Showing 36001 words to 37098 words out of 37098 words

Chapter 13 - RANA DAYA BOOK2 COMPLETE

11 Nov 2026

7

domin kareta a gurin Hajiya sai kawai taji Hajiya tace

"Badai shi Shatima ne yasata ba?"

Nafisa ta tabe baki "shiyasa ta mana Hajiya makaranta me shegen ts

ada"

Aliya tace "tsada ai ba kadan ba ma tsadar,kusan dubu dari harda doriya"

Amna ta kalli Aliya domin jin bakon lamari ita bata shiga harkar kowa batasan ma me akeyi a gidan ba.

Hajiy tace "Eyyeh!"

Aliya tace "to ai kudin shiga makarantar nan

dubu saba'in da biyar ne banda kudin motar dawowar ta da Kullum sai ya bada dari biyar ga kudin namanta da komai da yake badawa dubu daya,"Aliya takai karshen maganar tanajin dadin tasamu abinda takeso.

Hajiya ta kalli Salma cike da tsana tace hakane k

udin makarantar dubu saba'in da biyar?

Salma cikin rawar jiki tace "yanzu sun cike tamanin".

Hajiya ta mike da sauri tana fadin "lallai kam sun cike tamanin wato ke yakeyiwa aiki kenan kullum rana ta Allah dubu daya da dari biyar a wata nawa zai kama

? Jama'a kuyi mani lissafi?

Da sauri Amna tace dubu arba'in da biyar kenan zai kama duk wata"

Nafisa tace "Kan uba!! Muna zaune?"

Hajiya tace "to aikoni dana haifeshi idan ya yi man haka nasan ya kai daa"

Maman Nafisa tace "to shime yakaishi wa

nnan batan basira? Wai rokon Allah da goge"

Hajiya ta soma kiran layinshi ya daga tace "Ina gidanka Allah yasa ka kusa tashi" yace "insha Allahu nan da awa daya zan dawo" tace "saika iso" keda wayene? "Nida Mamanku ne Mustapha ne ya kawomu".

Salma wa

cce sautin kukanta ya fara fitowa tace "don Allah Hajiya kuyi hakuri....."jifar da Hajiya tayi matane da karamin filon kan kujera ya hanata karasa maganar ta.

Hajiya tacigaba da cewa "banason jin komai daga gareki Yar gidan masu asiri kawai,ai tundaga l

okacin da yaron nan ya zoman tamkar zaiyi hauka akan wannan kazamiyar Yarinyar nasan aikin asirine.

Ta kalli Maman su Nafisa ki tunafa be taba kwanciya a asibiti akan wata ba sai silar wannan Yarinyar dan nace bazai aureta ba ranar ya tashi a sankare id

anuwa a kakkafe mukai asibiti"

Duk matan nan suka kalli Salma cikin mamaki musamman ma Amna wadda take da matukar tsoron asiri.

Nafisa tace "wai dama ciwon nan nashi yanada nasaba da itane?"

Hajiya tace "inkinje gaba ma saiki fada daga nan abinda

nayi mashi ya yi yawa kawai sai nasa ayiman tambaya wajen malamai can ne suka fadaman wai uwar tane tasa akayi masa asiri da sunan Shatima kuma an hada da naman bakar akuya da yawun bakinta da ruwan hawayenta aka bashi yaci,daf da bikin nan fa har gida sa

i da ya siya masu da sauri Salma ta dago tana fadin "wallahi Hajiya ba siya mana ya yi ba hayace,"Hayar.....

Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta "karya zanyi maki kenan dan ubanki?"

Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba

Hajiya wayarki kar tayi lahani mana.

Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace.

Aliya ta kalli Hajiya kiyi

hakuri bari in zuba maku abinci.

Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan.

Nafisa tace"gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm"

Aliya tace "aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane"

Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi.

Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan

ga Salma nan an tsareta su Hajiya ne"

Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace "nagode Hameeda ganinan zuwa."

Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar wadda shedan ya rura

a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya.

Shatima ya nufi gurinshi "inasu Hajiya?" Mustapha yace suna falon Nafisa.

Shatima yac

e "to bari inje mu gaisa" Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya.

Hajiya tana fadin"ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar gidan nan".

Cikin kuka Am

na take fadin"yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in zauna ba,Ina tsoron asiri".

Nafisa take fadin" jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gida

n nan to wallahi Mama saidai mu tafi daku yau din nan."

Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine a tsaye.

Cikin tashin hankalin ya shigo cikin dakin gaba daya suka maida kallon su gareshi sannan kowacce

ta shiga nanata abinda zata nanata, kowacce ta nanata abinda ta fada.

Hajiya tace "duk kuyi shiru yanzun dai kai kazo ka zaba koni dana haifeka ko kuma iyalanka ko kuma wannan Yarinyar ita kadai? Ta nuna Salma wacce take durkushe tana cikin firgici da

matsanancin tashin hankali,itama kallon shi takeyi cike da tsananin bukatar taimakon shi,idanuntane suka nuna shi kadai take bukata,shine taimako na karshe da takesa rai zaiyi wani abu akan wannan halin da take ciki.

Hajiya ta katseshi da fadin "Zan la'

anceka!!!..." Zan la'anceka!!! In ka sake kallon ta,kuma na baka nan da minti daya rak ka yanke hukunci..........

*Alhamdulillah anan muka kawo karshen littafi na biyu,a yanzu kuma labarin zai fara, akwai cakwakiya fah,anan kuma muka kawo karshen free

pages idan kina bukatar 3&4 din littafin RANA DAYA ki turo kudin ki 300 ta wannan account number din

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan nu

mber 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi mag

ana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login