Showing 6001 words to 9000 words out of 20369 words
share idona da tafukana na ce, “In ba daina sona ka yi ba me ya sa za ka yi auren?” Ya ce,
“Zan yi aure ne saboda TAUSAYINKI”.
“Ni marainiya ce da za ka ji tausayina?”
“Ke ba mara
iniya ba ce, ba za ki iya da lalurata ba Sakinah! Wanda shi ne jigon auren. Ni kuma ba zan iya jurewa ba, ba tare da na nemi alternative ba.
Sakinah ina son ki son da ban taba yiwa komi a rayuwata ba, in kika dauke Hajiya da Daddy. Zan yi aure don amfanin
mu duka ba don na daina sonki ba. Ina so kashinki ya yi kwari kamin in dora miki hidimar aure, dalilina ke nan”.
“Ni kuwa meye wannan lalurar taka da kake tunanin ba zan iya ba? Ka fada min ko ta mece ce ni kuma na yi alqawarin zan yi maka ko da hakan shi
ne abu na karshe da zan gabatar a rayuwata...........in dai za ka fasa yin auren, na yi alqawari zan yi maka...”.
Da sauri ya rungume ni, “Da gaske kin amince Sakinah in dora miki nauyin kirjina?”
“Na amince Mijin-Sakinah.......sai dai don Allah idan
na mutu, ka nemi Mamana ka ce da ita INA SONTA……!!!’
Yadda ya rike ni cikin rawar jiki da gigicewa na raina wautata. Cikin wata irin dakusasshiyar murya ya ce,
“Balle ma ba za ki mutu ba, sai Mamanki ta goya ‘ya’yanmu”.
Bai lura da rashin tausayin da
ya yi min ba, sai da ya nemi numfashina ya rasa. Har asuba ban gama wartsakewa ba.
Har wankan shi ne ya yi mini, sannan ya gaya min yadda zan yi wankan sallah. Na yi yadda ya ce, ya nado ni a tawul ya kwantar a resting chair ya bani paracetamol.
Ya kuma
kwashe shimfidar ya wanke da kansa, ya ci gaba da bani treatment kamar wani likita har gari ya waye.
Ya mai dani dakina sannan ya durqusa a kan gwiwoyinsa, yana kallona da murmushin da ban taba ganin yayi irinshi ba, domin murmushi ne daya fito daga kark
ashin zuciya, ba daga fatar baki ba.
Sannan murmushine mai bayyanar da halin da ZUCIYAR MUTUM ke ciki., ya ce,
“Allah ya yi miki albarka Sakinah! Sakinah na gode Allah ya yi miki albarka!”.
Kunya ba ta barni na amsa ba, na rufe fuskata da tafukana in
a murmushi.
****
Kwananshi biyu ya koma Lagos, zuciyarshi fal da so da kaunar matarsa. Har yake jin bazai iya auren Farida ba, dama a rashin uwa ne akayi uwar daki, duk wata barakar da tasa shi tunanin yin auren matar shi ta tosheta. Sai dai yayi don s
on rai kawai amma ba don wani abu daban ba.
A wani bangaren kuma yana tunanin yadda zai tunkari Faridar, ba zai iya keta idonta yace da ita baya son taba. Da gaske Sakinah ba ta son kishiya, yarinya da ita amma ta san kishi a ‘yan shekarunta da yake rain
awa.
Sannan ita ma Farida yana sonta, don ita ce first love din shi, tana da wasu qualities da yake so a diya mace. Kamar kamun kai, nutsuwa da wadataccen ilimi.
Sannan yana son kasancewa da mace a kusa da shi a nan Lagos, tunda ba zai raba Sakinah da k
aratunta ba. Wadannan tunanikan su suka taru suka dagula mishi lissafi.
Yana zaune a ofis ya bude wayoyinshi, text din Farida ne ya fara shigowa kafin na sauran mutane. Ya kira Abdallah yake gaya mishi Sakinah fa ba ta son kishiya, ta yarda ko mutuwa ne t
a yi a kan turbar auren in dai zai janye niyyarshi na kara auren.
Abdallah ya ce, “To ban da abinka wace mace ce take son kishiya? Ba burina a quntatawa kanwata ba, sai dai ina so kaima ka samu peace of mind, don na tabbata kana son Farida.
In ka dawo sa
i ka sa Abbanta ya yi mata nasiha tana jin maganarsa sosai. Wannan ba wani abu bane, wace ce za ta buga kirji ta ce ayi mata kishiya don tana so?”
Ya dade yana tauna maganar Abdallah, kafin ya amsawa Farida cewa Daddy ya amince ya aure ta. Farin ciki a wa
jen Farida kamar ta yi ya ya.
Zuwan shi gidansu uku suna shirye-shiryen auren, sai dai Farida ta tsorata da yadda duk wata magana ta Abdulhakim daya-biyu, to zai ambato sunan Sakinah.
Ba ta tashi kara rikicewa ba sai da suka fara saye-sayen da zai zuba m
ata a lefe, ta ga komai biyu yake saye, in ta yi magana ya ce daya na Sakinah ne ba tare da ya damu da reaction dinta ba.
Ta cika ta yi fam, amma ita da take lallabawa ta samu ya aure ta, ta samu din ai fushin fari ba nata bane.
Da yake mace ce mai wayay
yen kai, sai ta biye mishi, har tana tambayarshi size din kafar Sakinah, ya ce, (38) ita kuma nata (40).
Lefe sosai na gani a ba da labari suka hada, wanda ya lashe miliyan uku cif! Da ya tashi tahowa a karshen satin ya taho dasu ya kaima Hajiya na Farida
don a samu masu kaiwa, don tuni Daddy da mahaifin Farida sun yanke magana an sanya daurin auren watanni uku cif!.
Babu yadda Hajiya za ta yi, ta nemi Jama’arta don su kai. Ciki har da Mami, Mami ta tambayi Hajiya dalilin kara auren na Abdulhakim.
Hajiya
ta ce, “Watakila ba haka yarinyar nan da iyayenta suka barshi ba, amma mai mace kamar Sakinah me zai nemo a jikin wata diya mace?”
Mami ta ce, “Baki lura bane Hajiya Lailah, Sakinah fa sai yanzu ta soma kirgen dangi. Ga dukkan alamu bai samun gamsuwa a j
ikinta ne”.
Hajiya ta ce, “To ba zai yi hakuri ba? Hakurin da zai yi ai ba zai kai wanda ya yi a baya ba”.
Mami ta ce, “Rabu da ‘ya’yan zamani Hajiya Laila, ai ba irin mutanen da bane da za su iya zubawa matansu ido har tsayin shekaru ba”.
“Hajiya Laila
i ta jinjina kai ta ce, “Allah ya kyauta”.
Ina kicin ina hada salad don tuni Abdulhakim ya yi min waya cewa yana bisa hanyar Abuja. Sadi da Uche wanda yanzu ya koma gidan Hajiya suka soma shigo da akwatuna ko in ce irin jakunkunan nan na zamani da ake k
ai lefe a cikinsu.
Ban fito ba sai da na kammala ayyukana, snanan na soma fito dasu bisa dining, nan na yi arba da akwatunan wanda ke tabbatar min Mijin-Sakina ya iso.
Na fada toilet na yi wanka na shirya cikin wani tattausan leshi ruwan zuma mai yarfen
qananun duwarwatsu kala-kala, na feshe jikina da turarena na din-din-din wato Azzaro Visit, na feshe gashina da turaren gashi mai sanyin qamshi, sannan na taje na matse shi da bound kalar leshin jikina. Ban daura dankwali ba.
Juyawa nake a gaban mudubi in
a kallon kaina, ko da inda bai yi ba a canza? Wani juyi da na yi sai na hango dan Alkali Ribadu cikin mudubin yana murmushin nan nasa mai ban sha’awa, cikin farin yadin filtex mai santsi, dinkin Mohammed.
Kamar kullum yau ma hannuwanshi ya bude mini, maim
akon in tafi da sauri kamar yadda na saba a da, sai na sarqe hannayena a baya na runtse idona, kunya kamar in yi ya ya.
Sai ji na yi ya sureni ya yi sama dani, sannan ya cillani tsakiyar gadona yana cewa,
“Tallafeni Sakinah….. da bukata na zo mai yawa..
.....”
[9/15, 2:47 PM] Asmau: An ci soyayya, so bege da kauna an gaji, wannan karon ban ji wuyar ba sai dan abinda ba’a rasa ba. Kankame muke da juna kamar masu tsoron kada wani iftila’i ya ratsa a tsakaninmu.
Zuwa yanzu na san mene ne auren, na san wa
ne ne mijina Abdulhakim Khalil Ribadu?
Idan maza sun yi dubu na san da kyar a samu uku kwarara masu nagartar nawa mijin. Sannan ko cikin laluben rufa- ido zan tsame mijina a cikinsu.
Mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, ya kuma san mutuncin dan adam d
uk lalacewarsa, ko daga yadda yake mutunta Sabuwa ya ba ta girma. Ya kuma kaunaci duk ahalina ko wanda ya shafeni.
Mutum ne da ya san soyayya mai tsayawa matarsa a qoqon rai. Bar ta kyawun halitta, Abdulhakim is classique da kowacce diya mace da ta san ci
won kanta za ta yiwa kanta burin mallakarshi.
Zuwa yanzu soyayyar mijina Abdulhakim ta gama ratsa kowacce jijiya mai gudanar da jini a jikina, ta ratsa kashi da bargo. Ta yi kwance cikin tsoka da fatar jikina. Wani mahaukacin so nake mishi wanda ni kaina
ban san iyakarshi ba.
Kamar ya san tunanin da nake yi, ya sake rungume ni, runguma mai karfi. Ya ci gaba da rikitani da wasu irin hot-kisses har na fita hayyacina. Saida dukkannin mu muka samu nutsuwa. Amma bai sakeni daga kyakkyawar rungumar da yayimin b
a.
Sannan ne ya ce,
“Zan yi miki laifi Sakinah, Sakinah zan kara AURE. Ba don kin gaza dani ba ta kowanne fanni, duk da karancin shekarunki.
Allah ya yi miki baiwarwaki da dama wadanda ke kanki ba ki sansu ba. Na yaba da kokarin ki…. na kuma yaba da j
arumtakarki........ Sai dai Sakinah ina son zama da mace kusa dani a inda nake zaune, ga shi bana so in rabaki da karatunki yadda kike jin dadinsa. (Shi akan kansa bayan ya fada yasan wannan dalilin bai isa hujja ba).
Zan auri Farida mu zauna a Lagos kafi
n in samu transfer. Ita ce wacce na ce miki na so in aura a baya Allah bai yi ba. Zan samu goyon bayanki Sakinah? Ina neman alfarmar ki. Idan baki amince ba wallahi zan bari, idan kin amince na yi alqawarin zamowa mai adalci a tsakaninku.....”.
Tunda ya
soma maganar kallon shi nake babu ko kiftawa har ya gama, wani abu ne dunqulalle ya zo ya tokare ni a kirjina, ina so in yi kuka amma kukan ya ki zuwa.
Da kyar na samu sautin dana ke ta tattarawa ya fito daga bakina,
“Ni kuma sai ka sallameni! Don ba
n ga sauran amfani na ba, kana nufin yadda muke dinnan haka zaka yi da wata matar ni ina gefe? Kuma ita ma ta samu ‘ya’ya da kai, nima ta dinga yiwa ‘ya’yana irin azabar da Mami ke min? Wataran ka sake ni a dalilin ta? Ka daina ganina yarinya haka, na san
wace ce KISHIYA!”
Murmushi ya yi irin na maza, a lokacin da suka fahimci matansu na kishin su, wanda baya sawa kuma baya hanawa kan abinda suka yi niyya, yana shafa kwantacciyar sumar kanshi, ganin yadda idanuwana suka juye ina amayar da dukkan radadin
kishin da ke zuciyata.
Ya kama hannuna na fizge na mike zan fita, ya sha gabana ya sanyani a kwana, ya zagaye ni da hannuwan shi babu hanyar wucewa. Na sulale kasa na zauna dirshan bisa kilishi, zuciyata na wani irin tafasa. Sai yanzu ne na samu hawaye
masu zafi da radadi suka zubo.
Shi ma bina ya yi ya zauna dabas a kasa, ya tara hannu ya taro hawayen ya ce,
“Haba Sakinah! Matar nan fa ba cinye miki ni za tai ba. Ba wani abu za ta cira a jikina ba, babu abin da za ta gutsira na soyayyata a gareki.
K
arewa ma mijinki za ta taimaka ta zauna da shi a inda ba shi da kowa. Ko kin fi son in dinga kula ‘yam matan Lagos masu bin maza har ofishinsu da in auro miki ta kirki?”
Na kai yatsuna na toshe kunnuwana ina kuka sosai, na ce, “Bana sonka..........bana so
nka! Bana son ka! Ta je na bar mata. Ba abinda zaka fada in yarda har yanzu kana so na. Amma ni ka mai dani gidan Abbana, na yarda Mamin ta yi ta dukana tana sani aikatau din in har akan haka ne aka yi min auren, da dai in hada miji da wata.
In kuma ka ki
mai dani wallahi zan kashe kaina da wuqa ka huta tunda yanzu baka sona........”.
Rigimar ke nan har tsayin kwana biyu, ga shi a gobe zai koma Lagos. Duk yadda ya so in saurare shi in ji hukuncin da ya yanke na ki. Duk wata kyakkyawar alaqa dake tsakani
nmu na janye ta.
Akwatunan da ya kawo min wai na fadar kishiya kananzir na zuba musu na qyasta ashana zan qona ya dauke ni da wani wawan mari sai da na ga wuta.
Ya kwace ashanar ya kwashe su ya maida dakin shi, ya fita sallar magariba bai tashi dawowa ba
sai tare da Abbana da Daddy.
Na fada jikin Abba ina kuka. Ya ce, “Ni dagani tun ban zane ki ba, sakarar banza shashasha!”.
Daddy ya ce, “Taho nan Sakinah, tunda ba kya so ba za a yi ba”.
Cikin haushi mai tsanani Abba ya ce, “In kin kashe auren saboda
rashin hankali sai ki nemi wani uban ba ni ba, ni mata nawa kika ga na aura a kan idonki?
Mahaifiyar ki ba ta dau kishiya a bakin komai ba sai ‘yar’uwa, abokiyar shawara.
Don haka wannan kishin dabbacin ban san inda kika samo abinki ba, sai ki koma waj
en wadanda suka koya miki ki kuma nemi gidan zuwa ba gidana ba”.
Daddy ya ce, “Haba M.T? Lallashinta ya kamata ayi ba a kara tunzura ta ba. Zo nan Sakinah, ki gaya min duk abin da ba kya so”.
Na ja shesshekar kuka na ce,
“Bayan ita ma idan ta zo sonta
zai rinqa yi har su haifi ‘ya’ya ni ban haihu ba”.
Gaba dayansu suka bushe da dariya har Abdulhakim da ya yi zugumm! Sai da ya murmusa.
Daddy ya ce,
“To ke nan yanzu haihuwa ce ba kya so ta yi?”
Na ce, “Eh, kuma ya ce wai tafiya zai yi da ita Lagos
ni su barni ina yi musu gadin gida”.
Daddy ya ce, “To ayi miki transfer mana ki bisu can ma ai akwai makarantu Sakinah?”.
Na share hawaye na ce, “Ni ba zan rabu da Nadiya ba, ina son makarantar mu sosai”.
Abba ya ce, “To shi ke nan za a gaya mata kada t
a haihu idan ta zo. Amma ita ma za ki sota kamar Nadiya? Kinga Auntynki ce”.
Na ce, “Au, babba zai auro don ta dinga turmushe ni tana duka idan ba ya nan?”
Daddy ya ce, “Ita ta isa ta taba ki ‘yar lelena? Bayan ma ba garin ku daya ba”.
Haka suka sani ga
ba suna ta lallashi, in bullo ta nan su toshe can har na yarda na hakura ya yi auren. Daddy ya ce,
“To kayanki fa na fadar kishiya ai za ki karba ko?”
Na daga mishi kai. Ya ce, “To Allah ya yi miki albarka, duk abin da ya yi miki ba daidai ba ki zo har
gida ki same ni ko ki yi min waya in zo, in ta kama in zane shi wallahi sai na zane shi, shi da matar tasa”.
Na yi dariya da hawaye jabe-jabe na ce, “Duka Daddy?” In affirmation ya ce, “Kwarai kuwa, duk girman nan nasa wallahi zan zane shi in dai a kanki
ne”.
Na ce, “Balle ma ba sai ka doke shi ba, ai ya yi girma da duka”. Daddy ya ce,
“Bai yi ba, sai idan bai yi miki laifin ba”.
Da haka suka lallaba ni suka tafi, ya bisu don ya taka musu. Ina kallon yadda yake satar kallona a kasan idanunshi yana mur
mushi.
Ya rakasu ya dawo, ina zaune inda suka barni ban tashi ba, ya zauna opposite dina watau ya kara bayanshi a bayana.
“Yau kwana biyu ba a bani abinci ba saboda KISHI. Hanjin cikina duk ya kanannade, wannan mai sauki ne idan aka kwatanta shi da babba
n abincin da ba’a bani ba don kawai na ce zan yi aure. Shin ba sunnar ma’aiki zan raya ba? Mene ne laifi a cikin yin aure?’
Ya juyo ya kuma juyo dani muka fuskanci juna. Hawayen da nake tattali kada su zubo sune suka zubo, yasa hannu yana taro su akan taf
ukansa. Cikin karyayyar murya ya ce,
“Me ya yi zafi Sakinah? Na ce in ba kya so zan bari........”
“Bayan ka riga ka hadani da su Abba, ni ban gaya musu marin da ka yi min ba sai kai ne mai bakin kai kara ta don kai ne dan gata?”
Ya yi murmushi ya ce,
“Ai marina mai hujja ne, almubazzaranci za ki yi na hanaki, ko su suka ji abin da kika yi niyya sai sun mare ki. Sakinah haka kike da kishi? Kada ki qona min matata fa?”
Na cika na yi fam! Na mike na barshi a wurin ya biyoni yana cewa,
“Ana sona ne, in
ba haka ba ai ba za a yi min haka ba”.
Biki ya matso, tun ana i gobe kamu lokacin Abdulhakim yana Lagos na hada kayan da zan yi amfani dasu a karamar jaka na shiga na yiwa Hajiya sallama na tafi gidanmu, na shige cikin ‘yammatan Safinah.
Sabuwa kad
ai na baro a gidan, harka da jama’a da kujiba-kujiba yasa na mance da damuwata, na mance cewa nima ana yi min bikin kishiya ne.
Mun kebe ni da Yaya Safina ta ce, “Wai da gaske Abdulhakim aure zai kara?” Na ce mata, “Eh”.
Ta ce, “Kin fa sa jikina ya yi sa
nyi, domin Abdulhakim da Abdallah bakinsu daya, shawarar su daya”.
Na ce, “Wallahi kuwa, don shi ma Abdallah ai ya so wata ita ta kishi kamar Faridan”.
Ta ce, “Tab! In nice wallahi za a yi bala’i, don ba zan yarda ba”.
Na ce, “Sai ki mutu ai, kuma sa
i ya yi. Ba abin da ban yi ba, ba boren da ban yi ba, ai bai fasa ba. Na yi kukan na yi fushin,