Showing 153001 words to 156000 words out of 159340 words
tsautsayi
to."
Munnira ta fa
ɗ
a ta na min dariya sai na ji haushi na kashe wayata na bar ta ta na min dariya.
Nima sai daga baya na yi ma kaina Allah ya ƙara da ban yi magana ba, da bai samu damar fa
ɗ
a min maganganu son ran shi ba, da haka na yaƙice tunanin haka
na shiga ayyukana amma a ƙarƙashin zuciyata ina ta auna maganganun Yalla
ɓ
ai ba wasa ba ya fa
ɗ
a min mganganu masu zafi amma tun da ni na shiga huruminsa duk ma abin da ya fa
ɗ
a min ai ni na jawo shi.
Ɗ
an wannan maganar ashe shi Yalla
ɓ
ai ya
ɗ
auka da zafi da
ya dawo gidan ina masa sannu da zuwa, da ƙyar ya amsa ni kamar na fa
ɗ
a masa cuta ina ganin haka na kama kaina domin nima ina da zafi ba zan bari ya
ɓ
ata min rai ba, in hakan ta faru to ni da shi ba za ta yi mana kyau ba. Abinci ma da na ha
ɗ
a masa nan ya ba
r min kayana bai ta
ɓ
a ba da safe ma tea kawai ya sha ya fice jira ya ke yi ƙila na sake bashi haƙuri bayan duk haƙurin da na bashi jiya ai ko sai da a yi zama a haka.
Ranar daman ya bar gidana kuma har ya koma gidan Gimbiya ya gama kwanakinsa bai kirani
ba, sau
ɗ
aya ya zo gidan daddare shima wasu takardu ya zo
ɗ
auka. Yadda ya basar da ni nima haka na basar da shi, tun da har na bashi haƙuri da farko ni kuma a raina na ƙudiri niyyar ba zan ƙara bashi haƙuri ba kuma. Kar ma ya haƙura shi ya sani.
Ga shi i
na son na tambaye shi maganar zuwa Rano amma ba fuska. Cefane ma Salisu ya kawo min kuma da in zai kawo Yalla
ɓ
ai na kiran waya ta ya fa
ɗ
a min amma ranar bai kirani ba, ni kuma da ya zo gidan ban yi masa mgana ba.
Ranar da zai dawo wajena ranar Matar Mus
bahu ta zo min yini Mubeena mai kirki da ita. Yadda Musbahu ya ke
ɗ
an gidana itama haka ta ke a wajena domin shi da kan shi ya nuna mata ta daraja ni shi ya sa ta ke girmanani. Ta na zuwa gidana sosai ta yi min yini. Ni ko bai fi sau biyu na ta
ɓ
a zuwa gida
nta ba da lokacin bikin su sai kuma da muka je tare da su Hauwa, na ji da
ɗ
n zuwanta da ya ke ta na da wayewa ta na ma karatu ne anan BUK Kano sai dai ta na shekaran karshe ne, ga ta ba ta son jiki in dai ta zo tare muke yin ayyukan mu, ita da bakinta ta ke
fa
ɗ
a min acikin hira Anty Bahijja har gida ta je ta na yi mata fa
ɗ
an wai ta kama ni kamar ni ce yayar mijinta. Su za ta kama domin su ne dangin mijinta ni ma bare ce kamar ita. Da ta fa
ɗ
a min dariya kawai na yi ni yanzu ai sun daina ba ni mamaki harkan ga
bana kawai na ke yi, tun da aka yi mana tsakani ba ta ƙara ha
ɗ
o mu ba, duk da dai suna yi ta bayan fage. Yanzu har Halima na daina ganinta a gidana ta koma yar tsagin Gimbiya.
Ƴ
aƴansu daman ba sa zuwa gidana amma gidan Gimbiya har truruwa suke yi mata
ni wannan bai dame ni ba. Amma nima ƴaƴana sun daina zuwa musu hutu tun da abin na su ya koma wariyan lautin fata kowa ya riƙe na shi, ko da ya ke yanzu sun daina mararin su sun koma mararin su Khalipa yanzu su ne komai suka samu na su ne ni na manta rabon
da su yi ma su Jidda ma wani abun ma ban damu duk da na san a baya sun yi daga baya da suka samu wa
ɗ
anda suka maye musu gurbinsu sai suka manta da su. Ban lura da wannan domin babu abin da ƴaƴana suka nema suka rasa. Yalla
ɓ
ai mai yi ma iyalan shi ne shi y
a sa ban cika damuwa da wasu abubuwan su ba.
Waina na yi ranar Mubeena ta ta yani muka yi aikin wainar. Har dare ta na gidana sai da Yalla
ɓ
ai suka taho tare da Musbahu sannan suka koma gida tare bayan shima ya ci wainar a nan na kuma saka musu a kula su
ka tafi dashi. Yalla
ɓ
ai ya
ɗ
an sake amma ba sosai ba har yanzu da sauran cin mgani a muryansa da ayyukansa ni kuma sai na nuna kamar ban ma san yana yi ba zuwa washegari sai ya saki ya dawo ya na min magana kamar ba shi ne ya ke ci min mgani ba. Fuskar da
na gani ya sa na yi masa mganar bikin Rano nan ta ke ya amince ya kuma turamin 30k ya ce na yi na mota da guddumuwa.
Da ya yi maganar yara na ce ga Jidda za ta iya kula da gida. Shi fa a ganin shi har yanzu Jidda yarinya ce ita kanta ta na bukatar kulaw
a sai na ce to ya kwashe su zuwa gidan Gimbiya kafin na dawo sai ya ce sai abin da ya gani.
Ko Munnira ban kira na sanar mata an bar ni ba. Sai dai na fa
ɗ
a ma Hauwa muna tafe ranar jumma'a ta na ta murna. Ita tun ranar litini ta na can, da na tura mata
ku
ɗ
in da muka ha
ɗ
a kamar ta yi kuka da ta kirani ta na min godiya na ce mata ai mun zama
ɗ
aya. Marwa na kira ranar al'amis ana gobe tafiyarmu na ce mata muna tafe ta buga tsallen ihu ta na murna daman ai ta san da bikin tun da ni da kaina bayan bikin na su
na je Rano na
ɗ
auki Marwa na kai ta har gidan su Hauwa na yi ma ta uwar
ɗ
aki da mamansu Hauwa da ƙannenta.
Su ka kuma kar
ɓ
eta hannu biyu suna zumunci yanzu bayan gidan iyayen mijinta ba ta da kamar gidan su Hauwa duk da har gidan su Gimbiya ta na zuwa
amma sai wani abu ya faru na jaje ko na murna. Kawu Abba kulle gare shi ba ya son yawo ko Kano tun da Marwa ta yi aure sai da ta yi wata biyar sannan ta zo ganin gida daga nan kuma sai da ta dawo gida jego da ta koma ba ta dawo ba sai bikin Antin Ya Murja
na su Jawahir ba su kwana ba a ranar suka zo tare da matan su Kawu Sa'adu a kuma ranar suka koma.
Kafin safiyar jumma'a na shirya kayana tsab don ma telana ya
ɓ
ata min lokaci akwai kala
ɗ
ayan da bai gama min ba sai da na jira. Munnira ta biyo min, ba mu
tafi ba sai da su Jidda suka dawo makaranta sannan muka
ɗ
au hanyar Rano. Yalla
ɓ
ai ba gidana ya kwana ba a waya muka yi sallama. Mun isa Rano da wuri shi ya sa ko su Anty Bahijja acan suka iske mu, mun baje ana komai damu a ka gaggaisa kusan ita Anty Bahij
ja ko yaya ne sai ta ta
ɓ
a hali sai da ta ce ma Munnira wai ka ga Aminan yayar amarya har an hallara akan lokaci Munnira ta ce tabbas dole mu hallara akan lokaci domin ta Hauwa shirye shirye a matsayin mu na Amininta.
Marwa nan gidan su Hauwa ta so muka
ha
ɗ
u da mangariba ta tafi za ta ce gida ta shirya ta na da aikin dare ne ranar. Mu kuma nan gidan su Hauwa muka kwana washegari aka tashi da yinin biki da
ɗ
aurin aure, ni kwata kwata tun bayan saukan mu ba mu yi waya da Yalla
ɓ
ai ba kuma bai fa
ɗ
a min zai zo
ba, duk da na san zai zo
ɗ
in amma ban
ɗ
auka tare da matarsa za su zo da yara ba sai ganin su Jidda kawai na yi wa ya kawo ku? Wai tare muke da Anty Gimbiya da Abba. Sai ga Khalipa da ita kanta Gimbiyar
ɗ
auke da Anwar kenan shi ya tuko su alhalin ni bai nu
na min ma za ta zo ba. Ban nuna mata wani abu ko a fuskata ba muka gaisa. Lokacin ni ban ma yi wanka ba sai daga baya ankon less
ɗ
in da muka yi mu uku muka saka gaba
ɗ
ayanmu wani marroon da baƙi yi yi mana kyau duk in da muka gifta sai an ce kai leshin nan
ya yi kyau. Har cikin gida su Yalla
ɓ
ai suka shigo Allah ya sanya alheri da shi da Kawu Abba da Tariq sai Musbahu sai Nasir da Muttaka. Sannan a
ɗ
akin samarin gidan su Hauwa suka zauna aka kai musu abinci ni dai ban je ba domin na ga Gimbiya ce ke kai da ka
wo sai na bar mata amma dai mun je dukkan mu mun gaishe da mazajen namu.
"Madam kin fa samu duniya"
In ji Yalla
ɓ
ai ya na kallona ni ko sai na kalle shi ina yi masa fari kafin na ce.
"Allah ko! In ma duniyar ce ai kai ka ba ni ita a hannuna Yalla
ɓ
a
i."
"Wannan gaskiya ne Uwargidan Alaji Tafida ba."
Tariq ya fa
ɗ
a ya na dariya Kawu kan cewa ya yi." Ba dole ya ba ta duniyar ba. Saboda ita ce ta san shi tun kafin duniyar ta same shi."
"Tariq ya su Farida? Sai ban gan ta ba."
Na fa
ɗ
a ina kauda m
aganar Kawu Abba tun da na ga Gimbiya ta shigo lokacin Yalla
ɓ
ai sai fama da yara ya ke yi, Khalipa ya manne masa ga Anwar a jikinsa duk sun ƙi bari ma ya ci abinci ni dai ina gefe a raina na ce can ku ƙarata.
"Wallahi ba ta samu zuwa ba saboda makaranta
r yara."
Tariq ya ba ni amsa, zan yi magana Munnira ta ja ni muka fita waje ta na min ra
ɗ
a.
"Ke na ga matar nan sai wani rawan kafa ta ke yi ne"
Sai na kalleta ban ce komai ba na wuceta ina fa
ɗ
in" Ta yi ta gama Munnira."
Daga haka na koma cikin gida
na bar su, can ma aka fara ƙidan ƙwarya muka je can muna chasewa da aka ce filin na yayyen amarya ne, muka shige fili ni da su Hauwa muna ta rawa ana yi mana liƙi sai can da yamma su Jidda suka ce za su tafi Gimbiyar ma ba ta min sallama ba a raina na ce
a gayas, to uban gayyar bai min sallama ba ballanta ita.
Amarya cikin garin Kano za a kaita a daran aka tafi da ita amma mu ba mu je ba. Tun da muna gari muka ce sai mu sa rana mu je daga baya.
Ranar a gidan Marwa muka kwana washegari muka yi shirin dawo
wa gida. An ba mu kayan biki su cincin da dublan da kayan robobin da aka raba can muka bar Hauwa sai ranar talata za ta dawo. Amma tare muka taho da wasu dangin su kuma za su je gidan Amarya.
Ko da na koma gida ba kowa, sai da na bu
ɗ
e ashe suna can shar
a
ɗ
a gidan Gimbiya. Yalla
ɓ
ai bai kirani ba sai ni da kaina da na kira shi na ce na dawo. Shi ne da daddare sai gashi sun taho da yaran har da Khalipa da na ke murnan kwana biyu ya bar ni na huta ashe ba haka ba ne. Ranar ga gajiyan biki hayaniya ta yi yawa
a can ba mu wani samun barci, amma yaron nan haka ya hana mu barci a
ɗ
akin su Jidda na kai shi ya kwanta saboda ya fara barci a falo amma sha biyu saura muna kwance a
ɗ
aki muka ji ihun shi dole Yalla
ɓ
ai ya je ya
ɗ
auko sa ya saka shi a tsakiyarmu kamar wani
yaro haka ya tashi cikin dare daga ya ce zai sha ruwa sai ya ce zai ci abinci. Gaba
ɗ
aya ya hana ni barci, ni ƴaƴana ba su hana ni barci sai
ɗ
an kishiya. Yaro kamar an haife shi da makirci da kissa a daran Yalla
ɓ
ai ya tashi ya ha
ɗ
a masa tea. Ban san yadda
aka yi ya cire masa pampers
ɗ
in jikinsa ba, kawai sai farkawa na yi da asuba na ga Khalipa ya kelayamin fitsari a sabuwar katifa ta.
Tsabar baƙin ciki ma na kasa mgana. Wallahi ko su Jidda ba su yi zaman yi min fitsari a kan katifa ba domin tun zamanin
napkin shi na ke yi musu in zamu kwanta. Kuma ba na bari su sha ruwa daddare ko su sha tea amma saboda iskanshi shi Yalla
ɓ
ai cikin dare ma ya ke tashi ya na
ɗ
ura ma yaro ruwa ba dole ya yi fitsari ba da na ga kalli wajen har sai da ya yi shaida a zanin gad
o kawai sai na kalli Yalla
ɓ
ai lokacin ya dawo daga sallar asuba Khalipa na can
ɗ
akin su Jidda.
"Yalla
ɓ
ai cire ma Khalipa pampers ka yi? Ji fa yadda ya yi min fitsarin kwance."
Kai tsaye ya ce" E jiya ne ya na ta rigima sai na cire masa sai na ga ma d
uk ya cika shi da fitsari."
Ban sake magana ba sai shi ne ya
ɗ
ago ya kalleni kafin ya ce" Ba komai ai fitsarin yaro ne. Ki kuna fanka kawai ni bari na je can
ɗ
akin na
ɗ
an runtsa."
Daga haka ya fice ya bar ni ina bin shi da kallon takaici. Sai da na cire
zanin gadon sannan na saka ruwa da omo na goge wajen na saki fanka zanin gado kuma na fita waje na jiƙa shi ina ta
ɓ
ata rai da sassafe ya sakani wahala, ba fitsarin ne abin haushi ba na ga dai ba jariri ba ne, ba zan hana shi kwana a gidana ba amma ba a
ɗ
a
kin da na ke kwana da mijina ba har kuma ya kwanta ya yi min fitsari.
Shi ya sa ko su Jidda ba su ga fara'ata ba har shima ko da ya fito na ha
ɗ
e rai na. Amma bai hana nai yi ma Khalipan wanka na sauya masa kaya ba. Ni kuma na je na wanke zanin gadon da
ya yi min fitsari na shanya. Duk da Yalla
ɓ
ai ya siya mana in ji min wanki amma da hannuna na wanke shi tun da guda
ɗ
aya ne. Da Yalla
ɓ
ai zai fita nan ya bar min shi wai maman shi ba ta nan za ta je asibiti Anwar ne ya kwana ya na ciwon ciiki. Ya fita ya bar
ni ina ta aikin a kitchen ina can ina wanke wanke bayan na gama gyara duka
ɗ
akunan na saka turaran wuta. Cartton na kunna ma Khalipa na yi masa jan ido da cewa in ya sake ya tashi sai na yi masa bulala ashe yaron nan bai ji ba ina can ina wanke wanke shi
kuma ya samu dispanser ya danna ya yi min ta min
ɓ
arin ruwa har ya gangaro ya jiƙa min cafet ruwa ne cike fa sai da ya yi rabi da shi kamar an ce na leƙa falon na ci karo da mummunan aikin da ya aika ta min
Na ko kama shi na yi masa bulala biyar, saboda
haushi ko
ɗ
ana ne ya yi min
ɓ
arnan nan sai na dake shi sai kawai ya fashe da kuka ko tsayawa bi ta kan shi ban yi ba haka ya ja min aiki sai da na na
ɗ
e cafet
ɗ
in nan na fita dashi na shanya. Sannan na koma na sake goge wajen yaro nan neman ya yi ya saka m
in hauka ranar ina can ina aiki amma ina fargaban abin da zan je na tarar na ƙudira a raina zan yi ma Yallabai magana sai dai duk abin da zai ce ya ce. Ga barcin gajiya a idanuwana amma ban isa na kwanta ba domin in na kwanta na san abin da zan ta shi na t
arar shi ya sa bayan na gama aikin jikina da zuciyata na son na kwana na huta amma na kasa, tun da in dai na bar shi na kwanta sai ya jawo min gagurumin aiki shi kuma ga shi ba ya barcin rana ballantana mu kwanta tare.
Ba ni na samu na huta ba sai da ya
mma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfi
ɗ
a wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yalla
ɓ
ai ma ya shigo. Na dai ha
ɗ
a masa abincin sa a dining, ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice