Showing 57001 words to 60000 words out of 129444 words
fiddo masa da kaina yasha"
Amrah ta maka masa wata harara ta zunb'uro baki sannan ta d'an juya k'adan ta tura yaron cikin riga ta
fara bashi nonon, aiko tsotsa d'aya biyu yaron ya sark'e ya fara tari, cikin tsananin firgici ta fara hura masa mad'iga inda shima ya kawo nashi hannun yana bubbuga bayan yaron, saukar d'imi akan hannunshi yasa yayi saurin kai kallonshi wajen, aiko sai ga
ruwan nono sai tsalgi yakeyi ya k'urawa nonon kallo gwanin sha'awa, ya cika fam har wani shek'i yakeyi ga kan nipple d'in bak'i k'irin gwanin burgewa, saboda yanda fatarta take fara tass tasa bak'in nipples d'in ya fito rad'am kamar anyi fenti, yabi wurin
da kallo cikin shauk'i ya damk'oshi da sauri ta zabura, bai damu da yanayinta ba ya tara hannu ya duk'a ya fara zuk'ar nonon tamkar yana shan fida, har da su kwandal kwandal yakeyi tamkar wani d'an jariri, zuk'ar da yakeyi har cikin ranta takeji ga wani s
abon yanayin da ya ziyarceta, ba shiri ta lumshe ido saboda dad'in da take ji har tsakiyar kanta, shiyasa ta hanashi abunda yake yi, shi kuma da abun yayi masa dad'i sai gashi da kamo d'ayan shima ya fara tsotso zumui zumui,gaba d'aya sun shagala sun manta
a ina ne suke Allah ya taimakesu wurin ba yawan mutane masu wulgawa, kukan da yaron ya canyara NE shi ya dawo dasu daga duniyar saman da suka shiga, cikin jin nauyin abunda ya faru tsakaninsu Amrah ta ture masa kai ya d'ago yana lasar baki saboda d'and'a
non zakin nonon da ya zuk'a, yana wata shuumar dariya yana kallonta da idanunshi da suka yi jajawur saboda jaraba, ta kasa had'a ido dashi ta kawar da kanta tareda turawa yaron nonon ya fara zuk'a sannan yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya.
Nazir ya
ri'ko hannunta yace,, "Ki tausayawa kanki kada k'i bari shirmen dake kanki yayi tasiri har ya hanaki abunda kike so, ni nasan kina bukatata a kusa dake saboda haka ki tausayawa kanki kizo ki mori kurciyarki, kada ki bari rudin zuciya ya jaki kije kina
cizon yatsa, don ba alfakhari ba ki tara maza goma bazaki samu kamata ba, saboda haka kiyi shawara da zuciyarki ki fiddowa kanki mafita."
Yana k'are maganar ya tada motar suka bar wajen, zuciyarshi cike take fam da soyayyarta uwa uba da mahaukaciyar sha
'awarta dake ranshi tun ranar da yasan wacece ita, don duk tsawon watannin da aka yi bai rabeta ba zuciyarsh cike take da kewarta, yana dauriya ne kawai ba don yana so ba.
Amrah dai k'anzil bata ce dashi ba sai shayar da yaronta take yi, amman fa zuciy
arta ta lula tuno ranar da ya rabata da budurcinta, sannu a hankali har zuwa lokacin da ya maidata mace da kyau tareda mamayeta da soyayyarshi da yakeyi a lokacin kwanciyar auren nasu, sannan yanzu wannan abun da ya faru yasa ta cikin wani rud'ani, har su
ka kai gidan bata daina nazarin neman mafita ba. Yayi horn maigadi yazo ya bud'e masa ya shiga da motar d'an wadataccen gidanshi, don baza'a kirashi da k'aramin gida ba, ya sami cikin wata rumfa yayi parking sannan ya fito, yayinda ita kam ko motsi kasa
yi tayi saboda zuciyarta da ke ta halbawa da sauri da sauri, har sai da ya zagayo ya bud'e murfin ya zura hannu ya d'auko Umar dake ta barcinshi, sannan ya d'orashi a kafad'a ya yi mata wani sihirtaccen kallo yace
"Welcome to your ne home my wify"
Amrah tayi kamar bata ji shi ba ta yunk'ura cikin sanyin jiki ta fito, ta kai kallonta ga gidan ya burgeta sosai amman ta waske ta tsaya jikin motar ta rungume hannuwa tana kallon k'asa, Yayi 'yar dariya sannan ya rik'o hannunta ba shiri ta rumtse ido sabo
da jin wani shock da ya ziyarci gangar jikinta, ba musu tabishi har zuwa 'yar k'aramar k'ofar da zata sadasu da sashen Inna, gaban Amrah sai fad'uwa yakeyi gaba d'aya jin kanta takeyi wata iri, saboda sabon yanayin da take jin kanta da gangar jikinta har m
a da zuciyarta da ruhi gaba d'aya.
Akafta
π
D/Auta ce
*
ππ
BAKAN GIZO
ππ
*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comment's d'inki yana sani farin ciki ba kad'an ba Alkhairin ALLAH
ya kai maku duk inda kuke, masoyana da masoya book d'ina na BAKAN Gizo dukanku ina maku son so fisabilillah
πππ»
*
*PAGE 34*
Da Sallama Nazir ya shiga d'akin Inna rungume da yaronshi, Inna ta amsa tareda k'ara fad'ad'a fuskarta da fara'a saboda
hango d'an jikallenta da tayi, Nazir kai tsaye wurinta ya nufa ya mik'a mata yaron cike da tsantsar farin ciki Inna ta karbeshi tana jin k'aunarshi har cikin ranta.
Amrah kam sai da tayi jim na d'an lokaci sannan ta shigo d'akin da sallamarta,
Inna da Nazir d'in duka suka amsa mata sallamar kai tsaye wajen Innar ta nufa tana gayar da ita cike da jin nauyinta, Inna ta amsa faran faram kamar ba wani abu a tsakaninsu sanna ta koma tana gyarawa Umar zaman hularshi, don barcinshi yake yi sharkaf sab
oda yasha ya k'oshi, Inna ta mik'e ta d'auko zane ta goye yaron ram abayanta, a cewarta yaro yafi jin dad'in bacci in aka goyashi aiko ya lafe abinshi yana ta barcinshi har da su ajiyar zuciya.
Inna ta mik'e ta je ta kawo masu abinc
i da ruwa sannan ta fice tana ta 'yan k'ananun ayukanta, Nazir ya kalli Amrah da ke rakub'e tamkar wata mai jin tsoronsu, yayi d'an guntun murmushi ya Mik'e tsaye ya cire babbar rigarshi da fula ya ajiye sannan yace, "Ki taso muci abinci" Amrah tayi
kamar bata jishi ba ta k'ara gyara zamanta, Nazir ya zuba abincin a plate d'aya ya saka spoons ya zo wurinta ya ajiye sannan yace da ita,
"Bismillah Maman Umar farouk" kanta a sunne tace, "Na k'oshi" ya d'ago kanshi ya kalleta yace
"Me kika ci?" tak'i bari su had'a ido tace "Bana jin yunwa ne kawai" kafin yayi magana sai ga Inna ta shigo tana fad'in, "Kici ki k'oshi don maijego bata zama da yunwa, ko don yaronta ai taci abinci don ya sami ruwan nono sosai" Amrah cike da
jin nauyin Inna ta d'auki spoon ta fara ci a hankali, Nazir ma ganin Inna yasa yana ta cin abincinshi ba tareda ya sake bi takanta ba, Inna gano kamar tana jin nauyinta yasa ta yi k'uryar d'aki ta bar masu falon, zuciyarta cike da tausayin Nazirunta
saboda tunanin Zuwaira bazata barsu suyi zaman aurensu ba, duk da ko ita kanta da zai sahale mata d'in da tafi son hakan tunda bata sonshi, kuma muddin idan suka ci gaba da zama a hakan shine a wahale, ga kuma Auren da zaiyi tana jin tsoron itama tazo
ta gano Amrah bata girmamashi itama ta bi sawunta su maida mata da yaro Mijin tace, motsin da yaron yakeyi abayanta yasa ta lallab'a ta saukar dashi a hankali ta kwantar dashi akan gadonta, tana k'are masa kallo zuciyarta cike da tsantsan k'aunarshi, w
ani gefen kuma tausayinshi take ji saboda tabbacin da take dashi na Zuwaira zata bi duk hanyar da zata bi ta raba auren Iyayenshi.
Amrah da Nazir kam sai aikawa juna sak'onni sukeyi ta ido, saboda idan ya kalleta ta maka masa harara yayi 'yar dari
ya, haka suka ci gaba da cin abincin har Amrah ta ajiye spoon d'in tace ta k'oshi, Nazir bai kulata ba yaci gaba da cin abincinshi har da su k'ari, Inna ta fito tayi waje tana ci gaba da hidimar had'a mata kunun ganyen da take yi mata, wanda tun kafin su
zo ta fara hidimarshi, aiko sai gata ta damo kunun da zafinshi cike da wani k'aramin bokiti ta ajiye mata tana 'yar dariya tace, "Ga kunu nan kiyi k'ok'ari ki shanyeshi kafin Dare."
Gaban Amrah yayi saurin fad'uwa saboda daren da taji ta ambata, sabo
da ta tuno da Zuwaira da 'yan k'annenta aranta tace,
_" waton dai ana nufin anan zan ta ci gaba da zama kenan har sai an kawo kud'in?"_
Zuciyarta ta karye sai ga Kuka shaaa akan fuskarta, Inna ta bita da kallo cike da mamakinta tace,, "Bakya
son kunun ne ko kuwa?" Amrah ta goge hawayenta ta janyo bokitin kunun gabanta ta fara zubawa tace, "Zan sha Inna"
Inna ta zauna tana nazarin yanayinta, Nazir kam Mik'ewa yayi ya yi sashenshi inda d'akinshi yake, zuciyarshi cike da tsantsar farin
cikin zuwan Amrah gidanshi, duk da wani sashe na zuciyarshi yana kokwanton zaman nata ya d'ore.
*********
Zuwaira kam ganin Abbati yak'i dawowa da wuri yasa ta sab'a hijabinta ta yi wajen bid'ar dillalin da kanta, ALLAH yasa ta taki
sa'a ta iskeshi gida suka rankayo gidan tare, koda suka zo sun taradda wani wanda Abbati ya kira gaba d'aya suka shiga gidan, duba nan lek'a nan ko'ina sai da suka tantance sannan wanda ta kira ya fara yiwa gidan kud'i da miliyan biyu da d'ari takwas,
ta nuna rashin amincewarta d'ayan kuma yayi masa kud'i da miliyan Uku saboda shi kanshi yasan gidan ko miliyan biyar aka sayeshi ya sayu, amman saboda ganin ita ke son sayarwar shiyasa, Zuwaira kam duk da taji dad'in cinikin nashi amman ta nuna rashin
amincewarta da hakan, tace da su su dai k'ara in har suna so ta sayar masu, dole haka suka rabu akan zasu je suyi shawara har d'ayan ya tafi wanda ta kira, sai ga wanda Abbati ya tafo dashi ya dawo yace ya k'ara mata dubu d'ari akai ta nuna masa idan dai b
a miliyan uku da dubu d'ari biyu ba bazata sayar ba, ganin ko a haka ya sayeshi zai ci riba sosai yasa ya amince da hakan, saboda yana jin tsoron abokin cinikinshi ya dawo ya saye gidan, amman ya rok'i alfarmar ta bashi nan da sati d'aya zai zo ya biya ku
d'in, Zuwaira ta dafe k'irji tace
"Ai WALLAHI idan bazaka biya nan da kwana Uku ba to da naga mai saye zan siyar ni ba ruwana,don ni in ta nice ma yanzu abani kud'in inje inyi abunda ke gabana, saboda ai kai kanka kasan haka kawai bazan d'aga gidan da
muke zaune ba ince zan siyar, tunda dai ba bakin Uwa ce dani ba, ka dubi girman gidannan kai kasan idan ba dole WALLAHI nida shi mutu ka raba, to amman dole ka dole ka bani kud'in kawai in kana son mu shirya ni da kai" Mutumin ya nuna mata shima idan
son samu ne ya biya yanzu a wuce wurin, to amma had'a kan kud'in yake so yayi shiyasa, yayi ta rok'onta da ta bashi kwana bakawi d'in kamar yanda ya nemi alfarma tun farko, Zuwaira tace da shi to kawai anman aranta taci alwashin da ta sami mai kud'i hann
u karb'a zata yi ta fita iskanshi.
Bayan fitarsu ne Abbati ya kalli Zuwaira yace, "Mama idan kika siyar da gidan to mu kuma ina zamu koma? Tunda ai ko ainahin gidanmu kin sayar dashi shima"
Zuwaira ta maka masa wata k'atuwar harara tace, "Ina
ruwanka da inda zamu zauna tunda babu ko kwandalarka a ciki, amman tunda har so kake ka sani to bari in sanar dakai gidan haya zamu Je mu kama mu zauna, sauran kud'in da zasu rage in fama sana'a mu sami abin rufawa KAI asiri, kagin ALLAH ya fitowa da Amrah
wani mijin aure"
Abbati yayi saurin kallonta yace, "WALLAHI ina jiye maki raba aurennan Mama, don ko har abada Aunty bazata sami wanda zai sota irin son da Yaya Nazir yayi mata ba, yanzu KO don albarkacin yaronnan da aka haifa bazaki bari ta zauna
ba? Duk fa wanda zai aureta yanzu da sunan bazawara zai aureta ba budurwa ba, sannan yanzu abun duba koda ya saketa ai dole ta jira har sai ta yaye yaron sannan tayi wani auren, don ba mai aurenta da d'an wani ya ajiye cikin gidanshi, to ko in hakane m
e zai hana ki barta cen har ta yaye yaronta sannan ta dawo, tunda dai mu nan idan ma ta dawo ajiyarta za muyi ba auren zata yi ba yanzu."
Zuwaira ta kalleshi shekeke saboda tama rasa abunda zata fad'a taji sanyi aranta, saboda Abbati ya kunnota
da kyau da kyau ta had'e fuska sosai sannan tace, "Abbati!!" ta kirashi da wata kakkausar murya tace,
"WALLAHI na koma jin sunan Matsiyacin yaronnan abakinka sai na ci ubanka munafukin ALLAH, waton dai atak'aice na ganoka bak'in ciki ne kake yiwa
'yar uwarka, saboda baka son taje inda zata huta taji dad'i muma muji, to ahir d'inka in kasan bakinka bazai fad'i alkhairi akanta ba to kada ka sake shiga wannan magana, idan kuma gigi ya jaka ka fad'i wata mummunar kalma akan haka to WALLAHI ban yafe ma
ka ba, idan ba don kana wawa ba ai ci gabanta namu ne duka, yanzu wannan gidan da muke zaune Ubanka ne ya bar muna shi cikin gado muka gada koko arzik'inta ne muke ci?da ana nuna maka hanya kana kaucewa, to ka kiyayeni bana son gutsuri tsoman munafuccinka.
"
Abbati ya shigewarsh d'aki abunshi ya k'yaleta tana ta zuba ruwan bala'i, har da su cewa ai ta gano ba mai sonta tunda yanzu gashi k'iri k'iri Asabe ta had'a kanta da Mijinta anci Amanarta, sannan su gasu dangin Baban nasu Amrah kowa ya zare jikinshi
akan maganar bakinta yana kunfa tace,
"Ai WALLAHI duk nasan zaman da nike yi da kowa, kuma duk bala'in mutum sai ya barni tunda na zo duniya da bisimillahta abaki na shigo."
To fa kunji sai ku rage zagin Zuwai don da shirinta tazo zaman du
niyar
πΉπΉπΉ
Manage plss
ππ»
ββ
οΈ
D/Auta ce
π€π»
*
ππ
BAKAN GIZO
ππ
*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 35*
Zuwaira kam ranar bata yi kwanan kirki ba saboda masifar da take ta yi
ita kad'ai, Abbati da kanenshi ma sai da suka gaji da sauraronta suka yi bacci, sai Alla Alla take akan safiya ta waye ta koma wurin dillalin da ta nemo in yana da kud'in shi ya bata ta sayar masa ta je ta karb'o 'yarta da d'an jikanta da tayi marmarinshi
da kewar jin muryarshi koda ta kukanshi ce ko.
**
Gefensu Amrah da Nazir kuwa Inna tace dashi yaje ya siyo masu kayan da zasu saka koda na kwana Uku ne, Nazir yaso ya tafi gidan Zuwaira ya d'auko masu kayan Inna ta hana tace yaje dai ya siyo masu
wasu saboda gudun tashin hankali, aiko yaje ya lafto masu kayan sakawa musamman Amrah da nata gaba d'aya ready mate ne sai wasu da ya bada a d'inka mata saboda shigar bikinshi da Sadiya idan har zamanta ya d'ore har lokacin, da wasu abubuwan da zasu bu
k'ata ita da d'anta cike da jin dad'i Inna tayi ta sanya masa albarka, Amrah kam iyakacinta ido ba baki saboda gaba d'aya daga shi har Innar sun dabaibayeta da karamcinsu, wanda har yasata rasa ta wane gefe zata ajiyesu, shin matsayin abokan adawarsu i
ta da Mamarta koko matsayin mutanen da suke da wani girma a idonta?.
Da dare ma Nazir ya dad'e d'akin Inna sunata fira yana gyarawa Umar kayanshi cikin wani k'aton riyo, Amrah dai kallone nata don ko godiya ma bakinta nauyi yayi mata tayi tagumi tana f
aman Nazari, har sai da ta fara jin bacci ne Inna tace dashi ya d'auki danshi suje sashensu su kwanta, Wani fad'uwar gaba ya dirarwa Amrah sai ga hawaye wasu na korar wasu ta kalli Inna tace, "Don ALLAH Inna ki barni nan in kwana dakinki har zuwa lo
kacin da zan bar gidan" Inna tayi 'yar dariya tace, "Ina kika tab'a ganin haka Amrahtu? Ace mace da Mijinta ta kwana wani d'akin? Kiyi hak'uri kinji kije kiyi kwanciyarki da safe sai ki zo nan d'in kiyi zamanki, in ma zaki kawo man Megidana ne ya tayan
i kwanan ki kawoshi sai kije kiyi kwanciyarki acen"
Amrah kam sai kuka takeyi yana rok'on Inna don ALLAH ta barta nan ita bazata je wurinshi ba, dole ba don taso ba tace da ita ta shiga d'akin to ta kwanta ita da yaronta.
Nazir dake rungume
da farouk d'in yana 'yar dariyar yak'e don yaso ace Inna ta tilastata sai ta bishi, amman ai duk da hakan ai ana tare kuma kwana k'alilan ne suka rage a kawo masa amaryarshi, don yasan abunda take wa gudu duk bai wuce kada ya sami damar rab'ar jikinta ba,