira ta d'auketa da wani bahagon Mari, Yarinyar tayi saurin dafe gefen da ta mareta ta zaro Ido tace
"Ni kika mar...?"
Zuwaira ta k'ara d'aga hannu ta sake sharara mata wani Marin, yarinyar tayi wata kuwwa tayi tsall
e ta cakumo Zuwaira da kokawa Aiko itama dayar Yarinyar ta iso wurin aguje ta yo kanta da duka, Mamarsu Kam Zaune tayi tana dariya tace
"Ku daki banza Ni nace Kuma ba za'ayi komi ba"
Amrah kam ganin sun rufu sunata kokawa da Zuwaira yasa tayi kitchen
aguje ta d'auko muciya Aiko ta Fara dukansu ta ko'ina iya k'arfinta Hafsa tayi tsalle zata kaiwa Zuwaira duka Amrah ta maka Mata muciya a fuska ta yi saurin fasa k'ara tace
" Wyyo Mummy Ta fasa man Ido wayyo ALLAHna ta kasheni"
Zuwaira ko ta d'aga
Zulfi ta jefar a k'asa ta tausheta sai dukanta take yi, Amrah ma tabita da muciya sai dukan Zulfi ta ke ga kafafuwa aguje Mamarsu ta rugo don Daman ta d'auka zasu ci galabarsu ne shiyasa ta kyale Amman tana ganin an bugewa Hafsa Ido tasha d'amara ta yo Kan
Zuwaira da duka, Ita ko tana ganin haka ta Mik'e tsaye suka Fara dambacewa tsakaninsu.
Hafsa dafe da Ido d'aya Yana tsiyayar jini tana kuruwar neman agaji, Amrah Kam sai dukan Zulfi take ta ko'ina da muciyar Zulfi ma ta yo Kan Amrah cikin zafin nama ta
Fara Kai mata naushi a fuska ta k'wace muciyar ta dinga dukanta da ita Amrah Kam ganin bazata iya da ita ba yasa ta fita gidan aguje wajen neman taimako, Aiko sai gata ta dawo ta taradda sun rufu Kan Zuwaira suna ta duka Zulfi da muciyar Mamarsu da wani g
untun icce, duk sun farfasa mata jiki da abun dukan mutane suka zo da sauri suka raba fadan.
K'atuwar matar tana ganin yanda jini ke zuba ga Hafsa cikin rud'ewa ta janyota zata fita ta kalli Zuwaira tana maida Numfashi tace da ita
"Sai na kasheku duk
anku a gidannan WALLAHI mutukar kuka nakasawa 'yata Ido"
Ta fita rungume da Hafsar Zulfi ta jefar da muciyar ta bi bayansu sai tsinewa su Zuwaira take yi.
Zuwaira ta kalli Amrah dake tsaye tana kukan saboda ganin yanda suka jiwa Mamarta tace
"Z
o muje Asibiti Mama a duba ki duk sun ji maki ciyo"
Zuwaira ta shafo goshinta taga jini cikin tsananin bak'in ciki ta yi k'ofar d'akinta tana wara idon inda ta watsar da kudinta amman ko dubu d'aya bata gani ba, cikin takaici ta kalli mutanen da suka yi
cincirindo cikin gidan tace
"Ubanwa ya d'auke Mani kud'i ??"
Aiko mutane suka Fara sulalewa wasu Kuma suka tsaya suna ta sa'insa da ita saboda jin haushin laka masu sata da tayi ,yayinda wasu suke ta rantse rantsen su basu bane wasu Kuma suce su da
i basu ma ga kud'in ba.
Wasa farin girki
🤣
Akafta
🏃🏻
♀
️
D/Auta ce
✍
🏻
*
🌈🌈
BAKAN GIZO
🌈🌈
*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Wannan page naki ne sukutum d'iyar kirki Mu
rjanutu Sa'idu ki dad'e kiyi lasting tawajena
👍🏻😛
*
*51*
Cikin tsananin tashin hankali Zuwaira ta dafe k'irji tace da Amrah,. "Cikon kud'in hayarmu ne fa da aka maidomuna WALLAHI duk Wanda yasan ya daukesu ya maidosu tun wuri don duk Wanda ya
kuskura ya cisu ya ciwa kanshi bala'i don WALLAHI ba zan barshi ya cisu ta dad'i ba"
Ta k'are maganar tare da zubowar wasu hawayen takaici, don ita duk jibgar da tasha bata ji zafinta irin kudinta da aka wawashe ba, Aiko salun alun mutane suka fice suka
barta da takaici goma da ashirin.
Amrah ta share hawayenta ta shiga d'akin Zuwairar ta d'auko mata hijabi ta saka mata sanna tace,. "Muje a duba maki ciyukan Mama tun kafin su fara yi maki tsami a jiki"
Zuwaira ta zura talkaminta ta nufi hanyar fit
a Amrah ta rufo masu d'akunan suka fita, kasancewar akwai wani chemist a unguwar cen suka nufa aka yiwa Zuwaira dressing d'in raunukan da ta samu, aka hado mata da magungunan da zata sha don su rage mata zafin zugi har ma raunin yayi saurin kamewa, suna Ka
n hanyar dawowa ne sai ga Lantana a firgice saboda taji labarin abunda ya faru, ganin raunukan da Zuwairar taji yasa ta zaro Ido tace
"Kan uban cen yanzu shikenan a haka za'a barsu su ci bulus?"
Zuwaira tayi Yar dariyar k'arfin hali tace
"Ai muma
basu ci bulus ba don kuwa Amrah ta fasawa tsagerar yarinyar Ido d'aya kin ko ga muma mun rama"
Tana Kare maganar ta ci gaba da tafiya don ta matsu ta je gida ta kwanta saboda gaba d'aya jikinta ciyo yake, Lantana ta biyo bayanta tana fad'in
"Gaskiya
dai wannan Abu bai yi dad'i ba sai kace daman jiraye suke daku? Kuma ace a hakan zaku zauna dasu?"
Amrah tayi saurin fad'in "bar masu gidan zamuyi mukam don ba zamu iya wannan bala'in ba mukam"
Zuwaira ta waigo ta maka mata harara tace
"Ai WALLA
HI ba inda zamu je sai dai in sune zasu bar muna gidan, ai in muka yi haka ganin zasu yi kamar tsoronsu muke yi shiyasa zamu bar masu gida"
Cikin jimami Lantana tace,. "Gaskiya fa maganar Yarinyarnan abun dubawa ce don kuwa gara ace kunji tsoron da suj
e su yi maku wata illar, don fa naji ana labarin cewa matar tace wai sai ta kasheku"
Kafin Zuwaira ta Sami damar mayarwa da Lantana amsa sai ga motar 'yansanda wiwi ta nufo unguwar, cike da mamaki duk suka bi motar da kallo har ta tsaya k'ofar gidan, sa
i ga matar biye dasu Kan acab'a ya ajiyeta tana hangosu tace da wani D'ansanda
"Gasu cen"
Aiko ganin yansandan sun nufosu yasa Lantana zankarawa da gudu, Aiko wani D'ansanda ya bita ya damkota tana fad'in
"Ba Dani aka yi fadan ba Nima yanzu na z
o"
Amman hakan bai hana a had'a da ita ba don kuwa tare da su Zuwaira aka turata Motar suka tafi,.
Koda suka je aka kaisu wani d'aki aka fara bincikar abunda yasa suka fasawa Yar mutane Ido d'aya? gashi ankaita Asibiti ance dole sai anyi mata aiki s
aboda gefen gilashin kwayar idon ya fashe, cikin rud'ewa Amrah ta fara kuka wani D'ansanda ya katsa mata tsawa yace
"Yi muna shiru bayani zakuyi kuje ku kawo kud'in aikin idan ba haka ba WALLAHI yanzu mu turaku cell"
Zuwaira tuno azabar da aka bata
yasa ta fara kuka tana fad'in
"Oga kalli jikina Nima gaka irin raunin da suka yi mani yanzu haka likita yace gefen Kwakwalwata Yana gaf da tab'uwa Nima biyana za'a yi kenan?"
Wani D'ansanda ya zarowa Zuwaira Ido yace,. "Wai ke ba ke bace kwanakin ba
ya aka kawo muna case dinki ba akan kin canyewa wani kud'i ko ba ke bace?"
Zuwaira ta marairece tace
"Nice amman ban ci kud'inshi ba b'acewa suka yi"
Yace " Ok Da kin kuskura kin sake shigowa hannunmu zaki gane kinyi kuskure don haka ki biya kud'i
n aikin Yarinya kawai aje ayi mata aiki sauri ake yi"
Zuwaira zata yi magana Amrah ta kalli D'ansandn tace
"Sir zamu bada nawa ne?"
Zuwaira ta maka mata Harara tace
"Ranka ya dad'e ka tausayamani Nima fa dubi yanda suka ji mani rauni haka kawai
fa suka rufemu da duka bamu yi masu komi ba"
Katotuwar Matar tace
"K'arya kike yi Munafuka ke kika Fara dukan yarana Sannan 'yarki ta saka muciya ta bugawa Hafsa a ido don haka ki biya kud'in kawai na baro Yarinya a Asibiti Ni kawai ake jira in kawo
kud'in"
Zuwaira ta maka mata Harara tace
"Ni da naje chemist aka dubani nawa nace ku bani? Koko don Ni bansan hanyar wajen yansandan bane?"
Wani babban yansandan da tunda aka Fara rigimar baice kanzil ba, don shi kam tunaninshi kacokam yana Kan A
mrah da farad d'aya yaji yana bala'in kaunarta, ranshi a had'e ya Mik'e ya fito waje yace da Zuwaira ta biyoshi.
Gabanta ya kire ya fad'i ba shiri duk da daman cen a tsure take don tasa a ranta kwandala bazata bada ba tunda har suka ja aka sace ata kud'
i, cikin firgici ta iskeshi inda yake tsaye ta k'ara marairecewa tace,. "Don ALLAH Oga kayi hak'uri WALLAHI bani da kud'in da Zan basu don ma Ni kud'ina har dubu d'ari da ashirin da biyar suka ja aka sace man lokacin da muke fadan"
Mutumin yayi Yar g
ajeruwar dariya yace
"Waccen Yarinyar 'yarki ce?"
Zuwaira tayi saurin d'aga Kai tace
"Ni na haifeta da cikina kuwa"
Ya gyara tsayinshi yace
"Wani taimako zanyi maku amman Nima sai in zaki taimakeni ki bani auren yarki"
Zuwaira ta zaro Id
o tace
"Ranka ya dad'e ai matar aure ce yanzu haka daga gidan Mijinta take ganina ta zo tayi dace da wannan rigimar"
Cikin jimami yace
"Ok ba damuwa yanzu dai tunda nayi niyarr taimaka maku to zaku bada rabin kud'in aikin yarinyar da aka nema zo m
uje"
Zuwaira ta biyoshi tana fad'in ,. "Ranka ya dad'e a taimaka muna WALLAHI kud'ina aka sace yanzunnan don ko na abunda zamu ci bamu da"
Mutumin ya juyo yace,
"Kuyi hak'uri kawai ku bada kud'in idan ba haka ba WALLAHI yarana zasu rufeku a ban
za"
Yayi gaba Zuwaira ta bishi da harara a zuciyarta tace
_"Ji wata fuskarshi kamar Namijin Saniya wai har yake zancen auren Amrah a hakan zan baka Yar tawa da wannan cin zanzanar a fuska??? Ai ko ni ban iya aurenka ballantana 'yata"_
Har suka kom
a d'akin bata daina aibatashi ba suna shiga Kai tsaye ya kalli matar yace
"Nawa ne kud'in aikin yarinyar?"
Matar ta kalli Zuwaira ta maka mata Harara Sannan tace,. "Dubu Saba'in ne"
Zuwaira ta zaro Ido tace
"WALLAHI ALLAH bazan baki dubu Saba'
in ba kaji munafuka"
Lantana ta D'an rik'o hannunta alamar ta sassafta don bayan fitarsu wani D'ansanda daga cikinsu yace
"Shi yama fi son kar ta biya kud'in a kaisu cell a ajiye sai sun lallasu Sannan a fito da su kuma dole sai anbiya kud'in zasu sa
ke su"
Shiyasa daga Lantana har Amrah cikinsu ya duri ruwa musamman Amrah da sai da taji cikinta ya katsa, aiko Zuwaira ta k'wace hannunta tana hararar matar tace
"Sakeni Lantana ba Zan yi shiru in zura ido wannan Muguwar Matar ta cuceni ba WALLAHI"
Wani D'ansanda ya yo kanta kamar zai daketa yace
"Kada kawo muna shirme anan ki bata kud'in kawai taje wurin yarta da kuka nakasa tun kafin ki jawa kanki in yi maki mummunan duka anan wurin"
Zuwaira tayi mukus dole amman idonta basu daina hararar
Matar ba, Babban yansandan ya Kara had'e fuska ya kalli Zuwaira yace
"Ki basu rabin kud'in da aka nema"
Zuwaira ta had'iye miyaun da kyar ta marairece zata fara rantsuwa kenan wannan D'ansandan da yake kufule da ita ya ce
"Bada kud'in kawai bama b
ukatar maganarki"
Amrah ta kalli D'ansandn tace
"Bari inje gida yanzu in kawo maku?"
Lantana tayi zumut tace
"A'a jira Ina dasu a nan na sak'on wata da ta bani"
Ta ciro kud'in ta kindanya dubu talatin da biyar cur! sannan mik'awa Zuwaira, ci
kin tsananin jin haushin bada su ta mik'awa Ogan ya karb'a, itama Lantana aka ce sai ta bada dubu biyar haka ta zaresu jiki yana rawa ta mika sannan aka sallamesu tare da gargadin kada wani abu ya koma shiga tsakaninsu, suka saka hannu a wata takarda suka
fito.
Manage plss
Akafta
D/Auta ce
✍
🏻
*
🌈🌈
BAKAN GIZO
🌈🌈
*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*GODIYATA A GAREKI BATA LISSAFUWA JAR MASOYIYATA RAHMA LADINGO YAR M
UTAN NIGER ALLAH ya bar zumunci ni da ke tawajena
🤝🏻
*
*PAGE 52*
Koda suka dawo gida Lantana bata bar gidan ba har sai da Zuwaira ta biyata kud'inta cas! sannan ta tafi zuciyarta cike da takaicin zuwa wajensu da tayi, don gashi ya jaza mata a
sarar dubu biyar bata ji ba bata gani ba tana zaman zamanta rabon fitar kud'in yasa ta nufo gidansu da zummar jaje, aranta tace
_"Naje jaje da neman jin gulma gashi ni ma yanzu na zama wadda za'a jajantawa, ai WALLAHI wurin Alhaji mai rumbun kud'in zan
je in k'ara turoshi Koda zuwan farko ne yayi nasan zan samu fiye da kud'ina da na rasa, ko da cikin ayi auren ni miye nawa in dai zan sami kud'i cen ta matse masu."_
Bayan fitar Lantana Amrah ta kalli Mamarta da ke kwance tana jinyar jikinta tace
"Ma
ma Ina da wata shawara"
Zuwaira ta kalleta ta gefen Ido ta b'ata fuska tace
"Don ALLAH in har kinsan abunda zaki fad'a ba zai yi man dad'i ba to don ALLAH ki bar maganar kawai ban son jinta"
Amrah ta yi narau narau da Ido wata kwalla ta taru a cik
in idonta tace
"Kiyi hak'uri Mama daman cewa nayi me zai hana mu koma Zamfara ne? Ni fa WALLAHI hankalina bai kwanta da mutanennan ba, Ina jin tsoron su cutar damu a banza gashi bamu da kowa Wanda zai tsaya muna a garinnan yanzu"
Zuwaira ta Mik'e zau
ne da k'yar saboda jinkinta da take ko'ina yana mata ciyo ta kalli Amrah tace
"Ba wai bana son komawa garinmu bane ni Ina hangen kada muje cen ne a takuraku don kinsan Mahaifiyata ta dad'e da rasuwa Matar Babana ce kad'ai a gidan gata masifaffiyar gaske
ce kuma kinsan yanzu abunda ya faru tsakanina da Asabe bazai tab'a yiyuwa inje gidan Inna Habi in zauna ba". Cewa da Mahaifiyar Asabe da suke Uwa d'aya Uba d'aya da Mahaifiyarta
Amrah ta share hawayenta tace
"Mu tafi kawai Mama ko da ace da sunan g
anin gida ne Kin ga sai mu karb'i kud'in hayarmu da muka bada idan mun dawo sai mu nemi wani gidan"
Zuwaira tayi shiru tana nazari sannan tace,. "Matar Babana fa masifaffiya ce ko kad'an tamu bazata zo d'aya ni da ita ba, don akanta ma Babana yace kad
a in sake zo masa gida a wani ganin gida da na tab'a zuwa shekarun baya lokacin da kasuwa take gara man idan baki manta ba, don ko abunda na kai masa a lokacin fushi yayi ya watso mani abuna yace baya so dole na tattara na kaiwa Inna Habi sannan na baro ga
rin, to Kinga yanzu idan mun je bamu san me zamu taras ba"
Amrah ta share hawayenta da gefen hijabinta tayi shiru tana wasa da Yan yatsunta, saboda maganar da take cin ranta akan ta fad'a tana jin tsoro amman dai dole ta dake cikin fargaba tace,
"Mam
ah!"
Zuwaira ta d'ago kanta daga kwancen tace
"Ina saurarenki"
Wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata cikin sanyin jiki tace,. "Me zai hana ki hak'ura ki barni in koma gidan Yaya Nazir????"
Zuwaira ta maka mata wata k'atuwar harara ta buga tsa
ki ta nuna mata k'ofa tace,. "Tashi ki fitar man daga d'aki tun kafin ki janyo in sauke fushina akanki"
Amrah ta mik'e cikin rawar jiki ta nufi k'ofar fita tace,. "Don ALLAH kiyi hakuri Mama akwai dalilin da har yasa kika ji nace haka, saboda bana son
muyi ta zama cikin wannan hali da muka fara tsintar kanmu a ciki, yanzu fa kina kallo har an fara yi muna gori wurin mutanen da bamu ma sansu ba amman su suna da labarinmu, me kike tsammani a gaba idan har aka ce a haka zamu ci gaba da rayuwa irin wanan ma
rar 'yanci??? A gaskiya ni dai ina son in koma gidan Mijina in kula da tarbiyyar yarana"
A zabure Zuwaira ta mik'e zaune Amrah ta fita da sauri tayi waje tana kuka saboda jin tsoron kada ta daketa, Zuwaira cikin tsananin mamakin da Amrah ta bata tace,.
"Banga laifinki ba don kin watsa man k'asa a ido saboda Namiji ki zab'i ki tozartani a gaban idon duniya, WALLAHI baki da laifi nice mai laifin tun farko da har na shiga cikin sabgarki, ki je ko