Showing 18001 words to 21000 words out of 37098 words

Chapter 7 - RANA DAYA BOOK2 COMPLETE

11 Nov 2026

16

/>
i mijin ya yafe mata fa kuma ta roki Allah?” Ya ce, “Za su yafe amma mijin zai rage sonta.” A ranta ta ce, “Ashe dai ina da mafita. Ya ma daina sona ba rage so ba

Ta dauki kwan ta ce, “Ni ga abin da zanci.” Ya ce, “Ke nan ba za ki ci kazar ba?” Ta ce, “Ka

yafe min zan roki Allah Shima ya yafe min.” Yayi dariya, har ya kusa kwarewa.

Ta bude ruwa da sauri ta mika mishi. Sai da ya sha sannan ya ce, “Ke ba Amarya ba ce yau.” Ta ce, “In dai don wannan kazar ne naji.” Ya ce, “To sai ki fada min me yasa ki ke gu

dun kazar ki ta daran farko?”

Tayi shiru. Ya ce, “Ina jin ki, in ba ki fada ba zan matse bakinki in baki.” Ta ce, “An ce biya ake, ni kuma dai ba zan iya ba.” Ta tsura mishi ido taga yanda zai dauki zancen.

Yayi murmushi mai sauti, “Biya kamar ya ya?” Ta

ce, “Nima dai ban sani ba, amma dai haka naji.” Ya ce, “Gurin wa?” Ta ce, “Wata Amarya ce a kauye ta ce haka.”

Ya daure fuska, “Ok! Dama kuna yin irin hirar nan mace take tona sirrin gidan mijinta?” Salma ta ce, “A’a ni ba ruwana.” fuskarshi a daure tam!

Ya nunata da yatsa,

“Ko da wasa naji kin ba da labarin abin da ke tsakanina da ke, ko maganar da muka yi, sai na bata miki rai, kina ji na?” Ta ce, “Wallahi ni ina jin kunyar fadi ma.”

Ya ce, “Ci kazarki, ni ba sai kin biya ni yanzun ba, nan gaba dai ki

n biya ni ko?” Ta daga kai. Ya dauki wani yanki ya ce, “Bude baki to.” Ta amsa. Ya ce, “Ko ke fa! Kina ta wani boye kirji ashe ma babu komai.”

Ta rufe fuska da hannunta daya. Ya ce, “Yanzun me da me kike so a nan dakin? Kin ga sauran suna da TV da Fridge,

ke ko hita din nan kina bukata.”

Ta ce”Ni dai in sona ne kawai a bar komai a sani a boko da Islamiyya.” Ya ce, “To shi kenan. Amma zan sai miki kettle na dafa ruwan zafi, don ki ke tashi da wuri kina hada min koda tea ne, kar in yi lattin gurin aiki. Kem

a in kin soma zuwa Makaranta kin ga za ki ke shiryawa da wuri.”

Ta ce, “To Yaya.” Ya ce, “Ba za ki daina ce min Yaya ba wai?” Ta ce, “Ni ban san to abin da zan kira ka da shi ba.” Yayi murmushi, “Shi kenan, shima na daga miki kafa zuwa nan gaba. Ki gama c

i kije ki wanke baki, sai ki kwanta don ki tashi da wuri ki min abin da ya kamata, don kar in yi latti ko?”

Ta ce, “To Yaya.” Sannan hankalinta ya kwanta.

Shi ko falo ya koma yana cewa na biye miki ina da aikin yi. Ya ciro Laptop din shi ya shiga aikinsh

i. Tabbas Salma ta birge shi, domin tana idar da sallar Asubahi yaga ta nufi kicin ta kunna Risho, domin shi a kan doguwar kujerar yayi kwanciyarshi bayan ya gama aikinsa.

Har zai shiga ciki sai kuma yayi tunanin kada ta tsorata da shi in ta farka, bare y

asa ta kashe wuta

Ta ce, da ruwan zafi zai yi wanka? Ya ce, “Ai bayin akwai na’ura mai dumama ruwa.” Ta ce, “Ita bata sani ba.” Ya ce, “Zo ki gani.” Ya nuna mata inda zata kunna ruwan ya dahu, da kuma in

da zata murda ya zo. Tayi ta al’ajabi, har ma tayi

masa tambayar da ta bashi dariya, wai ba za a iya diban ruwan ba a hada shayi? Yayi dariya sosai, sannan ya ce,

“Amma ina ki ka taba ganin an sha ruwan bayi?” Itama tayi dariya, ta nuna na’urar da ake tsarki da ita, “Wai wannan to mene ne amfaninta?” Ya

ce, “To kin gá dai wannan ruwan zafin shi an yi shi ne saboda in ba ka bukatar ruwan sanyi, ko kuma lokacin sanyi. Shi kuma wannan na tsarki ne, in ka gama

bayan gida ko fitsari, kin ga ba a bukatar buta.” Ta

saki dariya, “Ka san ni wanka nike yi da shi

abuna?” Ya ce, “Wanka?” Ta ce, “Na zata wancan na saman na ganshi da fadi na manya ne, wannan kuma na yara, shi ne na ce ni yarinya ce.

Ta nuna jerin sabulun wankanta da ke saman kwamin wankanta, ta ce “Kaga wadancan ko? Anty Badi’atu ta jera min su, sann

an ta nuna min amfaninsu.”

Ya ce, “To ban da wannan me ki ke son sani?” Ta ce, “Shi kenan.” Ya ce, “To zo ki taimaka min in yi wanka?” Ta fita da sauri tare da fadin “Sai ka fito.”

Yayi kyau cikin kananan kayan da yasa, ya ce “Ya ki ka ganni?” Lokacin da

take aje masa kayan shayi. Ta sake kallonshi. “Kayi kyau Yaya, dama kai me kyau ne.

Ya dauki flaks din ya tsiyaya ruwan zafin a kofi ya ce, “Sai dai sona ne da ba kya yi ko?” Tayi dariya, “Ni ai ba zan iya sani ba.” Ya ce, “Na ce ki nemo yanda ake so da

mene ne shi kanshi son amma kin ki.”

Ta ce, “Ban san ina zan nemo ba.” Ya ce, “Shima na daga miki kafa zuwa nan gaba.” Ta bude biredin sannan ta bude robar bluebond “In

shafa maka?” Ya ce, “A’a, ko kina son in yi

kato?” Cikin dariya ta ce, “Eh mana.” Ya

ce, “Saboda me?” Ta ce, “Saboda bana son a ce kayi aure kuma ka rame.” hankali?” Ya ce, “Ashe wani lokaci kina da

Ta ce, “Au! Da ni Mahaukaciya ce kenan?” Ya ce, “A’a ban ce ba, sai dai ke yarinya ce, baby ce ke.” Zata yi magana ya ce, “Ke kin dinga cin

wannan din ko ke ma kin yi katuwa.”

Bai lura da yana biye ma shirmen Salma, sai kawai yaga karfe bakwai ta gota. Ya ce, “Kai! Nayi latti.” Ya mike ya dauki Jakarsa, bata tashi daga inda take ba ta ce “Sai ka dawo to Yaya.”

Hannu ya daga mata ya wuce. Mot

arshi ya nufa kai tsaye a ranshi ya ce zai kira su a waya in ya je office.

Aliya da ke tsaye a jikin window din ta mamaki da al’ajabi ya cika ta. Me yasa yau da ya kwana a ďakin yarinyar nan ya makara? Sannan bai zo in da suke ba?

Nafi ta kalli agogonta,

“Bari ya shigo taga

minti nawa ita kuma zai mata.” Tana ganin ta haka

zata iya gane wadda ya fi so cikin su uku, domin

tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta.

Sai dai har karfe takwas bai shig

o ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya.

Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina

lafiya?”

Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.”

Ya dan yi jim, me hakan

ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi.

Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko

ko me? Ya juya ya shiga ki

ran layin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake

[8/18, 17:28] Ummi Tandama

😇

: _____

*

🏚

️

RANA DAYA BOOK 2

🏚

️

*

CHAPTER 9

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan litt

afin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09

068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*

Mun tsaya

tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta.

Sai dai har karfe takwas bai shigo ba,

gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya.

Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiy

a?”

Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.”

Ya dan yi jim, me hakan ke nu

fi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi.

Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko

ko me? Ya juya ya shiga kiran l

ayin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake

shigowa. Ta daga cikin daure fuska tamkar tana gabanshi.

Ta ce, “An tashi lafiya?” Ya ce, “Lafiya lau, kin karya kuwa?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kan me

sweety?” Ta ce, “Ba ka ki zuwa ba, kila ma kaje ka duba kowa ni ce ban da matsayin da za a zo a duba ni.” Muryarta ta soma rawa alamun kuka.

Ya ce, “Haba Nafisa! Ki min kyakkyawan zato mana, tun yanzun za ki soma dora zargi a tsakaninmu? Gaskiya ban ji d

adi ba. Na makara ne shi ne dalilin da yasa na tafi office na ce zan kira ku in ji lafiyarku.”

Ta ce, “To kayi hakuri.” Ya ce, “Ya wuce, amma kar ki sake. Sannan ki nemi abinci ki ci.” Ta ce, “Zan yi yanzun.” Ya ce, “To babu kuma wata matsala?”

Ta ce, “B

abu komai, sai ka dawo. Kayi tunanina.” Ya ce, “Zan yi, kema kiyi tunanina.” Ta ce, “Kullum kana raina.”

Aliya tana ta kai-kawo a cikin dakinta tsakanin kicin da dakunanta, abin karinta take dafawa. Taliya ta ke son ci dafa-duka ta manja, sai dafaffen kwa

i.

Sannan tana son hada shayi, zuciyarta kuwa cike da son sanin abin da yasa har ita da take ganin ta kai a zuciyarsa bai iya zuwa ya dubata ba.

Sannan tana son jin shin me ya faru jiya da ta ga rufe kofar Shatima bayan ya fito daga dakinta ya dau kaya

, ta zaga gurin windown Salma ta baya, taji kukan Salma tana fadin “Don Allah Yaya kayi hakuri..” amma bata ji muryar Shatima ba duk da tasa kunne sosai.

Kuma kukan na Salma yafi yi mata kama da kukan shagwaba fiye da kukan laifi. Karar wayarta da ke jone

a chaji ne ya sa ta fitowa da sauri, don tasan Shatima ne, domin ta ware masa ringing dinsa na musamman.

Tana dagawa ta ce, “Masoyina!” Ya ce, “Kin tashi lafiya abar sona?” Ta ce, “Lafiya lau.” Ta sauke ajiyar zuciya. “Na zuba idanu ban ji ka ba. Ya ce”Y

au nayi latti ne my love, shi yasa na ce bari in ji ya ki ke, cikin bai kara ciwo ba ko?”

Ta ce, “Bai kara ba, dama yana min haka ko a gida, wani lokacin cikin dare zai tashi.” Ya ce, “Kuma ba ki taba ganin Likita ba?” Ta ce, “Na gani sosai ma aka ce wai

ba komai, zan daina lokaci ne.”

Ya ce cikin muryar tausayi, “Allah Ya baki lafiya.” Ta ce”To Salma ta sha’afa ne bata tashe ka da wuri ba?” Tayi maganar cikin son ta ji kurilla.

Ya ce, “Wannan baby din kin san sai dai ni in tashe ta, kuma kin san tayi ko

kari gurin bani abin kari da wuri, ni kaina ban san me yasa ni yin latti ba.

Ta ce, “Soyayya ce tayi dadi.” Ya ce, “To, soyayyar ce gata nan kala-kala, kowacan ku da irin wadda take bani. Yau dai kina fes-fes ko? Don ke yau ne amarcin naki, kyalli na koya

cika cif.”

Tayi ‘yar dariyar tsokana, “Ai ko har yanzun ban yi fes ba.” Ya ce, “Haba dai, har ina cewa ke yau in mun zo me tazarce ne, dan watanni mu dauki baby.”

Cikin jin kunya ta ce”Haba dai?” Yayi ‘yar dariya, “Sai na dawo ke dai ki sa mu cikin addu

’a.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Tana kashe wayar ta ce, “Allah Ameen. Allah Ka sa ni zan soma dire da a gidannan, kuma namiji yanda ni ke Yayarsu haka ma dana ya zama babbansu.”

Aliya ta kammala karin kumallonta tana zaune shiru ta kasa kwashe kayan, tunda

bata ji abin da

take son ji ba a gurin Shatima, ya kamata ta bigi cikin wannan wawiyar yarinyar cikin dabara.

Dan kwanan silba ta samu ta shake da taliyar, sannan ta saka kwai guda daya ta nufi sashen Salma.

Salmar tana wanke-wanke a cikin kicin ta jiyo

sallama hade da kwankwasa kofa. Ta dauraye

hannu ta fito. Ganin Aliya sai ta saki fara’a “Sannu da zuwa Anty.” Ta saki fara’a itama “yauwa sannu kanwata. Na ce tun da ke ba ki zuwa gaida ni ni bari in zo mu gaisa.” Salma ta ce, “Lah! Ba haka ba ne Anty,

ki zauna mana.”

Aliya ta zauna a hannun kujera, tare da fadin “Ban sani ba ko an hana ki ne.” Ta ce, “Haba Anty, wa zai hana ni? An dai ce min ne kada na ke shiga dakunan kowa.”

Ta tsugunna tana gaida Aliya. Ta amsa tare da

fadin “Tashi ki zauna a kan

kujera.” Ta mika

mata, “Ga taliya ko kema abinci ki ka dafa?”

Salma tasa hannu biyu ta amsa tare da fadin “Na gode, ba abinci na dafa ba, Biredi na ci.” Ta ce, “Ai bani iya cin biredi kullum.”

Salma ta ce, “Ni ai duk abin da na samu bana tara.” Aliya ta

yi dan murmushi, “Kin huta.” Tayi

dan kalle-kalle a dakin. Salma ta ce, “Kin ga nawa dakin bai kai naku kyau ba ko?”

Aliya ta ce, “Ai wannan duk ba wata matsala ba ce, sannu a hankali za ki sai duk abin da ki ke so ko?” Salma ta zaro ido. “Ina zan samu k

udi, ni dai na gode ma Allah Anty tunda na samu mijin daba irin gama-garin maza din nan ba.”

Aliya taji mamakin kalamin Salma, har ma ta kasa boyewa. Ta ce, “Har kin san namiji me inganci?” Salma ta rufe fuska cikin kunya. Aliya ta ce, “Ashe kin iya soyay

ya shi yasa ki ka sa Angon naki ya makara?”

Salma tayi yar dariya, “Ni ban san wata soyayya ba Anty, shima ya sani.” Ta ce, “To ai jiya ina jiyo ki daga dakina kina kuka.” Salma ta zaro ido tana kallon Aliya.

Aliya tayi ‘yar dariya, “Ai ina ji kina kukan

shagwaba, Yaya kayi hakuri.” Salma ta rufe fuska. Aliya ta harare ta, lallai abin da take zato haka ne. Ta ci gaba da fadin “Har zan shigo ceto na zaci

laifi ki ka masa.” Salma dai tayi shiru. Aliya ta ce.

“Ko wani abin ki ka yi masa?” Salma ta sake ruf

e fuska tare da fadin “Babu ruwana, ya ce kada in fada ma kowa.” Gaban Aliya ya fadi, tayi shiru. Can ta ce, “To ai ba zan

fada mishi ba, ni na dauke ki kamar kanwata ne, duk abin da ki ka yi ba daidai ba zan nuna miki. Kuma shima ya bamu amanarki.”

Salm

a ta ce, “Ni dai kiyi hakuri Anty, tun da ya ce kar in fada ma kowa.” Aliya ta ce, “Shi kenan. Juye ki bani kwanon.” Salma ta ce, “Ki bari in na wanke zan kawo miki, dama naga dakin kowa naki ne ban gani ba.

Aliya ta mike, “To sai kin zo. Bayan ta koma sa

shenta, tana zaune a cikin dakinta tana ta nazari. Yanzu Shatima saboda rashin hakuri ga su su nawa sai da ya kula wannan ‘yar yarinyar saboda ja musu raini?

Duk da ta ki fada alamu sun nuna akwai abin da ya faru tsakaninsu. Sai dai zata gwada kishin yari

nyar ta gani kowane irin so take yi wa Shatima.

Ba ta ki ace ita kadai ba ce da Shatima, kuma

sannu a hankali da siyasa burinta duk sauran su

zama a karkashinta, sai yanda tayi, sai kuma yanda ta ce. Salma ta gama komai, sannan ta janyo kofarta,

ta dau

ki kwanon Aliya ta tafi kai mata.

Ta same ta tana zaune tana kallon TV, don rana daya yasa aka saita musu TV nan su, aka kuma saka musu Tauraron Dan Adam.

Salma ta shiga da sallama, Aliya ta amsa tare da cewa “Salma kanwar Anty.” Salma tayi murmushi, san

nan ta tsugunna.

“Sannu Anty.” Aliya ta ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login