Showing 150001 words to 153000 words out of 160346 words

Chapter 51 - MAYRAAH COMPLETE

dai in fara ci don yunwar ta gigita ni wllh, kada inje sallan bai yi dai dai ba" Hajiya Amina tayi murmushi kawai ta shiga kitchen, Mama Ladi ta dinga murmushi ganin uban liyafan abincin da

Hajiya Amina ta hado mata kamar wata matar sarki, babu abinda bata ta

ɓ

a a abincin ba don sai da ta kusa cinye duk abincin tass, ta kwankwade shayi me ƙauri da ta hado mata sannan ta tafi bandaki tayi alwala tana cewa "Alhamdulillah" ko kafin ta fito Hajiy

a Amina ta shimfida mata dardumanta me laushi da kamshi, bayan Mama Ladi ta idar da sallah ta koma bangaren Ammi tana ta murmushi tunda ta koshi, har a sannan Ammi kuka take a parlor, Aunty Mariya na ta bata baki, Mama Ladi ta kyabe baki ta kishingida kan

carpet tana sakace hakori tace "Mariya ga abinci can me shegen dadi Aminar ta dafa da zuka zukan kaji ki rufa ma kanki asiri kije ki deba ki ci kar ya kare, na ji tace har da na Umar Usman yaje daukosa a filin jirgi sun iso" Ko kallonta Aunty Mariya bata y

i ba ta koma daki don tuni Ammi ta mike ta shige daki, Mama Ladi tace "Kishiya sai kace kanki farau, abinda na ga Aminar ma na da hankali da biyayya, ina laifin wanda ya mutunta naka, tun dazu take ji da ni a parlor, sai kinga liyafar da ta hada min na abi

nci ko iya cinyewa ban yi ba, to ni dai ba ruwana wllh..." Mayraah dake kwance ta daga kai tana kallon Hajiya Amina da ta shigo dakinta, mikewa zaune tayi tana kallonta, Hajiya Amina tace "Ko dai baki da lafiya ne Mayraah?" Mayraah ta girgiza kai tana murz

a ido don ko kallonta bata son yi tace "Bacci nayi" Hajiya Amina tace "It's almost 3pm ki fito ki debi abinci ki ci" kai kawai Mayraah ta gyada mata, ganin Hajiya Amina taki fita yasa Mayraah ta sauko daga kan gadon, har sannan taki yarda ta kalleta, Hajiy

a Amina ta bude kofar dakin ta fita Mayraah ma ta fito tana tafiya a hankali, ita kanta tasan she is not okay she is just trying to be fine, Hajiya Amina ta shiga nata dakin, Mayraah ta sauka downstairs, tun da tayi ido hudu da Ammi bata sake bude dakinta

ba sai yanzu da Hajiya Amina ta shigo, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo Umar na biye da shi da jakansa a hannu, Umar na ganinta ya ajiye jakarsa yana kallonta, can ya nufeta yana murmushi, duk da maganganun da Usman da Maheer suka masa na ringing a

kansa hakan bai hanasa rungumeta ba kamar yanda ya saba duk sanda ya dawo, yace "Me kika dafa min Mimi?" Usman dai na tsaye yana kallonsu, Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta kasa ce masa komai ya daga kanta yace "Are you sick?" Kai ta gyada masa

tace "Amma da sauki" bata jira cewarsa ba ta nufi jakarsa ta dauka tace "Welcome back home bro" Daga haka ta tafi dakinsa dake downstairs, Umar ya bi ta da kallo sannan ya kalli Usman, zaunawa yayi kan kujera ya rike kansa, Mayraah na zuwa dakinsa wanda tu

n da sassafe Hajiya Amina ta gyara masa ta ajiye jakarsa sannan ta fito, bata sake kallonsu ba ta shiga kitchen, Usman ya bi bayanta, yana shiga kitchen din ta juya ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Kin shiga kin gaida Ammi?" Ta girgiza masa kai alamar

A'a, ya

ɗ

an yi shiru sannan yace "Yanzu me za kiyi?" Tace "Abinci zan zuba ma Ya Umar" Yace "Ke kin ci abincin?" Ta girgiza masa kai, yace "Debi naki kawai ki wuce daki, idan kin gama ci ki tafi ki gaida Ammi" Ta gyada masa kai, kasa cin abincin Mayraah ta

yi bayan ta deba ta tafi dakinta, can dai ta rufe ta mike ta fita daga dakinta ta nufi bangaren Ammi tana tafiya a hankali gabanta na faduwa, parlor ta bude a hankali kamar me tsoron ta

ɓ

a handle din, tana shiga Mama Ladi dake ta zuba gyangyadi ta bude ido,

gyara zamanta tayi da mamaki tace "Mera? wai dama kina gidan nan?" Mayraah ta gyada mata kai ta zauna kasa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Aunty Mariya da har a lokacin bata gaji da ba Ammi hakuri ba ita kanta tayi mamakin jin muryar Mayraah don ta ma

mance ta tambayi Maheer ko ya dawo da ita, Ammi dake zaune gefen gado bata daina kuka ba ta mike ta nufi kofar dakinta ta saka makulli, jikin Aunty Mariya yayi sanyi ta bi ta da kallo, Mama Ladi ta kalli kofar dakin jin an kulle da makulli, ta

ɓ

e baki tayi

tace "Tashi kiyi tafiyarki in baki ci abinci ba ki samu Aminar kice ta baki abinci, ta girka lafiyayyen abinci me kyau, nima ban dade da gama ci ba" Mayraah dai sai kallon kofar dakin Ammi da taji an sa makulli take, Mama Ladi tace "Ko kin ci abincin?" May

raah bata son taga hawayen da ya kawo idonta ta mike tace "Aa, zan ci yanzu" Daga haka ta juya ta fita ta koma dakinta, fadawa tayi kan gado ta dinga kuka tana jin zuciyarta na mata zafi... Babu yanda Aunty Mariya bata yi da Ammi kan ta gyara mata bangaren

ta ba don yayi ƙura Ammi ta ki daga karshe ta rufe Aunty Mariya da fada, Aunty Mariya ta ja bakinta tayi shiru.... Wajen karfe shidda Aunty Mariya ta fito rike da handbag dinta da akwatin Mama Ladi tana kallon Mama Ladi dake ta kallon TV a parlor ga bowl

din fruits cike a gabanta tana sha, ganin Aunty Mariya ta washe baki, bata ko lura da akwatinta dake hannunta ba tace "Kin ga yanzun nan ta kawo min wannan Mariya, anya kuwa ba er kirki bace matar...." Aunty Mariya ta wani hade rai tace "Za mu koma gidan H

ajja ne" Sai a sannan Mama Ladi ta lura da akwatinta dake hannun Aunty Mariya, ta ajiye slice din kankanan hannunta tace "Ajiya kika min a akwatin ne kika dauko min?" Aunty Mariya tace "Ae tashi za ki yi mu tafi magariba ya gabato" Mama Ladi ta matsar da b

owl din gabanta kamar zata yi kuka tace "To gidan uwarki na zo da za ki ce in tashi mu tafi Mariya? Ko ina ruwanki da ni fisabilillahi idan ba neman magana ba?" Aunty Mariya tace "Yanzu Mama Ladi ko wani yace ki kwana gidan nan sai ki kwana bayan kin san a

binda ke faruwa?" A fusace Mama Ladi tace "Aa ban san komai ba wallahi, wani sabon abun ya faru ne bani da labari? Ke ni fa ba yarinya bace Mariya da zaki kawo min raini zan ci uwarki la'ada waje wallahi, shi kansa Mamudan sai da ya tambayeni yace amma zan

kwana biyu kafin in koma ko, nace masa to tunda yace haka bari in zauna zuwa kwana biyun kuma shine zaki zo min da rainin wayo da maganar banza, ina ruwanki da sabgata, gidan uwarki ko gidan mijinki?" Ajiye akwatin Aunty Mariya tayi ta fice daga Parlon ta

bar gidan, Mama Ladi tace "Yau naga fitinanniyar yarinya kai, haka zan kama hanya in tafi in bar Ammin cikin wannan damuwan bazan zauna in dinga kwantar mata da hankali ba, sannan ga maganganu cike cikina da zan gaya mata game da tsinanniyar surkarta warc

e ni da kaina zan ja Hajja mu je gidan Mashir din da sassafe bayan na laka ma Hajjan karya Sanisar bata da lafiya rai a hannun Allah daga nan zan turketa ta fadi mugun abinda tayi da bakinta dama ga turarena da kasko na taho da shi a jaka, to ga dai na kis

hiya ya tabbata ko daga nan ai bai kamata a dinga shashantar da lamarina ba, ni ba boka nake bi ba Malaman gaskiya da suka san addini nake mu'amala da" Mama Ladi ta kare tana huci ta jawo bowl din fruit dinta tana sha..... Throughout ranan sai bayan magrib

Maheer ya shigo gidan tun da ya fita da Haseenah da Badiyyah, dawowar da yayi yanzun ma don Ammi ta kirasa yafi sau uku tana son ganinsa ne amma da bazai zo ba, yana shigowa parlor ya tadda Mama Ladi da Hajiya Amina zaune parlon ga malmalan tuwo biyu a ga

banta da miyan vegetable da yaji nama, Maheer ya karasa ya gaishesu, Hajiya Amina ta amsa, Mama Ladi tace "Ta zubo maka tuwon ne kai ma?" Maheer yace "Aa ai daga gida nake" Sama ya haura, direct ya nufi bangaren Ammi, zaune ya ganta a Parlon da Usman da Um

ar, alamar dai shi kadai ake jira, zaunawa yayi don tun dazu sun hadu da Umar a gidansa, sai da ma Usman ya fara kai sa gidansa har suka sanar masa abubuwan dake faruwa kafin su taho gida tare da Usman, a hankali Maheer ya gaida Ammi yana kallonta, duk wan

da ya ganta yasan ta ci kuka ba na wasa ba ranan, Maimakon ta amsa gaisuwarsa sai cewa tayi "kun san dalilin kiranku nan?" Duk suka yi shiru suna kallonta, Banda Usman da kansa ke kasa, Ammi tace "To kun ga Mayraah?" Sai a sannan Usman ma ya daga kai yana

kallon Ammi, ta girgiza kai as if counting her words tace "Babu ku babu ita har abada, ko magana ya sake hada ku da ita ban yafe maku ba, you 3 should just assume baku ta

ɓ

a saninta ba, baku ta

ɓ

a rayuwa waje daya da ita ba" Gaba dayansu kallonta suke babu k

o kiftawa, da wani expression Umar yace "How Ammi? It's not her fault all this happen...." Tsawa Ammi tayi masa tace "Questioning dina zaka yi?" Yace "No, amma bai kamata ki ce haka Ammi ba, ni har yanzu zuciyata bata yarda ba ke ce kika haifi Mayraah ba t

o be sincere" Ammi ta mike tana kallonsa da kyau tace "To ba ni ce na haifeta ba Umar gashi ina gaya maka da kaina yanzu, ban hada komai da ita ba, don haka ina sake jaddada maku ko gaisuwa ya kara hadaku da Mayraah wallahi ban yafe maku ba gaba daya, sann

an har yanzu ina kan bakata bazan zauna gidan ubanku ba, it's better ku samar min gida in koma don gidan Hajja ma bazan je ba" Tana kai wa nan ta shige Bedroom dinta.

MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 070878657

88

Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa

🫠

kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin

turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki

👸🏽

instantly wannan combo din shi ya dace dake.

[7/12, 8:11 PM] Khaleesat Haiydar

💖

: Usman ne ya fara mikewa after almost 5 minutes ya fita daga Parlon, U

mar ya mike ya shige dakin Ammi yana kallonta ya girgiza kai yace "Gaskiya ni bazan iya ba Ammi, zancen gaskiya kenan.... Me ta mana za mu daina kulata yarinyar da muka taso tare ku ka koya mana daukarta a matsayin little sister dinmu, me yasa tun a sannan

baku sanar mana wacece ita ba sai yanzu da rana tsaka ku ce mana ba ku kuka haifeta ba, that not being enough kuma all of a sudden kice mu daina kulata, how will that be possible?" Ammi ta juya tana masa wani kallo tace "Kasan dama i am against ur coming

back for this holiday ko? To kuwa zaka koma inda ka fito, in kuma kana da wata uwar da zata gaya maka kaji ne sai ka tafi ka sameta, get out Umar" Juyawa yayi ya fice daga dakin, ya bar parlon ma gaba daya banging the door behind him, Maheer ya bi sa da ka

llo ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, gaba daya ya kasa tashi a inda yake, Usman na komawa dakinsa ya dau jakarsa ya hada duk abinda zai hada a ciki ya fice daga gidan ba tare da yayi ma kowa sallama ba, Umar bai ma san action din Usman ba d

on shima yana shiga dakinsa dama jakarsa is already set, ya dauka kawai ya fice daga gidan trying to check if there is any flight to Abuja that evening with his phone. Sai da aka kira Magrib sannan Maheer ya tashi ya fita daga parlon Ammi, yana idar da sal

lah a masallacin layin ya shiga motarsa ya wuce gidansa. Daren ranan Mayraah bata yi baccin kirki ba, gaba daya taji gidan yayi mata zafi, sai kusan asuba bacci barawo ya sace ta kan darduman da ta kwanta bayan ta idar da sallah, washegari kafin karfe takw

as ta shirya, kawai tana son shiga school ta nemi waje ta zauna ko zata

ɗ

an ji sanyi a ranta, to gaba daya ta ma rasa wa zata ce ma zata tafi school yanzu, har cikin ranta taji tana tsoron Ammi ba kuma ta son ma ta hadu da ita, ta mike daga zaunen da tayi

gefen gado ta dau jakar makarantar ta duk da jirin da take gani ta nufi kofa a hankali ta bude, kamar ko da yaushe yau ma Hijab ne har kasa jikinta, sauka tayi downstairs dai dai nan Hajiya Amina ta fito daga kitchen tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma

za ki?" Mayraah ta gaisheta sannan tace "Ban gama project dina ba zan shiga school ne in je cafe" Hajiya Amina tace "Toh ai baki karya ba, ga breakfast can na gama ki je ki diba" Sai a sannan Mayraah ta tuna throughout yesterday fa kamar bata ci komai ba s

ai ruwa da tayi ta sha kilan ma shi yasa take ta jin jiri yanzu, a hankali Mayraah tace "Toh" karasawa kitchen din tayi kawai ta hada shayi ta fito ta zauna dining ta na sha bit by bit, Hajiya Amina dake zaune parlon tace "Aa Mayraah ki je ki debi abinci,

in baza ki ci Irish din ba akwai doya da kwai ki deba" Mayraah ta girgiza mata kai ba tare da ta kalleta ba tace "Bana iya breakfast da sassafe, idan naje school zan ci abinci" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah ta gama shan shayin ta mike ta kai cup

din kitchen ta wanke sannan ta dawo parlor, Hajiya Amina tace "Abban ya san za ki school yau?" Mayraah ta gyada mata kai still not looking at her, Hajiya Amina tace "To transport fa?" Mayraah tace "Ya tura min" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tsare" Mayra

ah tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har Mayraah ta isa school bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, har sai da mai adaidaita sahun ya juya ya kalleta don yana ta ce mata sun isa amma shiru kuma yaga idonta biyu ba wai bacci ko wani abu ba,

Juyowan da yayi ne ya dawo da Mayraah daga duniyar tunanin da ta fada, ta fara kalle kallen inda suke sae kuma ta sauka da sauri ta basa kudinsa ta shiga cikin makaranta, nesa da department dinsu ta zauna har sai da karfe goma yayi sannan ta mike da kyar t

a tafi cafe don yin printing copies din project din nata gaba daya, bata bar cafe din ba sai kusan 12, ita kanta tasan her Temperature is rising gradually, she is becoming so weak, ga wani ciwo da kanta yake, da kyar ta tako har department dinsu taga Motar

Musharraf a parking space, ta shiga cikin department din ta tafi sama, sai da ta fara zuwa office din project co-odinator dinsu tayi submitting masa copy biyu da zata basa, sannan ta fito da copy daya zata kai office din Musharraf, tsaye tayi for few seco

nds bakin kofar kafin tayi knocking, sai da ya mata izini sannan ta bude kofar ta shiga ya daga kai yana kallonta, ita dai bata yarda sun hada ido ba ta karasa kusa da table dinsa still not looking at him ta

ɗ

an risina tace "Good afternoon sir, i came to s

ubmit my project" Musharraf ya sauke idonsa daga kallonta after a minute ganin bazata dago kai ba, can kuma yace "When did i ask u to submit?" Shiru tayi bata ce komai ba, on a serious tone yace "I am asking u Madam" Still kanta a kasa tace "I can't rememb

er sir" Yace "Ok i see, go and come back around 5:40pm" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa suka hada ido, lokaci daya ta dauke kanta ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle masa kofar sa. Mayraah na fita office din tana share hawayen

da ya cika idonta ta sauka downstairs, ji tayi bata da strength din da zata ci gaba da zama makarantar har zuwa sanda yace, she is beginning to feel pain in all over her joint, nan da karfe biyar din da yace kusan awa biyar kenan fa, to ina zata je? In ma

ta je masallaci zata takura masu sallah ne tunda kwanciya zata yi, Ummi ce ta tado mata, ta ciro wayarta a jaka bayan ta nemi waje ta zauna tayi dialing numberta, suna gaisawa cike da karfin hali tace "Ummi don Allah kina hostel?" Ummi tace "Wallahi ina sc

hool kinsan yau za mu yi final paper dinmu, kuma paper din 4pm ne, za ki je hostel din ne?" Mayraah tace "Eh na shigo inyi submitting project dina ne kuma supervisor din yace sae 5pm, to na gaji baxan iya zama school din har zuwa sannan ba" Ummi tace "To b

ari in zo department

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login