Showing 6001 words to 9000 words out of 37098 words

Chapter 3 - RANA DAYA BOOK2 COMPLETE

11 Nov 2026

14

kafi damuwa da al’amarinta fiye da na sauran.”

Yayi mu

rmushi, “Duk ba za ku gane ba ne. Kin gama abin da na sa ki?” Ta ce, “Eh, bari ma ka gani.” Ta ciro wayarta ta fito da hotunan Salma ta mika mishi.

Yana ta kallon su cikin mamaki. Ya ce, “Amma kin yi editing ko?” Ta ce, “Sam! Ban yi ba.” Ya ce, “Ashe “yar

small din tawa kyakkyawa ce.” Ya mika mata wayarshi, “Ki tura min su duka yanzu.” Ta ce, “To.”

Tun sha biyu gidan ya soma dinkewa da manyan mata, don yau ne bikin Hajiyar karo na farko da zata aurar da danta, kuma zai auri mata uku, don ta ce su ta sani

bata san ta hudun ba.

An tsara gurin zaman amaran guda uku sai gurin da ango zai zauna da abokansa guda biyu. Sai rumfuna wanda jama’a za su zauna.Tuni wadanda aka baiwa kwangilar abinci sun kawo tare da wadanda aka dauko haya don su raba abinci, su ne za

su ba kowa har abin sha. Sun tsara budar kan za’a fara shi karfe daya, don haka aka ce kowacce Amarya ana son ta shirya kafin lokacin. stil

Hajiyar da kanta tasa aka kawo mai kwalliya. Amna a ka fara yi mawa, sannan Nafisa. Lokacin da ta zo gurin Aliya

ta samu suna shawarar siyo mata audugar mata don taje alwala taga al’ada.

Sai da ta gyara jikinta bayan Aisha ta fita ta siyo mata sannan aka zauna zaman yi mata tata kwalliyar. Duk kayan da suka saka a lokacin Hajiyar ce ta bada aka dinka musu tun kafin

zuwan ranar.

Duk da ba a auna su ba, doguwar rigar ta zauna

ma kowa har tana jan kasa, kowace da kalarta. Koda

yake sai da sauran suka za

ɓ

a sannan aka kawo ma

Aliya.

Masu kidan ‘yan kasar Mali ne aka dauko, guri dai ya tsaru sosai. Mc abin magana ya s

oma fadin “A fito da Amare don ayi musu budar kai.”

Salma tana jiyowa tamkar ta fito kallo. Lokacin ne Badi’atu tazo dauko ma Ango wasu kayan shi da zai sa shi ma. Ta ce da Salma “Ki fito kiyi kallonki, don Hajiya tana fama da mutane ba za ta gan ki ba.”T

a ce, “In

wani ya fada mata fa?” Ta ce, “Ai babu wanda ya sanki bare ya fada mata din, ni kaina ai sai da Yaya ya aiko ni sannan na ganki.” Haka tabi Badi’atu cikin fargaba. Da suka fito

harabar gurin shagalin bikin ta ce, ta shiga kujerun

tsakiyar gurin

ta zauna. Ta shige ta saje da Jama’a.

Amna ce ta soma fitowa rigarta kalar bulu mai haske, an sha dogon takalmi, fuskarta rufe da wani mayafi da ke manne a jikin rigar.

‘Yan’uwanta ke yi mata jagora suna fesa mata abin kamshi har izuwa kujerarsu. Can sa

i ga Aliya itama, tata rigar koriya amma komansu iri daya.

Da suka zauna kuwa zai yi wuya ka gane wannan wace ce, wannan wacece a cikinsu. Nafisa ce karshen fitowa ita kuma tata kalar siminti, sun yi kyau amma ita da ta zauna kasan ita ce karamarsu.

Me a

bin magana ya ce, “Kai! Wannan Ango dangata ne, nan da shekara me zuwa ka cike ta hudu, duk shekara ka dinga kwasar jarirai guda hudu.” Aka sa dariya. Ya ce, “Yanzun ango muke jira, kafin ya iso ina ‘yan rawar nan su nishadantar da mu?”

Nan fa ‘yan Mali s

uka shiga rawarsu mai ban sha’awa. Salma daga inda take zaune tana jin wasu mata suna musu. Wata ta ce, “An ce fa matan guda budu ne.” dayar ta ce, “Surutun mutane ne, su ukune. Ya dai so yin ta hudun Hajiyarsa ta hana.” Salma a ranta ta ce, “Gani ni ce ta

hudun.

Can Ango ya iso da gayyar abokai. Shatima ya yi matukar kyau cikin shaddar shi Gizna mai ruwan zuma. Hula da takalmi masu ruwan kasa kalar zaren Hula da aikin.

Salma har mikewa tayi tana kallonshi, ya birge ta sosai. Sai da ‘yan bayanta suka ce

“Zauna mana, kin tare mana.” Sannan ta zauna tana sauraron yanda matan gurin ke koda haduwar Angon.

Shi kan shi mai abin maganar fadi ya ke, “Ga kasaitaccen Angon mu nan ya iso, kyakkyawan Ango ya iso sauran abokan suka je inda aka tanadar musu. Shi da gu

da biyu suka zauna a inda aka tanadar musu. Nan fa aka soma shirin budar kai, wata kawar

Hajiya aka kira ta bude taron da addu’a, sannan aka

bukaci Ango ya zo ya bude kan wadda ya zaba a

uwargida. Abokanshi suka rako shi, ya zo gabansu ya tsaya. Nan ya

dabirce domin ya kasa gane Aliya. Ya gane Nafisa don bata kai su girma ba, ya dan yi shiru, ya

kuma tsura musu ido yana son gano Aliya. Da bai gane ba sai ya ce, “Aliya!” cikin sauri ta amsa, Ya ko sa hannu ya daga ‘mayafin fuskarta. Nan aka dauki tafi da

guda. Aka ce danginta su zo su nuna cewa ita ‘yar dangi ce.

Nan fa dangi suka yi tsuru-tsuru tunda ba su san da wannan irin lamarin ba. Abin da ke hannun su suka zo suka zuba mata, ba ma sabbin kudi ba ne, mutane sai kunkunai suke yi.

Aka ce yazo ya bud

e ta biyu, ya zo ya bude Amna. Ita ma aka yi guda aka ce dangin ta su zo su fidda ta. Ruwan kudi suka shiga zazzage mata sabbi fil! Haka Nafisa.

Salma da ke kallon ikon Allah ta ce, “Allah na gode maka da kasa Hajiya ta ce kar in fito, da wa zai zo ya fid

da ni?”

Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki.

Ta bude dan tire din,

nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.

Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan y

a yi musu.

[8/16, 21:35] Ummi Tandama

😇

: _____

*

🏚

️

RANA DAYA BOOK 2

🏚

️

*

CHAPTER 4

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*



*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

`

``ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account num

ber din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*

Mun tsaya

Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki.

Ta bude dan tire

din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.

Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun ha

kan ya yi musu.

Shima haka aka umarce su su ba shi daya ta bashi nama, daya ta ba shi ruwa, daya ta ba shi tataccen ‘ya’yan itatuwa.

Tsarin bikin ya birge mutane sosai, daga nan aka shiga daukar hotuna. Tsakiyar Aliya da Amna ya zauna, sannan ya rungum

o su duka. Ya sake dawowa tsakiyar Amna da Nafisa, ya sake rungumo su. Sannan yayi da kowacce rungume da ita. Daga nan kuma aka shiga ci da sha na abinci. Ana cikin haka sai ga gara tazo daga gidan su

Nafisa mota guda, kayan abinci da kuloli, da

zannuwa,

da shaddoji.

Sai ga ta Amna ta linka ta Nafisa sau biyu, aka ce wannan ta iyaye ce, ta Ango an kai can gidan shi. Aliya ta rude, nan ta dauki wayarta ta yi wa Aisha kawarta text cewa taje gidan su ta ce a kawo garar nan, a basu duka har nata din. Can kum

a sai ga shi an kawo, haka aka dire gara

kashi uku. Salma ta sake yiwa Allah godiya da

wannan rufin asiri da ya yi mata, ta ma daina jin

haushin Hajiyar

Karfe hudu biki ya tashi, aka ce da an yi sallah za’a kai Amare gidansu. Nan kowace Amarya ta koma

gurinta don kimtsawa.

Salma ma ta tashi da gudu don komawa samanta, wani abin mamaki har karo suka yi da Hajiyar a

Halima Abdullahi K/Mashi

kofar falo, cikin sa’a bata gane ta ba, sai ta ce “Wannan ‘yar waye haka ki ke gudu, tafi a hankali mana.

Sa

lma dama bata waiwayo ba, sai ta tafi saf-saf ta haye sama ta fada kan gado.

Ko minti shida bata yi da shigowa ba, taji an turo kofar, a zatonta Badi’atu ce, don haka ta taso da ‘yar fara arta zata bata labarin karonsu da Hajiya, kawai sai taga Angonsu.

Ta sauko cikin tsoro ta ce, “Don Allah Yaya ka fita, kar Hajiya tazo ta sake marinka.” Ya juya ya murda makulli, sannan ya dawo cikin tausayi. Ya ce, “Kiyi hakuri da zaman wuri daya, yanzun za ki fito, don yanzun za a kai ku.”

Tayi murmushi, “Ai na fito.

Badi’atu ta ce in fito

in yi kallo. Naga kun yi kyau sosai da matanka.”

Kalamanta suka sa tausayinta ya sake tsirga mishi. Ya ce, “Dama kina kallon mu shi ne ba ki zo .gurinmu ba?” Ta ce, “Tab! In zo in

ɓ

ata muku

abinku! Hajiya ma zata yi fada.” Yayi sh

iru yana kallonta. Ta ce, “Kun yi kyau da

ku ka dauki hoton nan, ashe gaske ne mu hudu ne? To a cikin su wa ka fi so?”

Yayi ‘yar dariya, “Ke barda ke?” Ta ce, “Ai ni na sani ka tausaya min ne ba na cikin su.” Ya ce, “Ni

dai kina cikinsu kuma nafi son du

k wadda ta fi sona.

Ta ce, “To wa ce ta fi sonka a ciki?” Ya ce, “Ban sani ba tukunna sai mun zauna.” Ya ciro wayarshi, “Kema ki zo mu dauka.” Ya zauna a kan kujera, bata ankara ba sai taji ya kamo ta ya dora a kan cinyarsa.

Ya rungumota ya daga waya yan

a daukarsu. Wani abu take ji yana ratsa mata jiki, ta yunkura zata tashi, ya ce “Ki tsaya mu kara daya.” Ta ce, “Ya yi haka?” Ya yi dariya “To mu dauka a tsaye.” Ya sake kwantowa ta bayanta, ya matseta a jikinshi ya dauke su.

Wayar ta shiga ruri ya daga t

are da fadin “Munnir ya ce kazo mana mun fa idar da sallah.” Ya ce, “To bari ni in yi tawa in fito.” Ya shiga bandaki yayo alwala, a nan yayi sallah.

Ya ce ta shirya. Ta ce, “Kayanta ne kawai da ta

cire.” Ya bata wata leda ya ce ta sa a ciki. Ya fita ya

bar ta tana sallah.

Amna su ne suka fara tafiya saboda da motocinsu a hannu. Duk an kwashe Amaren saura Salma a sama. Shatima ya kira Anty Momiyo ya ce, “Ki ce ma Hajiya don Allah Salma a sama wai ga motar daukanta.”

Halima Abdullahi k/Mashi

Momiyo ta

ce, “Tab! Ni na ma manta da ita, to ta ci abinci ko?” Ya ce, “Ban sani ba Anty, in kun yi ki sa ai kayi bayani.”

Da sauri ta nufi gurin Hajiya, tana fadin “Hajiya

‘yar mutane a sama. Sai da Shatima ya ce a fito da

ita sannan na tuna ko abinci bata ci ba

.”

Hajiya taja tsaki, “Nasan ba zai barta haka ba. Da zai ce a fito da ita wa zai fito masa da ita? Sauran ba danginsu ne suka fito da su ba! Ta sauko su wuce.”

Hajiya Saliha ta ce, “Yanzun dai kin hana ayi wa yarinyar nan budar kai?” Hajiya ta ce, “Ai h

ar abin da ya fi budar kai ita ya yi mata, domin jiya har biyun dare yana dakin.” Nan suka dauki salati, ita kuma ta nufi dakinta tana fadin “Ba ni da lokacin su.”

Anty Momiyo da kanta ta hau sama, samu Salma tana zaune a kan abin sallah. Ta ce, “Au! Har

da kaya ki ka canza? To taso ku je, kin ci abinci ko?”

Salma ta ce, “Eh naci, domin na sakko kallo, da ana ba mutane nima aka bani na ci.” Anty Momiyo ta kalli Salma, “Lallai wannan yarinya ce, komai nata a kuruciya. Ji yanda take magana, iyakar gaskiyart

a kawai take fada.

Shatima yana tsaye Salma ta shiga bayan sabuwar motarshi, har ma sai da tayi mishi

murmushi. Ya zo bakin kofar, “Ke kadai ce ko za a bi ta gidanku a dauki wasu?”

Ta ce, “A’a, ai ina zaton fa duk suna Kaduna din gurin jere.” Ya ce, “

Ina zuwa.” Ya shiga cikin gida ya kira Badi’atu ta fito. Ya ce, “Ke ba za ki ba ne?” Ta ce, “Zan je tare da su Anty Momiyo zamu je, in an tashi Dinner kuma mu dawo.”

Ya ce, “Dinner da za’a tashi sha biyun dare, karfe tara za’a fara. Sai dai ku kwana. To k

i zo ku zauna da Salma kuje tare, don Allah ki taimaka mata gurin kwalliya, don har da ita a dinner tunda wannan na abokaina ne.”

Badi’atu ta ce, “To bari in kwaso kayan da zan yi amfani da su.” Shima ya koma gurin Salma ya ce, “Ina kayan da na ce ki dink

a su za ki sa a Dinner?”

Ta ce, “An dinka suna gidan mu.” Ya daga waya ya kira Auwal ya ce, “Ka amso min kayan Salma yanzun ka kawo min gidanmu.” Auwal ya ce, “Ai an tafi da Akwatunanta duka can Kaduna din.” Shatima ya ce, “Yauwa, hakan yayi.” Badi’atu ta

na fitowa suka kama hanya.

Kowace Amarya tana gefanta da danginta suna kara kintsa mata guri, amma fa na Amna tun kafin ka shiga za ka hangi bambanci wanda iyayenta suka mata, har da wata Rumfa suka aje mata irin ta zamani kusa da na ginin don ta aje moto

cinta.

Rumfar zata ci a kalla mota biyar. Sannan ga furanni na zamani da aka jera mata. Nafisa da taji ana labari, har ta zo iya wuya, wato ita don ‘yar masu kudi ce shi yasa yake bambanta komai.

Haka da su Shahida suka shiga gurin Amna din suka ga dun

iya a tsire suka fito a rude suna labari. Suka ce, “Hatta fentinku na ciki ba iri daya ba ne.” Nafisa ta ce, “Ai ni na sani sai yafi sonta, kuna fadin ba dole ba ne ya zama haka.

Salma kuwa suna tafe tana kallon ‘yan kauyukun da ke tsakanin Zariya da Kadu

na, har tana tambayar Badi’atu “Nan ina ne?” Badi’atu ta ce, “Wai ba ki san Amarya shiru take yi ba?”

Usman da ke gaban mota ya ce, “Ai wannan Amaryar ta daban ce.” Salma ta ce, “To kuma an ce tambaya mabudin ilimi ce.” Ya ce, “Haka ne.” Badi’atu ta ce, “

Ba ki ta

ɓ

a zuwa Kaduna ba?”

Salma ta ce, “Tab! Ban taba fita daga cikin garin

Zariya ba.” Suna shiga cikin Gate din gidan Salma ta bi gidan da kallo, har kofar falonta motar ta tsaya. Su Yaya Hadiza suka fito suka tare ta zuwa ciki.

Badi’atu ta wuce nem

an gefen Nafisa, Salma tayi ta kallon ko’ina, har suna ce mata wai ba ta da kunya, tana leka ko’ina.

Kujerun sun yi tsurut! A falon saboda girmansa, ga kujeru uku rak! Ta shiga dakin gadon yafi kyau. Sauran dakunan dai ba komai, sai dan tarkacen da aka

sa mata.

Kicin kuwa shima a rame. Amma dadi ya cika zuciyar Salma, tana ganin kamar babu macen da ta kai ta sa’a a duniya, wai nan gidanta ne.

Kafin lokacin zuwa Dinner duk Amaran suna

cikin shiri, domin Ango da kansa ya kira kowace ya

ce ta zama cikin

shi. Salma ce dai da bata da waya ya kira Badi’atu ya ce ta shiryata da kyau kafin karfe tara.

Ya zaci Amna zata yi masa gaddama tunda ta ce, “in dai ‘yan’uwanta suna nan sai ya ji ta ce za su shirya da wuri.

Salma tayi matukar kyau cikin riga da siket

na

pink din material. Kayan sun kama ta tsam! Duk da

ba ta da kiba ko kadan, ‘yar singila. Badi’atu ta daura mata dankwali, sai tayi matukar kyau, tana ta kallon kanta a madubi. Mota daya aka so a dauke su, amma Amna ta ce a’a ita tana da motarta.

Nafis

a ta ce ba za ta zauna da kowa ba. Shatima ya kira Aliya a waya, ya ce za a dauko su da Salma ta ce ‘To.”

Shahararren Hotel ne in da za’ayi Dinner. Hall din kuma mai kyau da tsari, ba’a bari kowace Amarya ta shiga ba, sai da suka zo su duka.

Fuskar Naf

isa tam babu fara’a, Amna kuwa zuciyarta cike da tambayar wannan wacece a cikinsu? A tare suka fito, shi ne a gaba sai Amna da . Aliya, Nafisa da Salma na biye da su, kowace da kalar shigarta.

Kujerar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login