Showing 18001 words to 20369 words out of 20369 words
Katsina ne usul, amma Larabci a bakinsu kamar haifaffun kas
ar Libya. Kwanan Abba uku suna bincike sosai shi da Abulkhair da wani abokinsu Balarabe Ridhwan, wanda yake sanar da shi labarin Sakinah suka samo gidan.
Gidan gini ne irin na Larabawan Libya na red bricks (jan dutse). Flat mai hawa biyu, sai korran fur
anni masu ban sha’awa da suka yanyame gidan tun daga kasa har sama.
An kuma tabbatar musu Sakinah tana gidan tare da mahaifiyarta da ‘ya’yanta biyu, da kuma Yayanta Gaddafi da na shi iyalin.
Tunda Abba ya bani labarin ya ce kuma gobe zamu je jikina yake
rawa da karkarwa. Abba ya lura da halin da nake ciki, ya yi murmushi ya ce, “Relax Sakinah....... your mother is nice……. Qaddara ta rabamu, amma muna matukar kaunar junanmu”.
Sanye nake da abayat kirar Abu-Dhabi na nade kaina da bakin mayafi. Kafata ciki
n takalmi mai tudu sosai shi ma baki samfurin C.K, watau dan gidan Calvin Klien.
Hannuna cikin na Radhiyyah lokacin da Abulkhair ke danna kararrawar shiga cikin gidan. Wata yarinya Balarabiya ‘yar kimanin shekaru goma, ta zo ta bude kofar.
Kallo daya na
yi mata na dauka photocopy na ne a lokacin da nake shekaru goma. Ita ma yarinyar kallona take cikin tsoro da mamaki, kafin ta juya da gudu cikin gidan.
Dukkan mu aka rasa mai fara shiga, can anjima sai wani magidanci ya fito dan kimanin shekaru arba’in da
biyu.
Yana ganin Abba ya bude baki ya ce, “Mukhtar!” Sannan ya rungume Abba,a lokacinne ya hango ni a rabe a bayan Abba. Ya cika Abba ya kamo hannuna har cikin gidan yana ta qwala kira, “Sakinah! Sakinah!!”
Daga kicin ta leqo, doguwar rigar jeans ce a j
ikinta, ta daura apron (rigar girki) a kai. Gashin kanta jibgi guda nade cikin tafkeken ribbon.
A zahiri shekarunta talatin da takwas amma a idaniyarka ba za ta fice shekaru ashirin da tara ba.
Na rabe a bayanshi ina kallon Barabiyar da aka kira Mamana S
akinah. A haife dai ba za ka ce ta haife ni ba, zai fi kyau a kirata da yayata ba mahaifiya ba.
Na kasa kifta idanuna daga kanta, kamar yadda ita ma ta kasa dauke ido a kaina. Ta dauka mafarki ne cikin irin mafarke-mafarken ta, na dauka hoton zuciya ne wa
nda nake kwana da yini ina gani.
Kafin ka ce meye wannan hawaye ya kece mini. Sannan wani irin nitsattsen so da kauna na UWA- MAHAIFIYA (maternal love) ya shiga ratsa zuciyata, wanda ke rike dani din wato yayanta (Gaddafi) ya ja hannuna har inda take.
Ma
imakon ta yi magana sai ta saki ludayin dake hannunta ta yi daki da gudu ta rufo kofa. Ni kuma sai na durqushe a nan ina kuka.
Ya ya to ba zan yi kuka ba? Tunda mahaifiyar tawa da kullum nake kwana da wuni da burin ganin ta ba ta yi farin ciki da ganina b
a?
Wata dattijuwa Balarabiya sol ta fito daga wani daki dake cikin tafkeken kayataccen falon. Gaddafi ya yi mata magana cikin harshensu, na dai ji ya ambaci sunan Abba da nawa, bayan haka ban fahimci komai cikin bayanin da yake yi mata ba.
Don ko ta’al b
an sani ba. Ta taho da sauri ta kama kafaduna ta mikar dani tsaye, sannan ta rungumeni a kirjinta.
Hawaye suka kara kece mani, karo na farko da na ji feeling din cewa nima cikakkiyar mutum ce mai cikakken asali da nasaba, sannan gani rungume a kirjin maha
ifiyar uwata. Ko da wannan na tsira na gode Allah ko Sakinah ba ta yi farin ciki da zuwana ba.
Ya fita ya shigo da su Abba, Abulkhair da Ridhwan. Da shi da dattijuwar nan da na ji yana kira Khala suka shiga hidimar sauke ababan jiqa maqoshi masu sanyi.
S
annan yarinyar nan da ta bude kofa ta shimfida ledar cin abinci suka soma fiddo nau’in abinci kala daban-daban a ‘yan kananan tangaraye kamar dama sun san da zuwanmu.
Ko da yake lokacin cin abincin rana ne a can kasar. Gaddafi ya hau saman bene wato flat
din dake samansu suka dawo tare da wata Balarabiyar mai kimanin shekaru ashirin da tara, tana dauke da baby ga wani yaron karami na binsu a baya.
Nan na gane matarshi ce da ‘ya’yansu. Ta iso gareni da sauri ta jani cikin jikinta tana ta magana da Larabci
wanda bana fahimta.
Sai Abba ne yake mata bayani duk suka zagayeni suna murna, kamar su lashe ni. Ta yi kiran yarinyar da ta bude kofa da muka zo ta hada hannuna da nata.
Sai ga wani yaron shi ma da gani ba tambaya ka ga dan gidan, don shi ma muna kama s
osai. Sai dai ban san dan waye ba tsakanin Sakinah mahaifiyata da yayanta Gaddafi.
Su Abba suna ta cin abincinsu suna hira, wadda ban san me suke cewa ba. Gaddafi ya yi bugun duniyar nan amma Sakinah ta ki bude kofa.
Sai ya dauko safayan mukulli ya bude,
nan ya tadda ita ta hada kanta da gwiwa tana rasgar kuka. Ya zauna dirshen a gabanta yana yi mata magana cikin sanyin rai, sannan ya fito ya yi kirana, ya kama hannuna da nata ya hada sannan ya fita.
Ta tsagaita da kukan da ta ke yi tana kallona, har zuw
a lokacin ni ban daina kuka ba. Ta kai hannunta kan kafaduna tana jijjiga ni, sannan ta rungume ni sosai a kirjinta, dukkanin mu muka saki wata nannauyar ajiyar zuciya.
Ga mamakina sai na ji ta ce,
“Ajinki nawa a makaranta?”
Hausar tata ba ta fita sos
ai.
Na ce, “Na gama muna jiran sakamako ne”.
Ta koma Turanci don Hausar ta gagara, ta ce, “Ina su Zainaba, ina yayarki Safinah?”
Cikin farin cikin jin ta yi yaren da zan iya na ce, “Su Zainaba suna ‘Yan Leman, Safina ma anyi mata aure”.
Ta ce, “Ke kuma
fa?”
Na sunkuyar da kaina kasa cikin kunya ban amsa ba, nan ta gane nima anyi min auren.
Ta ce, “Baki da baby?”
Na daga mata kai.
“Ya ya sunan mijinki?”
A takaice na ce, “Abdulhakim”.
Ta ce, “Yana ina yanzu bai biyo ku ba?”
Nan da nan hawaye suka c
ika idona, na ce, “Mun samu sabani ne”.
Cikin damuwa da kulawa ta ce, “Wane irin sabani ne? Amma dai bai sake ki ba ko?”
Na ce, “Bai sakeni ba, amma ina so ya sakeni”.
Ta ce, “Kul! Sakin aure ba shi da dadi. Duk lalacewar mijin fari shi ne miji, tunda s
hi kika sani, shi kika san halinsa. Kinga na rabu da babanki ba don raina ya so ba, sai don abubuwan tsoro da nake gani cikin barcina.
Ana tsoratar dani da cewa in rabu da shi ko a sabauta ni. Don haka Babanki kotu na mayar mai da sadakinshi, Alkali ya sa
nya ya bani takardata. Na so in taho dake amma ya hanani, ya dauke ki ya bawa Lami.
Don haka na sanya ma raina hakuri na taho ba tare da ke ba, don na amince idan ke rayayyah ce, Allah zai raya ki har ki neme ni da kafafunki. Ga ranar yau Allah ya kawo.
Babanki mutumin kirki ne, don a tsayin zamana da shi na wasu ‘yan shekaru bai taba bata min rai ba. Na dauki auranmu a matsayin rubutacciyar qaddara daga Allah da kuma rabon haihuwarki.
Bayan na gama iddah na ci gaba da karatu, watarana Allah ya hadani da
marigayin mijina Uthman.
Haifaffen Libya ne, matukin jirgin sama a Qatar. Muka yi aure muka koma Masar, na dauke mahaifiyata da Yayana don bazan iya zama a wata kasa basu ba, a can na haifi Tananni waccan yarinyar mai kama dake, da dan’uwanta Mus’ab.
Na
samu aiki a babbar kotun Qatar, yau shekaru uku ke nan da rasuwar Uthman bayan gajeriyar jinya.
Muka hado komai namu muka dawo kasarmu ta gado, bana tashi daga inda na yi sallah tsawon shekaru goma sha biyar ban yi miki addu’a ba Sakinah. Ban bai wa Uban
gijina amanarki ba. Sannan ina roqon shi ya sada fuskokinmu da alheri, ga shi yau Allah ya kawo min ke. Bani labarin rayuwarki gaba daya kada ki rufe min komai.
Ban ga Abdulhakim ba, amma na ji zuciyata tana kaunarsa. Yadda ya yarda ya auri yarinya karama
kamar ki.......”
Na yi murmushi ina tuna rayuwarmu ta baya da Abdulhakim. Gaskiya ne Abdulhakim ba masoyin yadawa bane. Sai dai Farida ta rugurguza komai, ta murqushe soyayyar da nake yi mishi. Ta murkushe wadda yake yimin.
Na dago idona da suka canza
launi na ce, “Zan baki labarin rayuwata gaba daya, amma zan yi sallah in ci abinci. Sannan ina neman alfarmar ki GAISA DA ABBANA ba don ya isa ba, sai don albarkacin soyayya da kaunar da ya wanzar da rayuwarshi yana yi miki. Kullum ya budi baki alheri yak
e fada game da ke. Kullum sai ya ce min ‘my mother is a nice person”.
Murmushi ta yi kawai. Ta nuna min kofar toilet, sannan ta zuba abayat ta fita falo. Ta gaisa da Abba, Abulkhair da Ridhwan, sannan ta shiga hidimar dafa musu na’a’na’a.
Cikin dan lok
aci ta kammala, ta zubawa kowannen su a qanqanin kofi ta mika mishi fuskarta na cikin niqab.
Da suka kammala suka mike za su tafi, gabanta na faduwa kada su ce za su tafi dani. Kamar Abba ya san abin da take saqawa a zuciyarta.
Ya ce, “Sakinah za ta zaun
a nan kafin mu warware wasu ‘yan matsaloli a kanta. A qalla za ta yi watanni uku, zan dawo in mai da ita dakin mijinta idan mun sulhunta su”.
Ta ce, “Aiwa!” Suka hada ido suka yi murmushi, wanda ya tado da tsohuwar soyayya. Cikinsu babu wanda zuciyarshi b
a ta buga ba.
Ya fita yana waiwayonta, ita ma ba ta motsa daga inda take ba, sai da ta ji tashin motarsu tukunna.
Na yi wanka na dauro alwala na fito, na canza kaya na yi shigarmu ta Hausawa, wato atamfa super blue riga, zani da kallabinsu.
Juyawar nan
da zan yi na ga ‘yar kanwata tana lekena ta taga, na yi mata murmushi sai ta falla da gudu.
Na yi dariya daidai lokacin da ta murda kofar dakin ta shigo niki-niki da qaton ‘tray’, na yi hanzarin karbarta.
Ta ce, “Ke da wa kike dariya?”
Na nuna mata Tana
nni da ke lekena ta kasan labule. Ita ma ta yi dariya ta ce, “Ba ta da sakewa da mutane, amma ke ta ce min tana sonki ya sunanki? Na ce mata Sakinah. Sai ta ce sunan ku daya ke nan? Na ce mata eh. Ta ce a ina na samo ki? Na ce mata a wata kasa mai nisa, ke
yayarta ce”. Duk muka yi dariya.
Ta sake fita don ta kawo abin sha, wato na’a-na’a, ni kuma na tada sallah. Da na idar tare muka ci abincin duk gidan har da Amal matar Gaddafi.
Tananni da Mus’ab da kakarmu Khala, kowannensu da irin kulawar da yake nuna
mini. Uncle dina Gaddafi ya shigo da Inab da Tuffah fal leda ya miko mini.
Ban taba cin abinci mai dadin wanda na ci yau ba. Balarabe daban ne ta fannin kwarewa wajen girka abinci.
A nan Gaddafi ya gabatar min da kowa da matsayinshi gareni. Ya ce cikin w
atan nan nake sa ran zuwa Najeriya in nemi Mukhtar in ganki, sai gaki Allah ya kawo ki.
Mu dangin mahaifiyarki muna baki hakurin rashin neman ki har tsawon wannan lokacin. Kin san komai ka yi nufi sai Allah ya nufa, shekaru goma sha uku ke nan, wallahi Sa
kinah kullum kina ranmu”.
Na yi murmushi na ce, “Nima kullum zancen da nake yiwa Abbana ke nan, yana cewa lokaci zai zo da Allah zai sadani daku”.
Dare ya yi, misalin karfe goma sha biyu na dare, lokacin da kowanne dan adam ke nemawa haqarqarinshi mahuta
. Amma ban da mu, Sakinah da Sakinah, kwance muke a gado daya kowacce da pillow a karkashin hannunta.
Na soma ba ta labarin rayuwata a hannun Mami, tun daga kuruciya har girma. Auren da Abba ya yi min ina da shekaru sha biyu don kwatar min ‘yanci daga han
nun Mami, da rayuwata da Mijin-Sakinah, Abdulhakim Khalil Ribadu.
Na nuna mata hoton Abdulhakim cikin wayata yana cikin suit na ma’aikatan Julisu Berger ya cacume ni muna dariya.
Ta dade tana kallon hoton kafin ta ajiye. Na ci gaba da gaya mata alqawarin
da na ji ya yiwa matarsa na cewa ba ta yarda ya haihu dani ba don kar a yiwa ‘ya’yanta ‘yan uba, da kaini da ya yi aka zurmuqa min loopscikin umarninta, da matakin da na dauka na gayawa Abba.
Shi kuma ya ce zai nemi Daddy. To har muka taho ban san hukunc
in da suka yanke a kan al’amarin ba.
Shiru ta yi na lokaci mai tsaho, can ta ce, “Me ya sa kika gayawa Babanki? Me yasa shi baki fito fili kin gaya mishi kin san abin da suke ciki ba? Daga nan ki ba shi dama ya baki uzurin kare kansa?
Uzuri sau saba’in A
llah ya ce ki yi masa kafin ki kama shi da laifi. Kishiyarki wayo ta fiki, ba matsayi a zuciyar miji ba.
Kinga dai ba ta taba nuna miki ba ta sonki ba, amma a zahiri ba ta sonki. Sannan akwai sihiri irin naku na Hausawa da ake yi don a raba mace da mijint
a, kamar wanda Lami take yi a baya.
Ji na yi na tsani Abban ki, gara in ga mutuwata da in ganshi. Amma soyayya ta gaskiya ba ta taba gushewa. Shi sihiri ko Annabi (S.A.W) anyi masa, kuma ya cishi balle Abdulhakim.
Maganin hakan shi ne, mikewa tsaye da ad
du’a da neman kariyar Allah. Shi sihirin yana tasiri amma abune na dan taqaitaccen lokaci, sai dai idan za ka dauwama a cikin aikata shi, amma ko ba dade ko bajima yana da karshe.
Kada ki kara sama ranki wai za ki bar masoyin kwarai irin Abdulhakim saboda
wata can. Kar in kara jin wannan furucin. Aure da Abdulhakim yanzu kuka fara har zuwa ranar da muka daina numfashi”.