Showing 15001 words to 18000 words out of 20369 words

Chapter 6 - ZUCIYAR MUTUM COMPLETE

tafiya kasar Libya.

****

Kwananmu bakwai a Libya, Abbana da Sakinah kullum suna tare, tsumin tsohuwar soyayya na tashi. Daga karshe suka sasanta kansu, na cewa sun yarda za su kara zama karkashin inuwar aure a karo na biyu.

Sai dai ta ce ba za ta kuma zama da Lami ba,

ya amince kuma zai ware mata gidanta daban, ya kuma dauki alqawarin rike mata ‘ya’yanta Tananni da Mus’ab su zauna tare da ita.

Ya yi waya da Kawu Tasi’u ya sa shi ya yi musu shirin tahowa kasar Libya shi da Baffa Sule zai aiko musu da tikiti.

Ranar lit

inin suka iso Libya, washegari aka mai da auren Abbana da mahaifiyata a masallacin da ke maqwabtaka dasu.

A ranar ne kuma Abdulhakim da Daddyn shi suka iso Tripoli, suka samu walimar daurin auren. Karramawa ta musamman Gaddafi ya yiwa su Daddy jin cewa su

rukinshi ne.

Abba da Daddy suka zaunar da shi suna ta nasiha, wani zubin su hada da fada. Duk Mijin-Sakinah ya amsa cewa ya yi laifi.

Sakinah kawai yake so in dai za su ba shi a karo na biyu, to zai jure duk wani punishment da za su ba shi.

Waya ta samu

Abba cewa Mami babu lafiya ta samu ciwon iska, yanzu haka tana Psychiatrist na National Hospital. Nan aka soma shirin tahowa.

Ranar juma’a muka sauka a filin jirgin saman Abuja, kai tsaye asibitin muka wuce. Abun babu kyawun gani, Mami sai addu’a domin

hauka tuburan take tana tonawa kanta asiri tana cizgar gashin kanta, na gabanta dana

hammatarta, na duk irin abubuwan da ta yiwa matan da Daddy yake aure yana saki, da abubuwan da ta yiwa Sakinah.

Sakinah ta kama hannunta ta ce, “Na yafe miki Lami duniya

da lahira na yafe miki”. Amma ba ta fasa surutanta ba. Sai likitocin sun zurmuqa mata allura sannan ake samu ta yi barci.

Hajiya Laila ita ma ta dinga kuka tana cewa, “Da ban tuba ba nima da na san makomata ke nan, Alhaji ka yafe mini, duk tare muke yin

komai, ko mata dari kake so ka aura wallahi na amince maka”.

Dariya ta kama Daddy, ya ce, “A’a, ki bar casa’in da shidan na bar miki, guda ukun dai zan kara tambadaddu masu ja da abin da Allah ya halarta”.

Kwanan Mami goma sha hudu sannan ta samu sauki,

suka sallame ta da magungunan da za ta dinga sha. Gaba daya Mami ta yi sanyi, tana ji kuma tana ganin Sakinah da M.T Liman matsayin mata da miji a karo na biyu. Ta yi ladaf ta zama kamar idan ka sanya mata yatsa a baka ba za ta ciza ba.

Gidan da Abba ya

sayawa Mamana yana nan a Kubuwa, kwanan su Uncle Gadaffi uku a Abuja suka koma Libya.

Babu abin da babu a gidan na jin dadin rayuwa. Duk yadda Abdulhakim ya yi don ya ganni a wannan dan tsukin bai samu ba, Mamana ta boye ni, tana ta gyareni, gyara irin n

a Larabawan asali.

Jikina ya yi kyau, zuciyata sarai. Da kanta ta kaini asibiti aka cire min loops din. Sati hudu ke nan rabona da Mijin-Sakinah, ni kaina na san na yi kewarsa, yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Na yi kewar soyayya da kyautayinsa, na k

uma tabbata ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba.

Kwance nake a cinyar Mamana tana gyara min gashina da man (Bergamot), sallamar Abdallah ta tsinkayi kunnuwanmu, Abdulhakim na bayansa, wasu irin zaratan matasa masu kwarjini na daukar hankali, ilhama da cik

ar zati.

Mijin-Sakinah ya rame fiye da tsammanina, ya riga ya ganni, don haka babu damar gudu. Ko da damar gudun ba zan iya gudun ba, don kwarjinin shi ya cika ko ina.

Na tashi daga kwanciyar da na yi, na nemi dankwalina na daura. Tunda suka shigo Tanann

i ta zura daki da gudu saboda yadda tun a Libya Abdulhakim ke tsokanarta da kiranta “Zaujatee”. Wato matarsa.

Sakinah ta shiga marhaban dasu, cikin dan lokaci an cikasu da cima kala-kala. Mijin Sakinah kokari yake mu hada idanu amma na ki.

Abba ya yi sal

lama ya shigo yana murmushi, ya ce, “Manyan baki garemu a gidan? Da kun yi zamanku yau zamu kawo muku matarku. Ke Sakinah dauko mayafinki ku tafi bana son wata tashin-tashina, komai ya wuce Allah ya baku hakurin zama da juna”.

Idanuna suka cicciko zan yi

kuka, Abba ya ce, “A’a, kar ki yarda mu yi haka dake Sakinah.

Shi auren baki dayansa jigonsa shi ne hakuri, Abdulhakim ya yi laifi, amma ya gane da kansa bai kyauta ba, ki zamo mai afuwa ga wanda ya saba miki, amma bana son kullaci da sanya abu a rai fiy

e da kima, maza tashi kuje Allah ya yi muku albarka”.

Har mota suka rakomu ina ta kuka, Mamana rungume dani tana lallashina. Tunanina shi ne yadda zan ci gaba da rayuwa da Farida, tunda na gane ba ta sona da alheri.

Abdulhakim na tuki yana murmushi, Abda

llah sai zuba min hira yake, amma na ki in kula shi. Ya ce, “Haba Sakinah, dan wannan abu da bai kai ya kawo ba sai ki zo ki gayawa Abba? Maimakon ki neme ni ki gaya mini mu ci mu binne abinmu ba tare da kowa ya ji ba. Na raina wayonki, nan gaba kar ki sak

e yin haka, wannan rashin wayo ne, kin ji na gaya miki”.

Ko amsa ban ba shi ba ya gaji da babatunshi ya yi shiru. Abdulhakim bai tofa mana ba, tukin shi yake cikin kwarewa da sukuni.

Gidan Hajiya muka fara shiga don ta san na dawo, Hajiya kamar ta goyani

saboda lallashi da nuna kauna.

Sabuwa bakinta har kunne, tana “sannu da zuwa uwar dakina”. Daddy kansa sannu da zuwa yake min.

Abdallah ya wuce gidanshi, mu kuma muka nufo namu gidan. Sabuwa ta sa mukulli ta bude, ko ina fes kamar ba a je ko ina ba.

Sa

buwa na ba da baya ya sunkuce ni yana juyi dani a tsakar falon yana cewa,

“Yarinyar nan kin wana ni da yawa…..”. Daga nan muka rankaya ga dakin barcin mu, cikin wata irin soyayyah mai wuyar bayyanawa.

Gyaran Mamana yayi aiki sosai, lallai ‘gata’ sai uwa

r data haifeka. Babban goro sai magogin karfe….(sunan littafin TAKORI mai zuwa). Duk yadda Abdulhakim zai yi ya wanke laifinsa cikin hikima da soyayya ya sani. Na ji babu abin da nake so nake kuma kishi a wannan duniyar irin mijina Abdulhakim Khalil Ribadu

. Daya tamkar da dubu, abin alfaharina, farin cikin rayuwata. Bani da zabi ban da nima in mallaka mishi soyayyata mu raya daren cikin farantawa juna rai.

Na kalubalanci kaina da tunanina na baya cewa zan iya rayuwa babu Abdulhakim a cikinta.

Kwana uku

kwarara Abdulhakim bai je ofis ba, amarci sosai muke gudanarwa wanda a baya bamu taba yi ba.

Na sha mamaki da har kwana uku ban ga Farida ba, ban ji ya yi zancenta ba. Ni kuma ban tambaye shi ba.

Sabuwa ke kyankyasa min tana jin Abdulhakim ya saki Farida

, don taga sanda ake kwashe kayanta.

Na dade ina tunanin al’amarin, daga baya na watsar na shiga harkokina. Shi da kansa yake gaya min Farida tana gidansu, sun rabu.

Bayan wannan bai kara komi a kai ba. Na ji tausayin Farida, domin dai duk wacce ta yi ra

shin gwarzon miji irin Mijin-Sakina, dole a jajanta mata. Sannan ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne.

Sati hudun da na yi ba tare da Abdulhakim ba, ni kadai na san irin halin da na shiga. Na yi mana addu’a dukkanmu cewa, Allah ya sa hakan shi ne alherinmu.

J

arrabawarmu ta fito, daidai sanda Abdulhakim zai tafi qaro karatu (in-service) zuwa jami’ar (Waterloo, Canada).Ya yi cuku-cukun da nima na samu gurbi a can, inda zan yi karatu a kan tsimi da tanadi, wanda aka fi sani da tattalin arzikin kasa (economics).

Ranar litinin jirginmu ya daga zuwa kasar Canada, birnin ‘Vancouver’. Rayuwa ta mika mana cike da ci gaba da budi ta kowanne bangare. Da albarkar iyaye lullube da mu. A Canada na haifi Abdulhakim (Daddy), Ibrahim Khalil, da Mukhtar. Iyayenmu kullum cikin

sanya mana albarka suke, kuma albarkar muke ta gani har gobe, don kuwa kullum cikin ni’imomin Ubangiji muke. Tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayenshi zai ga da kyau a rayuwarshi ta duniya da lahira.

Masha Allahu la-quwwata illa billah!

Maman Safah

da Marwah ce ...

[9/15, 8:18 PM] Asmau: Cikin halin ko in kula ya ta da motar muka hau kan titi.

Ina daga waje inda ya ce in jira shi ya shiga wajen likitan, suka yi magana ya fito ya yi kirana. Ban yi musu ba na bishi da yadda ya ce.

Likitan ya ce in

kwanta, na dubi Abdulhakim kallo na al’ajabi, tsoro da mamaki. Ya yi saurin sunkuyar da kansa bayan ya daure fuska sosai alamun ba wasa.

Ina ji ina gani aka zurmika min wani abu. Sannan likitan ya shiga yi min bayanin wai bleeding zai dan qaru a lokacin

menstruation.

Muka fito daga ofishin ina kuka. Shi ma Abdulhakim ya sha jinin jikinsa, don na lura ya yi cooling, nadama baro-baro ta bayyana a fuskarsa.

Muna tafe ya daure ya ce, “Me aka yi na kuka? Don kawai an duba mahaifarki ko ta isa daukar ciki?”

Kallon da na yi masa na rainin hankalin ya isa! Shi ya sanya ya shiga taitayinsa. Ya kuma tabbatar Sakinar da, da yake treating ‘yar karamar yarinya ba ita ce yanzu ba. Jikinshi ya ba shi ko dai Sakinah ta san loops ne aka luntsuma mata?

Ya yi ta maza ya

ce, “Idan baki daina kukan ba, to sai a fasa zuwa gidan Abban”.

Jin haka na yi shiru ina share hawayena. Har muka zo gidanmu babu wanda ya kara magana. Ya ajiye mu ni da jakata ya ce, “Idan sun dawo daga dinar da zasu je shi da Farida zai dawo ya dauke ni

.

Na ce, “To”. Na bishi da kallo a sanda ya tada motar, domin na tabbata kallon karshe nake mishi. Na daga hannu ina share hawaye wanda ke fita tun daga karkashin zuciyata.

Ilyas ne ya fito, yana ganina ya sunkuci jaka yana yi min oyoyo! Duk al’ummar gid

an suna falon Abba, kowa ya shiga murnar zuwana, musamman Yaya Suwaiba. Na yi iyakar kokarin da zan yi don boye damuwar da ke tattare dani.

Nadiya ta taho da gudu ta rungume ni muka zube bisa carpet, Mami ta ce, “Wani irin rashin hankali ne haka Nadiya? K

aryata za ki yi?”

Ta ce, “Mami sister ta dade ba ta zo ba”. Na ce, “To ai gani yau na zo”. Aka ci gaba da hira har kowa ya zame ya barni da Abba, don sun lura cikin damuwa nake ina bukatar kadaicewa da Abbana.

Abba ya dube ni sosai yana nazarina, ya ce,

“Goben nan nake sa ran zuwa gidan ki in sanar dake labari mai dadi......”

Kafin Abba ya sanar dani albishir din nasa kuka ya kece mini, na yi ta yi ba qaqqautawa. Hankalin Abba in ya yi dubu to ya tashi.

Ya ce, “Me ya faru Sakinah? Fada mini ko mene ne?

Na ce me ya faru? Ko Abdulhakim din ya sake ki ne?”

Na girgiza kai, “Ko daya Abba! Illa na gane Abdulhakim ba kaunata yake yi ba. Ya so ni ne kafin ya samu matar da yake so. Abba ka karba min takardar saki a matsayinka na Alkali mai kare hakkin dan adam”.

Na kwashe komi na alqawarin da na ji yana yiwa Farida, na cewa da ita kadai zai haihu, ni ba zai haihu dani ba. Don kar ‘ya’yan matarshi su samu ‘yan uba. Da kuma abin da ya kaini asibiti yanzun nan aka saka mini.

Abba ya yi shiru kamar ruwa ya cishi, c

an kuma muryar shi ta yi sanyi ya ce,

“Yanzu akwai abin a jikinki?”

Na daga mishi kai. Ya ci gaba da yin shiru, Allah kadai ya san irin bacin ran da ya shiga.

Can ya ce, “Ke me ya sa kika labe musu? Kin san labe babu kyau ko?”

Na ce, “Wallahi Abba ba

labewa na yi ba, zama na yi ina jiransu su fito mu ci abinci Allah ya nufeni da ji. Duk da haka ban yarda ba sai da ya kaini aka sa min.

Sannan gaba daya ya sauya mini tunda ya yi aure, tamkar bai taba sani na ba”.

Ya ce, “Ni wannan bai dame ni ba, amma

maganar a hanaki haihuwa saboda wata ba zan yarda da ita ba. Tashi ki tafi dakin Nadiya zan nemi Ribadu gobe, amma ki kama bakinki ban yarda ki yi zancen nan da kowa ba”.

Sallamar Abdulhakim ta isa kunnuwanmu, ganina gaban Abba ina kuka duk ya sha jinin j

ikinsa. A sanyaye jiki babu nauyi ya durkusa yana gai da Abba.

Abba ya amsa mishi fuska a sake, wannan ne ya ba shi kwarin gwiwar da ya iya zama a falon. Abba ya ce, “Yaushe za ka koma Lagos?”

Ya ce, “Ai na samu transfer zuwa nan Branch dinmu na Abuja, d

on haka ba zan koma ba”.

Abba ya ce, “Allah ya yi jagora, amma Sakinah zan dan riketa kwana biyu. Ya ya babu damuwa?”

Ya dago fararen idanunshi ya dube ni ya yi hanzarin sunkuyar da kansa, cikin sarkewar murya ya ce,

“Babu komai Abba”.

Ya ce, “To Alla

h ya bamu alheri, a gai da Farida”.

Haka ya taso ya fito daga falon kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Bayan ya fita nima na yiwa Abba sallama na nufi dakin Nadiya, zuciyata na suyar da ban san dalilinta ba.

Shi ma Abban cikin tunani na barshi, ko ka

dan bai ji dadin abin da Abdulhakim ya yi ba. Sannan ba ya so aurena ya mutu a kan ‘yar wannan matsalar. Don haka a daren ya kira Alkali Ribadu ya ce ya zo gobe yana son ganinsa.

Da yake Mami ce da girki ta shigo cikin kwalliya tana ce da Abba, “Lafiya Sa

kinah za ta kwana a nan?”

Ya daure fuska ya ce, “Lafiya qalau sai alkairi”.

Jin haka ta mai da bakinta ta rufe suka shiga wata hirar daban.

Washegari ya kama lahadi. Tun karfe goma na safe Alkali Ribadu na cikin gidanmu, Abba ya kwashe komai ya gaya mis

hi.

Ya yi shiru sai zufa ke keto mishi ta al’ajabi da mamaki, sannan da kunyar amininshi da ta baibaye shi.

Ya fiddo waya ya kira Abdulhakim ya ce ya same shi yanzun nan a gidanmu.

Cikin mintuna ashirin ya iso, sai walainiya yake cikin danyen farin boy

el. Kai da ganinsa ka ga matashi mai jini a jika wanda ke cikin lokacinsa, yake kuma jiqe cikin rabar naira.

Abba ne ya amsa mishi sallama, amma Daddy bai amsa ba sai kallon mamaki da ya bishi da shi. Ya gai da Abba ya gai da Daddy, tun bai idasa rufe bak

inshi ba ya ce,

“Wane asibiti ka kai Sakinah aka sa mata abin hana haihuwa?’

Abdulhakim ya dago ya dubi mahaifinsa wanda idonsa ke cike taf da qwalla. Ya yi shiru bai yi magana ba.

Daddy ya ci gaba da cewa, “Tunda baka son hada zuri’a damu sai ka salla

me mu ka zauna da wadda kake so ta haifa maka zuria.......”

A razane ya dago ya dubi mahaifinsa cikin mamakin yadda a kai hirarsu shi da matarshi a daki ta fito waje har su Daddy suka ji.

Nadama sosai ta bayyana a fuskar shi, amma idanun Daddy sun rufe d

a bacin rai, ya dauki takarda da biro ya mika masa.

“Ina son takardar Sakinah yanzun nan.....”

Ya soma kuka yana bai wa Daddy hakuri da duk iya kalmar da zai iya. Ya ce, “Yanzun nan zamu je a cire, ni kaina ban san abin da ke faruwa da zuciyata ba kwanan

nan Daddy. Ina cikin tsoron matata Farida, na fada ne kawai don in kwantar mata da hankali amma ba don haka abin yake har karkashin zuciyata ba.

Ina neman addu’arku a kan Allah ya sa na fi karfin gidana na kasance mai adalci a tsakaninsu......”

Amma ina

! Ran Alqalan ya yi matukar baci, sun ce takarda kawai suke so, babu ruwansu da duk wani halin da yake ciki a kan matarshi.

Wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka, amma Sakinah ta gama aurensa.

Ya ce, “Har abada Daddy ba zan taba sakin Sakinah ba ko bindiga

za a dora mini”.

Daddy ya ce, “To ka je ka yi ta rikon igiyar aure amma Sakinah ta gama zama da kai, Allah ya ba ta mai kaunarta da zuri’ar da za ta fito daga jikinta.

Maganar za ka kaita a cire mata abin da ka kaita aka sa mata, muma mun san hanyar asi

biti, zamu kaita a cire”.

Ya ce, “Ku yi min alfarma Daddy in ga Sakinah in ba ta hakuri, wallahi komai ya wuce”.

Daddy ya ce, “Ba za a yi ba. Ta riga ta kubce maka, kuma da sannu za ta zama mallakin waninka”. A ranshi ya ce, “Ba sai in na sake ta ba?”

A ranar duka mutum hudun wato Daddy, M.T Liman, ni Sakinah da Abdulhakim babu wanda ya yi kwanan dadin rai.

Washegari Abba ya yi kiran Daddy ya ce zai wuce da Sakinah Libya don an gaya mishi mahaifiyar Sakinah ta koma Tripoli bayan rasuwar mijin da take

aure a Qatar din Masar.

Daddy ya ce, “Na ji dadin hakan, ko don a horar da Abdulhakim na wani dan lokaci. Sai kun dawo, Allah ya ba da sa’a”.

Cikin kwanaki uku Abba ya gama min duk cuku-cukun pasport da visa. Ranar juma’a muka daga zuwa Tripoli, babban b

irnin kasar Libya.

***

Agidan wani abokin Abba da suka yi karatu tare muka sauka, yana aiki da Nigerian Embassy Tripoli Libya. Sunan shi Abulkhair da matarshi Radhiyyah.

Mutanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login