Showing 33001 words to 36000 words out of 129444 words
fito d'an k'aramin d'akinshi tareda rufoshi har ya kai bakin k'ofar gida zai fita ne, na jiyo sautin wata mata dake zaune gindin murhu tana dama kullun koko tace, "Yau ma tafiyar zakayi ba tareda ka jira k'a
nwarka ba?" ya waigo ranshi a b'ace yace, "Haba Inna kinfa san Jamila bak'ar Nawa (ganda) ce da ita haka kawai tasa mutum yayi latti a dake shi a banza." ya k'are maganar cikin had'e fuska, Mahaifiyarshi wadda naji ya kira da suna Inna ta k'ura
masa kallo cike da takaici tace,
"Ai in baka jirata anan ba sai kaje inda kaine zaka jira har ma a saka ka aikin da zai janyo makka lattin."
Nazir ranshi a b'ace ya kalli kanwarshi da ba zata wuce shekara shidda ba, dake ta cin d'imamen tuwonta
yace, "WALLAHI kika yarda na isa gidansu Amrah baki shirya ba, ni ba jiranki zanyi ba don ma ki sani." yana k'are fad'ar maganar ya tusa kanshi zai fita NE Babanshi ya fito daga d'akinshi yace, "Saboda saurin kaje gidan Malam bukar yau har
kud'in taran ka manta kenan?" ya k'are maganar yana 'yar dariya sannan ya kalli Jamila dake ta guma lomar tuwonta yace, "Ke kuma kiyi sauri ki k'arasa kar kuje kuyi latti." Jamila ta mik'e tsam ta wanko hannunta tace, "Ni nama k'oshi ai" I
nnar tasu ta tsiyaya mata kunu a wata gora ta mik'a mata Baban ya basu kud'in taransu, kasancewar Nazir ne ya fara karb'ar kud'in ana bashi yace dasu "ya wuce" suka bishi da addu'ar "a dawo lafiya" Jamila kam sai da ta tsaya saka sucks da sandal d'
inta sannan ta rataya jakarta ta bishi da gudunta, koda ta fito har ya shige gidansu Amrah, da sallamarshi a baki ya shiga gidan, inda ya taradda lokacin ma aka k'are yiwa Amrah wanka, ta fito da gudu zuwa d'akin Mamarta tana yarfa hannu, Nazir ya kalle
ta yana 'yar dariya yace, "Lalle ma to kiyi sauri dai kada muyi latti yarinya" sai ga Zuwaira ta fito daga bayin tana ajiye bokiti tace, "A'a Nazir har an fito to bari inyi sauri in k'arasa shiryata sai ku tafi" ya d'an sosa kanshi yace, "B
a damuwa Mama ina kwana?" Tana amsa masa ta shige d'akinta da sauri tana shiryawa Amrah,Sai dai Zuwaira daga cen cikin d'akin tace dashi "Don ALLAH Nazir zubar man da sharar nan kafin in k'arasa shiryata." Aiko ya ajiye jakarshi ya sungumi sharar ya
je zubarwa ne sai ga jamila ta fito daga gidansu, tana hangoshi yana zubar da shara ta rufe bakinta tana dariya, yayi kamar bai ganta ba ya dawo ya ajiye abun sharar yana kakkab'e jikinshi da wani k'aramin hankacif d'in dake hannunshi, ta shigo gidan da s
allamarta ta tsaya tsakar gidan tana jiran Amrah'r ta fito su wuce.
Sai ga Amrah ta fito d'akinsu da hijab a hannunta tana saka sandal d'inta da sauri sai rawar jiki takeyi, Nazir ya kalleta yayi dariya yace, "Kiyi a hankali fa kar kije ki fad'i kaw
o hijabin in saka maki." ta mik'a masa bayan ta k'are saka sandal d'in yana cikin saka mata tana 'yar dariya, sannan Zuwaira ta fito da jakarta ta mik'a masa tareda kular abincin Amrah duka, idonta yakai kan Jamila dake rakub'e jikin gini tana kallonsu,
tana 'yar dariya tace. "A'a D'iyar Inna an fito?" tace "Eh ina kwana?" tace "Lafiya k'alau" ta k'arasa maganar da kallon Nazir tace, "Yau ma dai kam Amrah bata da kud'in tara, GA dai abincinta nan sai ta ci in an tashi break " Nazir ya ri'k
o hannun Amrah yace, "Ba komi ai sai in bata nawa zo muje kar muyi latti, mun tafi sai mun dawo" Zuwaira ta bisu tana yi masu ALLAH ya tsare hanya har k'ofar gida, sannan ta juyo tana 'yar dariya tace, "Ai tunda kana bata ni nawa sun huta sai in
k'ara a dashena da nike zubawa d'an kullum."
Nazir kam goye yake da tashi jakar a baya sannan ya rik'o kular Amrah da hannu d'aya, ya rik'e hannunta da d'ayan hannun suna tafiya Jamila tana biye dasu a baya, sai sunyi mata nisa ta biyosu da gudu t
ana fad'in, "Dob ALLAH yaya Nazir ku jirani" Nazir ya juyo ya maka mata wata k'atuwar harara yace, "Idan bazakiyi sauri ba WALLAHI bazamu jiraki ba, raguwa kawai sai shegen son jikin tsiya, amman in wajen CIN abinci ne lomarki tafi ta kowa auki.
"
Amrah ta juyo tana yimata dariya haka suke tafiyar har su kai makarantar, kasancewar ba wata tazara ce dasu sosai ba, don da sun fito kwararon gidansu Titi kawai zasu tsallewa sai makarantar.
kasancewar Makarantar had'e take da Primary da second
ary, shiyasa idan ya kai Amrah ajinsu ya mik'a mata kularta sai shi ya wuce sashensu na 'yan secondary, da kuma an tada su Amrah break indai ya manta bai bata kud'in tarar ba, to duk dabarar da zaiyi sai ya fito ya kai mata kud'in koda ko ace da malami a
ajinsu.
Shi kuma ba ya fitowa ma break saboda yasan baida kud'in da zai kashe, haka zaiyi ta zama a class har sai an dawo aci gaba da karatu, sai dai wani zubin idan abokanshi sun ja shi dole ya fito in har sunada kud'in su bashi ya siye abunda yake so
.
Idan aka tashi kuwa don su Amrah ake riga tashi kasancewar akwai yara da yawa 'yan unguwarsu, sai su had'u su tafi tare gida gaba d'aya, amman fa duk wadda tayi gangancin tab'a Amrah da ya dawo makarantar sai ya biya gidansu ya tambayeta, dawa da
wa suka daketa ita ko tayita lissafo masa su ko d'aya bayan d'aya, duk sai ya rama mata dukanta koda ko da Jamila a ciki, shiyasa da yawa ma basa tab'ata don sun san sauran, don da a daki Amrah gara adaki Jamila sai goma yafi son haka da a tab'i lafiyar 'y
ar gaban goshinshi.
Shiyasa wani zubin Inna take yi masa fad'a kamar ta dake shi, duk ko da take mace mai sanyin hali amman watarana Nazir sai ya janyo tayi ta fad'a kamar taci babu, Musamman idan yazo dukan Jamila akan ta daki Amrah, har sai dattijuwa
r nan mai kosai taji ta zagayo tana bata hak'uri, saboda katangarsu a had'e take indai ka d'aga murya dole ne a jiyo sautin juna.
Nazir kam ranar ma hakan ce takasance ya manta shaf bai bata kud'in ba sai da yaji an tada su break, sannan yace da mala
minsu dake ta rubutu a allo, yana son yaje ya kaiwa kanwarshi kud'in taranta, Ba tareda ya waigo ba yace dashi minti biyu ya bashi idan ya wucesu jikinshi zai gaya nasa, aiko da sauri ya fito yana ta rabon idon ta ina zai hangota, sai cen ya ganta rakub'e
jikin k'arfe k'ofar ajikinsu tana kuka, da sauri ya k'araso ya kira sunanta yace, "Wa ya dake ki?" Amrah ta fara goge hawayenta da hijabinta tace, "Kowa da kud'inshi yana ta kashewa ni kad'aice ba'a bani ba"
Ya dafe goshinshi yace, "Kash k
iyi hak'uri kingansu nan mantawa nayi ban baki ba, karb'i kije ki sayi duk abunda kike so kar ki baiwa kowa kinji?" ta d'aga kanta cikin murna ta karb'e kud'in ta ruga da gudu wurin masu sai da kayan k'walam, ya bita da kallo zuciyarshi cike da tausayint
a sannan ya koma class, shigarshi ajin keda wuya Malamin ya katsa masa tsawa akan ya fita waje ya durk'usa, ranshi ya b'aci sosai yak'i bashi hak'uri ya dawo k'ofar ajin ya duk'a, saboda Nazir ba dai Zuciya ba ko kad'an baya da hak'uri matuk'ar ba akan A
mrah bane, haka yayita zama wurin har malamin ya gama karatun, ya fito da bulalarshi ta dorina yayita jibgarshi har sai da yayi masa bulala goma sannan yace dashi ya tashi ya biyoshi Office, Nazir kan duk da yaji zafin bulolin amman saboda kafaffiyar zuciy
a yak'i yin kuka, ya biyoshi Office d'in ya duk'a yana jin rad'ad'in bulolin a jikinshi, Malamin ya ajiye littafan dake hannunshi saman benci, sannan ya zauna yana kallonshi ido cikin ido yace dashi, "Nazir me yasa kake son wasa da karatu ne duk da k
'ok'arin da kake dashi?, na fahimceka a duk lokacin da nike yi maku karatu sai kayi dabarar fita ka dad'e baka dawo ba, shin karatun ne nawa baka buk'ata ko kuwa dai a'a da gangan kakeyi karatunne gaba d'aya baka buk'ata ?" Nazir ya duk'e ba tareda yace
dashi k'anzil ba saboda zuciyarshi ta kawo wuya, duk maganar da zai fad'a a lokacin ba mai dad'i bace, har sai da Malamin ya k'ara cewa, "Kana da zuciya sosai na fahimta, amman kuma sam baka gudun b'acin ranta, shin dolene sai kai za'a baiwa kud'i
n tarar k'anwarka?me yasa ita baza'a bata abunta a hannunta ba sai kai dole?, da za'a ce a kullum sai ka shigo aji sannan ka fita zuwa kai mata kud'i" sai a lokacin Nazir yayi jarumtar magana yace
"Mantawa nayi" Malamin yayi saurin fad'in, "
To daga yau na tuna maka wajibi ne ka bata kud'inta tun kafin ka shigo class, don matuk'ar ka sake na ji kace fita zakayi sai jikinka ya gaya maka tashi kaje amman ka sani wannan shine last warning da zanyi maka"
Nazir ya mik'e ya fito yana gunguni aran
shi yana fad'in, _"WALLAHI sai dai akasheni bazan fasa fitowa na bata kud'in ba matuk'ar dai na manta ban bata ba, haka kawai sai in barta tayita kuka abanza wallahi bazai yiyu ba sai dai ku tanadi wuk'ar yanka ni. "_
Haka ya dinga zancen zucinshi
har zuwa class d'insu, inda suma abokanshi suka yo masa caaa akai suna fad'a masa gaskiyar abunda yakeyi ya daina, dukansu ba wanda ya kula don idan ya biyesu damben tsiya ne zai rabashi dasu, ya janyo littafinshi ya CI gaba da cofe rubutun dake allon, Wan
i abokinshi mai suna Jamilu da tunda aka fara dukanshi ranshi ya b'aci yaji ba dad'i, yayi tagumi yana kallonshi kasancewar kujerarsu d'aya da Nazir, haka ma unguwarsu d'aya dashi sai dai akwai gidaje a tsakaninsu sosai, cikin sanyin Murya yace dashi
"Yanzu shikenan Nazir haka ka zab'arwa kanka?, baka da aiki sai na bautawa Zuwaira da 'yarta? WALLAHI kayiwa kanka karatun tanutsu shikenan kai ka zama bawansu, har kud'in taranma don mugunta bazasu bata ba kaine zaka dinga bata wanda ake baka daga gida?"
cikin fushi Nazir ya d'ago daga rubutun da yake yi yace, "Shin wai kai Jamilu meye naka a ciki ne?, ina ga kud'ina ne ko kuma duk abunda nikeyi ba damuwar kowa bace, idan ba zaku iya zura ido kuyi kallo ba to don Allah ku daina tankani aduk abunda
kuka ga nayiwa Zuwaira ko 'yarta, ni naji na gani ku bari dani don ALLAH ba ruwan kowa, ya kukeso inyi da rayuwata ne? yanzu fa koda na fita na tarar da ita tanata kuka fa, to don kawai in farantawa wani zan barta tayi kuka akan abunda banfi karfinshi ba?
to WALLAHI bazai yiyu ba kaji na fad'a maka, da Amrah tayi kuka gara duk mutanen garinnan gaba d'aya suyi tayi WALLAHI." yana k'are fad'ar maganar ya fisgi littafinshi yaje wata kujera ya zauna yana ci gaba da rubutushi, Zuciyarshi sai zafi take masa sab
oda ganin yafi kowa sanin abunda ya dace.
Tofa
π€π€π€π€
kuci gaba da biyoni sannu a hankali har muje inda muke son kaiwa
π
Akafta
πΉ
D/Auta ce
π€π»
*
ππ
BAKAN GIZO
ππ
*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATIO
N*
*I love you all my fan's
ππ»ππ»ππ»
*
*PAGE 23*
Koda aka tashi School Sai da Nazir ya biya ta gidansu Amrah, Zuwaira ta bashi kayan miya yayo mata markad'e sannan yayi gida, inda shigarshi gidansu keda wuya yaci karo da Inna a baki
n k'ofar d'akinta tana sanya hijab, aiko tana jin sallamarshi cike da jin dad'in ganinshi tace
" Yawwa daman yaron da zai siyoman man k'uli nike nema, tun d'azu na k'are abincin ina jiranka ka dawo ka siyo a soya muci abinci" Nazir ya b'ata fuska
yace, "Haba Inna daga dawowata kofa SALLAH banyi ba gashi itama Mamar Amrah yanzu na dawo kai mata markad'e" Inna tayi sakato tana kallonshi rik'e da kud'i a hannu tace, "Eh lalle tunda Mamar Amrah ta fini ai dole ita kaje nata aiken ni kuma naw
a da zai amfane mu duka ka nuna baka son zuwa, to WALLAHI idan baka siyo shi ba yau bazaka ci abincin gidannan ba." ya karb'i kud'in fuska a had'e ya bud'a d'akinshi ya ajiye jakarshi tareda cire kayanshi ya sauya wasu, sannan ya fito fuu ya fice gidan
Inna tana nan inda take har lokacin cike da jimamin wannan hali na Nazir, ace shi indai ba abunda ya shafi gidansu Amrah bane ko ma menene sai rayuka sun b'aci kafin yayi abu a gidansu, ko da ko abunnan wanda zai amfaneshi ne ko, 'yan mintuna a tsakani s
ai gashi ya dawo ya ajiye mata man ya d'auki buta yayi arwallah ya nufi k'aramin masallacin dake unguwar tasu.
Bayan INNA ta soya man ta zuzzubawa kowa sannan ta zauna suna cin abincin ita da Jamila, sai ga Amrah ta shigo gidan ganinta yasa Inna ta k'
aro abincin suka zauna duka su uku suna cin abincin a kwano d'aya, suna tsaka da cin abincin ne Inna ta Mik'e domin kawo masu ruwan sha, abu ga k'urciya Amrah ta d'ebo loma jamila zata kai bakinta Jamila ta k'wace da k'arfi tace bazata ci shi ba, sai ga
shi aka yi dace wajen kwacewar akaifar Jamila ta yanki Amrah kad'an a hannu, aiko tana k'yalla ido taga wurin yad'an fasa kad'an har sawun jini ya fito, aiko ta k'walla k'ara tana kallon hannun, wadda yayi dai dai da shigowar Nazir gidan da 'yar guntuwar
sallamarshi.
Inna tace "Haba Jamila me kika yi mata daga tashina yanzunnan?" Nazir ko yana zuwa bai yi wani jinkiri ba ya fallawa Jamila Mari, da sauri Inna ta k'araso wurinsu tace, "Kai kuma me tayi maka daga shigowarka?nifa bana son cin zali
n" Nazir yana rik'e da hannun Amrah inda take nuna masa yace da Inna,
"Ji fa don ALLAH Inna yanda ta ji mata ciyo a hannu" ya kalli Jamila yace, "WALLAHI kika sake ji mata sai na rama mata kema kiji inda dad'i, bak'ar muguwa kawai haka kawai
baki da aiki a kullum sai zaluntar yarinya." yana k'are fad'ar maganar ya janwo hannun Amrah suka fita k'ofar gida suka zauna a kan dakalin k'ofar gidansu yana lallashinta, sannan yaja hannunta suka tafi wani shagon dake unguwar tasu, ya fiddo kud'in da
Jamilu abokinshi ya bashi yayi break baiyi ba, ya siyo mata minti da biscuit suka dawo yace ta shiga gidansu, sannan shi ya koma gida inda ya tarar da Inna zaune tana lallashin Jamila, don bashida kunya ya nufi madafi ya d'auko kwanon abincinshi, zai shig
e d'akinshi ne Inna ta kira sunanshi fuskarta a had'e alamun ba wasa, jin yanayin sautin muryarta yasa yayi saurin juyowa, don duk abunshi baya son ganin damuwa akan fuskarta, shiyasa ya dawo ya janyo kujerar tsugunno ya zauna sannan ya ajiye kwanon agaban
shi ya ce "don ALLAH Inna kiyi hak'uri WALLAHI kema kinsan Jamila bata jin magana, haka kawai tayita dukan 'yar mutane ko bata yi mata komi ba"
Inna tayi masa wani kallo sannan tace, "To me yasa bazaka dinga yin adalci a tsakaninsu ba, ai watar
ana agaban idona Amrah take tsokalar Jamilar, sai dai inji kace tayi hak'uri don nikam ban tab'a ganin ka doketa kan tayiwa Jamila wani abu ba." yayi 'yar dariyar rashin gaskiya yace, "Ni dai Inna don ALLAH yanzu kiyi hak'uri, nayi laifi ki yafemani
ai kin yafe man ko Jamila." Jamila dake kan cinyar Inna tana sharar hawaye ta yi saurin girgiza kai alamun bata yafe ba, gaba d'aya suka saka dariya sannan ya d'auko spoon ya fara cin abincin, Inna tana ta nusar dashi abunda yake bai dace ba, yayita bat
a hak'uri abu ga d'a da uwa atake suka shirya suka koma firar duniya, har ya k'are cin abincin yasha ruwa yace da Inna shi zai fita ya d'an lek'a gidansu Jamilu suje Kasuwa wurin Babanshi, in akwai wani aikin da zasuyi