Showing 123001 words to 126000 words out of 159340 words
dangin su Yusuf"
"Ma'u kuma?
Ya Aina ta maimaita sunan ta cikin mamaki. Kawai sai na
ji sabon kuka ya taso min ina kukan ina labarta ma Ya Aina abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un"
"Anty Bahijja ta ci min mutumci ta kirani dangin bokaye da asiri. Ta ce aurena da Yusuf ba ta ga amfanin shi b
a, Ya Aina wai ni suke zargi da ƙoƙarin zubar da cikin Amaryan Yalla
ɓ
ai? Duk ta dalilin Ma'u. Domin ita ce ta ba su damar duk abin da suka yi min Ya Aina."
Na ƙarishe fa
ɗ
a ina gunjin kuka da ƙarfi saboda sai na ji kamar a alokacin ma abin ya ke faruwa.
"Innalillahi. Ita Ma'un ce ta aikata haka? Amma ta ba ni mamaki matuƙa ban ta
ɓ
a tunanin haka daga gare ta ba."
"Ba in ina cewa munafuka ba ce sai a riƙa ganin laifina ba? Yanzu dai kun yarda ko? to Ma'u ta da
ɗ
e ta na ci duduniyata a dangin Yalla
ɓ
ai t
a da
ɗ
e ta na son rana irin ta yau ta faru sai yau burinta ya cika."
Na fa
ɗ
a ina goge idanuwana da hannuna kamar wata yarinya.
Ya Aina ta kasa mgana saboda lamerin ne ya zo mata cikin ba za tan da ba ta ta
ɓ
a tunani ko tsammani ba. Salati kawai ta ke y
i ta na
ɗ
aukowa ta na direwa.
"Ma'u ce ta je ta fa
ɗ
a ma Anty Bahijja dangin mahaifiyata yan asiri ne, sannan ita kuma Amaryan Yalla
ɓ
ai ta ƙara da cewa ta na gidan ma Inna Mariya ta kawo min asiri. Sannan kuma ta ce wai yadda na gama shanye Yalla
ɓ
ai haka
na ke so na tusa ma Kawu Marwa domin shima a shanye shi da asiri tun da mu ƴan na gada ne ba na haya ba."
"Na shiga uku ni Aina. A ina suka ji labarim Marwan? Ko shi Abban ne ya fa
ɗ
a?
"Ma'u ce ta fasa maganar. Ita kuma Ya Murja ce ta fa
ɗ
a mata. Ba i
na fa
ɗ
a muku munafuka ce kuna ganin kamar ban da haƙuri ba? Uhm ni ka
ɗ
ai na san wace ce Ma'u da kaidin ta."
Na fa
ɗ
a ina mai
ɗ
aura
ɗ
ankwali na rufe kaina kukan ya tsaya amma zafin da ke cikin zuciyata ya kasa raguwa.
"Ma'u. Lalle ko Ma'u ta ba ni matu
ƙ
ar mamaki."
Ta fada ta na mai yin tagumi cikin
ɗ
imuwa.
"Shi ya sa na ce an zo ƙarshe wallahi tallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da su Ya Aina. Ba zan bar wannan kazafin da suka yi min ya tafi a banza ba."
Sai ta kalleni kafin ta ce" Shi Babans
u Jidda me ya ce?
"Me kuwa? Ya ce shima zai
ɗ
au mataki amma ba shi zai hana ni
ɗ
au nawa matakin ba."
"Alhajinmu ya sa ni?
"Ke ka
ɗ
ai kika san abin da ya faru."
Na bata amsa ina kallonta sai kawai ta miƙe tana fa
ɗ
in" Ya zama dole ya sani domin maga
na ce da ta shafi zumunci. Kuma ni kaina ba zan so a bar maganar ba gwara a
ɗ
au mataki tun da ya shafi zuru'armu ya kuma shafi auran ki da mutumcin ki, ya zama wajibi a shiga wannan mganar domin a yi min lamarin tufkan hanci."
"Wa za ki kira?
Na tamb
ayeta ganin ta na
ɗ
aukan wayarta.
"Hamza zan kira. Shi sai ya kira Alhajinmu."
Sai na yi shuru saboda na san Ya Hamza zai ba ni dukkan goyon baya har sai ya ga an ƙwatamin haƙƙina. Da dai Ya Abubakar ne daman ba zan saka ran ya goyi bayana ya bar Ma'
u ba amma kuma ya sani wannan karon ba gudu ba ja da baya ni da Ma'u har abada sannan sai hukuma ta shata mana layi a tsakaninmu.
A gabana Ya Aina ta zauna ta labartama Ya Hamza duk abin da ya faru ta ƙarishe da cewa" Sadiya ta zo min ciki kuka na fitan
hayyaci. Hamza Ma'u ba ta kyauta ba, kuma tun da ta ta
ɓ
a auren Sadiya bai kamata a yi shuru ba. Ka kira Alhaji ka fa
ɗ
a mishi sai a san yadda za a shiga mganar. Domin Sadiya ta ce ba za ta yarda ba sai ta kai ta ƙara hukuma."
"Ta yi min dai-dai. "
Ya
Hamza ya fa
ɗ
a kafin ya cigaba da fa
ɗ
in" Ni ban yi mamakin abin da Ma'u ta aikata ba daman can halinta ne ta na wani muƙu muƙu na munafunci ba Sadiya ni nan Hamza Muhamamad Yashe jinin Sadiya ba zan bari cin zarafin da a ka yi mata ya tashi a banza ba. San
nan duk wanda ya ta
ɓ
a zuru'an Mama kamar zuru'an Gwaggo ya ta
ɓ
a. Sannan duk wanda ya nemi tozarta zuru'an Gwaggo kamar zuru'an Alhaji ya ta
ɓ
a. Kuma ta
ɓ
a wa
ɗ
anan zuru'an dai-dai ya ke da ka ta
ɓ
a mana mutumcin mu da darajan mu, kuma ta
ɓ
a darajanmu dai-dai ya
ke da ka nemi fa
ɗ
a damu. Saboda haka wannan lamarin ba Sadiya ka
ɗ
ai ya shafa, har damu gaba
ɗ
aya."
"Gaskiya ne wannan."
"Sabo da haka, yanzu zan kira Alhaji a waya na fa
ɗ
a masa abin da ke faruwa. Ya kamata ya sani saboda abu ne da ya shafi auren Sa
diya. Sannan za a yi zama zan kira Auwalu jibi asabar mu shigo Kano. Ba Ma'u ba har Baaba sai an kira. Za ta ci ubanta sai mun ji in yayar Yusuf ita ce jininta ba Sadiya ba. Kuma daga wannan a yi mata iyaka da komai yadda za ta fahimci Sadiya ma ta na da g
ata."
"Haka ne gaskiya ne. Haka yakamata a yi."
Nan take ya ce ta ba ni wayar da ya ke a speaker ta saka wayar shi ya sa na ji komai. bayan na amsa mun gaisa ya ce" An ce kina ta kuka? To ki share hawayen ki, mu ƴan'uwanki za mu tsaya miki har sai ga
skiya ta bayyana. Shi Yusuf
ɗ
in me ya ce? Ko wani mataki ya ce zai
ɗ
auka?
"Ya ce zai
ɗ
au mataki amma bai fa
ɗ
a min matakin da zai
ɗ
auka ba."
"Ok. Daman ai na can gidan su matakin na hannun shi, mu kuma na mu na gida mu ne za mu gyara lamarin. Ki kwant
ar da hankalin ki, in ba za ki koma gida ki yi kwanciyar nan ki samu natsuwa har zuwa da safe. Amma shi kan shi Yusuf
ɗ
in in bai wanke ki a wajen yan'uwansa da zargin da suka zarge ki ba, za mu saka baki mu mu
ɗ
aukan miki mataki, ba ta yuyuwa a
ɓ
ata miki s
una sannan a bar shi ya tafi a banza"
Bai kashe wayarsa ba sai da ya jadaddamin na kwantar da hankalina wannan karon Ma'u ta ƙai ƙarshe kuma sai ya ga ƙarshenta. Sai na ji hankalina ya kwanta ba tabbaci gareni akan Ya Hamza ba. Ina da kyakyawan yaƙini a
kan zai tsaya a kan wannan mganar har sai an ƙwatomin haƙƙina kamar yadda ya fa
ɗ
a, sai na ji hankalina ya
ɗ
an kwanta ko hukuma ba ta shiga ciki ba, hukumar ƴan'uwana za su tsaya min har sai gaskiya ta yi halinta. Har sai ainihin fuskar Ma'u ta bayyana a g
aban kowa ya gane ta.
Ya Aina ta dafa min ruwa zafi na sha da bombita. Ta ce na kwanta na huta ciki na shiga na haye gadonta kuma cikin ikon Allah na
ɗ
an samu barci amma zuwa hu
ɗ
u da rabi na tashi lokacin Marwa ta dawo daga asibiti ba ta dameni da tam
baya ba ƙila Ya Aina ta ce kar ta dame ni ne, amma dai mun gaisa har ina zolayanta da Amaryan kawu ta fita ta na fa
ɗ
in" Kai Umma."
Tsakar gida na fita na yo alwala na iske Ya Aina ta tanka
ɗ
en garin tuwo. Yaran duk ba sa nan sun tafi hadda yamma,
ɗ
aki na
koma na ta da salla, ina cikin sallar na ji muryan Rahila sai da na idar sai ga ta sun shigo ita da Ya Aina.
"Ah Sadiyalle daman kina nan?
Ta fada ta na ƙoƙarin zama a saman kujera.
Sai da na
ɗ
ago ina fa
ɗ
in" Ga ni ko kin gani Rahilatu."
Sai lokaci
n muka ha
ɗ
a ido ta ga yadda idanuwana suka kumbura saboda kuka.
"Ciwon ido kike yi?
Kafin na ba ta amsa Ya Aina ta ce" Kuka ta yi."
Sai ta kara kallona kafin ta koma kuma ta na kallon Ya Aina.
"Me ya faru?
"Daga ina kike da yamman nan?
Ya A
ina ta katse mata tambaryarta.
"Makociyata ce ƙanwarta ta haihu. Shi ne muka ha
ɗ
u gaba
ɗ
aya muka taho barka muna zuwa na ga anguwarku ne sai na ce su wuce bari na shigo mu gaisa."
"Me ya faru?
Rahila ta tambaya bayan ta dire maganarta.
"Lamarin
ne abin mamaki da takaici."
"Wai me ya faru don Allah?
Nan Ya Aina ta labarta mata dukkan abin da ya faru sai Rahila ta saki Sahla da ke hannunta ta na shan nono kafin ta ce" Innalillahi kai Ma'u ta yi asara. Kai jama'a wannan wani irin cin zarafi ne
da cin mutumci?
Ta fa
ɗ
a har idanuwanta ya na kawo ƙwalla
Ni ta kalla ni ko na dukar da kaina ne kawai ban yi magana ba, saboda ana ƙara maganar abin ne ina jin ƙunar zuciyata na ƙara ƙamari.
"Duk abin da ke faruwa tsakanin Ma'u da Sadiya ban ta
ɓ
a
ba ma Sadiya gaskiya ba sai dai na ba ma ita Ma'u saboda dai kar ta ji a ranta muna wareta saboda ita ba cikin mu ta ke ba. Amma ni kaina na san Ma'u da wani abu a ranta game da Sadiya. Sai dai har ga Allah ban ta
ɓ
a tunanin ta yi nisa haka ba. Ban ta
ɓ
a tun
anin za ta iya ba da goyon baya a ci zarafin Sadiya ba. Ban ta
ɓ
a tunanin za ta je ta kai mganganu masu muni haka ba, mene ne riban ta ? Me ta samu? Har wata can ta fi mata jininta? Mene ne riban abin da ta aikata?
"Riban ta na tozarta. Ribanta a ci mutu
mcina na muzanta na wulaƙanta a idon duniya. Daman ta fa
ɗ
a min a ranar da aka fasa auranta da Ya HamzaCds cewa sai ta yi sanadiyar muzgunama rayuwata kamar yadda na hana ta farincikinta nima sai ta hana ni nawa farincikin. Kuma ta da
ɗ
e ta na yi min bita da
ƙulli wannan ne dai ya yi munin da ba zai
ɓ
oyu ba."
Na fa
ɗ
a ina maida hawayen da suka cika min ƙwarmin idaanuwana.
"Ba shakka."
In ji Rahila kafin Ya Aina ta kar
ɓ
e da fa
ɗ
in" Shi ne daman ta ke riƙe da shi? To ai abin da kika yi ba laifi ba ne. T
a dalilinki aka samu masalaha sannan aka cece ta
ɓ
ar
ɓ
arewan zumuncin mu gaba
ɗ
aya."
"Uhumm. Ni fa mamaki na ke yi wai Ma'u ce za ta yi ma Sadiya haka? Me ta tsare mata? Me ya sa ta yi haka? Har da zuwa ta na ba da labaran da ba su da tushe ballatana makam
a."
Rahila ta fa
ɗ
a ta na ƙara bayyana mamakinta.
"To ai duk komai ya zo karshe. Domin Hamza ya ce ba za a bar mganar ba za a yi zama na musamman."
"Sosai. Ko ni ban goyo bayan a bar mganar ba. Ita kanta Ya Murja hakan sai ya zame mata darasi da kwas
he wasu labaarn ta na fa
ɗ
a mata."
Ya Aina ta ce" Kar ma ta yi hankali ita ta sani. Amma yaushe kana Babba ka riƙa bin yaro ƙarami kana gaya masa maganganu. Ni fa ban
ɗ
auka za ta fita da mganar Marwa ba har sai da na ce mata ya ce ba ya so kowa ya ji sai
sun gama dai-daitawa da ita Marwan sai ya je ya sanar da magabantan shi amman shi ne ta je ta fa
ɗ
a ma Ma'u ita kuma ta je ta sanar ma ƙanwar uwarta."
Ya Aina ta ƙarishe fa
ɗ
a cikin bayyana zafin abin har a cikin zuciyarta.
"Wata Marwan? Me ya samu it
a Marwa
ɗ
in?
Ya Aina ce ta sanar da ita abin ake ciki.
"Shi ne fa ta je ta kwashe ta fa
ɗ
a ma Ma'u ita kuma ta sanar ma Yayar mijin Sadiya shi ne ta ke ce ma Sadiya yadda ta shanye Yusuf shi ne za ta ha
ɗ
a shi da
ɗ
iyar yayarta domin shima a shanye shi tu
n da mu yan dangin asiri ne."
"La'ila. Ya Aina"
Rahila ta fa
ɗ
a ta na tafa hannuwana cikin al'ajabi da mamaki.
"Gaskiya Ma'u ta yi asara. Ta zama jaka tunda ta iya za
ɓ
an bare a kan jininta. Na ji ta fita daga zuciyata sam"
"Wallahi nima. Ta fita
daga raina kwata kwata. Ji wani tsohon labari da ko mu da aka yi shi muna da wayau, mun manta amma ita da ta ji labari ta iya riƙe shi a ranta har ta na kai shi gaba. Tir da ita. Tir da mai hali irin na ta."
Haka suka ha
ɗ
u suna ta tattaunawa ni dai ina
gefe ina jin su su sai yau suka san Ma'u? Ai ni na da
ɗ
e da sanin hallayarta mara sa kyau.
"Gwara da kika je gidanta kika yi mata hauka tun da ba ta da mutumcina."
In ji Rahila.
"Nima haka na ce."
Ya Aina ta maida mata martani. Rahila ta da
ɗ
e s
ai gabda mangariba ta tafi, ni kuma ina gidan Yalla
ɓ
ai bai kirani ba nima ban kira shi ba. Yau ko su Jidda ban tuna da su ba, sai na ji komai ma ni ya fita daga kaina, ba na son komai kuma ba na jin da
ɗ
in komai, har dare da Babansu Marwa ya dawo ya ganni a
gidan Ya Aina ba ta bu
ɗ
a masa ba sai dai ta ce yar matsala ce muka samu da Yalla
ɓ
ai. Nan fa ya zauna ya na min nasihan haƙuri da rayuwa jin sa kawai na ke yi domin duk abin da zan fa
ɗ
a masa ba zai yarda ba gwara kawai na yi masa shuru.
Can dare Ya Auwa
l ya kira Ya Aina ya ce Ya Hamza duk ya yi masa bayani kuma jibi shima ya na ta fe. Har Gwaggo sai da ta kira Ya Aina ta ce labari ba da
ɗ
i suka ji Alhaji ma duk ya shiga damuwa. Ita ta yi mata ma wasu bayanan, Gwaggo sai salati ta ke
ɗ
aukowa ta na direwa.
"Asma'u ta ba ni kunyam ban ta
ɓ
a tunanin sakara ba ce sai yau."
Gwaggo ta ce min bayan ta ce a bani wayar ta yi ta lallashina ta ce Alhaji zai yi adalci kuma Ma'u ba ta kyauta ba kuma za a gaya mata. A kallah dai yanzu sun yarda da cewa Ma'u munafuka
ce kuma fuska biyu gare ta.
Gidan Ya Aina na kwana akan gadon ta ni da Marwa. Ita kuma a turakan megidan ta kwana tun da asuba Kawu Abba ya kira wayata lokacin ma ina zaune kan darduma ina azkar ne bayan mun gaisa ya ce min.
"Sadiya na ji duk abubuw
an da suka faru. Ban ji da
ɗ
i ba. Amma ina so ki sani Tafida ba zai ƙyale wannan mganar ba. Yanzu haka ya kira su Kawu Sa'adu yau muna tafe za a yi zama a gidan Nene ki yi haƙuri duk wanda ya ha
ɗ
a maganar nan domin ya tozartaki sai dai shi ya tozarta ta in
sha Allahu."
"Allah ya sa."
Na fa
ɗ
a cikin sanyin murya.
Ba mu wani da
ɗ
e muna mgana ba har ya na ce min ina gidan su Marwanatu ko? Na kuma san ita Marwan ta fa
ɗ
a masa ina gidan su tun da ai na ji ta ƙasa ƙasa da daddare suna waya.
Da safiyar jumma
'a na wayi gari a gidan Ya Aina duk breakfast
ɗ
in da ta ha
ɗ
a min ban iya cin komai ba sai Tea kawai da na sha. Yara duk sun tafi makaranta Marwa ce kuma aikin rana gare ta yau, Ya Aina ta saka min ruwan zafi na yi wanka ta ba ni kayanta na saka tunda yawan
cin jikin mu duk
ɗ
aya ne sai dai ma ta dan fi ni ki
ɓ
a.
Munnira ta kirani a waya ta na fa
ɗ
a min suma an kira su gidan Nene ita da Hauwa.
"Ni ba wanda ya kirani ko Yalla
ɓ
an ma tun jiya da ya sauke ni gidan Ya Aina ban ƙara jin sa ba."
Munnira ta ce
" Hmm jiya bayan tafiyarki an yi abubuwa Sadiya. Daman ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Sadiya Allah ya wanke ki. Tafida ya tsaya miki jiya har ita Gimbiya sai da ta raina kanta."
"Me ya faru?
Na fa
ɗ
a cikin sanyin murya.
"Bayan fitan ki Mimisc
o ta zo itama ta yi ta fa
ɗ
a da Anty Bahijja. Da ita kanta Gimbiya Nene kuma ta ce tunda