Showing 123001 words to 126000 words out of 160346 words
ta mike tsaye tana dingisa kafafuwanta da suke mata azababben ciwo, ya kama hannunta suka nufi kofa ya
ce "Sai da safe Hajja" Hajja dai taki cewa komai don har ranta bata so Badiyyah ta sake komawa gidan ba to amma ya zata mata tunda taki ji, can ciki Haseenah tayi ma Hajja sai da safe ta bi bayansu fuskarta babu walwala, back seat ya bude ma Badiyyah ta sh
iga da kyar da kyar tana washh washh yana mata sannu, ya ajiye jakar kayanta a booth, Haseenah ta bude gaba ta shiga ta zauna, shi ma ya shiga motar suka bar anguwan, sai da suka yi nisa yace "Me za ki ci Badiyyah?" Badiyyah da ta kwanta bayan motar kamar
er yarinya ta marairaice tace "Ai bana iya cin abinci" Yace "Toh bari a siya maki kaza da yoghurt, kilan appetite dinki ya dawo" Haseenah ta juya ta
ɗ
an kallesa, ya samu inda zai siya ma Badiyyah abinda yace, yayi parking sannan ya sauka daga motar, bayan
wani lokaci sai gashi ya dawo da leda daya tal, ya bude back seat ya ajiye ma Badiyyah, nan da nan kamshin kazar ta gauraye mota, ya koma driver seat ya tada motar suka kama hanyar gida, suna isa gida a kofar gida yayi parking, duk tunanin Haseenah zai kom
a ne su ma ya siyo masu kazar, ya bude ma Badiyyah back seat ta lallaba ta sauko tana rike da ledan kazarta da yoghurt, ya ciro jakanta a booth, all this while ko kallo Haseenah dake ta bin su da ido bata ishesa ba, a haka dai suka shiga cikin gidan Haseen
ah na tafiya a hankali tana biye da su fuskarta a daure, ya bude ma Badiyyah wani spare room ba wanda Mayraah ta zauna ba, fuuu Haseenah ta shige dakinta ta zauna gefen gado ta cire hijab dinta don wani mugun zafi ta dinga ji, can dai ta kasa ci gaba da za
ma ta fito corridor ta gansa ya dauko plate da cup ya shiga dakin da Badiyyah take, da ido ta bi sa har ya fito daga dakin ya fice daga gidan gaba daya, mota ya shiga ya kama hanyar inda Mayraah take don tun dazu hankalinsa gaba daya na kanta, kaza ya siya
mata da drink din da yasan tafi so me sanyi, yana isa ya tadda motar Usman a kofar gate din hostel din, Mayraah dake zaune kan wani dakali tare da Usman dake danna wayarsa ta bi motar Maheer da kallo, tun da Usman ya zo after magrib basu yi maganar da ya
wuce na minti biyu ba ya fara danna waya, lkci lkci dai zai daga kai ya kalleta, ita dai kawai tana zaune gefensa tayi nisa tunanin da take har ta hango motar Maheer.
MAYRAAH is 500 Via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 070878657
88
[7/4, 7:37 PM] Khaleesat Haiydar
💖
: Usman ya mike bayan Maheer yayi parking, ya kalli Mayraah yace "Sae da safe" Daga haka ya nufi inda motarsa take, ita dae kawai ta bi sa da kallo, Maheer bai sauko ba har sae da yaga Usman ya tafi sannan ya bude mota
rsa ya fito, ya nufeta ya zauna inda Usman ya tashi yace "Hope kin ci abinci" ta kallesa ta gaishesa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, tana karba bayan taji abinda ke ciki tace "Yaya ya kawo min, but i will give my roommate this" Maheer yace "Ohk, me
kika dafa?" Ta girgiza kai tace "Roommate dina ta ban shinkafa" yace "Kuma kin ci?" Duk da ko spoon biyu bata ci ba a shinkafar da Ummi ta zuba mata kawai sae ta gyada masa kai, ya mata murmushi yace "Good, gobe za ki shiga school ae?" Ta girgiza masa kai
kawai, bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, Allah ya sani kawai daurewa take and she is trying to act she is okay, but deep down she is
soo heartbroken and sad, gashi gaba daya ta kasa kuka ko zata ji sauki a ranta, tun kukan da tayi da safe bata sa
ke ko digon hawaye ba har zuwa yanzu, ji take kamar hawayen nata sun ƙafe ne, babu irin tunanin da bai zo zuciyarta ba bayan sun ajiyeta dazu, da ta tashi zata yi abinda zuciyarta ke raya mata sae ta tuna da furucin Mamin Musharraf ta koma ta zauna a dakin
, did she really want her 5 years to go in vain, idan ma ta bar shi ya tafi in vain din zata iya farawa daga farko kuwa? Ƙwaƙwalwarta zai iya daukan karatun nan gaba ma kuwa? All this thought ke sa wa ta kawar da abinda ke running a mind dinta, amma minti
goma yayi kadan tunanin zai sake ringing a head dinta, ita kadae ce dakin don roommate din nata ta shiga school wai zata yi karatu, a haka kiran Usman ya shigo wayarta ta fita ta samesa, sae kuma Maheer da ya zo yanxu, ita kanta bata san she is this strong
ba sai yau, firgit ta dawo daga tunanin da ta tafi bayan Maheer ya dafa ta cause magana yake mata amma bata san yana yi ba, ta juya da sauri ta kallesa, da damuwa yace "Mimi tunani kuma? I tot u promise me not to, i just caught u now" Tayi resting kanta a
shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Yaya tunanin exams nake, i don't know where to start reading from, all the courses are bulky...." Maheer bai ta
ɓ
a zama uncomfortable with Mimi leaning on him ba sae yau, ya kasa ce mata komai sae gyada mata kai kawa
i yayi, for almost 5 minutes babu wanda yace komai cikinsu, ita dae kanta na shoulder dinsa, can dai yayi karfin halin cewa "Erm naga kamar ba wuta hostel din ko? let me go and get u rechargeable flashlight yanzu in dawo" Ta daga kai ta kallesa tace "Yaya
Usman ya kawo min with fan" Maheer yace "Good, yanzu za ki shiga ciki ki fara karatun ne? i will be calling u every now and then to know how far you've gone" A hankali tace "Ohk" yace "Good gal, go inside and start reading" Mikewa tayi tana rike da ledan d
a ya kawo mata tana kallonsa tace "Nagode yaya" Murmushi kawai ya sakar mata bai iya cewa komai ba, ta juya ta shiga ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya, for some minutes ya kasa tashi a wajen daga karshe ya mike ya nufi motarsa, his intention was to
be with her har zuwa 10 bai yi niyyar tafiya da wuri ba. Yana isa gida wajen karfe tara da wani abu bayan yayi parking ya shiga ciki, Haseenah na zaune parlon sanye da kayan bacci ga fruits da ta aika Musa ya siyo mata ta yanyanka ma Maheer ta rufe tana j
iran dawowar sa, yana shiga parlon tun da ya lura ita ce a parlon bai ko kalli inda take ba yayi hanyar corridor ya bude dakin da Badiyyah take, Haseenah ta mike ta bi bayansa, tsaye tayi corridor din ganin dakin da ya shiga, Badiyyah na zaune ta kusa tash
i da kazar da ya siya mata tana si
ɗ
e hannu yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ba a kawo min ruwa ba" Juyawa yayi ya fita, ya wuce Haseenah dake tsaye ya tafi kitchen, Haseenah ta karasa dakin Badiyya tana kallon ciki, Badiyyah na lashe hannunta tace "Ke naga
kamar yaya bai siya maki kazar ba ko?" Haseenah ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa taki ce ma Badiyyah komai sai kallonta take, Badiyyah tace "Ga yanka daya nan ki shigo ki dauka" Sai ga Maheer ya bi gefen Haseenah ya shiga dakin ya karasa kusa da B
adiyyah ya duka ya bude bottle water din ya zuba mata a cup ya dauka ya mika mata yana kallonta yace "Hannun ya maki sauki yanzu?" Ta wani marairaice tace "Har yanzu yana min ciwo wllh" Juyawa Haseenah tayi ta bar bakin kofar ta koma parlor ta zauna tana j
in zuciyarta na tafarfasa..... Mayraah na zaune kan darduma da handout a gabanta tayi tagumi, tun tafiyar Maheer ta dauko handout din amma ko layi biyu ta kasa assimilating gashi yanzu har kusan karfe sha daya, gaba daya taji kanta ya tushe ga wani ciwo da
yake mata, wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta kalli screen din ganin Dr Musharraf ke kiranta tayi silencing kiran, yana katsewa ya sake kira nan ma ta kara silencing kiran
daga karshe ta sa wayar a flight mode, ta tattara handout din ta ajiye gefe ta
yi kwanciyarta kan darduman, kuka take son yi amma ta nemesa ta rasa gaba daya, a haka roommate dinta ta dawo daga cikin school ta sameta kwance, Mayraah ta kulle ido kamar bacci take, bayan roommate din nata ta gama shirin kwanciya ta fara tashinta a hank
ali tace "Sis ki tashi ki hau kan gado" Mayraah ta bude ido tace "Ina son tashi inyi karatu ne anjima kadan ne" Ummi tace "Ki gaya min sanda kike son tashi zan sa alarm in tashe ki, kin ga kasa akwai sanyin tiles" Mayraah tayi shiru, can ta mike zaune a ha
nkali tace "Toh Nagode" Komawa saman gadon tayi tana kallon Ummi ta nuna mata ledojin kajin da su Maheer suka kawo mata tace "Ki dauki daya naki ne, yayana ya kawo mana" Ummi tayi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, karfe nawa zan s
a maki alarm din" Mayraah tace "Sha biyu da rabi" Ummi tace "To in sha Allah zan tashe ki lokacin" Mayraah tace "Nagode" sannan ta kwanta ta lumshe ido amma har karfe sha biyu idonta a bushe yake babu alamar bacci, sha biyu da rabi nayi Ummi da bata kai ga
kwanciya ba tana revision ta fara tashin Mayraah, duk Mayraah na jin ta amma tayi shiru, daga karshe ta mike zaune da kyar, Ummi tace "It's time" Mayraah ta sauko daga kan gadon ta sake dauko handout dinta ta zuba masa ido kamar hoto, tana ta zaune har ka
rfe biyu saura kawai daga karshe ta tashi taje ta dauro alwala ta dawo.... Sai kusan karfe hudu Mayraah ta kwanta kuma har a sannan ko line uku bata fahimta ba a handout. Ummi ce ta tasheta sallan asuba bayan ta idar ta koma ta kwanta, bata farka ba sai ku
san karfe takwas da rabi, sosai kanta ke mata ciwo ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, Ummi ta gyara ko ina ta share har wanke wanke tayi, takarda ta gani gefenta ta dauka taga note Ummi ta bar mata kan cewar ga breakfast ta ajiye mata a warmer,
akwai ruwan lipton ma a flask ita ta tafi school... Mayraah ta ajiye takardan ta dafe kanta, can ta jawo wayarta da ta sa flight mode tun jiya, bude wayar tayi ko minti daya ba ayi ba sai ga kiran Usman ya shigo, ta daga kiran ta kai kunne, daga daya bang
aren yace "Me ya sa kika kashe wayarki?" A hankali tace "Ina kwana?" Yace "Ko ba ki da caji ne?" Tace "Akwai, bacci nayi ne" Yace "To kar ki sake kashe waya malama" Cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Kin yi breakfast?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "To yi br
eakfast din ki fito" Ta daga kai tace "Ina?" Yace "Waje... Kar ki wuce tara da rabi zan tafi aiki" a hankali tace "Toh" katse wayar tayi ta mike ta shiga bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta saka kaya, ta bude warmer din da Ummi ta ajiye mata taga irish
ne da kwai, ko kamshin abincin bata son perceiving, ta bude dayan taga kazan jiya ne tayi masa kamar pepper soup, lipton kawai Mayraah ta sha ta saka hijab dinta ta fita waje, zaune ta gansa cikin motar, he was on suit, ya ajiye wayarsa bayan ya ga ta fit
o, ta karasa jikin motar ta bude tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" yace "Kinyi breakfast din?" Tace "Nayi" Yace "Karatun fa?" Kai kawai ta gyada masa alamar tayi, ya
ɗ
an yi shiru, ita dai kallonsa
kawai take, can yace "Baki bukatan komai?" Tace "Ba komai" Yace "If there is anything ki kirani, zan je aiki yanzu" Tace "To Allah ya tsare" Yace "Ameen, sai anjima" ta gyada masa kai ta juya ta koma ciki. Maheer na kwance parlor idonsa a lumshe kamar me b
acci amma ba baccin yake ba, yana jin Haseenah a kitchen tana ta soye soye tun karfe takwas, jin an bude kofa ya bude idonsa, Badiyyah ce ta shigo parlon kamar ba ita ke dingishi jiya ba, ta dawo garas abinta, ta
ɗ
an sosa kai tace "Ina kwana yaya?" Yace "L
afiya lau..." Sai ga Haseenah ta fito daga kitchen da tray din breakfast tayi ma Maheer, kallo daya tayi ma Badiyyah ta dauke kai ta isa dai dai inda yake kwance ta ajiye duk da tun jiya bata ga fuskarsa ba
tana murmushi tace "Honey ga breakfast nayi maka"
Bata jira me zai ce ba ta bude cooler din ta fara debar masa irish din a plate, Badiyyah tayi hamma sannan ta nufi kitchen, tana shiga taga wayam duk Haseenah ta wanke kayan da ta
ɓ
ata, ta gama dube dubenta a kitchen din bata ga alamar breakfast ba, can ta
fito ta dawo parlon tace "Haseenah ni ina breakfast din nawa?" Ba tare da Haseenah ta kalleta ba tace "Ni zan maki breakfast din da zaki ci? Baki san hanyar kitchen din bane?" Badiyyah ta wani hade rai tace "Ban gane ban san hanyar kitchen din ba, dama a
gidan nake da zaki ce min ban san hanyar kitchen ba? ina bakuwa dani baza ki bani breakfast a gidan yayana ba kike nufi?" Banza Haseenah tayi mata ta ajiye ma Maheer plate din irish da kwai ga ketchup a gefe, ta bude wani cooler din ta zuba masa farfesun c
atfish da tayi, shi dai bai ce mata komai ba, ta langwabar da murya tace "Bari in dauko madara in hada maka shayin baby" Daga haka ta mike ta koma kitchen, Maheer ya kalli Badiyyah da tayi wani mitsi mitsi da ido tana huci tana bin Haseenah da kallo, sai d
a ya ga Haseenah ta shiga kitchen yace "Zo ki dauka ki je ki ci" Badiyyah ta taho da sauri ta dau plate din irish din da bowl din catfish ta tafi dinning area ta zauna, sai ga Haseenah ta fito, sake baki tayi tana kallon Badiyyah, can ta nufeta a mugun fus
ace tace "Ke Badiyyah ki shiga hankalin ki kar in maki rashin hankali, breakfast din mijin nawa kika dauka saboda baki da saiti?" Maheer yace "To ke ina ruwanki, ba dai ni na bata ba?" Badiyyah na tafe hannu tace "Kuma baki isa ki hana yayana ya bani abind
a ya ga dama ba a gidan nan, ta ya ma zan zo gidanki saboda bakin hali ki hana ni breakfast kamar wata yar iska??" Maheer ya mike tsaye yace "Dauki breakfast din ki wuce daki" A mugun fusace Haseenah ta nufo sa tace "Ban gane ba Maheer?" Calmly yace "Kina
nufin da yunwa zaki bar sister na ko kuma ance maki bare ce ita?" Badiyyah ta ja tsaki ta dau breakfast dinta ta wuce ta gaban Haseenah har tana neman bangajeta ta wuce daki ta kulle kofa, Maheer yayi wucewarsa daki shi ma ya bar Haseenah wajen tsaye baki
bude kamar an dasa ta.... Wanka yayi ya shirya ya fito parlon, sai ga Badiyyah ta shigo parlon ita ma rike da kwanukan da ta shiga daki da su bayan ta si
ɗ
e tass kamar dama a yunwace ta tashi, tana ganin Maheer zaune parlor tace "Yaya aiki zaka tafi?" Yace
"Ehh" Tace "Don Allah nima sai ka ajiye ni a school, yanzun nan zan shirya" Yace "Ohk har kin warke kenan" ta sinne kai tana murmushi tace "Ehh hannun kawai ke ciwo amma zan iya zuwa school din" Yace "To kar ki bata min lokaci" Haseenah dake zaune kan kuje
ran dinning ranta a mugun bace ta dinga bin su da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunani zata yi, Maheer na ta jiran Badiyyah a parlor har ta fito, daga ita har shi babu wanda ya kalli inda Haseenah take suka fita daga parlon. Yana ajiye Badiyyah a bakin
gate din school din nasu ta kallesa da sauri tace "Aa yaya bakin gate kuma zaka ajiye ni baza ka shiga ciki ba? Da nisa fa department din namu" a takaice yace "Ana jirana a hospital ne" Tace "Toh shikenan" Sauka tayi daga motar ta rufe tana washe masa baki
tana daga masa hannu alamar bye bye, ya gyada kai ya ja motarsa ya bar wajen, A ranta tace kai wai ashe dama haka yaya Maheer ke da kirki bata ta
ɓ
a sani ba?? Ashe ya Maheer is this nyc? Ko da yake dama ita babu abinda ke hadata da shi kuma ko ta gaishesa
da can ma yana amsawa, iyaka idan yaga tayi ba dai dai ba yace zai mata fada ita kuma shine bata so, Usman ne kawai ya tsaneta tun asali, kwafa tayi a ranta tana imagining ta tura ma Usman yan daba su rama mata dukan da yayi mata har sau biyu kenan, da sau
ri ta shiga cikin makarantar tana addu'ar Allah ya sa Dr Musharraf ya shigo school ta samesa a office, sai murmushi take... Maheer kadai yasan yanda yake tausasa zuciyarsa na ganin ya biye Badiyyah ita kuma har ta wani sake
jiki da shi abinda ma ke kara ƙo
na masa rai kenan, da ta san irin mugun haushinta da yake ji