Showing 21001 words to 24000 words out of 24778 words
aikata tun farko,
*_(Dama ance farau batada zafi sai ramau)_*
"To yanzu dai nazo neman sulhu, yakamata mubar duk wannan abun damukeyi, kinga bekamata ace mun zauna muna yima kanmu abunda be da
ceba.
Auta tace "ni dama ban d'auki abun da zafi ba, kawai dai kinsan hausawa sunce _*"Ramuwar gayya tafi gayya zafi*_
Amma kome ya wuce Allah shige mana gaba, Fadila ta Amsa da "Ameen.
*```To you my namesy Autar Hajiay```*
💃🏻
_ina mi'ka gais
uwa ga masoya a duk inda kuke_
~kibiyo *Zee Mmn khady* akwai sauran labari~
Zee Elkaseem
Mmn khady.
[10/16, 7:55 PM]
*AUTAR HAJIYA*
💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN
KHADY_
😘
```page``` 171-175
✍
🏽
koda Hajiya ta farfad'o daga dogon suman datayi, doctor ya'kara dubata ya tabbatar da lafiyarta, sannan yace za'a iya tafiya da ita, amma ari'ka kula da kiyaye abinda ze jefata cikin tashin hankali.
Daga
asibitin gidan khaleed aka wuce da ita kai tsaye, dan an riga an wuce da gawar a can.
Cikin likaffaninsu ta iskesu, hankalinta yayi matu'kar tashi, ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa.
*shikenan zainab kin tafi kin barni bayan kinsan banida wani d
'a ko d'iya sai ke, Allah kai ka bani zainab kuma kai ka kwace abinka badan baka sonta ba, ya Allah ka ji'kan zainab ka kai haske cikin kabarinta*
Haka tacigaba da kuka tanayima Auta addu'a nan mutane aka shiga rarrashinta ana kwantar mata da hankali.
A asibiti kuma momyn khaleed da momyn Fadila sunacan suna jiran abasu dama su shiga su duba me jego da babynta,
sai bayan magrib aka basu izinin Shiga,
Haka suka shiga jikinsu ba 'kwari ko kad'an,
Zaune take kan gado, ga baby gefenta, kuka take
kamar zata fitar da ranta, idanunta sun kumbura fuskarta tayi ja, tayi face-face da hawaye,
jin motsin shigowar mutane yasa ta d'ago da fuskarta wadda ruwan hawaye yagama wankewa, takai dubanta garesu.
Momyn fadila itace gaba, tana zumud'in ganin fadil
a da babynta,
```Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un```
Ta faurta lokacin da idanunta suka sauka kan Auta, Zaune kan gado ga babynta kusa da ita.
Momyn khaleed ce ta dafe, 'kirji Alamar mamaki tace
*"Auta dama ba ke bace aka cemana kin mutu ba*
.Auta
ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa, Momy fadila.....fadila.... ce tatafi ta barni, wani sabon kuka ya kwace mata.
Momyn fadila najin haka tanemi numfashinta ta rasa, nan tafa'di sumammiya, Momyn khaleed tarud'e da ganin yanda 'yar'uwarta ta suma,
Da sauri ta ebo ruwa ta yayafa mata, nan ta farfad'o,
Zaunar da ita Momyn khaleed tayi tana rarrashinta, tana gaya mata, irin Rahamar da Wanda yamutu gurin haihuwa yake samu, tace "kawai yanzu Addu'a Fadila take nema garemu ba kuka ba.
Wani sabon k
uka Momyn Fadila ta fashe dashi, dan rarrashinma da akemata jitake kamar ana zuba mata garwashin wuta cikin zuciyarta, shiru suka d'anyi nawasu yan mintittika, bakajin kome sai sheshshekar kukan Auta, Momyn khaleed ta maida hankalinta kan Auta tana rarraah
inta, sai jin fad'uwar Momyn Fadila tayi,
A hanzarce tajuyo gareta, tarin'ka jijjigata tana kiran sunanta, amma ina ba maganar lumfashi tattare da ita, cikin tsananin rud'ewa momyn khaleed tafita tana Neman taimako, wasu leburori ne mata suka taimaka mat
a, suka d'ora momyn Fadila kan gadon da ake tura marassa lafiya aka nufi Emergency da ita, nan fa lokitoci suka taru anata Abu d'aya amma numfashi ko Alamarsa babu jikin momym Fadila, amma kuma da an Auna sai aga zuciyarta na bugawa Alamar akwai rai tattar
e da ita.
Oxygen aka sanya mata *(Abin jawo numfashi)*
Sai lokacin Momyn khaleed ta buga waya ta sanar da daddyn fadila halin da ake ciki, aiko cikin tsananin rud'ewa ya iso asibitin, dan shima yayi tinanin Auta ce ta rasu amma yanzu ance Fadila ce
d
'iyarshi wacce yakeso, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonshi, yasa hannu ya goge.
Sai 'karfe hud'u na asuba Momyn Fadila ta farafad'o, da misalin 'karfe takwas doctor yabata sallama dan ganin jikin nata da sau'ki sosai.
Lokacin kuma aka sallami
Auta, bayan likitan ya tabbatar da lafiyarta data babynta.
'Karfe tara dai-dai suka isa gida, lokacin an fito da gawar Fadila data babynta,
Aiko da gudu Auta ta fito daga motar, tana goye da babynta, yayinda momyn khaleed ke goye da 'diyar da fadila
ta bari.
Bata ko kalli yawan mutanen dake gurinba tabi tacikinsu ta isa gaban makarar ta ri'ke tana cewa ```Wayyo sister fadila kada ki tafi ki barni, fadila ki dawo mu zauna mucigaba da gina rayuwarmu yanda muka tsara....
Fadila kin manta munce zamu ri
ke yaranmu mu had'a kawunansu su tashi tsin-tsiya mad'aurinki daya, wayyo sister fadila ki dawo garemu....``` haka tayita surutai tana kuka, nan aka kakkamata ana bata ha'kuri aka shige da ita cikin gida,
Hajiya tana cikin gida tanajin hayaniya daga wa
je, sai kunnuwanta suka ri'ka jiyo mata kamar muryar Autar ta, amma saita share tacigaba da istigifari tana nemar ma Auta rahamar ubangiji, dan tariga tasan Auta ta mutu kuma Wanda yamutu baya dawowa.
Da sauri ta taso dan ganin anshigo da Auta tana kuka
, wasu mata sun rirrekata,
Cike da mamaki ta isa gareta tace Auta dama bake bace kika mutu, bata bata amsaba sai wasu zafafan hawaye dasuka 'kara ganagarowa daga idanunta.
Hajiya batasan lokacin data rugume Auta ba tana wani irin kuka me wuyar fassa
ra, na farin cikine kona ba'kin ciki.
Da misalin 'karfe sha d'aya yan kai gawa suka dawo, Allahu Akbar ankai Fadila makwancinta.
Lokacin Kuma akayi addu'a aka shafa, gidan yayi tsit bakajin kome sai sheshshekar kukan mutane 'kasa-'kasa.
📿📿📿😭😭😭📿
📿📿😭😭😭📿📿📿
```Kulli nafsin za'ikatul maut, dukkan mai rai mamacine " fadila tarigamu gidan gaskiya```
😭😭😭📿📿📿😭😭📿📿
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:56 PM]
*AUTAR HAJIYA*
💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_
😘
```Page``` 161-165
✍
🏽
Alhmdulillahi dan kuwa yanzu ansamu jituwa tsakanin Fadila da Zainab ```{AutarHajiya}``` yanzu kowace tarage jin h
aushin 'yar'uwarta,
Saidai fa maganar girki idan fadila tayi, basu iya ci sai dai su d'an yafuta su tashi badan sun 'koshiba, Auta kuwa kalaluwan girki takeyimasu masu dad'in gaske.
Watarana Auta na zaune falo tana kallon wani tsohon Indian film ma
i suna *(Maharaja)* ta maida hankalinta tsaf kan TV sai jitayi an rufe mata ido ta baya, takama lalube tana dariya, takama hannun da aka rufemata fuska ta ri'ke tana dariya, tana cewa "dan Allah ko waye ayimin afuwa kada ayi wani Abu a film dinnan ban gani
ba,
Sakin fuskar tayi ta zagayo ta zauna kusada ita, tana dariya itama Auta dariyar take, takai kallonta ga Fadila tace "Kai sister yanzu abinda kikayimin kin kyauta, kinja an wuce banga wani wurinba, Fadila tayi dariya tace "to ay sai kiyo tariya, cike
da nishad'ia Auta ta mi'ko mata remote d'in tana dariya tace "kar6i tariyo min, dan tasan ba maganar tariya tunda ba kaset bane ta sanya.
Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon, murmushi kawai Auta
tayi tacigaba da kallonta.
Kusan Awa d'aya da yan mintoci Fadila na zaune tana taya Auta kallo, saida film d'in ya'kare ana shirin sanyo wani, Auta takai dubanta kan agogon dake manne jikin bangon d'akin taga har 12 ta d'an gota.
Auta ta kalli fadil
a tace girki fa? Kinsan fa rana tayi baki d'ora mana ba, gaskiya ki tashi kada kiyi mana horon yunwa, fadila tayi dariya tace wace ni in horaki da yunwa, kinaso me gidan ya d'aga min yellow card kenan abani hutun sati biyu, Auta tayi dariya tace ayko baz
e fara ba, kinsan kuwa irin son dayake maki, ai ko hutun kwana biyu baze iya bakiba baranatana sati biyu, dariya sukayi su duka.
Bayan shiru ya ratsa na yan wasu mintittika Fadila takai dubanta ga Auta tace "Niko Auta me zaihana murin'ka yin girki tare,
ranar girkinki muyi tare nima idan nawa yazo muyi tare.
Auta tayi dariya, tariga tagama d'agowa da fadila, so kawai take tari'ka tayata dan itama tasamu girkinta yayi armashi kamar nata.
Tare suka shiga kitchen suka fara girki, farar shinkafa suka d
afa me had'e da makaroni, sannan sukayi miya mai rai da lafiya, cikin 'kan'kanin lokaci suka gama suka jera kome kan dining sannan suka gyara kitchen d'in tsaf sukayi moping, kafinnan kowace tawuce d'akinta ta sheka wanka suka
fito falo suka zauna zaman ji
ran me gidansu, sunyi kyau suduka shar dasu abin gwanin ban sha'awa.
Khaleed ne yashigo gidan da sallama suduka suka tashi suka tarbeshi sunayimashi sannu da zuwa, fadila ta kar6i jakar dake hannunsa ta wuce mashi da ita d'akinsa,
Saida yaba Auta la
fiyayyen kiss sannan ya wuce d'akinsa, ya tarar har fadila tagama had'a mashi ruwan wanka,
Wanka yashiga, bayan yafito ya sanya kananan kaya marassa nauyi, sannan suka fito suka zauna kan dining, sunfara cin abinci gwanin ban sha'awa sunata fira suna d
ariya,.
khaleed ya kai dubansa ga Fadila yace waini fadila kodai kema kin Shiga makarntar koyon girkine bansaniba,? Auta tayi saurin tashi ta d'auko filo daga cikin filon kujerun daka zagaye a falon ta mi'koma Fadila tana dariya tace "kar6i sister yima
sa waigi kada yafadi ace mune muka kadashi, suduka suka sanya dariya hada kyalkyatawa,
Fadila tad'an tsagaita da dariyar datake tace "bawata makaranta nashiga ba illah makarantar sister d'ita gata zaune kusa dakai, ta nuna Auta.
Cike da jin dadi, k
haleed yad'aga hannunsa sama, yace "Allah nagodema daka bani mata nagari masu sona masu 'kaunata masu son kasancewata cikin farin ciki koda yaushe, ya kallesu su duka yace Allah yayi maku Albarka suduka suka amsa da "Ameen.
Ranar dai haka suka wuni ciki
n nushad'i da annushuwa, dan ranar khaleed be fita ko'inaba, saboda jin dad'in zaman gidan dayayi.
*************************
*_BAYAN WATA TAKWAS_*
Ahankali take takawa zuwa d'ankin Auta saboda nauyin da cikinta yayimata, tura kyauren d'akin tayi
sannan ta shiga da sallama, Auta dake kwance kan kujera 3seater itama da 'katon cikinta, idanunta rufe kamar me bacci, jin shigowar Fadila yasa ta bud'esu takai dubanta gareta, sannan takai dubanta ga cikin Fadila, har cikin ranta take tausayama Fadila yan
da take fama da ciki, dan tinda tasamu cukin take ta rashin lafiya, yau zazza6i, gobe ciwon kai, ga kuma rashin 'karfin jiki, babban abin ban tausayin shine tinda Fadila tasamu ciki bata iya cin abincin kirki, ga wani irinkumburi datayi, danma koda yaushe
khaleed na kula da lafiyarsu itada Auta.
Duk da itama Auta tana d'an ta6a rashin lafiyar jefi-jefi, amma idan ka kalli fadila sai kace Auta ba ciwo take ba.
Tare suka fito falo suka zauna suna firar duniya, duk rabin firar tasu ta yanda zasu tsara ra
yuwarsu ne nan gaba, da yanda zasu had'a kan 'ya'yansu sutashi kansu a had'e.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[15/08 11:11 am] .:
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*AUTAR HAJIYA*
💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY
_
😘
```Page``` 166-170
✍
🏽
Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar ze 6are saboda azabar ciwo,
Daga khaleed har Auta sun rud'e sun rasa inda zasusa Kansu, cikin tsananin rud'ewa khaleed yaki
ra Momynsa yasanar da ita halin da fadila take ciki, nan ta umarceshi da sutafi asibiti gatanan zuwa asbitin, tare da taimakon Auta aka kai Fadila mota sai asibiti,
An wuce da ita labour room, nurses sun taru kanta anata faman amma, har 'karfe 3 na rana
bata haihuba, lokacin Momyn Fadeela ta iso asibitin cike da tashin hankali, nan ta iske Momyn khaleed sai kai komo take cikin asibitin, kallo d'aya zakayimata ka gane tana cikin tsananin damuwa, khaleed kuwa tagumi yayi yarasa me kemasa dad'i.
Lokacin
wayarsa tayi ringing, hannu yasa ya dauka, sunan Auta yagani yana yawo kan screen d'in wayar, da Sauri ya d'auka ya kara a kunneshi, muryar dayaji Auta tana magana da itace ta d'aga mashi hankali, cikin tsananin ciwo take maganar _"kha....khaleed kazo ka t
aimakeni zan mutu_......
Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun ajiye motarsu inda yadace.
Bedroom suka isketa cikin jini ma
le-male, ba Alamar numfashi tattare da ita, Cikin tsananin rud'ewa suka d'auketa suka nufi asibiti, khaleed kuwa banda kyarma ba abinda yakeyi, dan ko tu'kin yinsa kawai yakeyi, amma besan inda kansa yakeba, da taimakon Allah suka isa asibitin, labour roo
m itama aka wuce da ita.
Nan fa likitoci suka taru akanta, amma abin sai du'a,i
Wasa-wasa har karfe shidda na yamma basuji wani dadd'an kabari ba, lokacin kuma Hajiyar Auta ta dad'e da zowa asibitin, zazzaune suke sunyi jugum-jugum Kowa Allah-Allah
yake yaji ance d'anshi ya haihu, yayinda khaleed ke cikin matsanancin tashin hankali.
Can gurin 'karfe shida da rabi dictor yafito daga d'akin duk yahad'a gumi, duk illahirin jikinshi ya 6aci da jini, suna ganin fitowarshi sukayimashi caaa, suna tambaya
rshi "Yaya dai doctor sun haihu kuwa, wata nannauyar ajiyar zuciya likitan yayi sannan yace "ina mijinsu yake?, khaleed yace "gani, biyoni office, Momyn khaleed tace dan Allah doctor kayi mamu bayani anan Kowa yaji halin da suke ciki, ko hankalinmu ya kwan
ta, nan da kake gani muduka iyayensune, ba wani abu ka fad'i kawai.
Doctor ya share wani gumi daya tsatstsafo mai a goshi, yace " ina farin cikin sanar daku cewa su duka sun haihu, Fadila ta haifi yara biyu mace da namiji, sai kuma Zainab ta haif d'a na
miji.
Lokaci guda fuskokinsu suka washe cikin farin ciki suka fara yima Allah godiya,
Sai lokacin likitan yacigaba da magana "amma inaso Ku Sani Allah shi ke badawa kuma shine me kar6ewa a duk lokacin dayaso,
saboda haka ina me ba'kin cikin sanar
daku d'a namijin da aka Haifa ya rasu, kafin daga bisani itama uwarsa tabishi, Allah yafiku sonsu, saboda haka kuyi hakuri addu'a kawai zakuyi masu sai Ku d'auki gawar kuje gida ku shiryasu dan kada akaisu matuary,
```Innalillahiwa'inna,ilaihirrajiun``
`
Suka furta lokaci guda suka shiga matsanancin tashin hankali, khaleed kuwa jiyayi 'kafafunsa bazasu iya d'aukarsaba zaman dirahan yayi yana zuabar da hawaye, yana cewa "shikenan Zainab kin tafi kiin barni ina zan saka raina, yakama 'kafafun momynshi yar
i'ke gam yana cewa Momy kicema Auta kada ta mutu ta barni, sosai Momy ta taasayama d'anta ganin yanda yake aurutai marassa kan gado, itama hawayenne suka gangaro kan kumatunta.
Hajiya kau tinda likitan yafad'i rasuwar taji kanta yayimata wani Jim, tana
tsaye dafe da kai, kawai sai jinta sukayi 'kasa ta fad'i sumammiya.
Da sauri sukayi kanta, suna salati, nanfa aka shiga wani sabon tashin hankali, dan Hajiya an yayyafa mata ruwa amma ba Alamar numfashi tatare da ita.
Nan aka d'auketa Emergency aka n
ufa da ita, likitoci ne suka taru dan ganin an ceto rayuwarta, akalla ankai awa biyu kafin asamu numfashinta yafara dawowa.
Nan aka sanar da Baban Auta da baban khaleed abinda ke faruwa asibitin,
lokaci guda suka iso hadda mahaifin fadila, nan a
ka d'auki gawar jaririn data mahaifiyarshi aka nufi gida dasu, tin daren a kayi masu wanka, aka shiryasu, sukayi kwanan keso.
😭😭😭😭📿
``` Allahu Akbar, kulli nafsin za'ikatul maut" dukkan me rai mamacine```
📿📿📿😭
Zee Elkaseem
Mm
n khady
[10/16, 7:56 PM]
*AUTAR HAJIYA*
💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_
😘
```Page```176-180
✍
🏽
Bayan kwana bakwai da rasuwar Fadila,
kuma ranar aka rad'ama yaran suna, d'an gurin Auta yaci sunan Baban khaleed, Ana kiransa shaheed, sai kuma babyn Fadila wacce yanzu haka tana hannun Auta ta had'a da yaronta tana shayar dasu, ita kuma sunan Mahaifiyarta aka maida mata *_Fadila_* mashaAlla
h anyi suna lafiya lau, duk da ba wani taro akayiba, amma 'yan'uwa da abokan arzi'ki sunzo, Auta tasha kyaututtuka ita da baby's daga gurin danginta da dangin khaleed, 'yan'uwan Fadila kuwa sha tara na arzi'ki suka had'oma Auta, abinda yakara d'aga hankali
nta tari'ka sharar 'kwalla tana tuna sister d'inta Fadila.
momyn khaleed ce tasamo wata dattijuwar mata wacce zata zauna da Auta dan ta tayata rainon yan biyunta.
***************************
Bayan kwana arba'in su Auta sun gama wanka, suduka suna
cikin 'koshin lafiya itada yaranta, sunyi 6ul-6ul dasu yarinayar Fadila kya'kyawa kamarsu d'aya da mamarta, sai dai ta d'auko farin babanta.
shaheed kuwa babansa ya biyo, fari tas dashi, kamar d'an larabawa.
Haka yaran suka taso cikin kulawar iyayen
su, dan khaleed kullum idan yataso ayki be'kara fita zama yake suna raino tare.
*_BAYAN SHEKARA BAKWAI_*
Wasu kyawawan yara na hango a harabar gidan khaleed suna wasa da ball, cike da nishad'i.
Can kuma sai suka kama rigima bansan kome ya had'asuba
, macen ce ta rugo da gudu, tashigo gida, namijin na biye da ita, jikin Auta tafad'a tana cewa "Ammi kice kada ya dakeni,suanan dasuke Kiran Auta dashi kenan _*Ammi*_ Auta ta'kara rungumeta, tace"kai shaheed kada ka doketa, miye ya had'aku? "Ammi wai dan m
unyi ball naci 3 itakuma taci 1 dan nayi dariya shine ta dokeni ta rugo.
Auta ta rungumoshi jikinta tace yi ha'kuri kaji shaheed d'ina bazata 'karaba.
Ya kalli Fadila wacce ta'kara narkewa jikin Auta yace "kuma yarinya idan kika 'kara saina doddokeki.
Ta kalli Auta tace "ai dai Ammi bazaki bari ya dokeniba ko? Auta tace Bazan bariba mana, aiko Fadila najin haka sai