Showing 81001 words to 84000 words out of 129444 words
tsawa yace
"Hey you Madam come here where are you going???"
Cikin rud'ewa taji hantar cikinta ta kad'a wani zawo Yana Shirin sub'uce mata, cikin firgici ta Fara inda ind
a wani D'ansanda yazo ya tasata a gaba har k'ofar gidan sai Rabon ido take yi tana soshe soshen rashin gaskiya, cikin rawar baki ta kalli Malam Audu tace
"Malam Audu ya naganka da wad'annan maaikatan? Me nayi maka?" . Malam Audu ya kara tsuke f
uska tamau yace,. "Ai dole ne ki ganni dasu tunda har naji labarin wai kinsayar man da gida"
Zuwaira ta zaro ido waje tare da dafe k'irji tace,. "Waya fad'a maka wannan zancen, don Allah kayi hak'uri Wallahi akasi aka Samu Nima ba haka naso ba"
Malam Audu yace
"Ai Nima shiyasa banyi kasa a gwiwa ba na gayyato maki ma'aikatan da zasu titsiyeki ki bani kud'ina yanzunan, na fasa sayen gidan tunda Ashe daman cen cutata kika shirya yi ba wai sayar man da gidan kika tashi yi ba, don haka Wallahi kwa
ndalata bazata yi ciyon Kai ba, ki shiga ciki yanzu Ina jira ki bani kawai mu sallami juna"
Zuwaira tayi rau rau alamar kuka tace "don Allah Audu kayi hak'uri zuwa gobe kazo ka karb'i kudinka, Wallahi na fad'a maka matsala aka Samu bansan ya akayi b
a barayi suka sace kud'in".
Malam Audu da sauran Yan sandan suka zaro ido waje bakin Malam Audu Yana rawa yace,.
"Barayi suka sace kud'i har Miliyan biyu da d'ari takwas cabdi um lalle Zuwaira kin kware da d'ibar albarka ai billahillazi ko ki
bani kud'ina ko ki k'are sauran rayuwarki gidan yari matuk'ar Baki fito man da kud'ina ba, nafison aje dake cen ayita gana maki azaba har sai lokacin da kika fito da kud'in ,don Wallahi banci nanin ba nanin bazata cini ba cabd'i jam Lalle Zuwaira kin tarow
a kanki bala'in gabas da yamma wanda duk danginku sai sun sheda, ke nifa Wallahi bancin wani Abu ma da tuni na lakad'a maki shegen dukan da za'a kaiki Asibiti ba'a shirya ba"
Ya kalli wani D'ansanda yace
"Officer don Allah kuce da ita ta shiga gida t
a d'auko Mani kud'ina yanzunnan tun kafin hawan jinina ya taso tayi sanadina"
Ya Kare maganar cikin zubowar wasu hawayen takaici yace
"Allah ya Isa tsakanina dake Zuwaira Ina zaman zamana kika je har gida kika ce inzo in sayi gida Ashe Ashe yaudara
ta ce kika shirya kiyi ai narantse da Sarkin da ya busaman numfashi yau Akwai yak'i tsakanina dake matuk'ar Baki bani kud'ina ba"
Ya K'are maganar cikin muryarshi da ta karye Yana zubar da hawayen takaici, Zuciyarshi cike da tsantsar fargaba kada ace da
gaske babu kud'in, don shikadai yasan yanda yake jin zuciyarshi saboda hawan jini da yake fama dashi.
Zuwaira Kam tayi tsamo tsamo kamar ruwa sun cita ba Baki sai idanuwa da take rabo tana hadiyar yawun Dole, wani D'ansanda ya yi ball da ita har sai da
ta Kai kasa ba shiri Sannan ya katsa mata wata arniyar tsawa yace taje ta fito masa da kud'inshi, a zabure ta Mik'e jikinta Yana rawa ta fad'a cikin gidan dafe da zuciyarta tace
"Wayyo Ni Zuwairiyya tawa ta sameni yau Ina zan samo cikon kud'inshi in ba
shi?"
Wata zuciyar tace da ita,. _"Ki mayar da Amrah ki karb'o kudinki kawai"_
Tayi saurin girgiza Kai a ranta tace,.
_"Ina wannan ba mafita bace don tabbas na yi hakan zann bada kaina kuma in janyo su Rena mani wayo a banza bari dai in d'auko m
ashi miliyan d'aya din da tayi saura in nemi alfarmarshi akan yayi man lamuni zuwa kwana Uku in gani"_
Cikin gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata ta shiga d'akin taje ta d'auko kud'in zata fito suka yi kicib'is da Amrah zata shigo, ganin yanda ta ra
ba ta gefenta ta wuce yasa tayi kwafa ta fita zuciyarta sai halbawa take yi saboda tsoron abunda za'a yi kuma yanzu,.
Tana zuwa ta mik'awa Malam Audu kud'in cikin marairece fuska tace,. "Ga kudi'n Yaya Audu insha Allahu gobe zan cika maka sauran ko b
aka zo ba har gida zan je in Kai maka abunka kaji?"
Malam Audu ya bi kud'in da kallo fuska a had'e yace,. "Nawa ne?"
Bakinta Yana rawa jikinta Yana bari tace
"Miliyan d'aya ce Yayana Audu insha Allahu gobe......."
Ya katse mata hanzari wajen k'
wace kud'in Yana huci yace da yansandan
"Officer ku tafi da ita har zuwa goben idan ta bada cikon kud'in sai a sakota"
Zuwaira ta zaro ido ba shiri ta Kai k'asa tana rokon Malam Audu akan yayi mata hak'uri har goben zata bashi, Malam Audu ya tura ku
d'inshi aljihu yace da 'yansandan
"Officer kuyi aikinku"
Aiko wata 'Yarsanda mace ta cakumo k'ugun Zuwaira tana kuka tana tirjiya tana kiran "Yaya Audu ka taimakeni Marainiyar Allah ce ni kasani cutawa maraya haramun ne, ka dubi yanda Nike kuka K
una kasan Kukan maraya Abu ne babba ko ba komin Ina son kaji tausayin Marayun 'ya'yana kada ka tozarta masu Uwa, ka tuna fa kana da kanwa Ladidi idan aka yi mata haka kai ma ai bazaki ji dad'i ba"
Malam Audu Yana hurar hanci yace
"Ko itace zan bada g
oyon bayan a tafi da ita indai tayi irin abunda kika aikata man Wanda Allah ma ya haramta yin ciniki a kan ciniki, don haka ba wani sassauci har sai kin fito man da kud'ina WALLAHI"
Cikin fushi Zuwaira tace
"Allah ya tsine maka Audu tunda har baka S
an halacci ba meye ban yiwa matarka ba? Abinci sutura duk Ina Bata Amman wai yau nice zaka sa akaini mak'argama a kulle saboda kud'i, Shege bak'in Munafuki Mai fuskar shanu sai..... " Saukar marin da Yar sandar tayi mata yasata yin shiru dolenta, aka tura
ta motarsu ta shiga ba biya suka bar k'ofar gidan aguje, Aiko Mutane suka Fara tsegumin abun wasu suna ta Allah ya K'ara yayin da wasu suke ta ganin kamar Malam Audu bai kyauta ba, saboda mutuncin da ke tsakanin matarshi da Zuwaira.
Lantana kawar Zuwai
ra cikin sanyin jiki ta ja kafafuwanta ta shiga gidan, sai ga sautin kukan Amrah ya tarbeta cikin sauri ta nufi d'akin Amrah ta Fara Bata hak'uri tana cewa,. "Kiyi hak'uri Amrah in kinsan Akwai inda zaki je ki samo kud'in to kije ki samo ki kawo aje a
karb'o Mahaifiyarki"
Amrah tayi banza da Lantana sai kukanta take yi dama taga Lantana ta dameta tashi tayi ta turata waje ta rufo d'akinta taci gaba da gunjin kukanta, Aiko ciki fushi Lantana tace
"Ah lalle yanzu ke kina nufin bazaki tashi kije ki f
adowa 'yan uwanku ba asami kud'in akai su fito da ita ba ko? Ah Lalle Zuwaira sai hak'uri zama gidan Maza ya kamaki Kinga tafiyata idan kin gama kukan sai kisan yanda zakiyi da ita ke ta haifa ba Ni ba"
Ta fice abunta tana fad'a saboda taji haushin abun
da karamar yarinya irin Amrah tayi mata.
****
Nazir Kam jiki ba kuzari ya shiga gidan Kai tsaye d'akin Amrah ya shige, a cen yayi sallahr Magriba har aka yi Isha duk yana ciki bai fito ba, Sadiya tun tana sauraren shigowarshi har ta gaji da jira
ta yi sashen Inna domin taga me ya tsayar dashi, sai dai ganin Bata hango talkamanshi a k'ofar d'akin ba yasa zuciyarta ta Bata cewa Yana d'akin Amrah don ta hangoshi k'ofar a bud'e,. Kasancewar Inna ta ganta yasa ta shiga d'akin da fara'arta tace,
"Bar
ka da dare Inna"
Inna tana Murmushi tace ,. "Yawwa Sadiya Barka Ina shi Nazirun??". Sadiya tana fara'a tace
"Yana ciki Inna"
Inna tana yar dariya tace da ita,. "To kice yazo in na nemansa "
Sadiya tace "to Inna bari in kirashi" Sannan ta
fice jiki ba kuzari tana nazarin maganar da Inna ta fad'a mata d'azu ko ba gaskiya bane, tunda dai in har da gaske Nazir ya rabu da Amrah to me zai sashi ya je d'akinta yanzu?? Cikin damuwa da jin wani sabon kishin Amrah ta shiga falon da sallamarta Amman
taji shiru, cikin jin haushi ta nufi kuryar d'akin da nufinta na ganin koma me suke aikatawa tunda har suka yi banza da ita, ganin Nazir kwance shikadai idanuwanshi a sama yana kallon sealing hawaye suna kwaranya a gefen fuskarshi suna biyar kunnuwanshi
tamkar wani burgaggen famfo, Amman baisan ma suna zubowa ba saboda ya fad'a cikin zuzxurfan tunanin rayuwar jin dad'in da yayi da Amrarshi.
Cikin sanyin jiki ta k'araso ta zauna saman gadon ta rik'o hannunshi ta yi masa kiss Sannan ta kwanta saman k'ir
jinshin tana shafo fuskarshi a hankali, Nazir Kam cikin shauk'in son y Amrah da mayen sonta yake shiyasa yq K'ara rungumota jikinshi ya manneta tsantsan Yana sambatun fad'in
"I love u Amrahtah kece farin cikina kece fitilar dake haskaka Mani zuciya, ida
n Baki a tare Dani bansan Ina zan jefa rayuwata ba, ke Mai kyau ce don ko a cikin jerin kyawawa ke tadaban ce a wajena, zuciyar Nazir gaba d'aya kece a cikinta sonki ya tunbatsa ya cike kowane lungu da sak'on da ke zuciyata, Nazir naki ne ke tawa ce kiyi
yanda kike so dashi Nima haka I love u so much my milk wadda zakinta yafi na kowace 'ya mace a duniya"
Cikin zafin nama Sadiya ta tureshi daga yamutsatan da yake yi a haukace idonshi a rufe saboda wani bala'a'en kukan da ya zo mata na zallar tsagwaron
kishin Amrah, jikinta Yana rawa ta Mik'e tsaye tare da nunashi cikin Kuka tace
"Meyasa kasan kana yiwa Matarka irin wannan son ka aureni??? Meyasa ka zab'i da in zo gidanka inyi zaman boranci a gidan Mijina Wanda nafi so fiye da komi a rayuwata??"
Ta durk'ushe tana wani kuka gwanin ban tausayi Mai had'e da zallar tausayin kanta da kanta, don yanzu ta gano Ashe ita d'in ba kowa bace a wurin Nazir face Bora tunda har ya iya wad'annan kalaman Amman ita bai tab'a yi mata ko Rabin rabinsu ba.
Nazir K
am Wata kasala ta sauko masa ba shiri tare da razani akan jin sautin Muryar Sadiya cikin kunnenshi, saboda kalamanta da kukanta sun sa ya jishi wani iri duk ba dad'i ya runtse idonshi ya K'ara budewa yayi jarumtar mik'ewa zaune ya d'agota ya had'ata da ji
kinshi ya Fara lallashinta, cikin Kuka ta k'wace daga jikinshi tace
"Kar ka koma tabani kaje wajen Mowar Matarka wadda Babu kamarta a wajenka"
Sannan tana K'are maganar ta zo zata fita tace
"Inna tana nemanka idan ka gama mayen k'aunar"
Ta fi
ce tana kuka ta fad'a d'akinta sai gunjin kukanta take yi tayi datasanin zuwa d'akin Amrah don a ganinta da Bata je ba da Bata jiyowa kanta abunda zai hanata sukuni ba.
Cikin sanyin jiki ya Mik'e Yana tangadi saboda rashin k'arfin jiki ya nufi wurin Inn
a, tozalin da yayi na ganin Umar yasa yaji wani sanyi ya ratsa zuciyarshi, cikin rashin kuzari ya duk'a ya d'aukeshi Sannan ya zauna Yana yi masa wasa, Inna ta bishi da kallon tausayi tace
"Ka je inda nace kaje?"
Ya gyara zamanshi cikin natsuwa yace
"Na je Inna har ma anyi nasara wajen mutum biyun da naje wajensu". Daga Nan ya kwashe duk yadda yayi dasu ya sanar da ita a dunkule, cikin jin dad'i tace
"Alhmdllh mun godewa Allah gobe idan Allah ya kaimu sai kaje wajen sauran don ka Samu ka sau
ke nauye nauyen da ke kanka ko da zaka Sami natsuwar Zuciya"
Ya sauke ajiyar zuciya Yana kallon Umar a ranshi yace,
_"Ta yaya zan Sami natsuwar zuciyar alhali Amrah Bata tare da ni??? "_
A fili kuma yace
"Insha Allah Inna gobe zan je in samesu
nagode da kika hankaltar Dani tun da wuri"
Inna tace
"Allah ya kaimu Amman ka sani kar ka manta maganar da nayi da Kai a kwanakin baya, akan cewar da nayi ban yafe maka ba matuk'ar ka sake kauce Hanya akan Amrah da rayuwarta da kowa ma Kai ko da ko
bayan k'asa ta shafe idona ne, a kullum Ina son ka tuna da wannan maganar tawa don kayi takatsantsan da koma aikata irin abunda kayi a baya"
Cikin gamsuwa da maganarta yace
"Insha Allahu hakan bazata sake faruwa ba Inna nayi maki wannan alk'awali"
Cikin jin dad'i Inna tace,. "Allah yayi maka albarka kuma ya sawa aurenka da yaronka albarka ya bamu ikon kula dashi dai dai yanda ya kamata, kayi hak'uri da duk halin da zaka tsinci kanka a ciki ka barwa Allah komi da sannu haske zai shigo rayuwarka ya
haskaka maka zuciyarka har ma ya yaye duhun da kake ganin kanka a ciki yanzu"
Cikin jin dad'i yace
"Nagode Inna Allah ya barmuna ke muci gaba da dafaki muna jin dad'i"
Tayi Yar dariya tace
"Aiko bazai barni ba komin Daren dadewa zan tafi inda
kowa zai je, fatanmu kawai Allah yasa mu cika da kyau da imani"
Yace "Ameen" daga Nan suka ci gaba firarsu har goman dare ya buga, tace dashi "Kawo yaron tashi kaje wajen matarka"
Nazir ya marairece fuska yace,. "Inna ki Bari inje dashi da
safe in kawoshi"
Inna ta B'ata fuska tace,. "To Ni badani za'a yi wannan shirmen ba kawoshi kaje sai da safe Allah ya tashemu lafiya"
Nazir ya Mik'ashi yayi mata sallama ya fita Inna tabi bayanshi da kallo tace,. "Ubangiji Allah ya kawo haske cikin
rayuwarka Naziru"
Ameen Inna
😢
Dangin Xuwai a harhado kudi kuzo muje a karbota tun kafin zarnin fitsari ya kasheta
🙇🏻
♀
️
🙊
Akafta
🤣
Princess Dija D/Auta ce
✍
🏻
*
🌈🌈
BAKAN GIZO
🌈🌈
*
*NA HADIZA D/AUT
A*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 47*
Tun kafin ya Isa d'akin ya Fara jiyo sautin kukanta cikin wata sabuwar damuwa ya shiga d'akin da sallamarshi, Sadiya Kam duk da tajishi sarai amman tayi banza dashi ta ci gaba da
rera kukanta wiwi, ya k'araso wajenta ya janyota jikinshi ya Fara lallashinta da fatar Baki har ma da k'ok'arin nuna mata itama tana da matsayinta a zuciyarshi, kafin kace me sai ga Sadiya ta Ware saboda Nazir yasan ta kan yanda ake sarrafa mace har ma ta
manta da inda kanta yake,. Cikin natsuwa ya fara sarrafata a hankali duk da zuciyarshi Bata da natsuwa amman a hakan yayi jarumtar nuna Mata nata kalar matsayin, Bayan komi ya lafa ne wani mayen bacci ya Fara fisgarta ya Kira sunanta yace
"Kiyi hak'uri
da Ni kinji insha Allah zanyi k'ok'arin kwatanta maki adalci"
Cikin mayen bacci Sadiya tace,. "Ba komi hubbyna ai komi ya wuce Amman don Allah Ni ma ka soni Koda Rabin son da kake yiwa Amrah ne"
Ya yi saurin runtse idonshi yayi shiru Yana nazarin r
ayuwar jin dad'in da suka shinfida shi da Amrarshi, fuskarta sai GIZO take yi masa a ido tana d'an murmushinta Mai K'ara mata kyau ya sakashi natsuwa, Sadiya Kam shirun da taji yayi ne yasa itama tayi gum har bacci Mai dad'i yayi awon gaba da ita, Nazir K
am ganin tunanin Amrah bazai barshi yayi kwanan ba yasa ya Mik'e yaje ya d'auro arwallah ya fara jera Nafilfili, Sannan ya duk'ufa rok'on Allah akan ya yafe Masa laifukanshi da ya aikata, Sannan yayi add'ua sosai akan idan har aurenshi da Amrah alkhairi ne
to Ubangiji ya dawo masa da ita cikin gaggawa, idan kuma ba alkhairi a zaman nasu to Allah ya bashi dangana akan soyayyarta, ya raba dare Yana Abu d'aya Sannan ya d'an gincira sabida wani bacci Mai dad'i da ya ziyartoshi ba shiri, Aikuwa Nan take baccin
yayi awon gaba dashi bai tantance ba.
****
Amrah Kam tana cikin kukan ne taji muryar Abbati Yana k'wank'wasa Mata k'ofa, cikin sauri taje ta bud'e d'akin ganin Abbatin yasa taji wani sabon kuka ya zo mata,. Ta dawo Kan gadon ta zauna tana rera ku
kanta gwanin ban tausayi saboda izuwa lokacin har fuskarta tayi jawur idanuwanta sun kunbure suntum saboda kukan da tasha, cikin sanyin Jiki Abbati ya shigo d'akin ya zauna damuwa fal ranshi yace,
"D'azu Aunty ta kirani tana sanar da ni abunda ya faru a
kotu Ina Shirin zuwa gidanta ne, sai gashi Usama ya Kirani yana sanar da ni abunda yake faruwa wai Malam Audu ya d'aukowa Mama 'Yansanda sun tafi da ita, don Allah kiyi hak'uri kinji tunda har hakan ta faru to ki fawwalawa Allah komi da sannu zai yi maki
mafita, ki bari Ni zanje yanzu in karb'o maki yaronki kici gaba da shayar dashi har a yayeshi Sannan a mayar masu dashi, idan ma Allah ya daidaitaku shikenan sai ki koma kici gaba da kula da yaronki cikin natsuwa Bari yanzu inje in basu hak'uri su bamu ya
ron"
Har ya Mik'e Amrah ta kirashi cikin dusashiyar muryarta tace,. "Share da zancen Abbati na riga da na dangana dashi tunda har Mama Bata ji kunyar rabani da yarona ba, Amman WALLAHI Niko ta daina ganin fara'ata a gidannan"
Abbati ya dawo ya zauna
cikin sanyin jiki yace,. "Yanzu to ya kike ganin za'ayi da zancen karbota hannun yansandan? Don fa kud'in suna cikin d'akinta kawai dai don bata San inda suke bane". Amrah cikin Kuka tace
"Kaje ka d'auko kud'in ka Kai masu abunsu tunda har kasan ind
a suke"
Abbati yayi shiru Yana nazari Sannan yace
"Ni ko a ganina ba karb'o Mama ya Dace muyi da kud'in ba"
Amrah ta tsaida kukanta