Showing 27001 words to 30000 words out of 37098 words

Chapter 10 - RANA DAYA BOOK2 COMPLETE

11 Nov 2026

9

shakar sa a

jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya.

Bayan ya gama da abincin kuma ya jinjina

mata. Nafisa ta sha mamaki a kwanciyarsu, yanda ya tara da ita sau biyu a daran. Sannan da safe da yake Lahadi ce yana makale da ita sai gurin tara sannan ya tashi ya yi wanka.

Tayi ta tabara wai ya gaji da ita ba za ta iya tashi ta shiga kicin ba. Ya ce

“Zauna in shigar miki.” Shi ne ya hada musu abin kari, tayi wanka, tayi kwalliya suka karya. Ya ce, “To bari ya je ya duba lafiyar sauran Jama’ar gidan.

Nan ne ta

ɓ

ata rai, wai haka jiya ai ita bai zo ya duba ta ba, kuma ta fito taga ya dauki Amna. Nan t

ake ya dauke ta da yake Nafisa irin matan nan ne marasa kiba, sai dai tana da dan tsawo. Amma sanfurin jikinta, sanfuri ne irin wanda zai yi wuya tayi kiba ko me zata ci.

Ya ce, “To dauka dai gashi na dauke ki ina zan kai ki? Ranta yayi dadi ta ce, “K

a kai ni dakina.” Ya dire ta kan gado, a kunne ya rada mata wata magana da ta sata fashewa da dariya, tare da saka kanta cikin filo. Yayi mata cakulkuli ya fita ya barta tana dariya.

Sha biyu ya gani lokacın da ya kalli agogon falon Amina. Lallai yau hira

tayi dadi tsakanin shi da Nafisa. Ya samu Amna zaune tsakiyar gado

tana waya da ‘yan gidansu. A yanayin maganarta ya gane cewa ‘yan gidansu sun sani, ta fada musu kenan.

Ya zauna suyi da wannan, wannan ya kira. Bayan ta gama ta dubi Shatima, “Su Mom sun

a gaida ka.” Ya ce, “Ina amsawa. Ya jikinki?” Ta ce, “Naji sauki.” Ya ce, “To kin yi karin kumallo?” Ta ce, “Eh, su fa suka tashe ni da kiran waya. Yanzu kam dole in tashi in yi wanka in karya don Direba yana hanya zai zo mu tafi.”

Cikin mamaki ya ce, “In

a?” Ta ce, “Gida mana! Dad zai sa a duba ni na musamman. Shatima ya ce, “Ba ki fada musu cewa an duba ki a nan ba?” Ta ce, “Na fada musu, ka san Dad baya son wasa da lafiya.” Ta fadi tare da sauka ta nufi bayi.

Shatima yayi shiru kanshi a daure, lallai wa

ta

sabuwar matsala kuma zata kunno kai a gidan shi.

Shi ne mijinta shi ya kamata a nemi izininsa kafin a fada mata, shi ne ya kamata ya fada mata cewa Dad ya ce za ki je Kano a sake duba lafiyarki, amma sai gashi ita ce take bashi labari, babu wani neman

izini. Jiki babu karfi, ya shige zuwa gurin Aliya. Yanayin da ta ganshi taso taji ko menene, amma ta

san ba zai fada ba. Haka Salma duk shirmenta sai da ta lura cewa yau din yana cikin damuwa.

Domin taga be tsokane ta ba. Ya dai miko mata kudin nama.

Ta ce, “Me zata dafa?” Ya ce, “Tayi abinda take so. Gaba daya sai ya ji gidan yayi masa kunci. Dakin Nafisa ya nufa ya dauki makullin mota ya fita.

Shi kanshi bai san ina ya dosa ba don yana bukatar shawara. Titin da zai kai ka filin bajakoli nan yasha kw

ana ya tsaya, saboda akwai karancin zirga-zirga a titin. Ya kifa kanshi a kan sitiyarin motar.

Kamar minti daya ya dago, ya dauki waya ya shiga kiran layin Munnir. Babu jimawa Munnir ya daga, tun daga gaisuwa Munnir ya fahimci akwai matsala. Ya ce, “Ya ya

abokina, naji muryarka wata

kala?” Ya ce, “Akwai matsala.” Ya karanto mishi

komai. Munnir ya ce, “Tabdi! To ai tun da wuri

zaka yi maganin wannan matsalar ba sai ka bari

tayi girman da zaka kasa magance ta ba.”

Shatima ya ce. “Ta ya ya? Ni bana son n

e a ce daga aure dududu ko wata biyu ba mu cike ba amma na soma kuno da matsala.”

Munnir ya ce, “Kai da ka ke da basira ma, kayi kokari sosai fa, da harka tara mata guda hudu zuwa yanzun babu wata matsala ko wani korafi.

Mace daya ma in ka aje in ba a yi

sa’a ba kafin kuyi wata daya makota sun soma jin ku.” Shatima ya ce, “Ai kaina ya kulle, basirar tawa duk ta toshe, ka riga ni aure dai, ka san kuma yanda kowane Maigida yake takama da ikon gidansa.”

Munnir ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “To sai a ce a

n tauye maka wannan ikon.” Munnir ya ce, “Abin da yafi kawai ka cije ka hana, ka ce ba ka bada izini ba, nasan dai za a dan samu fushi da sauransu kayi lallashi daga baya. In ko ba haka kayi ba, tabbaci hakika matsalar ta samu gindin zama.

Shatima ya ce,

“Haka ne, bari in koma gidan kawai da na fito ne nayi fushi a kan in sun tafi suma wuce Kano don ni.” Munnir yayi dariya. “Ai ka tsaya a namijinka nawa.”

Shatima ya ce, “Har ina son in kira Hajiya itama in ji ta bakinta.” Munnir ya ce, “Kar ka sake kayi w

annan kuskuren, domin zaka yi da na sani a gaba. Bari in fada maka wata magana abokina, duk rintsi kar ka sake ka sako iyayenka a cikin abin da ya shafi matsalar gidanka.

Na farko zaka jona raini tsakanin Mahaifiyarka

da matarka, domin ka san suma iyayen

mu sai a hankali, basa so a ce kaza laifinmu ne, don haka sai kaga sun dora mu kan shawarar da mu zamu fitamma zamu cutar da iyalanmu.

kuma kayi rashin sa’a a goyi bayan matar kai kuma kiri-kiri ka dinga cutuwa. Don haka kar ka sake ka zama mai kai matsal

ar cikin gidanka ga Mabaifiyarka, shi ke haddasa irin rikicin nan na tsakanin sirika da sarakuwa, wanda har yanzun an kasa cimna nasarar kawo karshen wannan lamarin shekaru masu yawa.

Kawei abokina ka zama wanda kullum iyalansa suke ganin girman darajar i

yayensa. Su kuma iyayenka kullum kana fada musu labari mai kyau, mai faranta rai daga iyalansa.

Kai ko wata ce cikinsu ta kai kararka gurin Mahaifiyarka, in kaje kar ka ce ita ce ta min kaza da kaza, ka ce ayi hakuri zaka gyara.”

Shatima ya ce, “Amma dai

na gode da wannan shawara, in Allah Ya yarda zan kiyaye. Shi yasa a ka ce me shawara aikin sa baya baci, sai dai asirinsa ne a tone.” Suka sa dariya, sannan suka yi bankwana kowa ya kashe waya.

Ya aje mota ya nufi dakin Amna. Tana zaune a kan Dining tana

cin kwai da Tea. Ya kalleta, “Sai yanzun ki ke karyawa?”

Gira ta daga masa alamun “Eh.” Ya ce “Me yasa? Ki daina wasa da abinci ba fa ke daya ba ce yanzu.” Ta ce, “Na gama hada abin da ni ke bukata ne, kar ya zo ya yi tajirana, ban dauki kayan sawa ko da

ya ba, don ina da kaya a gida a dakina. Ko lefena ma yana can…” Ya katse ta da cewa, “Ina wai za ki je ne kina ta fadin kar ya zo ya yi ta jiranki.”

Ta cc, “Sau nawa zan fada maka cewa Dad ya ce a zo a tafi da ni.” Ya ce, “Amma Dad din bai fada min ba. Ya

za ayi ki tafi ba tare da neman izinina ba

Cikin mamaki ta kalle shi ya wani hade rai. Ta ce, “Dad dina fa na ce, ko ba ka ji da kyau ba ne?” Ya ce, “Naji ki sosai, amma tafiyarki kiran Dad din naki ikona ne ba ikonsa ba, don haka bisa ikona babu in da z

a ki je, ki kira shi direban a waya ki ce masa ya juya.”

Ta mike a fusace, “Shatima kana son ka ce min za ka hada kanka da Dad dina? Shi ne fa ya haife ni ya raine ni, ya sani Makarantu mafi tsada a in da muke, har waje ya kai ni a can ka ganni ka ce,

ka

na sona. To don Allah ka dawo cikin hankalinka bana son mu samu matsala, don… ihun murna da Summy ta shigo da shi, shi neya katse Amna daga zafafan maganganun da ta

tanada don fesar ma mijin nata. Ta rungume

kanwar tata, tare da nuna murnar ganinta. Suma

yya ta kai hannu ta shafi cikin Amna tare da fadin “Na riga Dad taba Baby.” Amna ta saki dariya tare da tambayar ko sun yi muhawara ne? Sumayya ta ce “Ai ba su san na biyo dircba ba, domin Dad yacd babu wanda zai fara shafa Baby.”saishi

Amna cikin dariya

ta kalli Shatima, wanda ya harde hannu yana kallonsu. Ta ce, “Honey dubi son kudi irin na Summy. Bai ce komai ba, Sumayya ta dan risina “Ina yini Ya Shatima, ban ganka ba fa.” Ya ce, “Ai ba za ki ganni ba, idonki ya rufe.” Suka yi ciki suka bar shi nan tsa

ye.malala

Kafın yayi wani tunani har sun fito, me aikinta dauke da dan karamin akwatinta. Sumayya da me aikin suka yi gaba, bayan ta ce “Yaya har da kai zamu?” Ya ce “A ‘a ina da office Summy.” Ta ce, “Yau Sunday.” Ya ce, “Gobe ni ke nufi

nima.” Amna ta

kalle shi, “Honey sai mun yi

waya.” Ya ce, “Za ki tafi ba da izinina ba? Za ki tafi cikin fushin Allah da tsinuwar Mala’iku?”

Amna ta ce, “Ni ban gane zantukanka ba, in ka gama fushin zamu yi waya.” Ta fice abinta. Bai fito ba har sai da ya daina jin sau

tin motarsu. Ya fito ya kulle dakin ya nufi dakin Nafisa.

Kan kujera yaje ya zauna ya zabga tagumi. Nafisa ta zo ta zauna kusa da shi, ta dafa shi. “Lafiya kuwa?” Shatima ya ce, “Kanshi ke ciwo.” Ta ce, “Gashi babu magani a gidan ko za’a aiki direba ne ya

siyo?” Ya girgiza kai tare da lumshe

ido. “Gajiya ce da kai-kawo, in ya dan huta zai daina.” Ta rage TV sannan ta ce, “In baka guri ko?”

Ya ce, “Ta zauna.” Ya janyo ta jikinshi suka yi shiru. Yana ta son ya danne bacin ranshi, yana karanta ma ranshi cew

a ga wasu matan nan yana da su, me zai sa ya damu kansa da bakin ciki don ta tafi? Amma duk da haka ya kasa.

Ya mike zumbur! Nafisa ta bi shi da kallo. Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikinshi zuwa shadda. Yasa hula da takalmi, yana saka turare Nafisa t

a shigo. Ya ce, “Zariya zan je.” Ta ce,

Lafiya kuwa?” Ya ce, “Lafiya lau.” Ta ce “To sai ka dawo.”

Ya leka dakin Aliya, ya ca “Beri ya shiga Zariya ya dawo.” Ta ce. “Allah ya tsare hanya.” Ya isa gun Salma. Tana jin ya ambaci Zariya ta daka tsalle ta ce,

“Yaya in zo muje?” Sai ya ji wani mugun bacin rai ya taso masa tamkar ita ce Amna.

Ya shigo rai bace “Ina za ki zo muje? Don na ce za ni Zariya za ki ce ki zo muje, ni sa’anki ne? kin san me zan je yi ne? in ki ka kara yi min irin wannan sai na miki duka

n tsiya!”

Salma ta tsorata iya tsorata, jikinta sai kar

karwa yake, tana mamakin dama haka Shatima ya

iya fada? Tsaki yaja sannan ya fita. Tayi ta kuka,

Tsonsa ya darsu a zuciyarta.

Kai tsaye gidan su Munnir ya nufa, don ya kira shi cewa ga shi nan za

i shigo Zariya ina zai same shi? Ya ce, Gida. A kofar gida suka tsaya don ya ce ba zai shiga ciki ba.

Ya ba Munnir labarin yanda aka yi da yaje gidan. Munnir ya ce, “To fa! Ai shi kenan tunda an riga an yi.” Shatima ya ce, “Kar ka ji yanda raina ke baci,

ni kaina ai zam fi so a ce suna kusa da ni

ina ririta cikina. Amma nayi alwashi a zuciyata ba zan je ba har ta dawo.”

Munnir ya ce, “In kayi haka ba laifi ba ne, amma kar kayi. Ka kira waya kuma kaje. Ta yiwu su basu da ilimin sanin mahimmancin aure, ko

bambancin da ke tsakanin miji da kuma iyaye. A hankali za ka ke nusar da ita, har ta gane. Kai

kuma ka kwantar da hankalinka, ka sani ma ko

cikin sauran wata na da cikin?”

Shatima ya ce, “Nayi ta kokarin in cire abin a raina, amma na kasa.” Haka dai Mun

nir yayi ta ba shi shawara kafin suka rabu. Yaje ya gaida su Hajiya, take tambayarsa “Lafiya da yamma?” Ya ce, “Lafiya lau, yaje gurin Munnir ne akwai abin da suka yi.”

Ta ce, “Ina mai jiki fa, laulayi da sauki?” Ya ce, “Ta ma tafi gida dazun.” Hajiya ta

ce, “Gida kuma?” Shatima ya ce, “Eh, ai za su dubata na musamman ne.

Hajiya tayi dariya, “Kadan da aikin masu hali, shima dan zai ga gata.” Shatima dai ya ce, “Umm!” Ya mike yayi mata sallama.

A hanya yayi Magriba. Koda yazo yayi fakin ya jima cikin mota

yana takaici kafin ya fito. Har

[8/19, 11:38] Ummi Tandama

😇

: *

🏚

️

RANA DAYA BOOK 2

🏚

️

*

CHAPTER 13



*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account n

umber

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku

ta account number din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku c

ikin sauki*

ya nafi dakim Nafisa sai ya tuna yau a gurin Salma yake. Ya juya ya nufi dakinta.

Tana kan Darduma a can kuryar dakinta, tunda

tayi sallah ta kasa tashi, ga faduwar gaba don

lokaci-lokaci sai ta dafa Kirji. Matuka ta tsorata da

fushin Shatima, har yana fadin zai mata duka!

Tana jiyo sallamar Shi tsoro da fargaba suka

hanata amsawa. Ya aje• hularshi a kan kujera ya

nufi kicin. Ya dauko goran ruwa guda daya, ya zauna.

Duk da babu sanyi da ya daga sai da ya sha fin rabi

, sannan ya aje goran. Yayi ajiyar zuciya. Ya

dauki wayarsa ya kira Nafisa, tana dagawa ya ce ta kawo masa jakarsa nan dakin Salma.

Babu-gardama Nafisa ta dauko ta nufo dakin Salma. Da alamu wannan bacin ran na Shatima ya saka matan nashi, shiga tait

ayinsu, musamman Salma.

Tayi sallama a Rofar dakin ya daga murya ya

Ce Shigo mana, kin coge kamar wadda za a cinye

ta." Ta shiga ta mika mishi tare da fadin "An lafiya?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Lafiya?"

Ta wurga, ido tana kallon falon

Salma, cikin

mamaki duk da take ji a family ana cewa su Salma

matsiyata Ne bata yi tsammanin tsiyar har ta kai

haka ba.

Ta taba baki tare da fadin "Uhum!" Ya dago

daga kokarin da ya ke na ciro Laptop a Jaka ya ce,

"Ya ya?" Ta girgiza Kai

tare da sake kallon dakin

ta ce, "Babu komai,

' Ya ce, "To kina iya tafiya.

Ya fahimci dakin take ma wanna yatsinan.

Salma da ke ciki tana jin su. Lokacin tana ta

shawara a kan ta fito ko kar ta fito? Jin fitar Nafisa

sai ta yi ta maza ta

fito.

Cikin tafiya tamkar Wahainiya ta nufi kicin. Ta

dauko Tiren da ta jera kuloli guda biyu, daya farar

shinkafa daya miya. Sai dan karamin kwanon silba

da ta zuba naman yau farfesun shi tayi.

Ta bude dan kwandon da ta yanka ganyen latas

da kokumba, shima ta dora.Ta.zo ta dire tiren, kan ya zube ma saboda

yanda jikinta ke Bari ta sauke daga tiren ta jere, ta koma ta dauko cokali da plate, da goran ruwa da kofi.

Ta dago da niyyar tambayarshi ta zuba.mishi, sai suka hada ido. Cikin

sauri ta sadda kanta har da dauke numfashinta. Domin ta zaci zai antaya mata mari ne.

Jin shiru ta sake dagowa. Muryarta na rawa taCe.

"Yaya in zuba maka?"Na koshi.

* Ya fada a daKile. Da gudu ta mike kuma a rikice zata yi daki, tamkar ya kwashe d

a dariya sai ya dake yace.Ke" Kamar zata saki fitsari ta tsaya cak amma ta kasa waiwayowa.

Ya ce,

"Zo nan ki kwashe kayanki, ko nine zan kwashe miki?"

•Ganin rawar jikin tata zubar da abincin a kofar kicin, da rasa me zata yi sai ta fashe da kuka.

Yana kallonta yayi murmush: ya dauke kai Ta kwashe ta kai kicin, tazo ta haye gado ta kudundune.

Lokacin ne Shatima ya samu dama har ya yi dariya sosai. Sai kuma ya ji zuciyarsa tayi masa sauki. Ya yarda da batun Likitoci, da suka ce dariya tana rage d

amuwa.

Yana bude aiki zai fara, sai •yaga sakwanni a

Emel din sa. Tun karfe uku sakon ya shigo cikin akwatinsa, suna da meeting a Abuja karfe tara na safe.

Yayi hamdala da yaga sakon yanzu, da sai da safen zai gani.

Dole Zai yi bukin din jirgin

safe na karfe

takwas.Salma bata yi bacci sosai ba, tana jin Shatima

ya shigo har da gyara mata kwanciya. Tana jin shi yayi alwala ya tada nafila.

Da asubahi ta tashi tayi sallah, ta fito zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login