Showing 9001 words to 12000 words out of 24778 words

Chapter 4 - AUTAR HAJIYA COMPLETE

15 Sep 2026

43

nasiha me ratsa jiki, da kuma yimata nuni da tayi ha'kuri, dan duk Wanda yayi ha'kuri duniya baze ta6a ta6ewa ba.

Bayan an fito da ita daga d'akin mahaifinta aka wuce

da ita d'akin Hajiya, itama Hajiya tayi mata nasiha me ratsa jiki, 'karfe hud'u da rabi aka fito da Auta aka sakata mota, ba abinda take sai kuka, da kyar aka rabata da hajiya,

A unguwar lay out dake cikin garin katsina, misalin 'karfe biyar suka isa

gidan, can suka iske 'yan'uwan khaleed dana Fadila dan ita tin 'karfe hud'u aka kawota.

Bayan sallar magrib ne aka fara gabatar da walimar da 'yan'uwan khaleed suka shirya, wanda aka gayyato shahararriyar malama wacce zata gabatar da wa'azi kan zaman au

re da kuma nasiha ga Amare, wato malama *AMINA ALIYU MOHM'D (BINTUSH~SHEIKH)*

Bayan malama ta bud'e taro da Addu'a, tayi wa'azi akan ha'kuri sanna tafara nasiha ga Amare kamar haka: "Alhamdulillahi Allah Kaine abin godiya, daka azurtamu da rai da lafiya

, bayan wa'azi da nayi akan ha'kuri yanzu kuma inaso inyima Amare nasiha akan zaman Aure, Wanda shima dai ha'kurin akeyi, yaku wad'annan Amare ina ro'konku da kada kuyi kishi irinna jahilai, kada kuyi kishi irinna wad'anda basu san ciwon kansuba.

Kuyi k

ishi irinna matan Annabi Muhammad _(S.A.W.)_ Kada kuyi kishin da ze tada hankalin mijinku, kuyi kishi Wanda kullum burinku Ku kyautatama mijinku, kunsan shi rai yana son me kyauatata mashi, sannan daga 'karshe na horeku da tsafta, Ku zamto masu tsafta kada

ku yarda mijinki yaga wata 'kazanta ajikinki ko ya sha'ki wani abu a jikinki sa6anin daddad'an kamshi.

Haka dai malama tayi nasiha me ratsa jiki, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a Kowa ya tafi gida, bayan an raba sadakar Qur'an Kowa izif sittin,



Ana Allah shima malama Albarka, Akan wannan wa'azi datayi.

Da misalin 'karfe takwas na dare, gida yarage daga Auta sai 'kawayenta guda biyu sadiyya da Zahra'u sune suka tsaya suka gyagayara mata kome suka share ko'ina suka kunna turaren wuta, ko'in

a na sashen ya bige da 'kamshi sannan sukayi bankwana suka tafi.

Itama Fadila 'kawayenta ne suka tsaya sukayimata 'yan gyare-gyaren daya dace, sai misalin karfe tara da rabi suka bar gidan,

*TO FAH MASU KARATU GIDA YA RAGE DAGA AUTAR JAJIYA SAI FADIL

A•

🤔

SAI ALLAH YA KAIMU GOBE MUJI WACE IRIN WAINA ZASU TOYA*

😂

Mmn khady

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZE

E MMN KHADY_

😘

_*Page*_ 81-85

✍

🏽

Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar gidan akwai 'kofa waccce

zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a 6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida khaleed da

yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake.

Fadaila ce ta kalli agogon dake manne jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar amma bat

aji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta d'auko wani tsadadden less ta sa, bata tsaya d'aura d'ankwaliba, bayan ta tsara make-up yafa d'ankwalin kawai tayi a kai, sannan ta fito general falo ta zauna jiran shigowar

angonta.

Auta kuwa itama tana d'akinta ta gaji da jiran shigowar ango, saboda haka, itama wanka tashiga, bayan ta she'ka wanka, ta fito, ta tsaya gaban dressing mirror tana tinanin me ma zatayi, yanzu dai kam batada lokacin

yin make-up da wannan daren,

lotion kawai tashafa me d'adin kamshi, sannan ta feshe jikinta da turarruka masu kyau, tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta, ta Sanya, tsayawa tayi tana kallon kanta, yanda rigar tayi mata, sharara tamkar batasa kome ba, dan duk illahirin surar jikinta

bayyane take, tayi niyyar canja riga saboda tana kunyar khaleed yashigo ya ganta haka, amma kuma tana jin zafi-zafin da ake a garin, saboda haka tace bari ta d'an sha iska, idan taji shigowarsa sai ta caja, gado ta haye,ta kwanta lamo, zuciyarta cike da t

inani kala-kala, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.

Karfe sha d'aya da rabi khaleed yayi horn Bakin get d'in gidan me gadi ya bud'e mashi yashiga,.

Fadila na zaune Falo saboda haka, da sauri tanufi d'akinta ta 'kara shafa humra, me dad'in 'kamshi

sannan ta dawo falon ta zauna.

Da sallama ya shigo falon, cikin kashe murya Fadila ta amsa salamar, tare da mi'kewa ta rugomeshi tayi Mashi sannu da Zuwa sannan ta kar6i ledar daya shigo da ita ta ajiye gefe.

d'akinsa ya nufa tabishi, acan ta ha

d'a mashi ruwan wanka, sannan ta taimaka Mashi ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka, bayan ya fito daga wanka, wasu 'kananan kaya ya sanya masu sakai-sakai, sannan ya umarci Fadila da ta tashi suje falo.

Bayan sundawo falo sun zauna, khaleed ya umarci F

adila data d'auko ledar daya shigo da ita, ta tashi tana wani yanga tana karairaya, ta d'auko ta ajiye, sannan ya umarceta ta d'auko plate da cup's, kitchen tanufa ta d'auko duk wani Abu datasan zasu bu'kata.

Tana fitowa daga kitchen d'in taga ba khalee

d, bata kawo kome a ranta ba, tana tinanin yana d'a'kinsa, saboda haka zama tayi tana jiran fitowarsa, amma har kusan minti talatin be fitoba, saboda haka d'akinsa tanufa, da sallam ta Shiga d'akin amma saitaga ba Kowa ciki, sai tayi tinanain koyana toilet

ne,

Bakin 'kofar toilet d'in ta kanga kunnenta bataji alamar mutum aciki ba, Ahankli ta tura 'kofar toilet d'in nan ta'kara tabbatar da baya ciki.

Take zuciyarta ta ayyana mata inda khaleed yake, a fili ta furta *~Wallahi bazan yarda ba~*

Zee Elkaseem

Mmn Khady

[04/08 11:19 am] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

*_page_* 86-90

✍

🏽

khaleed kuwa a lokacin daya umarci Fadila data d'au

ko plate kitchen, tana shiga kitchen d'in da sauri yanufi d'akin Auta , dan tunda yashigo hankalinsa na gun d'akinta ko zata fito amma shiru bata fitoba.

Ahankali ya tura 'kofar d'akin kwance ya hangota kan katafaren gadonta wanda yasha shimfid'a da wan

i 'katon bedsheet, da manyan filo da 'kanana.

Baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ahankali ya isa Bakin gadon ya tsaya yana k'are mata kallo, kaf surar jikinta bayyane take, ga fitila d'akin kunne haske fayau ko'ina, lokaci guda yaji jikin

sa yafara kyarma, besan lokacin daya hau kan gadon ba ya rungumota jikinsa baki d'aya yafara shafata, yakai hannunsa kan kirjinta yafara wasa da dukiyara fulaninta.

Cikin bacci tajita jikin mutum, gashi kuma anata romancing d'inta, cikin firgici ta bud'

e idonta khaleed tagani ya 'kura mata ido baya ko 'kiftawa, ta bud'e baki tana shirin yin magana, ya had'e bakinsa danashi yacigaba da kissing d'inta, lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi, itako auta 'kara narkewa tayi jikinsa, tana mashi sh

agwa6a shikuma sai kara matseta yake jikinsa kamar wani ze kwace mashi ita,

Ji yayi anturo 'kofar da 'karfi, a firgice yakai dubansa ga 'kofar, Fadila yagani tsaye tana cika tana batsewa, shi kwata-kwata yama manta da ita, wani irin haushinta yaji dan t

a yankemashi jin dad'insa, cikin d'aga murya yace, "Fadila meya shigo dake nan? Bata bashi amsa ba kuma bata motsa daga inda takeba, cike da jin haushin abinda tayimashi yace "get out, ki fita nace maki ganinan zuwa.

Ita kuwa Auta ganin Fadila yasa ta'k

ara narkewa jikin khaleed, ta dauki hannuwanta duka biyu ta sa'kalosu a wuyanshi, tana mashi wani shu'umin kallo wanda ya'kara rikitar dashi, tace "haba my dear, meyasa ka shigo baka sallameta ba, kamata yayi ka sallameta kuyi sallama kafin ka shigo, kaga

yanzu tazo muna cikin jin dad'in rayuwarmu ta mana cikas.

Da gudu Fadila ta juya tabar d'akin dan jin hawaye na niyyar zubo mata saboda tsabar takaici, falo ta zauna tana share hawayen ba'kin ciki, a zuciyarta tana cewa

*_Lallai yarinyar nan ni zata

gwadama duniyanci, to wallahi sai nayi maganinta cikin gidannan saina nuna mata nafita iya duniyanci_*

Nan suka isketa zaune suma suka zauna, Auta yanda take haka tafito, bako d'an kwali kanta, gashin kanta ya zubo kan kafad'unta, saboda haka hankalin k

haleed yana kanta duk wani motsi nata sai ya had'iyi yawu,

Da kanshi ya d'auko ledar ya d'auko plate ya juye dankwala-dankwalan kajine guda hudu, sai fresh milk daya ajiye masu gefe, da ruwan roba na swan.

Nan ya Uamrcesu dasu zo su ci, Auta dama

ta kwanta da 'yar guntuwar yunwarta saboda haka matsowa tayi taci me isarta, sannan ta kora da fresh milk tasha ruwa, shima khaleed yaci sosai, sannan yasha ruwa, Fadila kuwa kasa cin kome tayi saboda zuciyarta cunkushe take da ba'kin ciki.

Bayan sun ka

mmala ne khaleed yayi masu basiha akn zaman tare, sannan daga 'karshe, ya sanar dasu abubuwan dayake so da wanda bayso, dan su kiyaye.

Sannan ya kallesu yace idan akwai me magana zata iyayi, Fadila tace "babu,

Auta tace ni maganata kawai itace duk

abinda kakeso shi nakeso wanda bakaso kuma shine baniso kaga ra'ayimu yazo d'aya kenan.

Nan suka cigaba da fira sam-sama, yawancin firar ma tsakanin Auta ne da khaleed, Fadila duk takaici yahanata magana.

Saida suka kai 'karfe sha biyu da rabi suna f

alo, lokacin khaleed yafara jin bacci dan dama akwai gajiya tattatare dashi, saboda haka yace to yakamata mu kwanta hakanan dan dare yayi saosai, Fadila tace "Eh gaskiya nima baccin nakeji, kazo mutafi dan nima gajiyarce a jikina, Fadila ta tashi tanufi d'

aki tana lumshe ido alamar bacci, ganin Auta bata tankaba yasa khaleed ya tashi yabi bayan Fadila, Auta tayi saurin shan gabanshi tace "Ai d'akina zamuje ko, Fadila najin haka ta juyo tace "kamar ya d'akinki, amma kinsan ay na girmeki, kuma niyakamata ace

anba girmana, Auta tayi murmushi tace "ay nan gidan aure ne ba maganar girma, saboda haka kazo muje kawai,

nan rigima ta kaure tsakaninsu, wannan tace d'akinta za'a fara kwana wannan tace nata za'a fara kwana, khaleed yarasa yanda zeyi dasu kawai sai ya

koma falon ya zauna kan kujera three seater ya zauna, suma suka biyoshi suka zauna, kowace da abinda take sa'kawa a zuciyarta.

Shikuwa khaleed daya gaji da zama kwantawa yayi kan kujerar, tin yana kallonsu yana mamakin halinsu, har bacci yayi awon gaba

dashi.

Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tasheshi daga baccin dayake, zaune yagansu, suduka sunyi shiru, da Alama ba wacce ta runtsa cikinsu, tashi yayi yanufi d'akinsa yashiga toilet yayi wanka sannan yayo Alwala ya kabbara sallah.

Sai lokacin suku

ma kowace tanufi dakinta dan gabatar da tata sallar.

Zee Elkaseem

Mmn khady.

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MM

N KHADY_

😘

*_Page_* 91-95

✍

🏽

Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a gidan khaleed, yau kimanin kwana ukku kenan kullum kwanan zaune sukeyi a falo, dan Auta ta kafe ita a dole sai anfara kwana d'akinta, ita kuma Fadila tace Sam bata yardaba,

hakan ke sawa khaleed yayi kwanciyarshi kamar yanda ya saba, wato falo kan kujera three siter sukuma haka zasu zauna su tasashi gaba sunata hararar junansu.

Yauma kamar kullum, zaune suke babban falon gidan, da musalin 'karfe biyu da rabi na dare, shiku

ma khaleed yana kwance yanata sharar baccinsa hankalinsa kwance, yau ma atakaice haka sukayi kwanan zaune, asubah nayi ya wuce d'akinsa dan gabatar da sallah suma kowace tanufi d'akinta.

Khaleed abin na damunsa yarasa yanda ze 6ulloma Al'amarin, saboda

haka bayan yayi break fast ya shirya cikin 'kananan kaya, wandon jeans ba'ki da jar T-shirt yayi matu'kar yin kyau.

'Dakin Auta yashiga, zaune ya isketa tsakiyar falonta, kan carpet hannunta ri'ke da waya tana game, da sallama ya shiga d'akin bayan ta a

msa ya'karso inda take ya zauna kusa da ita, ta d'ago da manyan idanunta ta kalleshi tace "barka da kwana, yace "ku zanyima barka kuda ke kwanan zaune,

Kafin tayi magana yaci gaba da cewa, yanzu Zainab rayuwar da kuka za6ar mana agidannan kuna ganin

ya dace, ace ku duka ba wacce zatayima 'yar'uwarta hakuri,

Amma Auta kinga kece 'karama yakamata kiyi hakuri nafara kwana d'akin fad'ila duka fa kwana biyu ne zan dawo d'akinki, haba Auta bakison kwanciyar hankalina ne?

Wani irin kuka ta fashe

dashi, cike da mamaki khaleed ke kallonta, cikin maganar dayayima Auta miye abin kuka.



Kuka tacigaba dayi tana cewa "shikenan khaleed ka nunamin kafi son Fadila akaina, kaje ka kwana d'akinta d'in wallahi nikuma idan har ka kwana d'akinta ranar zan

bar gidannan, kuma idan natafi kada kayi tinanin gidanmu zanje, a'a zan tafi inda ba'a sanniba inda bansan kowaba, incigaba da rayuwata acan.

"Idan abin gaskiyane it's kace ta hakura ta barmin mana.

Haka khaleed yayi rarrashin duniyar nan amma Auta

ta kafe akan sai dai ya fara kwana d'akinta, haka khaleed yabar d'akin Auta yana mamakin rigima irin tata.

A d'akin Fadila ma haka yasha daga da ita yana rarrashinta akan ta ha'kura ya fara kwana d'akin Auta, amma tace sam ita bata San wannan ba, aiko

abin ya 6ata ransa nan ya balbaleta da fad'a ta inda yake shiga ba nan yake fitaba, yace "shikenan kuyi duk abinda kuka iya, yanzu ke Fadila bazakiyi hankali ki ri'ke girmankiba ki kawo 'karshen wannan kwanan zaunen da kukeyi,

Cikin masifa itama take m

agana "Wallahi bazan yardaba, yanda ita bakace ta hakura ta barmin ba nima wallahi bazan barmataba, ai ba fina sonka tayiba.

Cikin fushi khaleed yafita, a harabar gidan yanufi gurin ajiye motoci ya hau motarsa ya kunna, me gadi ya bud'e mashi get yadau

hanya,

Gidan abokinshi ya wuce Ahmad, a ranar can ya wuni be baro gidan ba sai bayan magrib, daga nan kuma gidansu ya wuce be dawo gidaba sai 'karfe tara da rabi na dare.

Zee Elkaseem

Mmn khady

[04/08 8:04 pm] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

🕊

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

_*Page*_ 96-100

✍

🏽

Da sallama ya shigo falon, Abin mamaki yau bega kowa a falon ba kamar yanda yasaba kullum nan yake iske matan gidan zaun

e suna jiran dawowarsa,

A hankali take tafiya dan bayaso suji karar dawowarsa, su fito su sashi kwanan falon nan,

d'akinsa yanufa toilet ya shiga ya she'ka wanka sannan ya saka jallabiya marar nauyi, a hankali ya fito daga d'akin yanufi d'akin Fadi

la, kwance ya isketa kan katafaren gadonta tayi dai-dai tana sharar bacci.

Dalilin baccinta kuwa shine, bayan fad'an da khaleed yayimata yana fita ta fashe da kuka, a zuciyarta tana cewa

_(Shikenan ni dama nasan khaleed ba sona yakeba, hakanan su Mo

my suka ma'kale akan sai ya aureni, kuma nima ina masifar sonshi, sai yanzu na tabbatar da son maso wani nakeyi, dan kuwa kome Auta zatayi khaleed baya ganin laifinta, dama hausawa sunce so hana ganin laifi)_

Haka tasha kukanta ta gaji,

Nan take

kuwa kanta yafara ciwo, dama ga rashin bacci na kwana ukku, bayan magrib taji ciwon kan yayi tsanani tasamu magani tasha, da misalin karfe takwas na dare tad'an kwanta aikuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Nan khaleed ya 'kare mata kallo, yayi murmushi, s

annan ya fito daga dakin, cikin hankali yakeyin kome dan kada 'yar rigimar tajiyoshi, aiko yana fitowa daga d'akin Fadila ita kuma tana fitowa daga d'akinta.

Da sauri ya 'karaso inda take ya had'a jikinsa da nata yayi mata ky'k'kyawar runguma, ita kuwa

ganin ya fito daga d'akin Fadila yasata jin wani irin ba'kin ciki, ta bud'e baki zatayi magana yayi saurin had'e bakinshi da nata, hot kiss yake mata, yana romancing d'inta lokaci guda ta mance duniyar datake ciki.

'Daukarta yayi kamar wata jaririya, be

zame ko'ina da'itaba sai bedroom d'inta ya kwantar da ita kan gado yacigaba, da aika mata da sa'konni, a ranar dai saida khaleed yasan Auta a matsayin mace, aiko Auta tasha wahala ba kad'anba, shikuwa khaleed banda rarrashinta ba abinda yake,yanata shimata

albarka, sai gurin 'karfe d'aya da rabi bacci yayi awon gaba dasu Auta tana jikin khaleed duk ta wani shagwa6e mashi.

Kiraye-kirayen sallar asubah ne ya tashesu daga baccin da suke, khaleed ne yafara tashi yashiga toilet d'in dakinta yayi wanka, san

nan itama ya ha'da mata ruwa me dumi da Kansa yazo ya d'auketa yakaita toilet yayi mata wankan tsarki tare da gasa mata jikinta, sannan yasa sabulu ya wanketa ya d'aura mata towel ya d'aukota, kan gado ya direta sannan ya d'auko mata doguwar riga ta atamfa

, simple ta sanya sannan suka gabatar da sallar asuba, bayan sun gama suka koma kan gado suka kwanta.

Wani sabon bacci yayi awon gaba dasu me cike da nisha'di da tsantsar 'kaunar juna.

Zee Elkaseem

Mmn khady.

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login