Showing 6001 words to 9000 words out of 17483 words

Chapter 3 - AUREN WATA BAKWAI COMPLETE

suke,na shiga ukuna na mutu na lalashe ki bani abunshi inci ka

r in mutu."

Ta ƙarasa maganar tana birgima akan gadon harda rike ciki kamar mai nakuda.

Uwar soro ta ce , "Oh ni Jummai na gamu da gamona, ga shi zan baki kici amman kimun alƙawari in kinci zakiyi duk abun da nace kiyi kin yarda?"

Ta girgiza kai.

Mika mata tayi, tuni ta fisge ta fara ci kamar tsohuwar mayunwaciya.

Sai da ta cinye tas Uwar Soro ta ce, "Yawwa yanzu bara in dauko miki zani ki cire kaya muje bandakin ko."

Uwar Soro na shigewa dayan dakin ta kalli gefe da gefe taga ba kowa da gud

u ta fice ta shige bangaren Prince Adeel.

Tana shiga ya fito daga wanka kenan yana zaune yana shafa mai ya zame towel din jikinsa babu komai a jikinsa.

Tana shiga tana ganinsa da ta kwallara wani ihu....

*DUK WACCE KE SO TA BIYA A MATA ADVERT A

PAGES KOFA A BUDE TAKE YI MUN MAGANA KAI TSAYE TA NAN 08103080717*

Urs Xayyeesherthuo

[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath

🥀

: https://chat.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o

*AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

© *Xayyeesherth

ul-humaerath*

Page-7&8

Rufe idonta tayi tana kankame jikinta tamkar zata suma ta wata irin gigitacciyar ƙara.

Prince Adeel ya kalleta ya kauda kai,yaja towel din sa ya daura, yana kokarin sa kaya,ci gaba da ihun tayi kamar wacce aka sawa saban

batir, har cikin Dodon kunnensa yake jin saukan kararta.

Cike da takaici ya karasa inda take yana daka mata tsawa.

Maimakon ta nutsu tsawar da ya mata yasa ta ci gaba da kwallara ihu tana kokarin shidewa.

Rufe mata baki ya yi da hannunsa yana mata

alamar tai shiru.

Ita kuwa ido ta kafa masa suna kallon juna,aransa yana sakawa , "Anya wannan yarinyar na da hankali kuwa? Watakila ma mahaukaciya ce ga dukkan alama."

Ita ma a zuciyarta ta ce, "Cab lallai wannan ƙasurgumin Dan ishka ne,kawai ya zauna

tsirara ba kaya, Aradun Allah watarana na kara ganinsa haka nan sai na yanke masa wannan jelar mai kama da beraye."

Kusan Minti Daya suna haka kafin ya saketa yana sauri ya shige toilet zuciyarsa na tashi, wanke hannunsa ya yi ,yana jin kyamarta dama b

ai kai hannunsa bakinta ba don gabadaya yanzu a tsarge da kansa yake.

Har zai fita , haka ya koma ya kara wani sabon wankan Amman duk da haka hankalinsa bai kwanta ba,hannunsa ji yake kamar har yanzu da yawunta a jiki.

Ita kuwa yana saketa,ta falfala a

guje ta koma bangaren Uwar Soro tana haki kamar wacce ta dibo kaya.

Da sauri ta riketa tana, "Ya Salam, Gaaji ina kika je? Ba wanda dai ya ganki ko? Ki daina fita in kina fita kamaki za ayi a kulle."

Gaaji ta ce, "Ni fa gun Yareema naje in ce masa

ina Baffana ya jikinsa, shine fa kawai na gansa a tu

ɓ

e aradun Allah Yareema dan iska ne ashe, kin gansa kamar wani Dodo cab."

Uwar Soro ta ce, "Kul kada in kara jin hakan a bakinki kinji."

Cuno baki tayi tana, "To wayace ya zauna ba kaya,ai yan iska

ne ke zama tsirara dai ga shi fa wani katon garde da shi abun tsoro ni Allah sa ma kar nayi mafarkinsa in kasa barci."

Ta fada tana rufe idonta.

Uwar Soro ta yi dariya kafin ta ce, "Na ji dai, daga yanzu in zaki je bangarensa kina fadamun kuma sai kin

kwankwasa kofa ya baki izinin shiga kafin ki shiga."

"Ni ban kuma zuwa masa ma inje inga abun da zai makantar dani in daina gani ana cemun makauniya, Shikenan in kasa ganin Baffana." Gaaji ta fada tana dafe ha

ɓ

a.

Rike mata hannu Uwar soro ta yi tana,

"to na ji, yanzu kizo muje in miki wanka, kuma kin ga wannan kan naki ma dole a wankesa arage masa Dauda a gyara sai in miki kitso."

Take Gaaji ta bata rai tana hada girar sama da ƙasa ta ce, "ni fa nace miki bana shon wankan nan bana sho nikam fatar j

ikina zata zama roba, kuma ta dafe."

Uwar Soro ta ce, "Ba zata dafe ba fa zata yi kyau ne tafi yanzu haske kuma karfin ma zaki kara ne,ki zama yan mata Sosai."

Uwar Soro ta ce, "aiko in baki yarda anyi wankan nan ba bake ba abincin Rana irin me dadin

nan."

Ko magana Gaaji ba tayi ba ta fara cire kaya tukun ta ce, "Mu je kin ji, Wallahi ba zan iya zama da yunwar ga ba,gwanda kawai ayi wankan nikam na hakura fatar ta ta kodewa karfin ma ya tafi amman dai abani abinshin in ci Don Allah."

Da kanta t

a shiga toilet din,Uwar Soro ta mata wanka, ta dan wanke mata gashi aka rage masa dauda dan ba za dai ace ya fita duka ba, dan kwana biyun nan har ta fara chanja kala haskenta da ya dafe dan dauda har ya fara dawowa kyanta na asalin bayyana.

Dole wasu k

ayan Fulani Uwar Soro tasa aka nemowa Gaaji domin duk kayan da ta bata tasa cewa take ita bazata sa ba,ba shine kayan su ba.

Yau ya kasance ranar Juma'a wacce ta kasance a kowacce Juma'a Yareema na zuwa su gana da Mai Martaba kafin su shiga Masallacin

Fada suyi sallah tare.

Hakan ne ya wakana kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya ,Shamaki na tsaye yana jiran fitowarsa yana fitowa suka nufi Cikin Fada tare.

Bayan Shamaki ya raka Yareema fada dukansu suka fice waje kamar yadda aka saba.

"Barka Da S

afiya Ranka ya dade." Cewar Prince Adeel.

Mai Martaba ya ce, "Barka dai Yareema, ina fatan komai yana tafiya daidai ba tare da wata matsala?"

Prince Adeel ya ce, "AlhmduLillah komai na tafiya daidai kuma abisa tsarin da ka umarta."

Mai Martaba ya sa

ki murmushi kafin ya ce, "Ma Sha Allah, wato kaidai ba zaka taba barin wannan shigar kasar wajen ba, ka riga ka gama sabawa da hakan ko ince kafi jin dadin hakan ko?"

Shiru Yareema ya yi kansa a kasa yana sakin Murmushi.

Mai Martaba ya ce, "Kodayake

nima nayi na gaji na hakura watarana da kanka zaka daina sawa har ma ka manta da yadda ake sawan."

Shi dai Yareema bai ce komai ba sai Murmushi.

Shi kuwa Mai martaba kara jin so da kaunar

ɗ

an nasa

ɗ

aya tilo a duniya yake har cikin ransa, a zuciyarsa sh

i ma bai da muradin da ya zarce ace Yareema ya yi aure ya haifa masa jika ya gani tun yana raye,amman sam baya iya masa maganar hakan aransa ji yake cewa haka ba karamin takura bane,kuma babu abun da yafi so fiye da farincikin Yareema zai so ace da kansa y

a ji sha'awar kasancewa mai iyali.

Sun dan taba hira daidai gwargwado kafin suka nufi masallaci suka saurari Huduba sannan suka yi sallah.

★★

Nasmah na Tabbatar da cewa an idar da sallah ta nufi kitchen kai tsaye ta ce wa Magajiya, "Ina abincin Yareem

a?"

Magajiya ta ce, "ga shi can ina jira Uwar Soro ta turo a daukan masa ne."

"Aa ni zan kai masa yau,ya ce in kai." Ta karasa maganar tana kada kokarin daukan abincin.

Daga nesa taji tsawar Khalesa na fadin , "Dakata! Kada ki kuskura ki yi gigin

daukan Abincin Yareema domin yau Ni nake da alhakin kai masa."

Nasmah ta ce, "What? Ban gane kamar ya?"

Bige hannun Nasmah, khaleesa tayi akan tiran abincin tana janyewa, "eheen abun da kunnenki suka jiyo shi nake nufi, Ai Babban Ɗa Sai babbar 'Ya ka

mar yadda nake Babbar 'Ya mace a Masarautar nan haka zan kasance mata ga Yareema atakaice dai Gimbiya duk da kin sani gwanda in kara jaddada miki don kuwa na lura da cewa kunen kashi gareki."

Ta karasa Maganar tana kare mata kallo sama da kasa tana wani

irin juyi.

Magajiya ta ce, "Amman dai dukanin ku kun san cewa babu mai alhakin kaiwa Yareema abinci ba tare da izinin Uwar Soro ba ko?"

Khalesa ta ce, "agunki kenan don ni ai a yanzu nafi Uwar Soro kusanci ga yareema zan gansa a lokacin da na so kum

a nayi niya Don haka ni zan kai abincin Yareema ba wanda ya isa ya hanani kaiwa."

Nasmah ta ce, "ai bai zam mallakin ki ba a yanzu Don haka kowacce na da hakkin amfani da damarta duk wacce tai nasara shikenan." Ta karasa magana tana kokarin fisgewa.

Wani azababben mari Khalesa ta sake mata a afuska da sauri Magajiya ta karasa inda suke daidai da lokacin da Jakadiya ta shiga kitchen din.

"Kai kai kai.. mai zan gani haka me ke faruwa ne?" Jakadiya ta fada.

Nasmah na kuka ta ce, "na zo daukan abinc

in Yareema ne zan kai masa Khaleesa ta kwace wai ba zan kai ba kuma ta mareni."

Khalesa ta ce, "Karya kike karamar munafuka."

"Aa fa ba ayi haka ba kema dai Nasmah kin fiye tsaurin ido taya Khalesa zata kaiwa Yareema abinci kice ke zaki? Ai ido ba m

udi ba amman yasan

kima,ita da muke fata nan da kwanaki kadan muji ta zam gimbiya, aa aa Maza Khalesa je ki kai wa Yareema abinci."

Kuka Nasmah ta kara fashewa da shi ta fice da gudu a kitchen.

Khalesa tayi tsaki tana, "Kya yi kya gama Yareema dai ka

m nawane." Suka hada ido da Jakadiya suna sakewa juna Murmushi.

Nasmah na zuwa ta fada jikin Hajiya Maimuna tana kuka tana fada mata abun da Khalesa da da Jakadiya suka yi mata.

Hajiya Maimuna ta share mata hawaye tana murmushi, "Hakanne ya saki kuka?

Mene ne na kuka akan haka? Lallai baki tanadi zuciyar da zaki tallafi soyayyarki ba, ki zam jaruma,mai maida komai ba komai ba koda kuwa komai dinne,ki sa aranki cewa indai Yareema mijinki duk rintsi duk wuya babu fashi sai ya kasance naki, rabon kwado ai

baya taba hawa sama,ko ya hau ma dole ya fado, don haka ki kwantar da hankalinki."



★★

Fita tayi tana tafiya tana rangwada tamkar bazata taka kasa ba,tana zuwa Tayi Nocking shiga bangarensa, Shamaki ya fito ya sanar da ita yana barci ta bada abincin a a

jiye masa.

Khaleesa ta ce, "ka tashesa ka ce nice ina son ganin sane Don Allah."

Shamaki ya ce, "Kin san dai in ba wani uzuri babba ba ba damar tada Yareema a lokacin da yake hutawa mussaman rana irin ta yau."

"Ni dai Don Allah yau kadai amun wann

an alfarmar."

Komawa ciki shamaki ya yi,ya yi dace kuwa yana zuwa ya tarar da Yareema zaune yana danna laptop ga dukkan alamu yana duba wani abu mai mahimmanci ne.

Shamaki ya ce, "Ranka Ya dade Khaleesa ce awaje ta kawo ma abinci."

"To ka karba m

ana."Yareema ya fada hankalin sa na kan system din dake gabansa.

Shamaki ya kara da, "Aa ta ce wai kai take son gani abata izini ta shigo."

Da Okay kawai Yareema ya amsa, Shamaki ya fita ya cewa Khaleesa ta shiga.

Tana shiga ta ajiye Abincin kan d

aining sanan ta karasa daf inda yake ta zauna tana, "Good Afternoon Darling Prince."

"Afternoon." Ya amsa kawai.

Shagwabe fuska ta yi tana, "I Call You but you didn't pick Why?, i just want to hear Your Sweet Vioce, nikam ko laifi Nama ne?"

Tana

ta surutun ta yana ji amman hankalin sa baya kanta kuma bai da niyar bata amsa.

Ta ci gaba da magana. , "Wai yaushe zaka gabatar masu da cewa nice za

ɓ

inka ne? Nikam na matsu ina so ayi adaura mana aure."

Sai a lokacin ya juyo ya kalleta cike da mamaki

ya ce, "Aure? Dawa?"

"Da kai mana, ka san dai nice babbar 'Ya mace kamar yadda kake namiji So mu muka fi dacewa da juna ni yanzu ma da zaka barni dawowa nan part din zanyi ya yi mun kyau gaskiya in munyi aure zanji dadin zama anan Sosai."

Ganin bai

da niyar kara kulata ta fara mannewa a jikinsa tana magana cikin sanyayyar murya.

Prince Adeel ya yi saurin.......

Comments,Share&Like, Fisabillah.

😻🙏

08103080717

Urs Xayyeesherthuo

[8/7, 9:47 AM] Xayyeesherthul-humaerath

🥀

: https://chat

.whatsapp.com/C1kXo17nLmb7vCXlubtu5o

*AUREN WATA BAKWAI*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

© *Xayyeesherthul-humaerath*

Page-9&10

Ya yi saurin kauce mata yana zame jikinsa.

Kara damƙosa tayi ta ce, "Please Just Once Prince."

"Stop it, i said

stop it Nasmah, bana so ki je Ki tafi Don Allah inna gama aiki zan nemeki da kaina."

Murya a shagwabe ta ce , "Promise?"

Girgiza mata kai ya yi kawai yana gyara zamansa.

"Alright ga abincin ka nan byebye." Ta fada tana kokarin fita.

Har taje bakin

kofar ta dawo, rungumesa tayi tana kissing dinsa sannan ta ra

ɗ

a masa a kunne, "For me, you're like a lethal deadly drug. Once taken, you're addictive,I Love You So Much Darling Prince."

Ta karasa maganar tana kara kai masa kiss ta fita tana sakin wani

irin ƙayataccen murmushi.

"Yes, komai ya kusa tafiya daidai, burina zai cika Soon To Be Mrs Adeel Muhammad Rohaan (Gimbiya)"

Ta fada fuska fal farinciki.

Ci gaba da aikinsa ya yi hankalinsa kwance.

Adnan ne ya shigo dakin yana fadin, "An kammala ko

mai fa kan Baban Zainab har ma an fidda shi India komai da ake bukata ina tunanin an samu."

"Okay." Kawai Yareema ya amsa da shi.

Adnan ya kara fadin, "Ina take ne? Ta zo nan kuwa? Amaryar tamu." Ya karasa maganar cikin sigar tsokana.

Da harara Yare

ema ya bisa da shi yana, "Mahaukaciya dai." Daga nan ya yi shiru ya ci gaba da abun da ke gabansa.

Dariya Adnan ya yi, ya fice yana, "Haka dai ka gani kana so bara ma inje mu gana in gaida Gimbiya Matar Yareema."

Bangaren Uwar Soro ya nufa yana shiga

kuwa ya tarar da Gaaji zaune ta baje Uwar Soro ta aje mata wasu manyan teddies ban da sambatu ba abun da take masu.

Tana ganinsa ta mike tana rike ha

ɓ

a, "ka kawo mun Baffana ne? Ya ji sauki dai ko? Ina yake? Ka kaini gunsa in gansa ka ji."

Adnan ya ka

rasa gareta yana, "Baffanki na asibiti an fara yi masa aiki zaiji sauki In Sha Allah."

"To akaini gunsa mana,nikam akaini inga Baffana." Cewar Gaaji da idanunta suka cika da hawaye tana kokarin yin kuka.

Adnan ya durkusa gabanta yana rike mata hannu,

"Aa fa kar ki mun kuka, kin manta ke babbar yarinya ce yanzu? Kuma Kin manta alkawarin ku da Yareema? Sai nan da Wata bakwai kafin Baffanki ya gama jin sauki shikenan zaki koma rugarku kije ki zauna da Baffanki."

Gaaji ta Ta

ɓ

e baki, "Tom ni dai ka gais

he mun da Baffana in kaje Kuma in baka labari?"

Adnan ya ce, "Eh."

Daidai da fitowar Uwar Soro daga cikin daki kenan.

Gaaji ta kalleta ta ce, "Kawo kunnenka in fada ma Kar taji Sirrine."

Dariya Adnan ya yi ya kalli Uwar Soro ya ce, "Barka da fitowa

Baba."

"Barkanmu Dai Adnan kana tare da mutuniyar ne?"

Adnan ya ce, "eh Wallahi na shigo bakya kusa."

Gaaji ta katse su da fadin, " Ni kajo kaji in fada ma , in ba haka na fasa."

Murmushi Adnan ya yi ya ce, "Oh Sorry gani Ranki Ya Dade Gimbiy

a."

"Ni ba Soro ce ba ehee saidai kaine Soro nidai sunana Gaaji kuma ba gimbiya ba." Ta fada tana murguda baki.

Dariya ya yi ya ce, "To afwan gani nan."

Tsalle tayi ta janyo kunnensa ta fara ra

ɗ

a masa, "Aradun Allah Yareema Dan ishka ne,tsirara fa

yake zama a dakinsa naje na gansa kuma ranar ma na gansa yana fa

ɗ

a da wata ita ma tsirara, kai dai ba dan ishka bane ba ko?"

Dariya ce ke kokarin subucewa Adnan ya ce, "Ni ai ba ruwana."

Sake masa kunne tayi tana, "Yawww to ni kai ma ina sho kai zan

aura in Yareema ya sake ni."

Uwar Soro ta ce, "Kai dai yau ka gamu da gamonka."

Dariya kawai Adnan ya yi.

Gaaji ta mika masa hannu , "mu ma kulla ƙawance daga yau kaine babban abokina."

Mika mata yayi suka kulla Gaaji tana washe baki.

Ya ce, "

To Shikenan dai yanzu bara in tafi ko ,ki kula da kanki."

Gaaji ta ce, "Tom sai ka dawo,ka dawo fa muyi wasa ka ji."

Murmushi Adnan ya yi,yawa Uwar Soro sallama sannan ya fice yana murmushi.

Bangaren Adeel ya koma.

Yana zuwa ya tarar da shi yana

cin abinci.

Zama ya yi kan 2siter ya ce, "Safina tazo gidannan ko?"

Adeel ya amsa masa da ,"Eheen."

Nan take fuskar Adnan ta canja cikin fushi ya ce, "Na rasa mene ne yake damunka Prince na rasa mene ne damuwarka da ma abun da zaka so ji ajikin wa

ccer yarinyar yar bariki, Mace ta dunga kawo kanta gareka kuma kana amince mata, shin wai kana mantawa da matsayinka ne? Ka manta kai wane ne?"

Ko kallonsa Adeel bai ba ya ci gaba da cin abincinsa cikin kwanciyar hankali tamkar bai san da zaman Adnan ba

bare batun da yake.

Adnan ya kara fusata ya ce , "Ni dai bazan fasa fada ma gaskiya ba, Duk abun da zaka yi kana tuna kai wane ne da kuma darajar mahaifinka da Masarautar nan in ba so kake ka zubdawa kowa mutunci ba, in ma macen kake da bukata ba ga wacc

er yarinyar ba ka aura kayi koma miye da ita Ba wasu yan iskan titi ba."

Cikin fushi Prince Adeel ya dago fuska ya ce, "Ya isa! Na ce maka hakan ya isa, ni ban aureta Don ina sonta ko kasancewa da ita ba, sannan Safina da sauran ma baka da sanin abun d

a ke gudana a tsakaninmu."

Ya yi shiru yana ajiyar zuciya kusan Second Uku kafin ya ce, "Ka bar shiga abun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login