Showing 1 words to 3000 words out of 17483 words

Chapter 1 - AUREN WATA BAKWAI COMPLETE

[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath

🥀

: *AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

*© Xayyeesherthul-humaerath*

*Dedicated To NimcyLuv*

_*Auren Wata Bakwai!* daga jin sunan kun san cewa za ayi cakwakiya Iya cakwakiya,ba zan dai baku s

atan amsa ba, kar ku bari a baku labari, wacce ta karanta ta huta.

😻

_

Page-1&2

*MASARAUTAR BENONI*

Ihu take da magiya hannunta rike da get din shiga masarautar tana jijjigawa ,"Useni aççe am mi nasta,Hokkam dama je Karshe useni,Don Allah ku barn

i in shiga Inga Yareema,ku bani dama ta karshe,Miyida misandiri denyo 'am,Ballite yonki am, Baffana zai mutu, ku taimakawa rayuwata."

kuka take na fita a hayyaci.

Tana fada cikin muryar fulatanci wacce daga ji zaka Tabbatar da cewa hausar bata isheta

ba.

Daya daga cikin dogaran ya ce, "Karya kike, Mayya anaci,turo ki akayi ki cutar mana da yareema."

Yana fada suna janyeta daga jikin get din tana kara kankamewa.

Ta ce, "Aradun Allah,na Rantse ba abun da zan wa Yareema, taimakonsa nake nema, Don Al

lah ku barni."

Bulala suka shau

ɗ

a mata wacce ta kara hargitsa mata tunaninta wani irin tsalle tayi ta dire da gudu tana neman hanyar gudu.

Wata farar mota ce kirar MERCEDES-BENZ ML350 ta tawo a hankali.

Adnan dake gefen glass yana hangota cikin sau

ri ya ce wa Driver ya dakata.

Ya na tsayawa Adnan ya fita yana, "Kee! Kee."

Idonta a rufe ta daura hannu akai.

Jikinta na rawa.

Yarinyace da bata zarce shekara Goma sha hudu ba, sanye da kayan fulani, duk ya fita a hayyacinsa kamar yadda ita ma

ta fice a hayyacinta,kallo

ɗ

aya za ka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin wani mawuyacin yanayi,ko dankwali babu akanta, gashi duk a cucure ga yawo da santsi, Dogowa ce siririya mai dirin Fulani,ba a sata sahun farare can can ba kuma baza asata sahun ba

kake ba,duk da yanayi na tashin hankalin da take ciki hakan bai hana bayyanar da kyawunta ba.

Karasawa ya yi gabanta ganin kamar bata san yanayi ba ya cire hannunta da ta rufe fuska da shi.

Cike da mamaki ya ce, "You ,?

Cikin isa da kasaita gami

da Izza ta jinin sarautar da ke yawo ajinin jikinsa duk wata ilhama da kamala ta bayyana a tare da shi, Prince Adeel Muhammad Rohaan ya fito a motar ya yin da aka bude masa.

Cikin second guda ga gukkan kwayar Idon da ya kallesa zai fahimci tsantsar jinin

sarauta ne anan wanda Ubangiji ya tsara masa hallita mai cike da kwarjini da Izza, Fatar jikinsa bakine ba irin sosai dinnan ba,baƙi mai kyau da sheƙi,ga idanunsa da suka kasance Sexy Eyes da ke birkita yan mata, yana da fadin kirji da duk wani abu da 'Ya

mace ke bukatar kasancewa ga Namiji ko ince fiye da haka ma.

Kananun kayane a jikinsa kamar yadda ra'ayinsa da tsarinsa yake baya taba sa kayan sarauta har sai in da wani dalili wanda ya zam dole.

Saukarsa kenan daga America wanda ba kowa ke sanin shi

garsa da fitarsa ba domin tsaro.

Driver bai ajiyesa a ko ina ba sai daidai kofar part dinsa dake ta bayan masarautar kebantacce wanda ba kowa yasan da nan din ba.

Yana Parking ya fito ya Bude masa kofa cikin hanzari.

Tafiya yake tamkar ba zai taka

kasa ba.

Shigewa Adeel ya yi kaitsaye ba tare da ko kalli inda Adnan yake ba,bare har ya yi tunanin yi masa magana ko jiransa.

Adnan ya gyara tsayuwar sa ya na kare mata kallo ya ce, "What is your Name?"

Zaro masa manyan idanunta da taci kuka

ta koshi ta yi.

Ya ce, "Oh Sorry Ya Sunan ki?"

Cikin Muryar fulancinta da gurbatacciyar hausarta ta ce, "Zainab a rugar Jauro ana she mun Gaaji."

Adnan ya ce, "Alright biyo ni mu je." Ya karasa maganar yana mata nuni da hannu.

Bayansa ta bi tana

kalle kalle har suka shiga cikin bangaren Adeel.

Kai tsaye bangaren Prince Adeel suka nufa cike da mamaki take kallon wajen tamkar wata duniyar a zuciyarta take rayawa, "Oh ba don na san ban mutu ba nace nan shine Aljannata yadda Baffa yake fadamun anya

ma aljannar takai nan ko?"

ADEEL na zaune a parlour ya dan kishingida zama irin na sarauta.

ganin Adnan da Gaaji kawai sai ya tsaya yana kallon su ba tare da ya ce komai ba cike da mamaki.

Adnan ya kalli Gaaji la

ɓ

e a bakin kofa duk alamar tsoro ya

gama tattara game da ita.

Ya ce, "ke ya kika tsaya abakin kofa bakya tunanin za a dake ki ne?"

Fashewa ta yi da kuka.

Ta ce, "Don Allah ni taimaka mun Baffana zai mutu."

Adnan ya juyo yana kallon Prince Adeel ya ce, "Exactly da Mamaki,meyake faruwa

ne? ni dai san zuciyarka irin haka ba."

Prince ADEEL ya bi sa da ido kawai ba tare da ya ce komai aransa yana so ya yi magana,amman saboda isa da Izza irin ta jinin sarautar da ke yawo a jinin jikinsa ya kasa furta komai illa yanayinsa da ya canja na b

ayyanar da

ɓ

acin rai.

Adnan kuwa sanin halin abokin nasa sarai yasa bai damu da shirun nasa ba ya ci gaba da magana.

"Atlest koda zaka daina taimakon al'umma, wannan ya zama taimako na karshe da zaka yi, sai ka ga Ubangiji ya kara buda maka hanyar sa

munka,idan ka taimaki wannan fulani girl din,ba ka san wani hali take ciki ba,da condition din da mahaifin nata ya shiga ba,tunda ka ga har ta nace zuwa wajen biyar, tana zuwa neman taimako baka saurarenta kana wulakanta ta,Don Allah ka taimaka ba don hali

nta ba, kuma ba don ta isa ba,sai Don Allah,da kuma darajarata na abokinka da nake rokonka."

A fusace Adeel ya juyo yana, "Kai Mahaukaci ne,ko mahaifiyata bata taba shigo mun parlour ba,amman kai ka dauko wata kazamiyar fulanin yarinya ta shigo mun parl

our."

Yana gama fadan hakan ya yi shiru.

Adnan ya ce, "Ai awajen Ubangiji da kai da ita duk dayane babu bambanci, kawai dai anan kai mai kudi ita talaka,kai mai mulki ita baiwarka,so shine bambancin kuma ya zame maka dole ka taimaketa."

Rai bace

Adeel ya furta abun da bai taba furtawa ga duk wanda ya nemi taimako gunsa, "BA ZAN TAIMAKA BA, may be ma uban nata mutuwa zaiyi,ka fitar mun da wannan kazamiyar yarinyar daga part."

Nan Shi ma Adnan rai ya baci cikin fushi ya ce, "ba zan fitar da ita b

a,in kanaso ka tashi ka fitar da ita da kanka ta karfi in zaka iya ko kuma ni ka dakeni ka sa in fidda ta."

Girgiza kai Prince Adeel ya yi ya sunkuya yana wuce tare da kokarin danne fushinsa a zahiri.

Sai da suka haura sama sosai, ita kuwa Gaaji ma

maki take tana kallonsa cikin ranta take sakawa daman akwai mutumin da zai iya yiwa dan uwansa mutum fatan mutuwa? Kenan zuwa zaiyi har rugar su ya kashesa? Ban da haka don kawai baffanta na kwance bai da lafiya sai yana yi masa fatan mutuwa? Wani abu take

ji na yawo a cikin ranta na rashin son ganin Prince Adeel

bata san miye tsana ba Amman ji take ta washe sa kamar yadda ta washi mutuwarta.

Shiru suka yi dukan su na yan mintuna

Sai da ya ja numfashi kafin ya ce zan iya taimakonta in ta yarda Amman

da sharadi zan.....

Ya yi shiru nan zufa ta fara keto masa tamkar mai nakuda.

Ya yi shiru.

Adnan ya ce, "Kai muke sauraro fa kuma yi shiru."

Goge zufar da ke kokarin jika masa jiki ya yi ya ce, "Zan... Zan....zan Aureta na tsawon Wata Bakwai kawai

in ta yarda, Ana daura auren zan biya ko million nawa ne a fidda mahaifinta waje a masa magani,sannan duk inda wata bakwai ya yi zanyi signing a takadda in saketa."

Cike da mamaki Adnan ya ce, "Aure? Kuma wannan? Prince,Why?"

Da hannu ya masa alamar

dakatarwa kawai ba tare da ya ce komai ba.

Gaaji ta kallesa ta yi tsalle ta diri tana, "ni? Aure ka? Inma kai mai yankan kai ne ki yanka ni? Cab Allah Saa'anam mi yi

ɗ

a ma. Allah ma ya sutura ni bana shonka."

Murmushi Adeel ya yi yana mamaki wai wanna

n yarinyar ce ke cewa bata sonsa, shi da yan mata ke bi amman wannan kwailar kazamiyar ce ke cewa bata sonsa.

Tashi ya yi ya shige ciki yana, "In ta yi tunani to,in kuma so take Mahaifin nata ya mutu fine wannan ba damuwata ce ba,ban da hadi da shi."

Adnan zai mata magana kenan ko tsayawa batai ba ta fice a zuciyarta tana sakawa,me ma zata yi da wannan wanda yake yiwa Baffanta fatan mutuwa.

da take ji hanjin cikinta ban da kadawa ba abun da suke.

Waige-waige take ko zata samu abun ta

ɓ

awa ban da ru

wan wani kogi ba abun da ta samu.

Haka ta tsaya bakin kogin tasa hannunta ta dibo ta sha sannan ta ci gaba da tafiya.

Tsakanin Rugar Jauro da cikin gari sai anyi tafiya ta kusan minti arba'in ko fi ma wani zubin akanyi awa guda indai tafiyar kafa ne,do

min mota bata shiga Rugar har sai ranar kasuwa kadai sau daya a sati.

Tun tana tafiya da kwarinta har sai da ta koma jan kafa a haka ta isa rugarsu.

Shigewa bukkar su tayi jiki a mace.

Numfashin da taji na tashi sauri sauri a cikin bukkar yasata

saurin karasawa ciki.

Aiko baffanta ne ranga-ranga jiki ya kara tsanani tuni ta birkice ta ma rasa abun yi tamkar za a zare ransa.

Ta kasa yi masa komai ban hawaye da ke ambaliya daga idanunta.

Ficewa tayi da wani mugun gudu.

Tuni har ta manta g

ajiyar da ta kwaso a hanya.

Gudu take ba kakkautawa ta fadi ta kurje ,ta kara tashi bata fasa ba,har saida ta isa cikin gari tsabar sauri a minti talatin ta isa.

tana zuwa kuwa

Bangaren Prince Adeel ta nufa kai tsaye da mugun gudu kasancewar babu k

owa agun.

Tana shiga ta na numfarfashi daga kan da zata yi ta ga abun da kara firgitata tuni jikinta ya dau kyarma.

Price Adeel ne kwance da wata matashiyar budurwa suna Wasanni, babu komai jikin budurwar shi kuwa daga shi sai gajeran wando.

Jikin

ta ne ya fara karkarwa ta kasa motsawa tsabar tsorata bata san lokacin da ta sake fitsari ba.

Sautin Numfashinta na kara fita da sauri-sauri

Dogowan da zaiyi suka hada ido da ita nan fa ta kara firgita ta ja kafa zata gudu.

Wata irin tsawa ya mata yana

janyota, "Mene ne ke kuma?" Ita ma budurwar sai a lokacin ta juyo tana kallonta."

Cikin yanayin firgici ta ce, "Naaa,naaa,naaa ga fada kuna yi ne na zo na fada ma na amince ne,na yarda."

Like, Comments And Share Please

😻🙏

08103080717

Xayyeeshert

hul-humaerath

[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath

🥀

: *AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

*© Xayyeesherthul-humaerath*

Page-3&4

Tashi ya yi daga Kan Safina Yana kokarin janyo rigarsa ya sa.

Ita kuwa wani irin takaicine ya t

urniketa da jin tsana cike da haushin wannan gazamiyar yarinyar da ta katse mata jin dadi, domin har cikin ranta ta gama kudurta cewa lallai yau sai tayi nasarar kasancewa da Prince Adeel amman sai dai kash wannan yarinyar ta hana hakarta kaiwa ga ruwa.

C

ikin kasalalliyae muryarta ta ce, "Prince ina zaka kuma? Me wannan yarinyar take anan kasan fa bamu gama ba kuma?"

Ko kallon inda take baiyi ba take ya shige toilet, ganin hakan tasan sarai ba zata taba samun kansa ba yasa ta tashi ta maida kayanta jiki

nta tana bin Gaaji da wani irin mummunan kallo.

Ita kuwa kanta a kasa bata ma san tanayi ba domin har yanzu jikinta rawa yake,karo na farko da ta fara ganin mace da namiji cikin yanayi irin haka.

Yana fitowa ya sanya riga sannan ya dauki Wayarsa ya kir

a Shamaki ya sanar da shi ya je bangaren Uwar Soro.

Sanan ya kira Adnan ma a waya ya fada masa.

Tashi ya yi sai da yaje har kofa zai fita kafin ya juyo ya ga tana tsaye ya mata alama da hannu kan ta biyosa, sannan ta bi bayansa.

Ɓ

angaren Uwar Soro d

ake daf da bangarensa suka nufa wanda yake shima ke

ɓ

antacce ne ban da Yarima ba mai zuwa in ba da wani babban dalili ba, kasancewarta wacce ta raine shi tun yana karami har kuma ya girma a yanzu babu mai sanin sirrinsa fiye da ita.

Yana shiga ciki Gaaji

ta bi bayansa da mamaki Uwar Soro take binsu da kallo daga shi har gajin cikin sauri ta gyara zama tare da amsa masa sallamar da ya yi.

Yana zama sai ga Shamaki da Adnan sun shigo.

Bayan sun zo duka ban da kallonsu babu abun da Prince Adeel Ke yi.

H

ar cikin ransa yana jin nauyin furta masu abun da ke zuciyarsa ta wani fannin yana jin cewa hakan ba karamin kaskanci bane garesa,amman ya zaiyi? A tunanin sa hakan dai shine kawai mafitar da zai dakile duk wata kofa da ke kokarin bude masa.

Zufa ce ta ci

gaba da keto masa tamkar ba yanzu ya fito daga wanka ba.

Adnan ya ce, "Prince, ka kiramu kuma ka yi shiru Go On Please."

A gajarce ya ce, "Daura mun Aure da wannan Yarinyar za ayi."

Cikin yanayi na Mamaki Uwar Soro ta ce, "Ran Yareema ya dade, Au

re kuma wannan? Ina tunanin in ma itan kake so akwai bukatar a gyarata kuma a Yantata daga baiwa tukunna kafin a gabatar da ita ga MAI MARTABA da FULANI."

Dakin ya dauki shiru na kusan Second Arba'in kafin Prince Adeel ya kara da, "A haka za ayi, ba tar

e da sanin kowa cikinsu ba, kuma a yanzu nake so a gabatar da komai."

Dukkannin su suka koma kallon kallo.

A ƙarshe Adnan ne ya katse shirun da fadin, "Shikenan Shamaki ki kira liman yazo."

"An gama ranka ya dade."

Shamaki ya amsa da haka ya fita d

omin kiran liman kamar yadda aka umarta.

Ba jimawa sai gashi da liman, Adnan ne da kansa ya sanarwa da Liman dalilin kiransa domin ya san in Prince ne zai kara magana sa gaji da zaman jira.

Ba tare da bata lokaci ba Liman ya aiwatar da abun da aka um

arce shi da yi, Adnan ya zam Waliyin Amarya, Shamaki ya zama Waliyin Ango Bisa sadaki Million Uku wanda Adnan ke hasashen ya wadatar a fidda mahaifin Gaaji kasar waje har a kammala masa komai na bukata.

An daura auren amman har yanzu mamaki ya gagara ba

rin zuciyar Adnan domin ya gagara sanin dalilin da zai sa Prince ya ce zai auri yarinyar nan wanda ya tabbatar da cewa koda kyauta aka basa bazai ta

ɓ

a kar

ɓ

a ba, mutum da a kullum ma bijirewa batun aure yake,tare da nuna cewa bai da lokacin tsayawa kula wat

a mata da niyar aure,dole akwai Dalili,to Amman miye dalilin?.

Ana kammala daurin Adnan ya ce da Uwar soro , "Baba zamu tafi yanzu, ki ajiyeta agunki ana yi mata dukkanin abun da ya dace kawai."

Sun tashi zasu fita itama ta tashi tana kokarin binsu

.

Rike mata hannu Uwar Soro ta yi da alamar su tafi Gaaji ta ce, "Aa Baffa, Baffana Yana shen."

Adnan ya juyo yana, "ki zauna anan kinji zamu je akai Baffanki gun mai magani ne yanzu In Sha Allah."

Haka ta bita ba don ta so ba zuciyarta fal tsoro k

ar suje su kashe mata baffa tunda daman Yareema ya fara yi masa fatan mutuwa, ita kuma su cinyeta.

A cikin Part din ta shigar da ita wani dake, dake babban wajene tamkar gida guda wanda ciki da wajensa ya tsaru cikin ƙawa tamkar wata duniya ta daban.

Ko da suka shiga dakin kara binsa da kallo kawai Gaaji keyi tana mamakin kasancewarta a gun shin da gaske nan kuwa duniya ? Cai wannan duniyar inaga dai wacce ake zuwa lokacin da mutum zai bar duniya ne.

Abun da take ta radawa aranta kenan.

Uwar Soro ce

ta katse mata tunani tare da fadin, "Ranki ya dade mu shiga ban

ɗ

aki na ha

ɗ

a miki ruwa zan miki wanka."

Binta da wani mugun kallo tayi tana zare ido, wanka kuma? Ita ai ta jima da manta cewa ana wani abu wai shi wanka,ko da baffanta ke lafiya ma ita sai

ranar sallah kadai suke wanka a rafi da sauran matan karkararsu, wannan shekarar kuwa da yazo bai da lafiya ko yi bata yi ba,bare kuma yanzu da ba sallah ba mai zai kaita yin wanka? Katse tunanin tayi da furtawa a zahiri, "Cab Wanka? Aradun Allah banyi ha

ka kawai ba sallah she tazo ba zaki ce nai wanka? She kace fara?"

Uwar Soro ta ce "Ranki Ya Dade ai ba sai agwagi ne masu wanka ba, hakan tsaftane da tsaftace jiki,kuma kin ga Yareema Baya son kazanta ba za kuna shiri ba in bakya wanka zai ce ma baya

sonki."

Gaaji ta cuno baki ta ce, "Ni bana shon shi daman ai tunda yake yiwa Baffana fatan mutuwa kuma sai dai shi ya mutu ya bar mun baffana raye."

Dakyar ta samu ta shawo kanta tare da Tabbatar mata cewa in bata yarda an mata wanka ba Yareema ba za

i kai Baffanta a masa magani ba.

Suna shiga Toilet din ta fara ihu tana, " nan ai ba gun wanka ne ba ni ki barni kawai ai Dau

ɗ

a karin karfine karki ragemun karfina a dakeni in kasa ramawa."

Uwar Soro ta ce, "nan ne ban dakin wanka anan duk haka suke,

kuma in kika yi wankan ma kara karfi zakiyi saboda muna da sabulu mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login