Showing 15001 words to 18000 words out of 24778 words

Chapter 6 - AUTAR HAJIYA COMPLETE

15 Sep 2026

48

murna, Auta kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce d'akinsa,

Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace

kullum mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe ma haka za'ayishi,

babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne.

Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wu

ce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya, koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani juya mazaunai.



Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo, dining suka sauna dan cin abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shig

ewarsu d'akinta tanufa tafad'a kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta dauko man le6e ta shafa,

wad

rope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen duwatsu daga gabanta ta Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba.

Kan dining ta iske Fadila da

khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da fadilar suka fahimci halin datake ciki ba.

Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa

nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare dayin hanyar

toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta, khaleed kuwa binta ya

yi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure da

n bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya,

Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa

```lallaima yarinyar nan niz

akima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da kifin akwai dai inda kika dosa```.

Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake tayi filo da cinyar khaleed,

Shikuwa sai wani rarrashinta y

ake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba.

Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, c

ikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici.

Zee Elkaseem

Mmn khady

[11/08 11:44 am] .: [11/

08 10:19 am] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

```Page``` 126-130

*_BAYAN KWANA BIYU_*

✍

🏽

Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin

tsayawa tsayin daka tayima mijinta abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta

duk wani 6acin rai na baya, kuma ya dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata.

Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau

ta fere ta d'ora kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta

d'auko abarba domin yau *(pineapple juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu datayi lemun da ita.

'Dakinta tanuf

a ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba me gadi ya siyo mata Abarba,

Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba mus

u ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit.

Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata da kitchen d'inta kai tsaye,

tazo dai-dai window kitchen dinta kama

r ance tayi duba gurin,

Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta.

Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka z

allah tayi amfani da ita gurin yin miyar.

Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah,

Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali ta juye, saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa

cokali ta motse,

Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in.

Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi

ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in,

'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan

ta d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai 'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta k

ulle kitchen d'in ta tafi da makullin d'akinta.

Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar hannunsa tayi gaba zuwa

d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito zuwa falo

Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya mamaye falon,

Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta t

saya ta kalli khaleed tace "my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara yaci ba dad'i.

Auta tayi murmushi ta

ce "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma ma

tsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah.

Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in dazeji,

Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwan

yarsa.

Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata

da kuma addu'ar da mijinta yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya tsakaninmu, yace "Ameen my wife.

Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya, batasan lo

kacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su 'koshi,

Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in ya

u bare na gobe

Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa,

Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta.

```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata nuna 6acin ranta ba```

*_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta da Fadila_*

Zee Elkaseem

Mmn khady

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

```Page``` 131-135

✍

🏽

"Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna dani,

Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima m

utum yawa sai ahankali, Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali, Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu,

"Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambaya

ta ma kike, duka yaushe mukayi waya dake na gaya maki.

Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina uwar gidanki? Tunda nazo ban gantaba, "Auta ta harereta tare da kaimata duka cikin wasa tace "Uwar gida fa kikace, kodai amar

ya' ay nice uwar gidan kamar yanda nad'au Alwashi, nan auta tabata labarin yanda sukayi ranar da aka kawosu da kuma kwanakin da suka kwashe suna kwanan zaune.

Sadiya tayi dariya sosai sannan ta kalli Auta tace "kai Auta bakida dama gsky rigimarki tafiki

'karfi, khaleed d'in kuka samu shiyasa kuke yanda kukaga dama, idan nice shi wallahi sai in za6i d'akin danikeso kawai inyi kwanciyata kuma dole wacce ban za6a ba ta hakura.

Auta tayi dariya tace" Ay koda hakan yayi nasan d'akina ze za6a dan na dad'e d

a fahimtar irin tsananin son da khaleed kemani, shiyasa bani yarda inyi abinda zai 6ata ransa,

Sadiya tace Yauwa 'kawata haka yakamata kiri'kayimasa shine zesa ya'kara jin sonki da 'kaunarki, kuma kada ki yadda koda wasa kiyi fad'a da abiyar zamanki w

anda ze d'aga hankalinsa randa duk haka ta kasance sai son dayake maki ya ragu a cikin zuciyarsa.

Auta tace "ina ay bazan yarda haka ta faru ba, dan nayi al'kawarin babu ranar daza'ayi kace-nace dani a gidannan, amma kuma naga take-rakenta tana Neman t

a ragemun son da mijina yakemin ta haryar 6atamin duk wani Abu dana girka dan na faranta ransa.

Nan Auta ta kwashe labarin yanda Fadila tari'ka zabga mata gishiri cikin abinci, Wanda sanadin haka khaleed yafara juya mata baya,

Sadiya tace "tab ammaf

a yarinyar nan makira ce, wato ita nata ba dad'i shine ta 6ata maki,

tsabar ba'kin ciki kawai, amma kin kyauta da kika kyaleta, kawai ki ri'ka kaffa-kaffa da duk wani Abu wanda kikasan zata iya 6ata maki.

"Tab wallahi bazan 'kyaletaba, Auta ta fad'a cik

in d'aga murya, Sadiya tayi saurin sa hannunta ta rufema Auta baki, tare da cewa "ki rufamin

asiri kada kiyi wani Abu ace nice nazo na sakaki, kuma kinsan fa yanzu haka tana jinmu,

Sai lokacin Auta tayi 'kasa da murya tace "wallahi bazan 'kayletaba dole

sai na rama abinda tayimin, sadiya tashiga bata hakuri akan ta hakura ta 'kyaleta ai dai tasan tafita, Auta tace "Hmm Sadiya inaga kin fara manta ni, sadiya tayi murmushi tace "ina zan manta da rigimarki Auta, amma ai yanzu yakamta ki rage wasu abubuwan sa

boda yanzu gidan aure kike ba gidan iyayenki ba.



Auta tasan halin Sadiya idan ta biyemata tsaf zata sage mata gwuyawu taji bazata iya aiwatar da kome akan ramuwar abinda Fadila tayimata ba,

Yawarta ta d'auka dake ajiye kan bedsite ta duba, sannan

ta kalli Sadiya tace "kinga rana tayi har karfe sha d'aya da yan mitoci, bari nashiga kitchen na samo maki abinda zakici, nasan bazaki iya cin abincin waccan matar ba,

Sadiya tayi murmushi tace "wallahi da kin barshima dan tafiya zanyi yanzu, Auta tace w

allahi bazaki tafiba sai kinci abinci, kinsan me zan dafa maki, bata jira abinda zata fad'a ba tace taliya da manja da yaji zan dafa, nasan ke mayyar tace, suduka suka sa dariya.

Tare suka shiga kitchen d'in, cikin minti talatin suka gama girka taliyar

suka zuba a flate, sauka zabgo uban yaji, amma duk da haka saida Auta ta taho da wani Yajin cikin wani 'karamin vowel wai zata 'kara gabanta.

Sai gurin karfe sha biyu da rabi Sadiya tayi haramar tafiya gida, tare suka fito daga d'akin a babban falo suka

had'e da Fadila ta fito daga d'akinta zata shiga kitchen, nan suka gaisa da Sadiya kowanensu ba yabo ba fallasa, sannan suka wuce, har kusan get Auta ta rakata sukayi bankwana, tare da mi'ka mata wata yar 'karamar leda wacce ta had'amata kayan make-up aci

ki.

Auta na komawa d'akinta, toilet ta fad'a ta she'ka wanka, bayan tafito ta zauna gaban mirror ta d'and'asa kwalliya, sannan ta d'auko wasu 'kananan kaya riga da wando ta sanya,

Rigar ta d'an sauko dan ta rufe mata rabin cinyarta, amma ta matseta so

sai, sai wando pencil, sannan ta dauko wani karamin gyale tayi rolling, lokaci guda ta tashi daga jinsin Hausa zuwa na larabawa, dan idan ba magana tayiba sai kace bata ta6a jin yaren hausa ba.

Fadila kuwa itama lokacin tagama tsara kome na abinci kan d

ining, sannan takoma d'aki ta she'ka wanka shigar doguwar riga tayi ta atamfa, itama tayi kyau gwargwadon nata.

Da misalin 'karfe biyu da minti arba'in khaleed yadawo gidan, suduka falo ya iskesu, sukayi mashi sannu da zuwa, hankalinshi duka nakan Auta,

kallonta kawai yake yanajin wani feeling tattare dashi,

Saida Fadila ta lura da irin kallon dayakema Auta sannan tayi dabarar zuwa kusa dashi tace, "muje ka watsa ruwa ko, ga kuma abinci yana jiranka.

Beyi mata musu ba suka wuce d'akinsa, amma cikin

ransa jiyake inama Auta ce suke tare da ba abinda ze hana su kashe arna kafin su futo.

Zee Elkaseem

Mmn khady

[12/08 4:14 pm] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_



😘

```Page``` 136-140

✍

🏽

Zaune suke kan dining sunyi shirin cin abinci, kamar yanda suka saba duk wacce ke girki ita ke zuba ma kowa ta ajiye masa gabansa, yauma Fadila ce ta zuba masu ta ajiye masu, lokaci guda Auta ta ebi abincin takai ba

kinta,

Dadai lokacin shima khaleed ya ebo abincin yakai bakinsa,

Wani irin zafi yaji ya ziyarci 'kwalwarsa, ya mamaye duk illahirin Kansa, har cikin kunnuwansa yakejin bala'in yajin da aka zambad'a cikin abincin,

Wani mugun attaruhu aka zabga irin m

e yajin nan,

Kalmar innalillahi kawai yashiga furtawa, dan shi mutum ne wanda be shiri da yaji ko kad'an,

Robar ruwan dake gabanshi yayi saurin jawowa, ya tsiyaya ruwan cikin cup ya shanye, ya kara cika cup d'in ya shanye ko zeji sau'kin rad'ad'in yajin

dayakeji amma abanza dan ko alamar zebar jin zafin beyiba.

Dai-dai lokacin kuma yaji Auta ta fashe da wani irin kuka, yanda kasan wata 'karamar yarinya ta tashi tsaye, duk ta wani gigice tanata yarfa hannu, ta bud'e baki tana sha'kar iska tana fad'in

yaji, lokaci guda fuskarta tayi jawur, abinka ga farar mace, ga hawaye share-share.

```{Niko zee da nike tsaye ina kallon ikon Allah ri'ke baki nayi ina mamakin Auta dake kukan yaji, kamar ba ita bace tagama cin abinci da 'kawarta suka zabga yaji amma i

ta saida ta 'kara kan wanda suka zuba}```

Khaleed kuwa koda yaga yanda Auta ta fita hayyacinta, tanata kuka saboda yaji, besan sanda yayi saurin zuwa inda takeba ya rungumota jikinsa, ya nufi kujera three saater da ita ya zauna ya d'orata kan cinyarsa,

yana rarrashinta kamar wata 'karamar yarinya, ruwa ya d'auko ya zuba cikin cup yabata ta shanye amma yana cire cup d'in daga bakinta saita fashe da wani sabon kuka,

Lokaci guda khaleed ya rud'e yarsa yanda zeyima Auta taji sau'kin yajin.

Bakinsa ya

d'ora kan nata tare da tura harshensa cikin bakinta yashiga tsotsar bakin nata kamar yasamu wani sweet

🍬

, wai a dole ze tsotse mata yajin,

Dama abinda auta ke nema, itama tacigaba da kissing d'insa tana 'kara shigewa jikinsa, lokaci guda khaleed ya susu

ce ya manta da maganar wani yaji dayakeji, yacigaba da aika mata da sa'konni masu wuyar fassarawa, ita kuma sai wani 'kara shigewa take jikinsa tana shagwa6ewa,

Abu yayi nisa hannuwan khaleed kan 'kirjin Auta yanata wasa da dukiyar fulaninta, itako batayi

'ko'karin hanashiba saima 'kara mi'ka mashi kanta datayi.

Wani irin kukan ba'kin ciki Fadeela ta fashe dashi, dan duk abinda sukeyi gabanta sukeyi, kallonsu kawai take takasa magana saura kad'an zuciyarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login