Showing 36001 words to 39000 words out of 160346 words
ya dau mataki a kai ko
wa ya goyi bayan Mera, wllh ina ta tausayinta nace amma kun ci amanar Rukayya, kuma idan baku yi hankali ba sai wuta ta ci ku, har na kullaci Meran dazu tana gaisheni nayi mata banza ashe masharanciya ce Badiyya ban sani ba, nasan da Mera aka saka wannan s
uyan da tuni na kusa cinyewa ina neman kari, aa gaskiya Hajja ta cuci Badiyya, kuma nayi da na sanin goya mata baya da nayi da taje wajena" Mikewa Badiyya tayi ta nufi kofa fuuuu ta fice daga dakin kamar zata tashi sama, Mama Ladi tace "Muguwa kawai, Mijin
Mera sai gani sai hange tunda ke makaryaciya ce warce bata iya girki ba" Ammi dai ta rasa ma me zata ce, wato karya Badiyya ta musu ta tafi bichi ashe Karaye ta tafi wajen Mama Ladi, Mama Ladi ta koma ta zauna tace "Gaskiya a fitar min da wannan azaban a
kira Mera ta soya min kwan da zan iya ci" Ammi ta sunkuya ta dau plate din kwan tace "Kiyi hakuri Mama Ladi, yanzu za a kawo maki wani" Mama Ladi tace "Hakuri ai ya zama dole, munafukar yarinya wai Mera ta kwace mata saurayi, wani saurayin arziki ne zai au
reta bata iya girki ba, wanda bai iya soya kwai ba ai babu abinda zai iya kuma a rayuwarsa har ya mutu" Ammi dai ta fita daga dakin. Bayan la'asar Hajja ta tafi sama har zuwa dakin Mayraah wajen Mama Ladi, Rabon Hajja da haurawa saman gidan zai yi shekara
bakwai, tun wani rashin lafiya da Ammi tayi, Hajja na tsaye bakin kofa bayan ta shiga dakin tace "Ke Ladi tashi zaki yi tunda kin huta mu tafi gidana don nan baƙi yawa za su yi zuwa nan da kwanaki kadan, gwara mu je inda zaki sake babu takura" Mama Ladi da
ke kishingide jikin pillow tana sakace hakora bayan ta ci kaza tayi nak tace "Ko yaya?" Hajja tace "Kwarai kuwa, kinga ni ma gida zan tafi Maheer zai ajiye ni yanzu" Mama Ladi tace "Toh shikenan, a kira min Mariya ta zo ta dau min akwatina mu sauka kasa ak
wai dukiyana a ciki bazan ba yara ba gaskiya" Hajja tace "Toh bari in mata magana" Hajja ta juya ta fita, bayan wani lokaci sai ga ta ta dawo tare da Aunty Mariya, Hajja tace "Akwatinta zaki dauka a saka mata a mota za mu tafi gida" Aunty Mariya ta shigo d
akin da sauri ta nufi inda akwatin yake ta duka zata dauka Mama Ladi tace "Munafuka algunguma wato daukar akwatin zaki yi, to babu inda zanje ina nan tunda ba gidanki bane balle na mijinki, har zaki je ki wani ce ma Hajja ta lallabani ta tafi da ni tunda g
ani barbadaddiya, to ina nan har sai an gama biki tunda ba wajen Hajja na zo ba, ke har kin manta irin azabar da kika min kina yarinya da zaki dinga kakkabi da ni? To wallahi babu inda zan je, ai ba gidanki na zo ba, babu wanda ya isa ya hanani zama gidan
nan har sai bayan biki" Aunty Mariya was sooo shock, don kasa motsawa tayi a inda ta duƙa, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin magana kike Ladi, a ina kika ji wannan maganar haka?" Mama Ladi tace "Badiyya ce ta zo nan ta gaya m
in, kuma wllh bazata maku sharri ba ji tayi an fada ne, in dai an ga na bar gidan nan to Mamuda ne ya koreni, amma ita kanta Ammin tayi kadan Al-qur'an, ai bikin jikokina biyu na zo Mera da Mashir" Tana kai wa nan ta juya masu baya ta ci gaba da kwanciyart
a, Hajja dai ta kasa cewa komai balle Aunty Mariya da ta kasa dagowa kamar kasa ya bude ta shige, Ammi da ke kokarin shigowa dakin dama a kan kunnenta aka yi komai, ta juya sum sum sum ta bar wajen ba tare da ta bari an ma san tana wajen ba.... Hajja na sa
ukowa parlor ta dau er jakarta tace "To da Alkhairi na tafi gida ni kam" Ammi dai na zaune kan kujera banda dariya babu abinda take, sai ga Aunty Mariya ta sauko kasa kamar wanda ruwa ya cinye tace "Wallahi wallahi sai na yi ma Badiyya abinda bata ta
ɓ
a tun
ani ba, ba tace ita magulmaciya bace
munafuka, Ni zata je ta hada da wannan matar?" Hajja tace "A dai dinga tunawa marainiya ce" Daga haka ta bar masu parlon, Nan Aunty Mariya ta hau shiga dakunan gidan ranta a bace tana neman Badiyya, Sabira tace "Ai Aunt
y Badiyya ta bar gidan nan tun dazu fa Hajiya"
Musharraf yayi parking kofar gidansu wajen karfe shidda na yamma zai shiga ya gaida Mami don bai da intention din kwana a gidan ranan, throughout today wayarsa a flight mode ya bar sa yasan Mami ta nemesa har
ta gaji, balle kuma Mayraah, duk yau ita ma basu yi magana ba, yanzun ma da ya taho gida ba kunna wayar yayi ba still, kawai baya son Mami ta daga hankalinta ne, Yana sauka motar ya nufi gate din gidan, ya amsa gaisuwan da Mai gadi ke masa without looking
at him, zai shiga ciki Mai gadin yayi kasa da kai cike da ladabi yana biye da shi yace "Yallabai an samu akasi fa" Musharraf ya juyo da sauri yana kallonsa yace "Akasin me?" Mai gadi yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Wallahi dazu Hajiya za su fita d
a Dreba sai ga dai wannan mutumin da ya kawo takardan nan wancan ranan...." Musharraf ya katsesa a rikice yace "Sai me ya faru??" Mai gadin da har ya tsorata ya fara kame kame, a fusace Musharraf yace "Malam ka gaya min ya aka yi??" Mai gadin yace "Wallahi
a kan idonta mutumin ya bani irin wannan takardan na ranan nan, don dreba ya fito da motar kenan daga cikin gidan za su tafi... Shine Hajiya ta sauke gilashin mota ta amshi takardan a hannuna, kaga ai bazan ce mata a'a ba ranka shi dade" Musharraf da yaji
wani zufa na keto masa yace "Ita da waye a motar??" Mai gadin yace "Aa ita kadai ce, ina jin Check up zata je" Musharraf bai sake sauraronsa ba ya shige cikin gidan da sauri, cikin few seconds sai ga shi a parlor, babu kowa a parlon ya haura zuwa bangaren
Mami, a parlonta ya sameta da mai aikinta dake shiga tayata hira a kai a kai, Mai aikin ta mike ganin Musharraf ta gaishesa da ladabi sannan tayi ma Mami sallama ta fita, Musharraf yayi kokarin calming kansa down yana kallon Mami dake kallonsa ita ma, A h
ankali yace "Good evening Ma" Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace "Evening, me yasa ka kashe waya tun safe?" Ya zauna saman kujera zuciyarsa bai daina bugawa ba yace "Ina hutawa ne yau" Mami tace "Okay" Daga haka ta mike ya bi ta da kallo gabansa na mu
gun bugawa, bedroom dinta ta shiga sai ga ta ta dawo rike da Envelope a hannunta tana kallonsa, kadan ya rage Musharraf bai samu heart attack ba a lokacin, don sai da yaji komai nasa ya tsaya for some seconds....
A gigice Aunty Mariya ta shigo dakin Amm
i tana kallonta tace "Ammi dama baƙi na shiga dakin Usman ne?" Ammi da lokaci daya hankalinta ya tashi ganin yanayin kanwar tata ta mike tace "Me ya faru Mariya?" Aunty Mariya da zufa ke karyo mata tace "Kinsan a dakinsa na ajiye jakata da akwatina tun ran
da na zo..." Ammi tace "To me ya faru? Ai babu wanda yake shiga dakinsa a gidan nan sai Maheer shima ba ko da yaushe ba" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Ammi ban ga zinarin akwatin lefen Mayraah da na saka a handbag din
a ba na kai dakin dazu bayan da aka nuna ma Hajja" Sosai gaban Ammi ma ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna gefen gado tace "Yanzun nan na shiga dakin zan dau kudi a jakar naga babu kudin, kusan
dubu talatin, nan na duba inda na ajiye zinarin da sauri, naga wayam babu an dauke har shi" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Ammi tsabar confusion ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta fice daga dakin tana kuka tace "Waye ya mana wannan aika
aikan...."
*Start making ur payment before the end of free pages fans, kar a ji ni shiruuuu*
07087865788
✍
🏻
WhatsApp only
[6/4, 7:47 PM] Khaleesat Haiydar
💖
:
💖💖
*MAYRAAH*
💖💖
_By Khaleesat Haiydar_
✍
🏻
10.....
Mikewa Musha
rraf yayi ya amshi Envelope din hannun Mami ya dake yace "What is it for?" Mami tace "Ka duba" Tana fadin haka ta zauna saman kujera tana kallonsa, a hankali ya ciro takardan cikin Envelope din ya warware yana karanta rubutun jiki, same content ne da wanca
n da aka fara kawowa, sai dai wnn an kara abubuwan da suka linka na farkon tsayawa a rai, Musharraf ya kalli Mami dake ta kallonsa babu ko kiftawa, zaunawa yayi side dinta yayi kasa da murya yace "And did you believe this Mami?? ke kin yarda da wannan taka
rdar?" Mami dai kallonsa kawai take, can tace "Uhnn abun ne ai da mamaki da daure kai" Musharraf ya mike a fusace yace "Mami i swear to God wannan ba komai bane facce sharri, karya da hassada, daga ganin wannan rubutun kasan mahassadi ne yayi sa, beside da
ma ai babu wani auren da baya zuwa da kalubale barin idan shaidanu suka cika lamarin from every angle, all i know is that, koma wani mara aikin yi ne ya turo da wannan saƙon to yayi a banza, babu abinda hakan zai canza...." A hankali Mami tace "Musharraf"
Kallonta kawai yake bai ce komai ba, Mami tace "Akwai abubuwan dubawa a lamarin nan...." Da mugun mamaki yace "Mami so u believe all this?" Mami ta girgiza kai tace "No ba wai nace maka na yarda bane my dear, kawai dai ina gudun abinda zai je ya dawo ne, t
his isn't a minor issue, sannan babu wasa a zancen aure don abu ne da ake son ayi sa na har abada...." Bai kuma ce mata komai ba ya bar parlon kamar zai tashi sama ya wuce dakinsa Mami ta bi sa da kallo, mikewa Mami tayi ta bi bayansa, bayan ta shiga dakin
nasa tana kallonsa tace "Look Musharraf, bana son ka daga hankalinka, pray hard about it, Allah Ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairi, and i pray this should be between me and you, ba sai kace ma kowa komai ba, Allah ya daura mu kan makiyanmu, no need to
disturb ur self, i gat ur back" Musharraf ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dama yasan Maminsa bazata ta
ɓ
a juya masa baya ba, duk abinda yace mata ba haka bane, ita ma a hakan zata tafi a ba hakan bane, bata son komai yayi stressing din mata son dinta,
because she loves him so dearly, he always reminds her of her late husband, shi yasa take jin sa har cikin ranta, and she can go any extent for him, mikewa Musharraf yayi ya kamo hannunta yace "Thank you for always believing in me Mami, and i appreciate u
r support always" Ta sakar masa murmushi tace "Anything for you sweetheart"
Ammi ce zaune dakinta sai Aunty Mariya da har a sannan ta kasa daina hawaye da ta tuna a hannunta zinarin nan yake aka sace sai ta kara rushewa da kuka, Maheer ma na tsaye dakin
ya ma rasa abinda zai ce bayan Ammi ta kirasa ta gaya masa abinda ke faruwa, Ammi ta kalli Aunty Mariya tace "Wai baza ki rabani da wannan kukan da kike ba Mariya?" Aunty Mariya ta kara fashewa da kuka tace "Dole inyi kuka Ammi, ni fa aka ba abun nan a han
nuna, kowa yasan ni aka ba ajiya, yanzu ta ina zan fara fisabilillahi? Waye yayi mana wannan aika aikan? sarkan kusan miliyan biyar, na shiga uku na lalace" Maheer yace "Yaushe Badiyya ta bar gidan nan?" Duk suka daga kai suna kallonsa, Aunty Mariya tace "
Babu wanda tayi ma sallama kawai nemanta aka yi ko sama ko kasa" Maheer yace "To ita ta dauka" Ammi ta zaro ido tare da dafa kirji tace "Ka rufa mana asiri kada Hajja ta tsine mana Maheer, ta yaya zaka ce Badiyya ce ta dau zinari?" Aunty Mariya tayi shiru
tana nazarin abinda Maheer yace, dazu fa da Hajja ta Kirata tana mata maganar zinarin Badiyya na zaune parlon, daga ita sai Hajja a parlor, kuma throughout today babu baƙin da suka hau sama banda Mama Ladi, Aunty Mariya ta mike tace "Wallahi babu tantama i
ta ce, don babu wani visitor da ya haura sama duk yau, Mama Ladi kuwa ko motsawa bata yi daga dakin Mayraah ba har yanzu" Aunty Mariya ta figi Hijab din Ammi zata fita, Ammi ta rikota tace "So ku ke ku jawo mana tashin hankalin da bashi da ranan karewa ne
Mariya? Ta yaya za ace Badiyya ce ta dau zinari bayan ba ita kadai bane a gidan nan?" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "Ai kin ji irinta, ban san me yasa Ammi take haka ba, kuma wllh yanzu zan tafi gidan Hajjan duk inda Badiyya ta kai zinarin nan sai ta f
ito da shi wallahi idan ba haka ba in kakkarya yar iska" Aunty Mariya dake huci tace "Tare za mu tafi Maheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru yau, idan ba tasan ta aikata rashin gaskiya ba ta yaya zata sidade ta gudu ta bar gidan ba wanda ya sani, yari
nya shaidaniya kawai bayan gulma da munafurci ashe har da halin bera duk tana yi?" Ammi da hankalinta yayi mugun tashi ta fashe da kuka tace "Ni dai duk wanda ya fita da sunan zuwa gidan Hajja ya samu Badiyya da zancen zinari ban yafe ba koma waye" Daga Ma
heer har Aunty Mariya haka suka tsaya kallonta, Maheer yace "Toh Allah ya baki hakuri Ammi, yanzu dai gold din nan zai yi miliyan 5 ko ma fin haka, kuma babu ta yanda za a kai Mayraah gidan mijinta babu wannan gold din tunda su suka saka a lefe, don haka s
ai a san yanda za ayi" Ammi na goge hawayenta tace "Ba komai, ai anyi hotonsa a waya, Zan sa a shiga kasuwa a duba min sak irinsa, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" Maheer ya juya ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayansa. Aunty Mariya ta bi Maheer
har zuwa dakinsa ta kulle kofar, a fusace Maheer yace "Kinga exactly abinda kika gani yanzu Aunty? To kullum a haka ake, kwata kwata Ammi bata son ace Badiyya tayi laifi balle a hukuntata, idan kayi magana tace bata son Hajja ta kullaceta ne saboda wasu d
alilan da ta bar ma kanta sani, Hajja bata da aiki sai lakaba ma Badiyya maraici wanda wannan mentality din ya riga ya makale a kwakwalwar yarinyar yanzu, an lalata mata rayuwa kawai, babu wanda ya isa ya hanata ko ya sa ta, iskancinta take zubawa yanda ta
ga dama...." Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Ai kaga Malam Bahaushe sai Allah kawai, da mutum ya rasa iyayensa ko makamancin haka sai ayi ta binsa da wai maraya ne shi, wanda wnn kalmar ba karamin tasiri yake a zuciyar yaron ba, yayi ta amfan
i da shi yana iskancin da ya ga dama, dama shi Maraya saboda iyayensa sun mutu sai aka ce a sangartasa har a bar sa ya lalace?" Maheer ya zauna gefen gado yace "Toh baki samu labari bane kwanaki har cewa tayi ita idan ba lecturer din da ke neman Mayraah ba
to ita fa sai dai ta mutu, tayi ta iskanci iri iri a period din Ammi da Hajja na biye mata,
infact i am fed up with all this wllh, har bana son a nuna Badiyya a kirata da er uwata saboda mugun halinta da yayi tsamari, yanzu ai ya ci ace tana da tsayayye i
ta ma tayi auren nan, amma babu ko daya, kullum sai dai wannan ya zo ya dauketa a mota ya dawo da ita, wancan ma ya zo ya dauketa ya dawo da ita a gidan Hajja, kuma Hajja bata da bakin magana don rufeta da fada take kamar zata mata duka" Aunty Mariya tace
"Yanzu dai ba Ammi tace taji ta gani kar a ma Badiyya magana ba ita zata siyo wani gwal din? To ai shikenan, ko ba komai ni dai hankalina ya kwanta" Tana kai wa nan ta fice daga dakin....
Haseenah ta rike ha
ɓ
a tana kallon Badiyya tace "Yanzu ke baki ji t
soron wannan abun da kika aikata ba Badiyya? Kilan ba ana can gida ya hautsine ana neman zinarin nan" Badiyya tayi wani dariya hade da ta
ɓ
e baki tace "Kuma babu wanda ya isa yace ni ne don Hajja kadai ta ishesu wllh" Haseenah tace "Gold din nan fa zai yi m
iliyan hudu kila Badiyya" Badiyya ta hade rai tace "Ni dai in zaki hada ni da masu siyar da Gold da kika sani a kasuwa ki hadani in kai abun nan su bani kudina, waye zai san na sata ne gwal din idan ba fada aka yi ba tunda dai ba waya bace balle ace za ayi
tracking, kawai ce masu zaki yi Mummynki zata siyar amma reciept ya
ɓ
ata tunda kince sun saba ciniki da ke" Haseenah tace "Ai ni tsoron abinda zai je ya dawo nake Badiyya, what if daga karshe suka gano na sata