Showing 12001 words to 15000 words out of 24778 words

Chapter 5 - AUTAR HAJIYA COMPLETE

15 Sep 2026

45



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

```Page````111-115```

✍

🏽

Ahaka Fadila tayi kwana biyu tana masu girki, kullum daurewa kawai kha

leed keyi yana cin abincin ba dan yana jin dad'insa ba, Auta ma daurewa kawai take dan ta lura da yanda shi kanshi me gidan yake cin abincin yana 6ata rai kamar yana cin magani, amma beta6a bud'a baki yace beyi dad'iba, saboda haka itama bata ta6a nuna kom

e ba.

6anagaren Fadila kuwa tayi mamakin yanda khaleed ke daurewa yana cin abincinta, wanda ko ita kanta data girka shi bata jin dad'insa.

Da misalin 'karfe shidda na yamma Auta ta shiga kitchen ta d'ora girki, kasancewar yau Fadila ta cika kwanakint

a biyu.

Cikin tsari da tsafta da 'kwarewar girki Auta take aiwatar da girkinta, jalouf din shinkafa da makaroni ta dafa, Wanda yaji kayan lambu da kayan kamshi, da kayan d'and'ano na girki, hanta zallah tayi girkin dashi maimakon tasanya nama, cikin 'ka

n'kanin lokaci 'kamshin girkinta ya gauraye gidan.

Fadila na d'akinta taji k'amshin girkin Auta ya daki hancinta, take ta had'iyi wayu, dan tasan yau zasu debi girki,

😋



```{Kaji fadila iyayen kwadayi ansan aci da dad'i amma ba'asan a girka da dad'i

ba

😜

}```

Haka Auta tagama girkinta ta kammala kome ta jera kan dining table, gefe kuma ga kunun ayar data had'a Wanda yaji dabino da kwakwa tun a gurin markad'en ayar, sannan ta zuba mashi sugar dai-dai kima saboda bataso yayi za'ki da yawa, ga kamahi

n flavor mai d'andanon ayaba, sai 'kan'kara data jefa ciki lokaci guda jug d'in yayi ra6a.

Da misalin karfe takwas da rabi suka hallara kan dining domin cin abinci, Auta ce ta zuba ma kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda suka d'ebi abincin suka kai baki

nsu, Fadila taji dad'in abincin har cikin kwanyarta, khaleed kuwa lumshe ido yayi, yana taunar abincin cikin nishad'i ya kalli Auta yace " Zainab amma bayan kinyi candy kin shiga makarantar koyon girki koh?, Auta ta tuntsure da dariya tare dasa hannunta ta

tallabo bayanshi, tace "bari ayima waigi kada ka fad'i daga kujerar, shima dariyar yayi yace "Allah kuwa da gaske tambayar ki nake, indai ba makarantar koyon girkiba yaushe mace zata iya tsara abinci haka wanda ko hotel baze kama 'kafarsaba, lokaci guda t

a rage dariyar datake tare da gyara zama tace "wannan makarantar Hajiya ce, domin itace ta dage gurin ganin na iya girki kala daban-daban, tin daga na zamani har zuwa na gargajiaya, cike dajin dadi da nishad'i khaleed yakara kai abincin bakinsa, yace "Amma

gaskiya Hajiya ta kyauta mana Allah saka mata da Alajannah Firdausi, Auta tace Ameen ya rabbi.

Fadila kuwa wani irin kishi ne ya tokare mata zuciya, lokaci guda taji bata iya cin abincin duk da dad'insa datake ji haka tabarsa.

Bayan sun kammala cin

abincin, Auta ta zuba masu kunun ayar suka sha, nan ma saida khaleed yayi wani santin, Auta kuwa dayayi saita tareshi tace bari ayimashi waigi.

Fadila kuwa Auta tagama 'kuleta wani irin haushinta takeji,

Auta kuwa ta lura da yanda Fadila ta 6ata r

anta saboda haka, ranar dad'i har cikin ranta, basu wani dad'e suna fira ba Auta ta nuna tana jin bacci, haka suka tashi suka nufi d'aki tare dayima Fadila saida safe, itama d'akinta tanufa tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, cikin ranta tana ga

nin laifin momynta da bata koya mata girkiba, kodayake itama Momyn tata ba dakanta takeyiba masu ayki ne kemata koda kuwa dahuwar ruwan zafine.

Haka tacigaba da tunani kala-kala, daga 'karshe bacci 6arawo yayi gaba da ita.

Zee Elkaseem

Mmn

khady

[09/08 1:02 pm] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

```page``` 116-120

✍

🏽

washe gari da safe Auta ta had'a break fast, nan suka zauna sukaci kamar y

anda suka saba, bayan sun kammala khaleed ya tashi tare da d'aukar makullin motarsa, yace "nizan wuce gurin aiki saina dawo, Fadila tace Allah kiyaye hanya ya kuma bada sa'a yace "Ameen, sannan ya kalli Auta yace "zan tafi amma zan dawo da wuri, inaso kiyi

mani girki me dad'i wanda zesa kunnena ya tsinke, wani tattausan murmushi tayi mashi tace "zan yi maka girki me dad'i, amma ba wanda ze tsinka kunnenka ba, sai dai Wanda zesa kayi santi wanda yafi Wanda kayi jiya, yace to shikenan nizan tafi, ita ta d'auk

ar Mashi jakarsa tarakashi har bakin mota saida taga tafiyarshi tana daga mashi hannu harya fice daga gidan sannan takoma zuciyarta cike da farin ciki.

Fadila tariga ta gama 'kulewa da yanda koda yaushe khaleed ke yabon girkin Auta, amma ita idan girkin

tane yanaci yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta.

Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba.

Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da sauransu, ga kam

shin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake.

Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa.

```{

😄

kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}```

Da ka

rfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya, wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan dining, Auta cike da nishad'i da

jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya

cokali, sannan ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido.

```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa```

Lokaci

n itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan komin dauriyar mutum baze iya cin saba.

Cikin tsananin rud'ewa Auta

ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta *Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka, yaushe na zabga gish

iri cikin abincina har ya wuce misali.

Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya bu'katar a can-cana maganar.

Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har gi

dan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special coaking

😜

.

Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wa

ni sabon d'and'ano a zo6on wanda beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata motsawa daga inda take,

Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi ya wuce d'akinsa,

Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa,

Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6

aci, nan tashiga rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o.

Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Aut

a dani kike magana```~

Zee Elkaseem

Mmn khady

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

*_Page_* 101-105

✍

🏽

A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada khaleed ya dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba.

Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan ta

bbatar ma idonta abinda ta gani gaskiya ne,

Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba, safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta tura 'kofar d'akin tash

iga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki.

Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale 'kasan d'ak

inba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta take cewa:

*_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_*

Shiru tayi na kimanin

minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi wani shu'umin murmushi, tace

*~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~*

: Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi

wanka sannan ta d'auro Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta

d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan turarrukanta masu dad'in 'kam

shi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa ajikinta.



Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin,

Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sal

lamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya kwana, shima w

ani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani sabon sonta ya shiga zuciyarshi.

Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata k

ya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man.

Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu

break fast,

Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu Eng

lish wear riga da siket, siket d'in farine har 'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu, sai wani siriri kamar

na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak.

Zee Elkaseem

Mmn khady

[06/08 11:42 pm] .: [06/08 11:10 pm] .:

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

*AUTA

R HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

*_Page_* 106-110

✍

🏽

Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin, dan kuwa Auta ba daga baya ba gurin iya girki, ita k

anta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel abinci baze wuce wannan dad'i ba.

Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da

wannan dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa, domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina.

Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana d'akinta kinga

kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu.

Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta.

Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata ku fidda, sai

lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi.

Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita haushi ke hanata magana, dan ita kom

e Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila.

A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura, kuma kullum girkin Autar takeci, da

n kuwa tare suke cin abinci su duka,

••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare,

Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin a

binci, Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi.



Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace

" ~_S

almanu!...... kada inga salame idan haka take_~"

Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda yaushe yana yaba m

ata kan iya girki.

Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta

Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba yanda

za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki.

Bayan sun kammala sun d'an ta6a

fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka ba.

Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci

nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka wuce d'aki.

Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya

wata doguwar riga ta bacci ta haye gado da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata.

Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagay

en d'akin zuciyarta nata tafarfasa, falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan lokacin data fashe da wani irin k

uka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.

Zee Elkaseem

Mmn khady

[10/16, 7:55 PM]

*AUTAR HAJIYA*

💃🏻

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

®NWA



👇🏻

_ZEE MMN KHADY_

😘

```Page```121-125

✍

🏽

Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki tun kafin ta k

ai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa

ba ita ta zuba gishiri haka ba,

ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba dad'in ji.

*******************

*********

Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan swan, abin gwanin ban sha'awa.

Da misalin 'karfe biyu

da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login