Showing 15001 words to 18000 words out of 37098 words

Chapter 6 - RANA DAYA BOOK2 COMPLETE

11 Nov 2026

6

koshi. Ya bata madara, shima kur

ɓ

arta daya. Ya sauka yayi shirin bacci. Yana hawa gadon ya ce “To tashi in fada miki abinda zai biyo bayan kazar nan da ki ka ci.”

Ta ce, “Ka kwanta ka fada min.” Ya kwanta, sannan ya dagota zuwa saman cikinshi. Ya kai hannu ya latse fitilar dakin.

Ya fit

o daga bandaki, ya zo ya sake jan yatsunta. Tashi mana honey kiyi wanka muyi sallah. Da kyar ta sauko ya jirata tayi wanka da alwala.

Shi ne ya ja su sallah, sannan suka koma kwanciya, ya janyota jikinshi. “Jiya kin hana ni bacci.” Ta ce, “Ka hana mu dai

Honey.” Cikin shagwaba tayi maganar, suka rufa sai bacci.

Kamar jiya ya shiga dakin kowacce ya duba lafiyarta tare da tambayar bukatarta. Su ukun

kowacce tana bukatar Gas don dafa abinci. Salma kuma tana bukatar kalanzir tun da wuri ya ba kowaccen su abi

n da take bukata.

Salma da Aliya ya siyo musu kayan abinci, kayan miya ne ya ce bai san ina zai samo ba. Ya tambayi Maigadi, ya ce a ba shi ya siyo. Aliya ce ta rubuta mishi kuma ya ba shi kudin mota zuwa kasuwar Kawo.

Da aka kawo ta raba hudu, ta ba da

na kowa. Kafın yamma duk ya sallame su. Ranar dakin Nafisa zai kwana, kuma washegari zai koma aiki.

Itama dai yasai Kaji da sauransu kamar dai na Amna. Ya ji dadin darenshi da Nafisa, domin ta kasance mai shagwaba tare da kokarin faranta mishi, kuma da sa

ssafe ta hada mishi abin kari. domin ya fada mata dan hutun da aka ba shi ya kare office zai koma.

Tana rataye da jakar a kafada ta rike wayoyinsa, ta ce “Sweety muje in raka ka mota.” Ya ce, “To.” Suna fitowa barandarta ya ce, “Bari in duba yanda sauran

‘yan uwanki suka kwana.”

Ta dan taba baki, tare da fadin “To.” Dakin Aliya ya nufa, wadda dama tana tsaye a windownta na falo tana hango lokacin da suka fito, kan ya Karaso ta koma cikin uwardaki da sauri.

Taki amsa sallamar har sai da ya nufo dakin da y

a san zai same ta a ciki yana kiran “My love!” Ta amsa daga ciki. Ya shiga, ta gaida shi tare da dan yatsina fuska. Ya ce, ” ba dai ba ki jin dadi

Ba

Ta ce, “Na kwana da ciwon ciki ne.” Ya ce, “Shi ne ba ki kira ni ba?” Ta zo ta dafa kafadarsa. “In na ta

so ka da wannan daren ina za ka neman magani, gashi mu baki ne a unguwar, sannan kuma na tuna kai da Amarya ne zan katse muku

soyayya.” Yayi murmushi, “Komai soyayya ai ciwo ya fi komai.” Ta ce, “Na samu sauki har za ka fita office!” Ya ce, “Eh.” Ta ce, “

Allah Ya ba da sa’a, Ya tsare mana kai, Ya saka samo mana halak.” Ya ce, “Ameen.” Ta rako shi har zuwa Barandarta.

Nafisa ta kalli lokaci a wayar hannunta ya dauki tsawon minti tara a dakin Aliya. Ya nufi gurin Salma ya kwankwasa kofar don ya murda ba a b

ude take ba.

Ya buga sosai sannan ta bude, daga gani bacci ta tashi. Ya shiga ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa tare da tambayar kafiyar ta. Ta ce, tana

lafiya. Ya mike yana tambayar ta karya kuwa? Ta ce, tun da tayi sallah bacci ya dauketa.

Ya ce, “To ak

wai abinda take bukata?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “To zai tafi office. Ya koma yau. Ta ce, “To Allah dawo.dakai lfy ya bada sa’a.” Har ya fita ya tuna ya

“Yau a nan zan kwana fa!” Shiru yayi yana kallonta yanda tayi tambayar cikin tsoro. Ya ce, “Naga kin tsor

ata ne.” Ta kirkiro yake, “A’a ban ji tsoro ba, sai ka dawo to.”

Yayi ‘yar dariya,sannan ya fita. Nafisa ta kalli wayar, ya ci minti shidda ya zo zai je dakin Amna. Ya ce, muje tare da na fito zan shiga mota, tunda kin ga motar tana kusa da dakinta. Nafis

a ta ce, je ka fito.

Amna ma bata tashi ba, yana tsaye ta bude bayan yayi ta bugu. Kayan bacci ne a jikinta, zai shiga ta rungume shi, suna rungume da juna ya ce, “Zan tafi office.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, “Zamu yi waya

ko?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “Kin ci abinci?” Ta ce, “Yanzun na tashi, ban san me zan ci ba, in da ka siyo shawarma din nan da nisa?”

Ya ce, “Sai an fita unguwar nan, can cikin gari ne. Shi za ki ci?” Ta ce, “eh.” Ya ce, “To bari in tafi da Maigadi sai ya ka

wo miki. Allah Yasa dai suna da shi da safe nan.” Ta ce, “Amin.”

Leda hudu ya bashi, ya ce ya mika kowane daki. Salma ta yini cikin damuwa da tunani tun da Shatima ya sanar da ita. Duk tsoronta tafi son ta kwana ita daya da ta ya zo dakin.

Da rana ta daf

a shinkafa dafa-duka, shirman da Salma tayi ta manta bakinta ne ita daya, ta shirga abincin fal tukunya. Yini tayi ci, bayan ta shake masa kula.

Da dare ma shi zata ci. Karfe shida ya shigo, dakin Nafisa yayi wanka, itama sai da yaje siyo kajin amarci. Ya

na can ne ma ya ga kiran Amna. Cikin sauri ya daga. Ta ce, “Honey.” Ya ce, “Na’am honey ya aka yi?”

Ta ce, “Ina jin yunwa ne, da rana ma banci komai ba.” Ya ce “Ba akwai danye ba kuma nasa muku Gas.” Ta ce, “Honey indomie kawai na iya dafawa, kuma ta gush

e ni, kai kuma ba ka kawo min me aiki ba.”

Ya kasa magana, can ya ce “To bari in zo gidan amma yanzun me ki ke son ki ci?” Ta ce, “Chips.” Ya ce, “Shi kenan.” Leda hudu yayo, ya kuma mika kowane daki.

Lokacin da ya shiga gurin Salma tana zaune cikin kuje

ra sanye take da riga doguwa baka da dan kwalinta. Har kafafunta ta zauna a saman

kujera, zuciyarta cike da tsoro, fatanta kada ya ce zai bukace ta, domin duk wautar ta dai tana da labarin abin da ake yi in an yi aure.

Bai lura da ita ba ya ce, “Salma!”

Ta amsa, daga in da take ya waiwayo. “Dama kina nan?” Ta sakko tazo ta tsugunna a gabansa. “Gani Yaya.” Ya ce, “Amshi wannan ki kai ciki.” Ta amsa tare da cewa kicin zan kai?”

Ya ce, “Daki dai ki kai tare da plate da cokali da kofuna.” Ta ce, “To.” Da ta

aje bata fito ba, sai ta zauna a bakin gado cikin sake-sake. Ya ce, “Salma!” Ta amsa daga ciki. Ya ce, “Zo.” Ta tsugunna a gabanshi. Ya ce, “Kije gurin Nafisa ki ce ta baki jakata ta office.”

Har ta kai bakin kofa sai ta waiwayo, “Yaya dakin da muka ci ab

i Anty Nafisa din?” Ya ce, “A’a na farkon.” A bakin kofar ta tsaya ta kwankwasa. Nafisa ta fito ta dan bude ta leko.

Ganin Salma sai ta hada rai tayi, mata kallon sama da kasa. Sannan ta ce, “Lafiya?” “Yaya ne ya ce ki ba da jakarshi ta office.”

Ta sake

tabe baki, sannan ta juya. Salma da karambani ta shige ciki don kawai tana son ganin dakin. Cikin sha’awa take bin falon da kallo, har ma bata san Nafisa tana miko mata ba.

Sai da ta ce, “Dalla ni karbi.” Da sauri ta kalli Nafisa. Cikin ‘yar fara’a ta c

e, “Kema Anty dakinki yayi kyau wallahi.” Nafisa ta taba baki tare da fadin “Ni rike da Allah.” Yaya Shatima ya rasa wadda zai aura mata sai wannan abin?”

Salma cikin sanyin jiki ta amshi jakar ta fita. A zuciyarta kuma tana cewa ita wannan bata san abin

arziki ba.” ta shiga falonta bata ganshi ba in da ta bar shi ba.

Ta dora jakar a kan doguwar kujera. Sannan ta leka dakin ta don ta ga ko yana ciki. Daga bayan ta taji sallamar shi ya shigo. Ta waiwayo, dama ka fita ne?”

Ya ce, “Eh.” Ya shiga cikin daki

n ya aje kayan hannunshi a kan gado. Ta kalli kayan da na bacci ne da kuma gogaggu kala uku.

Ya ce, “Ina za ki sa min kayan nan?” Ta ce, “Ga akwatuna na nan an kwashe kayan an saka a sif sai waccan bababr ce kadai da kayan da suka min yawa a ciki.

Ya ce,

“Wane kaya ne suka yi miki yawa?” Ta ce, “Ga su can cikin akwati, wannan rigar ma ta jikina ai ta min yawa.” Ya kalli akwatin, cikin zolaya ya ce, “Dauko.” Ta ce, “Ba zan iya ba, rannan ma Anty Badi’atu ce ta sakko da ita.”

Ya ce, “In daga ki ki dauko?

” Taja baya, ba zan iya ba. Ya sauke akwatin a kan gado ya zauna a bakin gadon. Ya bude, kayan cikin ne ya gani. Yayi murmushi tare da daga wata bireziya, yanzun wannan tayi miki yawa?”

Tasa tafin hannunta ta rufe fuska. Ya ce, “To wannan fa?” Ta bude tag

a pant a hannunshi. Da sauri ta juya baya. Ya ce, cire in gwada miki in tabbatar. Ta waiwayo ta zare ido cikin mamaki.”

Ta ce, “Haba dai!” Ya daure fuska, ina wasa da

ke ke ne! Laifi ne Inna ce ki cire ki gwada in

gani? Idanunta suka yi rau-rau a lamun

kuka. Ta ce, “Don Allah kayi hakuri Yaya.” Tamkar yayi dariya amma sai ya dake. Ya ce, “Ban isa ba ke nan ko?” Ta fara buga kafa tana fadin Yaya don Allah kayi hakuri ka ji.” Yanda

take yin abin ya birge shi, dan shi mutum ne mai son shagwa

ɓ

a.

Ya tura ak

watin gefe, ya hau gadon gaba daya ya mike kafa. “Zan kirga uku in baki cire ba zan zo in cire miki. Kuma duk abin da ya biyo baya ba ruwana.”

Ta ce, “Yaya babu kyau kallon tsiraicin wani, Allah haka Malaminmu ya ce Shatima ya sake

daure fuska tamkar gas

ke ya ce, “Shi Malamin naku har da miji da mata ya ce?” Tayi shiru.

Ya ce, “daya!” Da sauri ta cire dankwalinta ta jefar a kasa, tana kuka kasa-kasa. Ya ce, “Biyu!” Ta ce, “Wayyo! Don Allah Yaya kayi hakuri.” Ya ce, “Ina cewa uku zan taso.”

Ta ce, “To ba

ni wannan din.” Ya wurga mata pant da bireziyar. Ta dauki bireziyar ta zage zif din da ke makata zuwa kafadarta, ta soma saka bireziyar.

Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawa

r ido goma in ce uku.”

Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi ma

ta yawa sosai.

Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta

ɓ

ari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.”

[8/18, 17:21] Ummi Tandama

😇

: _____

*

🏚

️

RANA DAYA BOOK 2

🏚

️

*

CHAPTER 8

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number

👇🏻

*

```ACT<<0700549935

Halima Abdullahi Access ban

k sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama

👆🏻👆🏻

ko kuma ka

tin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*



Mun tsaya

Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zak

i yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.”

Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakam

akon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai.

Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta

ɓ

ari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin

kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.”

Yanda tayi maganar ya sake ba shi dariya. A ranta kuwa cewa take, “Mugu kawai, dole ka min dariya. ” Ya ce, “To kwance wannan madaurin.” Ta ce, “In na kwance zai fadi fa Yaya.” Ya ce, “Kin juya baya kina

min magana bana jin me ki ke fada. Bari in zo in juyo da ke.”

Ta ce, “Yi hakuri Yaya, Allah zan juyo.” Ya ce, “To juyo.” Ta juyo. Fuskarta ya kalla sharkaf da hawaye, idanunta a runtse, hannuwanta a makale a kirjinta.

ya tashi ya tafi a sannu, bata ji z

uwanshi ba sai dai taji an ja dankwalin da ta kulle siket din, lokaci daya kuma ya warware. Da sauri tasa hannu ta riko siket din. Ya saki sabuwar dariya tare da fadin, “To ai

kuma kin bude kirjin.” Ta tsugunna da sauri tare da fadin “Na shiga ukuna!” Yay

i dariya sosai sannan ya shige bandakinta tare da fadin “Ki zo kiyi alwala muyi sallah irin ta ma’aurata.” Yana wucewa tayi maza ta saki siket din, sannan ta dauki rigarta ta maida.

Ya fito ya ce, “Kije kiyi alwala.” Wuf! Ta

shige bandakin. Taci kuka

, a ciki sannan tayo

alwalar. Ta samu ya maida akwatin ya ciro wata

yasa kayanshi, sannan ya cire na jikin shi yana saka na bacci.

Ta juya baya don lokacin da ta fito yana kokarin saka dogon wando a kan gajeren jikinshi, sannan bai kai ga sa riga ba. Ya

kalle ta yayi murmushi. Sai da ya shimfida Darduma, sannan ya ce, “Kin juya baya kamar kin ga abin tsoro, ki sa hijabi ki zo muyi sallah.”

Bayan sun idar ya ce ta dauko musu kajin

Amarci su ci. Gabanta ya fadi, ta tuna da suka je

kauyen Innarsu biki wa

nshekaren da aka kawo

Amaryar suka je dakinta shi ne ta ke ba su labari,

wai in ango ya kawo kaza da daddare amarya ta yarda ta ci, to ango zai ce ta biya shi. Sai Salma ta ce, “To kudi za ka ba shi?” Sai Amarya ta ce, “Tab! Kama ki zai yi yata wahalar d

a

ke, kuma ko kina ihu ba zai bar ki ba.”

Duk da Amaryar ba ta fayyace ba, Salma ta gane abin da take nufi. Ya katse mata tunani da cewa, “Shima abin tsoro ne cin kazar?” Ta ce, “Na’am!, a’a dama na tuna ne da abincin da ka ce in yi da kai.”

Ya ce, “Kaw

o in ga irin shi ko kin iya girki.”

Ta dauko har da goran ruwa da kofi, da ya ke yasa

an kawo musu katan-katan na ruwa da lemon roba.

Ya bude shinkafar, yayi dariya. Ya ce, “Ai ni bana cin shinkafa haka tsura, ba wani dan ganye, ba wake, ba komai.

Kuma

ina zan kai wannan abincin? Kin dauki kula irin ta can kasan saiti, babbar ciki, kin shake.” Yasa cokali ya dan tona, kamshinta sun hadu da warin lalacewar, ga wani kauri.

Ya ce, “Salma ai wannan ma ya lalace. Sannan kuma gashi yana kauri.” Ya dube ta, “

Ba ki iya girki ba ko?” Ta ce, “Ni dai ban san irin naku ba, amma a gida ni nake yi mana.” Ya ce, “Dan kadan za ki ke dafawa, kar kiyi

la’aklari da yawan na gidanku. Fita da wannan ki

aje da safe ki zubar, kin ga kin yi ta’adi. Zubar da

abinci ba shi da

kyau.”Ta ce, “Zan bar shi a bude, da safe sai in

dindima în ci, da rana ma in ci.” Ya zaro ido. “Wa

ya fada miki ana barin abin da za a ci ya kwana a bude? Ba’a fada miki ba Manzon Rahma (S.A.W) yayi mana umarni da rufe abincin mu da na sha in dare yayi

sannan mu kashe fitilunmu. Ranar fa naji kina cewa ba kya iya bacci, sai a

haske.” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To dama kin daina,

don ba shi da fa’ida. Maida ki zo muci wannan.”

Duk da kamshin ya ishe ta amma bata jin zata ci wannan kaza ta mugunta. Ya ciro c

inya ya ce, “Bude baki.” Ta tuno da zancen wannan Amarya, in da a hirar take cewa, “Har fa a baki za ki ga suna baki naman.” Cikin sauri Salma ta girgiza kai, “Na koshi, bari dai in ci dankalin nan da kwan.’

Ya tausasa murya cikin sigar lallashi, “Kin san

muhimmancin kazar nan kuwa?” Gaban Salma ya sake faduwa, a ranta ta ce, “Na sani sarai, ta zalinci ce.

Ya sake maimaita tambayar. Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kowace Amarya ana kawo mata a daranta na farko, daran ta na alfahari, kuma dole ta ci.” Ta ce, “To in

bata ci ba me zai faru?”

Ya kai bakinshi ya gutsira, sannan ya ce, “In bata ci ba Angonta zai ji haushi, kuma zata hadu da fushin Allah.” Tayi shiru, a ranta ta ce, “Kai! Ana cewa aure hutu ne, gaskiya babu wani hutu a cikinsa…

Ta dube shi. “To in ta rok

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login