Showing 9001 words to 12000 words out of 20369 words
na yi haukan sai mari da na sha, sannan ba’a fasa ba”.
A nan harabar gidanmu aka shirya yin kamun, an qawata wurin sosai. Safinah ta yi kyan har ta gaji. Tan
a cikin runfarta, ta kishingida da tuntu mu kuma da sauran kawayenta mun sha anko muna gefe da gefenta wasu a bayanta.
‘Yan kamu suka iso aka yi kamun mai ban sha’awa na mata zalla. Washegari karfe takwas na dare motocin angwaye suka zo diban mutane zuwa
wajen dinner.
Sai da aka kwashe kowa tsaf ya rage daga ni sai amarya da wata qawarta Hamida Sajoh. Na yi saurin kashe wayata kada Abdallah ko Abdulhakim su nemeni na gudu dakin Yaya Suwaiba wadda ke fama da tirtsetsen ciki na haihuwa yau ko gobe, na yi ca
n quryar dakinta na yi kwance abina. Ko Safinah ba ta san inda na shiga ba”.
Yaya Suwaiba ta shigo dakin tana cewa, “Au ashe kina nan? Kika bar mijinki yana ta neman ki? Ga shi kin sha ankonki kin yi kyau, sai dai kuma kin bata gwaggwaron. Sai ki tashi ki
je yana waje har su Safinah ke suke jira”.
Nasa kuka na ce, “Ni wallahi ba zani ba, ya je can ya dauki matarshi”.
Ta yi dariya ta ce, “Oh! Ni ‘yasu. Sakinah ban san yaushe kika koyi wannan kishin ba. To ita ba a dadinta ba kin bar mata mijin ke kin haku
ra”.
Na ce, “Eh, na ji, su karata can ba inda za ni”.
Ban ankara ba sai jin sallamar Mijin-Sakinah na yi a falon Yaya Suwaiba”. Ta ce, “Gara dai ka zo da kanka don ta ce ba inda za ta”.
Kai tsaye ya shigo dakin ya sha wata jiqakkiyar farar excellencior
mai maiqo da yarari, wadda a qalla ta bai wa naira dubu casa’in baya.
Qamshinsa da kwarjininsa sun cika dakin. Haiba da kamalarshi sun cika idanun kowa. Ya dauki Gwaggwaron yana gyara lanqwashewar da ya yi ya kifa min a kaina.
Ya ce, “Tashi ki taka da ka
fafunki ko in sungume ki wallahi....”. Kunya ta kama Yaya Suwaiba ta fita ta bar mana dakin.
Na balla mai harara sannan na yi saurin tashi don na san kadan da aikinsa.
Cikin motar Abdulhakim (SL 360) Abdallah ne da Safina a baya, wani abokinsu ya dauki H
amida, na shiga gaba Abdulhakim ke tukin.
Wayar Farida ta shigo, ban dai ji me ta ce da shi ba ya ce, “Bana son mita, gamu nan?”
Ya dan juyo ya dubi Abdallah ya ce, “Ba sai mun je gidansu Farida ba tana can already”.
Abdallah bai yi magana ba, hirar shi
yake da amaryarshi. Ina jinsu tana cewa, “Ka gayyato Safiyyah?” Ya yi dariya ya ce, “Ta yi aure”.
Harabar Hotel din na (Rock-View) cike take da motoci na zamani danqam! Haka al’umma danqam. Su Safina ne a gaba rike da hannun junansu mu kuma muna biye das
u.
‘Yammatan Safina suka taho suna take mata baya. Tun daga nesa Farida Alqasim ta zuba min ido ta cikin medicated glass dinta, tana mamakin yadda aka yi Abdulhakim ya auri kankanuwar yarinya haka wadda ko nonuwan kirki babu a kirjinta.
Sai dai da ganina
ka ga (half caste) watau ruwa biyu. Ta ci gaba da kallona kamar mai son karanta ta. Ba ta karanci komai ba, sai zallar kuruciya da rashin fara’a.
Fuskata a dinke tsaf, amma ba karamin kyau na yi ba. Musamman sanda idanuwa da attention din kowa ya dawo ka
nmu, masu vedio na yi masu camera na yi. Har muka zauna a kujerun da aka tanada domin mu.
Ina gefen daman Abdulhakim, Farida na gefen hagu, ta kama hannun Abdulhakim na hagu ta rike cikin nata.
Tana murmushi ta ce, “Sakinah ba gaisuwa?” Sai sannan ne na
juyo na dube ta, kyakkyawa ce sosai hasken fata da yawan gashi kawai zan nuna mata.
Sai dai ta kusa sa’ar Abdul din, tunda shi yana (32) tana (27). A raina na ce,
“Ki qwacen mijin sannan ki ce in gaishe ki?”
Ganin ban ba ta amsa ba sai ta dauke kanta t
ana sauraron Hamida Sajoh wadda ke ba da tarihin Safinah.
Ta gama sannan tata qawar ta tashi ta ba da nata tarishin. A nan na ji wai har masters ta yi. Na ce, “Tsohuwa kawai, ashe kwantan ‘yammata aka kwaso mini, Allah ya isa!”
Ashe Abdulhakim ya ji Alla
h ya isan. Dariya ta kama shi ya hanata fita saboda masu vedio. Ya sunkuyo daidai kunnena wani irin lafiyayyen qamshi na tashi a jikinsa da bakinsa, ya ce,
“Da bai isa ba ya yi dan dama da kabewa?”
Harara na manna mishi sannan muka kyalkyale da dariya d
aga ni har shi. Haushi ya kama Farida, amma ba ta yi magana ba. Sai dai za ka iya karantar kishin a kwayar idonta.
Karfe goma na dare aka tashi daga taron. Wannan karon Safinah motar Abdallah ta bi, ina kokarin guduwa in shige motar da su Hamida suka shig
a caraf! Ya damqo ni ya fizgo hannuna muka nufi tashi motar.
Tuni Farida ta kame a gaba tun kan mu karaso. Na ce, “Lallai yau za ayi ta”. Ya ce, “Da aka yi ya ya?”
Na ce, “A gaban mota na saba zama yau kuma ba zan canza ba”. Ya yi dariya ya ce, “Sakinah-
Sakinah! My Queen my princess........I love you girl!!”
Daidai sanda muka karaso jikin motar ya bude gaban, ya ce, “Fito Farida ki koma baya”. Ta daure fuska sosai ta gyara zaman gilashinta a idanunta ba ta motsa ba. Can kuma ko me ta tuna? Ta fito ta kom
a bayan. Na yi mata gwalo a qeyarta ba tare da ta sani ba.
Ita muka fara saukewa a gidansu. Daga ganin gate din kadai za ka san naira ta zauna da duwawunta a wannan gida.
Ya fita ya taka mata har kofar reception dinsu, suka yi ‘yar magana sannan ta shige
, shi kuma ya juyo.
Ganin ya dauko hanyar gidanshi na ce,
“Ni fa gidanmu za ka kaini, duk kayana suna can sai an gama biki zan komo”.
Bai kula ni ba har na yi mitata na gama. Saura kadan in fashe da kuka lokacin da muka shigo gate, na ce, “Yanzu don Al
lah da gaske ba za ka mai dani gidan bikin ba?”
Ya ce, “Ba za ki ba, za ki fito ko in sunkuce ki?’ Ganin yana nade hannun riga na balle murfin motar na fice fuuu! Uwa guguwa. Ya yi dariya ya kwaso wayoyinshi ya fito ya rufe motar. Kishin Sakinah har tsoro
yake ba shi.
Ina wanka lokacin da ya shigo, na yi saurin kammalawa na fito don na san kadan da aikinsa ya shigo toilet din.
Shi ma wankan ya yi, na zuba hijabi na soma sallar isha’i da ban yi ba. Shi ma sallar ya yi sannan muka kwanta.
Yana ta lallashi
na, ya ce.
“Don Allah Sakinah ki sassauta min. In kina nuna min fushinki za ki sa in zamo mara adalci in tashi ranar alkiyama da rubabben barin jiki. Kina son hakan?”
Na girgiza kai.
“To ki rage wannan kishin bana so, idan kina so mu shirya”.
Na ce, “T
o”.
Ya janyo ni yana cewa, “Matso nan ki gani in daga miki kofar shiga Aljannah”.
Washegari aka yi daurin aure, Safina da Abdallah, Abdulhakim da Farida. Daga nan angwayen suka wuce walima ta maza zallah.
A cikin gida kuma a kowanne bangare na amaren
yinin biki suke. Ban kara tsinkewa da al’amarin ba sai da na ga an bude daya flat din dake jikin namu an fara sauke kaya, na tabbatar dai da gaske Mijin-Sakinah ya tashi daga mijin Sakina ya zama mijin Sakinah Da Farida.
Na karbi hakan a matsayin abin da
Allah ya rubutawa Abdulhakim wanda bawa bai isa ya kankare shi ba.
Da daddare Hajiya ta aiko Sabuwa ta yi kirana in je can gidansu a karbi amayar a can. Zuwa yanzu na koyawa zuciyata dauriya da tawakkali.
Muna can falon Hajiya wanda ke cike taf da jama’a
rta da matan abokan Daddy. Safinah aka fara kawowa, nan gidan Hajiya aka sauke ta kafin baki su watse su wuce Kaduna. Sannan aka kawo Farida.
Bayan jama’a sun watse Daddy ya shigo ya hadamu mu duka biyun ya yi mana nasihar hakuri a zama da juna da yin biy
ayya ga mijin aurenmu don samun mafificiyar rayuwa a duniya da lahira.
Hajiya da kanta ta rakamu har gida. Ta raka kowacce sashinta, sannan ta yi mana addu’a ta tafi.
Tafiyarta da wajen awa daya na yi wanka na yi shirin barci, amma barcin ya gagara duk j
uyin da na yi Abdulhakim nake gani rungume da Farida.
Na shige toilet na yi kukana mai isata. A karshe na yi tunanin ban isa in haramta abin da Allah ya halasta ba. Sannan Abdulhakim din bai rageni da komai ba, sai ma wata sabuwar kauna da a kullum take k
ara habaka kamar ya mai dani cikin kirjinsa saboda
kauna da soyayya.
Da wannan na rarrashi zuciyata na kwanta rigingine a gadona ina karatun addu’o’in littafin HISNUL MUSLIM. Tareda duba littattafaina na makaranta.
[9/15, 8:18 PM] Asmau: A hankali ya m
urda kofar ya shigo, ya zauna daidai kafafuna, qamshin masifaffen turarenshi (Aqua D’gio) na dukan hancina.
Ya dora hannu akan yatsun kafata yana ja a hankali. Na samu kaina da rashin son daga ido in dubi Abdulhakim, domin son da nake mishi ya ragu, yayi
rauni, yana nema ma ya rikide zuwa tsana mai tsanani, ga shi na yiwa
kaina alqawarin na daina nuna mishi fushina tun ranar da ya tunatar dani illar hakan a gare shi.
Sai na sauke littafin a hankali ina kallonsa. Ba tare da na ce dashi komi ba. Ya ce, “Ki
yafe ni idan na yi miki ba daidai ba, ki yafe ni idan na yi wani abu wanda ya bata miki rai.... ki....”
Nayi saurin kai yatsuna na rufe mishi baki,
“Ni baka yi min komai ba, nice ma zan baka hakuri a kan abin da na yi jiya wajen shiga mota. Ita ma amary
a ka ba ta hakuri......”
Farin ciki ya bayyana a fuskarsa, don bai zaci hakan daga gareni ba, musamman a daidai wannan lokacin da kowacce mace ke azabtuwa da shi.
Ya kama hannuna muka mike tsaye, ya ce, “Abinci nake so zan samu?”
“Akwai, Hajiya ta aiko
dashi tun dazu”.
“To dauko muje wajen Farida”.
Na nufi kicin na fiddo abincin cikin kwandon abinci, ya karba ya wuce gaba na sanyo hijabi kan kayan barcin da ke jikina na cimma shi muka isa side din Farida.
Shi ya fara shiga kafin in bi bayanshi. Tana
kishingide tana waya tana dariya. Shigowarmu tasa ta kashe wayar ta yi fara’a sosai ta mike ta karbi kwandon hannunshi ta aza a dining na falonta.
Ina kallon ta ina tazbihi ga sarkin halitta, ashe akwai mata masu kyau haka a duniya ban sani ba? Na ji tau
sayin kaina, ko da yake Abdulhakim ya ce wai nima ina da kyau? Oho!
Da kanta ta yi serving kowannenmu, duk inda ta motsa tattausan qamshin Estee-Lauder ke tashi. Maimakon ta ci wanda ta zuba, sai ta sanya cokalinta cikin plate din Mijin-Sakinah.
Bai yi m
agana ba, da haka aka kare cin abincin. Ya dubi Farida sosai ya mai da fuskarshi ya dinke. Ya ce,
“Farida ga matata Sakinah, lafiya muke zaune ba don ta yi min wani laifi bane ko ta gaza dani ta wani bangare yasa na aure ki ba. Na aure ki ne don ina sonk
i kamar yadda nake sonta.
Bamu taba samun rashin fahimta ba a tsayin zamanmu na shekaru uku, ina fatan shigowarki cikin rayuwarmu ba zai canza komai ba.
A girme dai kin girme ta, kin fita hankali, don haka ki rike ta kamar kanwarki. Alfarma ce nake nema,
zan samu Farida?”
Ta dube ni sosai cikin ido, Allah kadai ya san abin da take saqawa a ranta. Ba tare da ta ce komai ba.
Ganin ba ta da abin cewa sai ya juyo gareni ya ce, “Sakinah ga nan Farida, ita ma matata ce kamar ke, na aure ta don ina sonta, ba d
on mu quntata miki ba.
Idan ta girme ki a shekaru, kin girme ta a aure. Don haka ke ce uwargidana a duniya da lahira. Ki zauna lafiya da ita, duk da ba tare za ku zauna ba. Ki rike girman da na baki, kada ki yi wasa da shi. Tashi ki je ki kwanta, Allah ya
bamu alheri”.
Tun kan ya idasa rufe bakinsa na mike, don bana son wannan kallon qurillar da matarshi ke yi mini.
Abin da ban sani ba shi ne kowa ya firgita da kowa. Sai dai kuma Hausawa sun ce ‘ZUCIYAR MUTUM.......BIRNIN SA’. Don haka ban san abin da
Farida ke saqawa a tata zuciyar ba.
Duk da wannan kyawun nata, da gayun nata ban ji gwiwata ta yi sanyi ba har in ji tsoron da zan sallama mata Abdulhakim Ribadu. Kowacce ta murza irin kambunta in yaso mai sa’a ta kwace.
A wannan daren idan na ce na
yi barci babu shakka na fadi karya, sanda na tashi da safe idanuwana sunyi luhu-luhu na rashin barci.
A haka na yi wanka na sanya uniform. Ina daura sandal na fata a kafata Abdulhakim ya turo kofar ya shigo.
Ya zuba wani farin yadi caftan mai yarari da
rashin kauri, ta yadda har ana iya hango vest din da ke jikinshi.
Na ci gaba da daura igiyar takalmina ba tare da na dago na dube shi ba, don bana son ganinsa. Ya zauna gefena, sai na ji shi ma yana qamshin (Estee-Lauder) maimakon kamshin jikinsa na tun f
il azal.
Na finciki jakata zan wuce ya rike hannun jakar, na ja ya ja bai cika ba sai na sakar mishi. Hawayen da nake tattali suka shimfido a kundukukina.
Cikin sassanyar murya ya ce,
“Me ya yi zafi haka Sakinah? Ki yiwa Allah idan laifi na yi miki ki
yi hakuri, gaya min me na yi miki ya saki kuka?”
Na zumbura baki tareda sharce wasu matsiyatan hawaye na ce, “Ni ka bani jakata zan makara, kuma John yana jirana a waje”.
Ya ce, “Ai na sallame shi, ni da kaina zan kai ki. Amma sai kin yi kalaci ko yaya t
ukunna”.
“Ni ba zan ci ba”.
“To ki sha ruwan tea kadai, ina zuwa”.
Ya fita wajen Sabuwa ya hado tea din da coconut-cake guda uku a kan dan tangaran ya dawo. Da lallashi da ban baki na karba na sha, amma ban daina zubar da hawaye ba.
Sai da na shanye sa
nnan muka fito, muna tafe a mota ya damu ya ji abin da ya sanyani kuka da sassafen nan. Da ya isheni da naci na bude baki na furta mishi abin da bai yi tsammani ba.......
“……Ba kai bane ka fesa Estee -Lauder!”.
Ya kama baki, sannan ya yi dariya, ya kwa
ikwayi muryata shima ya ce.
“Ni Abdulhakim na fesa Estee-Lauder.....!”
Ganin ya maida abin wasa sai nayi fuska, na fuske suntum. Shima nan da nan ya zama ‘serious’ ya shiga taitayin sa, yace.
“…..Fesa min ta yi, ba ni na fesa ba. Tunda kuma ba kya so b
a zan kuma bari ta fesa min ba”.
Na kara kuluwa kamar in fashe don bakin ciki. Na ce,
“Ka ga tada motar nan mu tafi na makara”.
Don na lura idan na ce irin wadannan kananan abubuwan zan dinga sanyawa a raina suna damuna nice zan kamu da hawan jini a
banza.
Da muka tashi ma shi da Faridan suka zo dauka ta, duk da a ranar za su wuce Lagos. Allah sarki, sai ta fito daga gaban mota tun kafin in karaso ta koma baya.
Ni kuma na ce ba zan shiga gaban ba ta dawo wajenta ta zauna. Ba ta yi musu ba ta koma
gaban, shi dai bai ce komi ba.
Kafin mu iso Abdallah ya rigamu isowa, domin shi zai kaisu filin jirgi. Ya bani wasu kaya cikin leda wai in ji Safina akwai wasiqa a ciki.
Ina zaune gefen gado ina duba wasiqar Safinah ya shigo, ya zuba sabuwar shiga na s
hadda deep-blue.Da ganinshi kaga ango sosai sai zuba qamshi da sheki yake. Ya ce,
“Zamu tafi Sakinah sai upper week, me zan samu ne?”
Na kawas da kai ganin yadda ya yi kyau da yawa, ban taba ganin mutum mai kyau da sigar Abdulhakim ba. Wani takaici na c
ina a zucci.
Da kyar na ce,
“Allah ya kiyaye hanya”. Ba tare dana dago ba.
Ya ce, “Ba zan samu komai ba?”
Kai tsaye na ce,
“Ba za ka samu ba!”.
Yayi murmushi cikin damuwa ya ce,
“Not even your smile?”
Na hade girar sama da ta kasa na yi
banza da shi. Ya bude baki zai kara magana, na yi kicin-kicin da fuska. Ya ga ba alamun wargi, sai ya yi murmushi ya sosa kai ya ja tsumman rayuwarshi yai gaba.
Bayan tafiyar su na ci gaba da zuwa makaranta ta, bani da lokacin wasu tunaninnika balle
tunanin su ya dame ni, musamman da muka soma jarabawar shiga aji shida.
Safinah ta gama, sai ni da Nadiya wadda take a SS1, yayin da ni kuma nake shirin shiga ajin karshe. Mijin-Sakinah yana kirana a waya yana jin lafiyarmu.
Ita ma Faridar ta kira sau bi
yu wai mu gaisa. Mun gaisa din amma daga jin muryarta ka san tursasata aka yi. Nima ban kara cewa komai ba bayan gaisuwar.
Sati biyu da tafiyarsu na soma wani irin azababben ciwon mara, kwanana biyu a kwance ina murqususu ba tare dana bari Sabuwa ta gan
e ba, don ban fito falon ba.
Ina can bed room dina ina juyi ina salati. Ban ji karar bude kofa ba sai tausasan hannun Abdulhakim a kafaduna, ko iya