Showing 30001 words to 33000 words out of 159340 words
samu ba shi ta ke nema. Ki kuma gode ma d
a Allah da ya baki har biyu sai ki yi ma Allah butulci da cewa gazawa ce? Maza ki nemi gafaran Allah domin ya yi miki kyauta ba ki gode masa ki nemi gafaran shi ki gode masa sai ki ga ya ƙara miki da ni'imar da ta fi irin Ni'imar da ya baki a baya."
"As
tagafurilla. Astagafrilla."
Haka na shiga furtawa da sauti, domin sai na ji tsoro kar na batulce ma Allah ya ƙi ƙara min wata haihuwar domin nan duniya ba ni da wani buri sai na ganin Allah ya sake ba ni haihuwa ko da guda
ɗ
aya ne. Zuciyata har rawa ta
ke yi in na yi hasashen ƴaƴa biyun da Allah ya ba ni wata rana in ya so zai iya
ɗ
auke kayansa sai na ji jikina har ƙwaƙwalwata ya na amsawa cikin wani yanayi wanda ba ki ba zai iya misaltawa ba.
Nene ta ga yanayina ina ta rawan jiki sai ta ce na yi ta k
iran sunan Allah har sai na samu natsuwa innalillahi na cigaba da maimaitawa a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai ga shi na dawo cikin natsuwa Nene ta durkusa da kanta ta bu
ɗ
e ruwa ta zubamin a kofi ta ba ni ta ce na sha da bismillah. Ban yi musu ba na ka
r
ɓ
a na sha da yawa na miƙa mata kofin ta kar
ɓ
a ta maida shi saman farantin sannan ta koma ta zauna ta na kallona ina ta sauke numfashi.
Sai da ta fahimci na samu natsuwa sannan ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da cewa duk abin da na ga ya faru da baw
a daga Ubangiji ne kuma duk abin da ya aikata dai dai ne shi ba ya kuskure, mu ƴan adam mu ke kuskure amma shi Ubangiji duk abin da ya yi a garemu mai kyau ne. Ta umarce da shawaran da daaina tunani na fauwalama Allah komai. Wataƙila jinkirin alheri ne nan
gaba Ni'imar za ta fi ta baya yawa. Ina gya
ɗ
a kaina cikin gamsuwa ina fa
ɗ
in.
"Allah ya sa. Allah ya sa. Na gode Nene Allah ya saka da alheri"
Ta amsa da Amin kafin ta ce" Ina fatan kin fahimce ni. Sannan a mganganuna kin fahimci irin matsayin da kik
e da shi a zuciyar Tafida ko?
Sai na kalleta alamun bangane ba sai ta gyara zama kafin ta fara da kiran sunana.
"Sadiya ba ki fahimci irin martaban da ubangiji ya yi miki a acikin zuciyar mijin ki ba? To ko kin fahimta ba ki gane ba. Ni bari na warware m
iki irin taki baiwar da ubangiji ya yi miki ba ki sani ba."
"Sadiya."
Ta ƙara kiran sunana na amsa ina kallonta sai ta nuna kanta kafin ta ce" Kin san kishiyoyi uku Marigayi mahaifinsu su Tafida ya auro kafin rasuwarsa? Ba ta damu da mganata ba ta ci
gaba da fa
ɗ
in" Zan fa
ɗ
a miki wani sirrin da ban ta
ɓ
a fa
ɗ
a ma ko ƴaƴana ba. Ina yar yarinyata ya ƙara aure a lokacin cikin maimuna ƙarami ne a jikina. Maman farko da kike gani bashi ita a ka yi abokin mahaifinsa ne ya bashi
ɗ
iyarsa. Da maganar da auren tsak
ani wattani hu
ɗ
u ne, amma ya kasa fa
ɗ
amin saboda ya na tsoron tashin hankalina gashi ina da ciki kar wani abu ya samu cikin jikina kar na
ɗ
aga hankalina wani abu ya same ni ya sa bai iya fa
ɗ
amin da kansa ba sai amininsa marigayi Tafidan Rano ne ya zo ya sa
me ni ya sanar da ni a lokacin sai da ya kalleni kafin ya ce" Hauwa'u ki godema Allah kin yi dacen samun nagartatten mijin da ya ke gudun
ɓ
acin ranki da tashin hankali. Yususa ya ƙi sanar da ke labarin matar da aka bashi ne saboda ba ya so ya tashi hankal
inki wani abu ya same ki, ya na jin kunyar ki matuƙa duk da ba haramci zai yi ba, a lokacin ya ce min Hauwa ba duka maza ne irin Yunusa ba, ba duka maza ke iya jin kunyar matansu kamar yadda Yunusa ke jin kunyarki ba ya sake sanar da ni cewa ba duka maza k
e tsoron tashin hankalin matansu ba, saboda haka ki daure ki kuma yi haƙuri ki ba ma mijikin goyon baya kar ki
ɗ
aga masa hankali, ki yi masa alfarman guje ma tashin hankalinsa kwatanƙwacin yadda ya guje ma na ki."
Sadiya tun daga wa
ɗ
anan kalaman da ya yi
mini har ya bar duniya da gangan ban ta
ɓ
a
ɗ
aga masa hankali ba, in ma na ga hankalin shi ya
ɗ
aga ni ce zan zama sillar kwantar masa da hankali, har ya yi duka aure aurensa ban ta
ɓ
a
ɗ
aga masa murya ba, na yi hakuri na danne saboda wannan nasabar da Ubangiji
ya yi min a zuciyar mijina ba na so na bashi kunya. Na ci riban hakurina na zauna lafiya da shi da matansa tun yana rage ni ce giwarsa a cikin gida da waje har kuma ya koma ga Allah hakan bai sauya matsayina a wajensa ba sai ma ya ƙara hauhawa ninƙi ba ñi
nƙin, faruwan wannan lamarin ya sa kawai in na kalli Tafida sai na ga kamar na ga makwafin mahaifinsa ne a tare da shi, Sadiya ba wai ina fa
ɗ
a miki wannan ne saboda tausan baki ba. A'a ina fa
ɗ
a miki ke ma Allah ya yi miki wannan nasibin. Ba kowacce mace ba
ce za ta samu miji na jin nauyinta ba, ba kuma kowace mace ba ce ke samun darajawa da mutumtawa a wajen mijin auranta ba. Ba kuma kowacce mace ke iya samun namijin da ke gudun tashin hankalinta da damuwarta ba. Ke Allah ya baki wannan nasibi na kawo miki
wanman labarin ne saboda na ankar da ke wasu abubuwa guda biyu zuwa uku."
Ta ƙarishe fa
ɗ
a ta na kallona. Na kuma natsu na ba da duka hankalina a kanta ina sauraranta.
"Sadiya."
Na amsa da "Na'am Nene."
Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kin ga duk
sanyin halin Hauwa na sha yin shari'a tsakaninta da muttaƙa."
Ido na zaro ina kallon Nene sai ta gya
ɗ
a min kai kafin ta ce" Ba tonon asiri ba ne Sadiya Nasabar da Ubangiji ya yi miki na ke son ƙara tunasar da ke. Sadiya tun auran ku da Tafida bai ta
ɓ
a ka
wo min ƙaran ki ko da rana
ɗ
aya ba. Bai ta
ɓ
a zama ya kushe ki ba sai dai ya yabeki, ke ma haka ba ki ta
ɓ
a kawo min ƙaran Tafida ba,duk da na san kuna samun matsala domin babu auran da bashi da matsala sai dai ku binne shi ku ka
ɗ
ai ba tare da sanin kowa ba
. Sadiya wannan ma wata Nasaba ce da Ubangiji ya yi miki, kuma a cikin idanuwana ina karrama wannan ƙimar ta ki."
Sai na ji kaina ya yi girma cikin alfahari Nene ba ta bani damar mgana ba ta cigaba da fa
ɗ
in" To ba na so saboda wata ta zo ki sauya Sadiya
. Kin zama turken gidan Tafida duk matar da ta zo daga bayanki sai dai ta
ɗ
ora igiyanta a kan wannan turken da kika riga kika kafa shi Sadiya. Kar ki sake da wannan matsayin da Allah ya ba ki na uwargida kan gida, kar ki yi sake da shi ya tashi a banza. Ak
wai zafi amma ki daure ki gani ƙi ƙi gani, ki ji kuma ki ƙi ji, a zo a gaya miki ki toshe kunnen ki in kika yi haka za ki zauna lafiya, ki ba ma mijinki dama damar da ya ke so daga wajen ki, ki yi ta addu'an zaman lafiya da salama Sadiya wallahi tallahi ba
Saudatu ba ko Tafida bai isa wata rana ko halin su na maza ya motsa masa ya tozartaki ba saboda kin tsare mutumcin kan ki, na san Saudatu ke ma na san ki Sadiya in kuka yi hakuri za ku ba da shaidar kyakyawan zurua anan gaba. Ina roƙon ki da ki riƙe wann
an nasabobin da na sanar da ke Ubangiji ya yi miki, ko an yi miki wani abu in kika tuna su sai ki danne zuciyarki ki yi haƙuri in kika yi haka tabbas wata rana sai kin ci riba in sha Allahu."
Kamar hadda haka na haddace kalaman Nene a cikin kaina kuma
cikin ikon Allah da kalamanta sai na ji zafin da ke cikin zuciyata ya na raguwa. Ina jin haushin ta da na fara ji ita da Yalla
ɓ
ai ya na raguwa. Duk da an ce tsakanin miji da mata sai Allah gaskiya ne zan kalli Nasabar da na ke da shi a wajen Yalla
ɓ
ai na lu
llu
ɓ
e duka sharrinsa a gareni kamar yadda shima
ya ke kallon alherina ya lullu
ɓ
e sharrina ba kuma wai domin ba ni da shi ba, kowani
ɗ
an adam ya na da na shi alherin kuma ya na da na shi sharrin.
Sai kawai na kalli Nene ina murmishi kuma tabbas murmishi
daga ƙasan zuciyata ya fito ba a iya saman le
ɓ
ena ba ne.
"Na gode Nene. Kuma na yi miki alkwarin ba za ki ji sa
ɓ
anin tunanin da kike da shi a kaina ba in sha Allahu."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Amin. In sha Allahu na gode nima da samu abin da nima n
a yi tsammani daga wajen ki. Na gode Allah ya yi muku albarka Allah kuma ya zaunar da ku lafiya ya kuma ka
ɗ
e fintintunu."
Na amsa mata da Amin Amin sai ta ce za ta wuce amma kafin nan na yi ma Yalla
ɓ
ai mgana kafin ta wuce, ni na tashi na leƙa falon da suk
e zaune shi da Musbahu na kira shi muka dawo tare wannan karon kasan cafet muka zauna ni da shi gaba
ɗ
aya ta kallemu kafin ta ce.
" Na ƙara tunasar da Sadiya abin daman ta riga ta sani na auranka da Saudatu. Tafida sauran aikin na ka ne, ka zauna da mata
rka ku yi mgana ku fahimci juna ku tattauna rayuwarku tare. Dukkanku ina fatan tsamanin abin da na ke tsammani daga gare ku. Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Dukkanku da ku da yayanku Allah ya yi muku albarka gaba
ɗ
aya."
Muka yi ta amsa ma
ta da Amin sannan ta yunƙura ta miƙe ta na fa
ɗ
in" In ina da rai wata rana ina fatan alheri ya sake dawo dani gidan ku."
Muka ƙara amsa mata da Amin. Yalla
ɓ
ai ya shiga ƙwalama Musbahu kira ni kuma na je na kwaso mata takalmanta na jera mata ta zo ta saka t
a na fa
ɗ
in" Allah ya shi albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya."
Ni na bu
ɗ
e mata kofa muka fita har haraba sannan sai ga Yalla
ɓ
ai da Musbahu, sun fito na bu
ɗ
e mata gaban mota ta shiga sannan na rufe ina
ɗ
aga mata hannu Yalla
ɓ
ai kuma ya tafi bu
ɗ
e musu get
har Musbahu ya fita da mota na ga ya tsaya Nene na mgana da Yalla
ɓ
ai ta window na ga ya na gya
ɗ
a mata kai sannan suka wuce shi kuma ya rufe get
ɗ
in ina tsaye na har
ɗ
e hannu a kirji ina kallonsa sai yanzu da na ƙare masa kallo na fahimci ba ni ka
ɗ
ai na yi
raman tsaye ba Yalla
ɓ
ai ma duk ya rame sai karan hanci kamar bashi ba.
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji yana shafa kumatuna sannan na fahimci ya ƙariso kusa da ni.
"Ya dai?
Ya fa
ɗ
a ya na kallona sai kawai na sauke ajiyar zuciya.
"Bakomai.
"
Na sauke hannayena na juya zan tafi sai ya riƙo hannuna na dama, na juyo ina kallon shi.
Sai kawai ya wuce gaba ya na riƙe da hannun nawa, nima ban kwace ba sai na bi bayan shi. Bai direni ko'ina ba sai a kan kujeran mai zaman mutum
ɗ
aya shi kuma sai y
a durkusa a gabana ya na mai riƙe duka hannayena biyu a hannayensa ina kallon shi ya na kallona sai na ji rauni ya na kama ni. Zan iya fashe masa da kuka sai na yi saurin kauda kai, shi kuma sai ya kai yatasun hannuna
ɗ
aya bayan
ɗ
aya a bakinsa ya na sumbat
a. Kallon sa na ke yi da duka zuciyata ina jin ta na sake bu
ɗ
ewa a karo na biyu na yarda da kaddara wataƙila zantu kan Nene ne suka farkar da ni, wataƙila ba za
ta ga laifina ba domin itama ai ta san kishi ta kuma ce ya na da zafi sai an daure.
"Sadiya
ta."
Ya kira sunana cikin raunin murya sai na
ɗ
aga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah.
"Sadiya wallahi ban
ɓ
oye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa. Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata
kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki kar
ɓ
i mganar ba. Ba na so na fa
ɗ
a miki wani abu da zai
ɓ
ata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan
Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe min don Allah SADIYA TA."
Ya ƙarishe fa
ɗ
a ya na mai
ɗ
ora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa
lokaci
ɗ
aya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma
ɗ
in ma hawaye na ke yi, ina danne abin da ke taso min a cikin zuciya ta. Kai na ƙara y
arda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i domin a lokacin ji na ke yi ko na ce gani na ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin Gimbiya itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta
, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta.
Bai san ina kuka ba sai da ya ji
ɗ
igan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya
ɗ
ago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zau
ne ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara
ɓ
ul
ɓ
ulowa.
"In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi?
Haka ya fa
ɗ
a ya na share min hawaye, kawai sai na fash
e da kuka har da bu
ɗ
e murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ru
ɗ
e ya cicci
ɓ
eni shi ya koma ya zauna ya
ɗ
ora ni bisa jikinsa ya rumgume ya na ta share min hawaye, ya na kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin
na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwa
ɓ
e hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwa
ɓ
ewa sai ya tsaya ya na leƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa.
Sai kawai ya daga hannayensa sama ya na fa
ɗ
in" To na bari tunda b
a ki son lallashin."
Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan fa
ɗ
i kasa kuma shi bai riƙe ni ba, gani zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni?
Ya fa
ɗ
a ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a ra
ina na ce ai in Gimbiya ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci
ɗ
aya na saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena
suna zagaye a wuyansa.
Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda
ɗ
aya da ke bayana da shi ya ke
ɗ
an bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi
cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya
ɗ
auke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci na ke yi ba. Mun zauna a haka sama da awa
ɗ
aya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a ra
ina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai