Showing 12001 words to 15000 words out of 17483 words

Chapter 5 - AUREN WATA BAKWAI COMPLETE

/>
Tana ganinsa ta bata rai, "Ni nayi fushi,na daina Shonka kuma ma mun kunce." Ta karasa maganar tana mika masa hannu alamar su kunce.

Durkusawa gabanta Ad

nan ya yi ya kama kunnen ya ce, "Afwan Gaaji Beauty kin ga na kama kunne na ko sai na mari fuskata?"

A shagwa

ษ“

e ta ce, "E amman kar ka mara da zafi a hankali kuma sai kace zaka goyani yadda baffana ke mun,kuma zaka na zuwa guna da wuri."

Marin fuskar

sa ya yi yana dariya ya ce, "To na mara kuma zan goyaki in mun fita, sai kuma me zan yi yanzu ? Kin ga bakiyi murmushi ba."

"Umm umm ni na daina ma murmushi ai kuma?" Gaaji ta fada.

Adnan ya ce, "in dai bakiyi murmushi ba,to ni kuka zanyi ma."

Da

sauri tayi murmushi tana, "tom nayi kar ka yi kuka."

, "yawwa Good girl bara in nuna miki wani abu sai mu tafi ko."

Ta ce, "Guduo gu ."

Dariya Adnan ya yi ya ce, "ni fa ba gudou gu bane, Good Boy zakina cewa."

"Tom Gudu bu."

Dariya yayi kawai

yana girgiza kai.

Wayarsa ya ciro ya danna video call A WhatsApp likitan da ke kula da baffanta ne ya daga suka gaisa sannan ya bukaci da anuna masa shi.

Nuna wayar ya yi inda Baffan Gaaji yake, yana barci hankalinsa kwance jikinsa har ya fara canja

wa.

Tsabar mamaki Gaaji ta kasa magana kusan minti daya kawai ta washe baki tana kallon baffanta nan take Farinciki ya gama bayyana a fuskarta ta ce,

"Baffa am Noi

ษ“

anduma? Volwunam,. Anani koi

ษ—

um ko?a umman a vawami ko? (Ya jikinka? Ka yi mun magana ma

na, ka ji sauki ko? Zaka tashi ka goyani?)."

Ta ka baiyi magana ba kallon Adnan ta yi ta ce, "Ka ce ya mun magana ina sho nayi magana da shi."

Adnan ya ce, "ba ki ga barci yake ba? Tunda aka masa aiki bai farka ba sai ya huta sosai inya farka sai mu ka

ra kira ko." Ya karasa maganar yana yiwa likitan Sallama ya katse wayar.

Gaaji cikin yanayin Farinciki ta ce, "Baffana zai ji sauki."

Adnan ya ce, "In Sha Allah yanzu ta shi muje."

Suka shiga Parlourn Uwar Soro suka mata sallama sannan suka fita

tare.

A mota ya sata tana ta kalle-kalle da tabe ya koma yawa Yareema magana.

"In ba abun da kake,kadan raka ni wani waje mana?"

"Okay." Kawai Yareema ya amsa.

Ya canja kaya ya fito.

Yana zuwa ya shiga gaban motar, Adnan ya ja su suka dau hanya

.

Daga kansa da zaiyi a madubi ya ga Gaaji nata washe baki.

, "Adnan! Kana cikin hankalinka kuwa, Wannan yarinyar fa?"

Adnan ya ce, "Za muje SHOPRITE ne ta sha iska taga abubuwa sannan kuma ina so in mata siyayyan kayan sawa."

"Me zai sa baza ka

bada a siyo ba har sai mun fita tare?" Prince Adeel ya fada.

Kafin Adnan ya yi magana karaf Gaaji ta ce, "Ehdin sai anje dani din ina ruwanka ai shi ba dan ishka irinka bane kuma ina shon shi."

Dafe kai Adeel ya yi don takaici yama rasa abun fada.

A

dnan ya ce, "zuwa da kanmu da itan ne zaifi wani inya fita da ita za a iya samun matsala."

Daga nan Adeel bai kara cewa komai ba,ban da zafi ba abun da kirjinsa ke yi masa ji yake kamar ya dauki Gaaji ya jefar tsakiyan titi domin ya tsani rashin kunya a

rayuwarsa,ita kuma ga bakinta kamar barin jinin magana da rashin kunya yake.

Ihbb

Ita kadai da Adnan suke ta surutunsu har suka isa SHOPRITE din.

Tare suka fita duka, suna shiga Suka fara cinkaro da irin Manyan Teddies dinnan da mutane ke shiga ciki.

Ganin abu kamar mutum yana motsi da rawa yasa gaaji ta rikice tuni ta rufe ido tana ihu bata san lokacin da ta kankame Prince Adeel ba.

Saukar wani zazzafan mari kawai taji a fuskarta

Comments,like & Share Fisabillah.

08103080717

[8/9, 12:24

PM] Xayyeesherthul-humaerath

๐Ÿฅ€

: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o

*AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

ยฉ *Xayyeesherthul-humaerath*

Page-15&16

*Na ce ko zaku ramawa Gaaji marin ne? Na lura kun hasala da yawa

๐Ÿ˜‚

to me

ya hwaru ne?

๐Ÿคฃ

*

โ˜…โ˜…

Marin ya shiga jikinta sosai sai da taji canji tun daga kwakwalwar kanta har kafa, wani guntun suma ne ya risketa take hannunta rike da kumatu ban da hawaye ba abun da take kwalalarwa, tuni fuska ta damule da hartsin majina da hawaye

n dake artabu,Tsigan jikinta duk ya tashi daga nesa ana iya fahimtar cewa ta shiga wani yanayi da ya firgitar da ita.

Adnan ya ce, "Haba Prince? Wai me yasa kake yiwa yarinyar nan abubuwan da basu kamaceta ba, Don kawai ta rikeka sai ka mareta?"

Pri

nce Adeel Muhammad Rohaan Idanunsa sun fito sosai wanda ya kara bayyanar da bacin ransa karara wanda ana iya jiyo sautin bugawan zuciyarsa.

Kau da kai ya yi ba tare da ya takanwa Adnan ba ya koma mota kawai.

Yana shiga ya dafe kansa yana wani irin huci k

aman bijimin Sa.

Adnan ya kalli Gaaji tausayinta ne ratsa masa zuciya a sanyaye ya ce, "Ki yi hakuri kinji ba zai kara marinki ba,bude idonki."

Ya karasa maganar yana miki mata hankicif ta goge fuska.

A hankali ta bude idanun domin har yanzu taurari

basu daina yi mata shawagin zafin marin da taji ba.

Cikin shashshekar kuka ta ce, "Mu gune ,kuma Allah zai saka mun,mai Idon kuliya kawai ni ba ruwana da shi."

Adnan ya ce, "Naji dai yanzu share hancinki muje ciki in siya miki kayan kawai sai mu koma g

ida ko?"

Ta girgiza masa kai tana share hanci, tana gamawa suka shige cikin SHOPRITE din, tare suke Adnan ne da kanshi ke za

ษ“

a mata kaya, tana bin bayansa da kalle-kalle, Wani Pad ta gani kato ta dauka ta na, "Aboki ka siya mun wannan burodin zaiyi dadi

ko? Baba Uwar Soro na bani irinsa ai."

Adnan na karba ya ga Pad ne maimakon Bread din da take fada ya ce, "Aa fa wannan ba Bread bane Gaaji wani abunne daban."

"To mene ne in ba burodi ba? Aradun Allah burodine ai ko lokacin ma da Baffana yana siyom

in in ya shigo birni nidai ka siyamun." Ta fada tana ta

ษ“

e fuska.

Adnan ya karba kawai yasa cikin besket din ba tare da ya ce komai ba.

Kara dauko wasu guda biyu tayi ta ce, "Yo ai Aradu wa inshen sunmun kadan akara wa innan su zama uku yau inta shin ab

una in ji dadi."

Shi kam dai bai ce mata komai ba tasa a ciki.

Kaya ya za

ษ“

a mata daidai wa inda zasu mata dogayan riguna da wasu mini hijab, chocolate ,sweet da su biscuit ma kamar wa inda zasu bude provisions ban da washe baki ba abun da take tana jin

dadi.

Saida suka gama tas kafin suka koma mota, Prince na ciki yana danna waya, sai da Adnan ya budewa Gaaji ta shiga sannan shima ya shiga, tana shiga tayi tsaki da kwafa, ganin Adeel bai ma san tana yi ba ta dunga dage tana harararsa da murguda masa

baki.

Kamar ance ya kalli morrown gaban motan suka hada ta takarkare tana murguda masa karamin bakinta ta ko ina a fuskarta ba inda baya motsi.

Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba don ya fara fahimtar Indai ya biyewa wannan yarinyar sai ta maidasa

karamin mahaukaci.

Kan su isa Fada an fara kiran sallan magriba, haka yasa Adnan ya na aje mota ya bude mata cikin sauri ya ce tazo ya maida ta ciki gun Uwar Soro tun kafin wani ya gansu.

Ita kuwa Gaaji tsayawa tayi lallai fa sai ta ci gaba da murgudawa

Adeel baki kan ya fito a motar taje tana kokarin tura kanta daidai da lokacin da yake kokarin turo kofar ya fito bai na ganta ba.

Da sauri Adnan yaja hannunta yana, "kina so muyi fada ko? Baki ga lokacin sallah ya yi bane? Oya muje ki shiga ciki muma zamu

shiga Masallaci."

Shigewa tayi da tarin ledar kayanta guda biyu tana juyowa tana daga masa hannu a dole byeebyee.

Aiko tana shiga ciki ta baza kayan nan kaf a kasa tana murna take ta cire kayan fulaninta tasa wata Abaya ta mata kyau Sosai, Uwar So

ro kuwa binta da kallo take kawai na mamaki ganin yau da kanta ta cire kayan Gadonta tasa wani ah lallai Gaaji an fara canjawa.

Ita kadai tana ta sambatu, "Ai aradu ba a tabani a zauna lafiya She na gyarawa mutum hankali tunda shi an ishka ne kuma mugu,

Shi kam Abokina ba ruwansa Dan albarka she siyamun kaya yake."

Pad dinnan ta ciro ta jera gabanta tana, "Yawwa wannan Burodin zanci yau Baba ba zan ci abinshinki ba abokina ne ya sayo mun mai dadi."

Uwar Soro ta ce, "Mu ga Burodin naki Gaaji."

Tash

i tayi tana yage ledar ta ce, "Kadan fa zan sammaki ba duka ba ,zan shi abina duka ni kadai."

Uwar Soro na karba ta ce, "Wannan ai Audugace ba burodi ba."

Gaaji ta karbe abunta tana, "Audugar me? Burodi ne fa aboki ya siyamun."

Dariya Uwar Soro ta

yi ta ce, "na san dai kin fara al'ada to Da kika fara jini na fito miki da me kike amfani lokacin kina Ruga?"

Gaaji ta ce, "Ni tsumma nake sawa in tare sai ranar da naga jinin ya dauke sai in Jefar a shara."

Da sauri Uwar Soro ta riketa ta ce, "Subh

anallahi to wannan abun ake sawa ba tsumma ba,kin san tsumma kuwa cuta yake sawa? Zai saki ki yi tsutsa,yana fito miki kuma kina wari a karshe ma ki mutu."

Nan take Gaaji ta gwalalo ido tsoro ya gama cikata.

Uwar Soro ta ci gaba da cewa, "Kin ga shi wann

an kullum ma in kina yi a kalla sau biyu ko sau uku ake so kina canja wani,da zaran ya baci ko ya dan dau lokaci ake cirewa saboda gujewa shigar wata cuta kinji ko?"

Jikinta ya yi sanyi ta ce, "ni kam ba zan kara sa tsumma ba kar inyi tsutsa Ysn ba ruwa

na na daina, tun yanzu ma zansa wannan din ya fara taremun kafin ya zo."

Uwar Soro ta yi Murmushi tana, "Aa ai sai yazo ake sawa yanzu zan boye miki kinji baza ki yi tsutsa ba In Sha Allah."

Saida Adnan ya dawo ya mata tatsuniya kafin tayi barci kuma

ya tafi.

โ˜…โ˜…

Khalesa ban da zabga kira a waya ba abun da take yiwa Adeel ya ki dauka da ta gaji kawai sai ta nufi bangarensa tana zuwa ta tatarar da shi tsaye da Nasmah suna magana.

Wani irin kallon raini ta bi Nasmah da shi, ita ma ta maida mata da

kallon tara saura kwata.

Karasa tayi daf da Adeel ta ce, "Prince na zo gunka ne fa kuma na ga wata."

Adeel ya ce, "Nasmah ce ai dukan ku

ษ—

ayane."

Cikin bacin rai Khalesa ta ce, "Aa wallahi ni da ita ba

ษ—

aya bane kama daina ha

ษ—

amu ko a shekaru na fi

ta bare kuma batun kasancewa gareka muna da tazarana matsayina daban nata daban, so ta bani waje ina so inyi magana da kai."

Nasmah tayi murmushi kawai tana kallonta.

Prince Adeel ya yi shiru shima ba tare da ya ce komai ba sun maidata fanko kawai.

A har zuke ta kara fadin, "Magana fa nake, ke Nasmah wai ba kyajine? matar sa na son yin magana da shi?"

"Matata?" Yareema ya fada cike da mamaki fal a fuskarsa.

"Eheen ko ka manta ne?"

Khalesa ta fada cikin isa.

Ya ce, "ke da ita duk dayane du

k abun da zaki fada ki fada gabanta zai fi miki."

Wani irin fusata Khalesa tayi tana sakin tsaki ta kara bin Nasmah da wani kallo tare da yin kwafa,ita kuwa Nasmah gwalo ta mata da wata irin dariyar mugunta.

Nasmah na ganin Khalesa ta tafi murya a ra

unane ta ce, "Na dameka ko Prince? Sorry Gudnyt ka je ka kwanta ka huta gobe kawai mayi maganar ko Lokacin da kake free ka kula da kanka."

"Alright thanks." Ya fada kawai ya shige.

Sai da taga shigewarsa sannan ta tafi tana sakin murmishin da ita kad

ai ta san Dalilin sa.

โ˜…โ˜…โ˜…

Misalin karfe Tara na safe Gaaji ta sha wanka ta karasa kaya da

ษ—

aya cikin wanda Adnan ya siya mata sau juyi ake, ranar ba fada ta tsaya aka mata wanka tayi brush da kanta, wanke dambun gashin ta ne dai har yanzu taki Yarda Uwar

Soro ta taba bare a wanke mata shi.

Daukan hanya tayi bijigun-bijigun zata fita, Uwar Soro ta ce, "Ina zuwa?"

Tunani ta tsaya yi ta tana sakawa a zuciyar ta indai ta fadawa Uwar Soro asalin abun da zata yi bazata barta ba , can sai ta washe baki ta ce

, "Zan ni in nunawa abokina Adona ne ns irin kayan yan birnin da ya shiyamun inshe mishi na gode."

Uwar Soro ta ce, "to kardai kiyi wani gun kina fita ki shiga can in ba haka ba ana kamaki yanki ki za ayi na fada miki."

Gaaji ta ce to sannan ta fice.

Bin bayanta Uwar Soro tayi saida ta tabbatar ta shiga bangaren Yareema kafin ta dawo nata bangaren.

A hankali ta tura kofar ta shige.

Tana shiga kuwa taga Yareema na barci hankalinsa kwance daga shi sai gajeran wando.

Ta ce, "Ji an ishka barcinm

a ba kaya yake yi aiki yau zaka shi gidanku aradu."

Ta karasa gabansa a hankali tana zuwa ta sake masa mari a kumatu tauuu ta kara sake wani tauuu.

Yareema ji ya yi kamar a maraki ana zabga masa wasu irin zafafan maruka.

Ya yi saurin bude idonsa ya gant

a tsaye kansa amman ya kasa gasgata hakan.

Rike hannu tayi a kugu tana fadin, "Kalle ni da kyau mai idon mage nishe nan Zainabu Gaajin Baffa ramawa na zo yi na rama marin da kamun ehee kai ma Kaji inda Dadi ai da wani wandon ka kamar nafkin."

Sai a lok

acin ya tabbatar da a zahiri yake kokarin tashi ya fara a fusace.

Ai Gaaji da taja dogayen kafafunta masu kama da sandar sunuka sai waje.

Tashi ya yi ya.........

*TO FA FREE PAGES NA DAF DA KAREWA SAURA PAGES BIYU IN SHA ALLAH, ZAKU IYA FARA P

AYMENT YANZU โ‚ฆ300 KACAL VIA 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717*

Luvs U Oll

๐Ÿ˜˜

๐Ÿซถ

๐Ÿ’ƒ๐Ÿ˜ป

[8/9, 8:47 PM] Xayyeesherthul-humaerath

๐Ÿฅ€

: *AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

ยฉ *Xayyeesherthul-humaerath*

Page-17&18

Cikin Fushi zai fita har sai da yaje bakin kofa ya tuna da gajeran wando ne a jikinsa, tsaki ya yi ya koma,yana zura jallabiya ya fita zuwa bangaren Uwar Soro.

Gaaji na ganin shigarsa da gudu ta koma bayan Uwar Soro tana kankameta, "

Baba Wallahi shin zalina zai kara yi don kawai na rama marin da ya mun."

Bude baki Uwar Soro tayi da mamaki tana kallon Gaaji ,Don ita a iya saninta babu wani mahalukin da ya taba dagawa Yareema hannu,bare kuma batun mari, ah lallai Yar nan kin taro ruw

a.

Ta fada aranta.

Yanayin yadda yake huci ita kanta Uwar Soro ta razana ta yadda ta kasa ce masa uffan.

Gaaji kuwa kara kankameta take tana, "Aradu mugune karki bari ya ta

ษ“

ani zai kashe ni."

Ji tayi kawai ya dauketa cak.

Ya fice da ita,ba direta a

ko ina ba sai kofar wani kurkukun daki, karami, mai bala'in duhu mutum baya iya ganin ko hannunsa a ciki, jefata ciki ya yi ya rufe kofar sannan ya koma dakinsa.

Nan take Gaaji ta birkice, Wani irin kuka take tamkar ba mutum ba, ta gama ficewa a hayyaci

nta, kayanta duk ta yayyaga su da fisga,gashin kanta ma sunyi carko-carko, tana ta fisga cikin lokaci kalilan ta dawo mahaukaciya.

Uwar Soro kuwa Tana ganin Prince Adeel ya shigar da Gaaji dakin nan hankalinta ya matukar tashi,tasan Manya ma aka shiga

r da su ya suka kare bare kuma mutum? Dakin da babu ko windo bare wani sakon da haske zai

shiga, nunfashi ma mutum na ciki in ya dau lokaci dakyar yake iya yi, wasu ma kan a cirosu sun mutu.

Ganin bata da wata mafita yasata saurin kiran Adnan ta sanar d

a shi halin da ake ciki, Wayar Adnan sam bata shiga domin ya tafi India gun aikin Baban Gaaji Ya duba yadda lamuran ke gudana, kuma daga nan zai koma America domin yin wani bincike da yake.

Tun tana gwada kiran har ta gaji ta hakura, domin babu alamar s

higa.

Adnan ya sanar da shamaki cewa bai yarda wani yaje Gaaji take ba sai shi,kuma shi ma din ruwa kadai zaina bata kada a kuskura a bata abinci.

Gaaji tun tana ihu har ta gaji ta daina ban da ajiyar zuciya babu abun da take,kamar wasa har dare ya y

i,ya tabbata dai sai da ta kwana adakin, duk da cewa ita batasan dare ko rana ba saidai wani lokacin kawai ta ji barci ya dauketa, inko ta farka ma duk daya tunda duk abu

ษ—

aya idonta ke gani wato duhu,barcinma tana farawa wasu irin samudawan sauro zasu ish

eta da kuka a kunne, a jiki suna cizo, ya zamana bata da aikin yin da ya zarce kuka.

Uwar Soro ce ta roki shamaki da ya taimaka yana bata abinci ko da kadan ne ba tare da sanin Yareema ba, tunda ita ma ya ce ba ruwanta kada ta bari a hannunta ya shiga c

iki,hakan kuwa ya kasance a boye kullum yake bata abinci da ruwa.

Gaaji na cin abinci tana kuka,laluba take domin ko bakinta ma takan iya rasawa wani abincin ma kan ya shiga bakinta ta zubar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login