Showing 12001 words to 15000 words out of 20369 words

Chapter 5 - ZUCIYAR MUTUM COMPLETE

bude idona bana yi saboda azaba.

Ganin yadda nake kankameshi kamar mai shirin haifo da ya sunkuce ni, kafi

n ya kai bakin kofa jini ya balle, har da guda-guda. Ciwon kuma ya lafa.

A take na ce, “Sauke ni, wani abu yana zubowa”.

Ya yi toilet dani ya dire ni cikin kwami ya kwance min zanin, sai ga jini na ta shatata. Daga ni har shi duk mun rude mun firgice mun

rasa abin yi.

Da sauri ya fita ya aika Sabuwa ta siyo always pad, cikin dan lokaci ta kawo. Ya ce, “Kin iya amfani da ita?”

Na girgiza kai alamar “A’a. Ya fita ya kira Sabuwa, ita ta taimaka min na yi wanka na yi qunzugun. Ya dawo muka fita sai asibiti.

Likita ya dubani sosai, ya ce “Kada ku damu menstruation ne ta fara”. Ya rubuta min qwayoyin da za su taimaka mini muka fito.

Abdulhakim cike da tunanin Sakinah ta girma, daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ta iya daukar ciki.

Don haka ya shiga damuwa so

sai, amma da ya yi tunanin ta cika shekaru sha biyar sai bai damu sosai ba.

Shi da ya zo da qishin Sakinah, haka ya hakura ya bige da jinya, saboda yadda na firgita da wannan sabon al’amari da ya same ni.

Na yi zaton wani ciwo ne Allah ya dora mini, yan

a lallashina yana nuna min ba wani abu bane, abu ne da kowacce mace ke yinsa. Har ya koma jinin bai dauke ba.

Wannan tafiyar da Mijin-Sakinah ya yi har aka kwana goma bai neme ni a waya ba, nima ban damu ba saboda karatunmu ya yi zafi.

Wani satin ya shud

e babu Abdulhakim babu wayarshi. Tun bana damuwa har na soma damuwa. A satin Abdallah ya zo, ya kawo min cheque din kudi wai in ji Abdulhakim.

Kamar in yi shiru sai kuma na daure na ce,

“Yau satinshi hudu ke nan bai zo ba”.

Abdallah ya ce, “Lafiyarsu l

au, don last week na je Lagos din, kin san yanayin aikin nasu ba wuri daya suke zaune ba, kuma na ji yana cewa zai je Akure yin wani aiki wanda zai dauke shi lokaci mai tsawo”.

Kamar in ce waya fa? Na ga babu amfanin tambayar, sai na yi shiru.

Wasa-was

a sai da Mijin-Sakinah ya shafe watanni hudu bai zo ba, sai dai bai fasa turo Abdallah ya kawo min kudi ba.

Shi kadai ya san me yake gayawa Daddy har bai damu da zuwan nashi ba. Hajiya ce dai ba ta yarda ba, ta kira shi ta ce, “Duk abin da yake ya bari ya

zo gida ta gaji da uzurirrikan sa”.

Da ya tashi zuwan sai ga shi da Farida, lokacin muna tsaka da shirye-shiryen jarrabawar fita. Watanni bakwai cif ban sa Abdulhakim a idona ba.

Ina study room ina nazarin litattafaina ya yi sallama a kofar studyn Farid

a na bayanshi, muna hada ido ta kasheni da murmushi wanda da gani za ka san na gayya ne.

Na rufe littafin ina yi mishi sannu da zuwa cike da karfin zuciya kada Farida ta ga weakness dina. Nima murmushin na yi mata cikin nuna ban gane irin murmushin da ta

yi min ba.

Na ce, “Ga shi ban san za ku zo ba, bamu sanya sanwa daku ba”.

Ta ce, “Ba wani abu zamu iya jira har a dafa tunda ba a yunwace muke ba, bamu dade da cin abinci ba”. Dakinshi ya shige ya barmu a falon.

Ta ci gaba da yi min wannan mugun murmus

hin nata, na fara tsorata da sha’anin matar nan, don ba ta yi min kama da mutane masu dauke da alheri ba. Na soma karanto duk addu’o’in tsarin da suka zo bakina, na tashi na bar mata falon. Ganin haka ita ma ta koma sashenta.

Da daddare mun kammala hada a

binci ni da sabuwa, Abdulhakim ya shigo kai tsaye ya wuce sassan Farida.

Ko a fuska Abdulhakim ya sauya, kai yadda yake nunawa ma kamar bai sanni ba. Ya sosa zuciyata, ga tsoron matarsa a gefe.

Na tambaye shi inda za a shirya abinci ya ce ba tare da walw

ala ba,

“Ki kai sassan Farida”.

Da taimakon Sabuwa muka jera abincin a dining din Farida. Sabuwa ta fita, ni kuma na zauna cikin kujerun falonta ina jiransu.

Sai na jiyo shesshekar kukan Farida, irin kukan nan da ake kira kukan kissa. Tana cewa a hanka

li......... “Ni dai don Allah kada ka bari ta dau ciki, ka yi min alfarma in fara haihuwa tare da kai. Bana so ‘ya’yana su samu ‘yan ‘uba........don na tashi cikin ‘yan ubanci na san rashin dadinsa. Plz Hakim ka rike alqawarinmu da ka ce ni kadai zan haihu

tare da kai.......”

Da alama ya tsaya ne yana lallashinta, ya ce, “Na ji na yi wannan alqawarin, sai dai kuma kina nufin ba zan kusanci matata bane ita ma in ba ta hakkinta mai yawa da yake a kaina? Watanni bakwai tunda na aureki bana tare da ita, kin ha

nani zuwa, na zama makaryacin karfi da yaji ga iyayena.

Yanzu kuma da muka zo ki ce ba za ki ba ta girki ba? Kada ki manta ita ma ‘yar adam ce kamar ki. Don kin ganta yarinya karama sai ki dinga ribatata mu zalunce ta? Wata bakwai fa, haba Farida!”

Cikin

sassanyar murya ta ce, “Ni ban ce kada ka kusance ta ba, tunda akwai contraceptions kamar kwararon roba da loops ka kaita a sanya mata.....”

Da gudu na yi daki bana ganin abin da yake gabana. Lallai gaskiyar Hausawa da suka ce ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA.

Id

an wani ne ya gaya min Abdulhakim zai taba yi min haka ba zan taba yarda ba, sai ga shi Allah ya yarda kunnuwana sun jiye min, don ya san bani da hakkinsu. Allah abin tsoro, mutum ma abin tsoro ne. Soyayya KARYA ce a yau na kalubalanci duk masu yarda da it

a.

Na yi kukana ya isheni na gode Allah. Ba abin da zuciyata ba ta kimsa mini ba a a daidai wannan lokacin.

Wanda ya ce ba zai haihu da kai ba, shi ne kuma yake ikirarin yana kaunar ka. To wace irin kauna? Ko dai yaudara?

Lokaci daya na ji Mijin-Sakinah

ya sire mini, duk wata soyayya da kaunar da nake yi mishi na nemesu na rasa.

Wata zuciyar ta ce, “Hada kayanki ki yi tafiyarki gidan ubanki”. Wata kuma ta ce, “A’a, in kin je ki ce me? Baki da hujjar da Abba da Daddy za su yarda dake, ki ce labe kika yi

musu ko ya ya? Ke za a bawa laifi. Zuba musu ido ki ga kamun ludayin su tukunna.

Shin da gaske ne zai aiwatar da abin da matarshi ke so a kanki? Ko zai dubi soyayya, kauna da amana?

Jin takun tahowarshi yana tahowa na yi saurin gyara kwanciyata na rufe

ido kamar ina barci, ya dade tsaye a kaina yana mamakin kansa.

Ya kama kanshi da hannuwanshi biyu. Ya ce, “Me ke damuna ne?

……TSORON FARIDAH?”

Ya kai hannu ya ja babban dan yatsana na kafa na bude jajayen idanuna a kanshi, wanda ya yi zaton barci n

e ya mai dasu hakan.

Mun dade muna kallon juna, kallon da babu so da kauna a kwayar idon kowannenmu. Ya yi karfin halin cewa.

“Ya za ki kai abinci ba ki zama mu fito mu ci tare?” Na kawar da idona a kansa, “A qoshe nake, shi ne dalili”.

Bai ce komi ba y

a juya yana cewa, “Ki shirya yanzu asibiti zamu je”.

Na bishi da kallon mamaki da tsoro, tare da kara sarewa da al’amarin Da-Namiji. Na amince lokaci ya zo da zan koma gidan Mami, in koma cikin rayuwata ta baya, ta da mara ‘yanci ya fiye min da in zauna d

a mayaudarin masoyi. Sai dai na qudurce ni da aure hai-hata-hai-hata.

Ina shiryawa ina kuka wanda ba zai sa ba, ba kuma zai hana ba. Na qudurce a raina in na fita gidan nan a yau na fita ke nan har illa masha Allahu.

Na dauki daya cikin jakunkunana na zu

ba duk abubuwan da zan bukata, na yankewa zuciyata rabuwa ta har abada da Mijin-Sakinah, ina maraba da duk irin rayuwar da zan tsinci kaina a gaba.

Har jikin mota Farida ta rakamu, kamar ta hadiye Abdulhakim don tsatsiba. “Plz Hakim kar ka dade ka san zam

u je dinar Iman karfe takwas”.

Ya ce, “Ina sane ba zan dade ba”.

Ta juyo kaina tana murmushin nan nata, “To Sakinah sai kun dawo”.

Ban kalle ta ba, sannan ban amsa ba. Ya yi mamakin ganin na bude but na jefa katuwar jaka.

Ya ce, “Ina za ki da wannan ja

kar?”

Na ce, “Ina so in mun gama da asibitin ne mu biya gida in kai wa Nadiya kayanta ne a ciki”.

[9/15, 8:18 PM] Asmau: ****

Dawowar shi kenan daga sallar juma’a ya shigo falon Farida babu kowa, Sabuwa ta koma gidan Hajiya tun bayan tafiyar Sakinah.

Y

a duba dining babu wani abincin kirki da aka ajiye, sai wata dankararriyar taliyar Indomie fara sol. Ya yi tsaki ya rufe, matsalar Farida ke nan, shegiyar kiwa da lalaci.

Ba ya jin wannan farar taliyar za ta iya quenching wannan gigitacciyar yunwa da yake

ji. Don tun safe haka ya fita ya barta tana barci ko karin kumallo ba ta ba shi ba.

Sannan Hajiya ta ce kada ya sake ya kara zuwa wajenta neman abinci, ta kuma gargadi masu aikinta kada wanda ya ba shi, ya je ya soya Faridar ya cinye, amma babu ruwanta.

Ya shiga kicin ya bude firij babu komi ciki, sai doyin rubabben nama, ga tulin wanke-wanke ba a yi ba.

A store din da ke cikin kicin din kayan miya ne fal da potatoes duk sun rube, sai wari suke. Cike da bakin ciki ya nufo dakin Farida don ya sauke mata

bala’in da ke cin zuciyarshi, ya dora hannu akan marikin kofar dakinta ke nan ya jiyo dariyarta, da alama ba ita kadai ba ce.

Ta ce, “Duk magungunan da na karba na yi amfani dasu yadda ya dace, zancen nan da nake miki Mama, yanzu ba ta gidan nan, shi kans

a bai san inda take ba. Kuma ya tabbatar min ta tafi ke nan, don ta bi mahaifiyarta kasar su.

Aikin na Bakin-Kogi ya fi na dan Tsubura’u, don na ga yakini, tunda na hada na zuba mishi a juicy shi ke nan bai kara tunata ba tsayin watannin nan, sai da uwar

ta bude mishi wuta.

Duk da haka ya ce sai dai in tare zamu je, amma in ba haka ba to ba zai zo ba. Ni kuma gudun bacin ran iyayen ya sa na ce da shi ya yi hakuri mu zo don na lura ba tun yau ba Hajiyar ba ta sona, Balarabiyar take so.

Sannan na hana shi

haihuwa da ita kuma ya amince, har ya kaita an sa mata abin hana daukar ciki da yake yarinya ce ba ta san komai ba. Ni yanzu hankalina kwance yake ya tsumma a randa, don haka na fasa fitowa in komawa Alh. Garba, don ba zai shayar dani soyayyar da Abdulhaki

m ke shayar dani ba. Saidai ya bani kudi.

In kuma don naira ne ga inda nairar ta zauna da gindinta nan. Ada kam ban san yaya aljihun Abdulhakim yake ba, shi ya sa naki aurensa na yarda da auren Alh. Garba......”

Ji ya yi numfashinsa na shidewa, ya juya b

aya ya jingina da kofar don ta dauki nauyin gangar jikinshi.

Uwar ta ce, “Kina nufin bai san kin taba aure ba? Kada fa watarana ya binciko liki ya balle?”

Ta ce, “Ni mahaukaciyar ina ce zan gaya mishi na taba auren? Ai duniyar nan Mama yanzu kawai ZUCIYA

R MUTUM..........BIRNIN SA, wallahi da ya ji da ba zai aure ni ba yadda yake da masifaffen kishin nan.

Dinki na je aka yi min kuma bai gane ba, don har yau bai taba tada zancen ba. Yanzu abin da ya rage min shi ne, ina jiran aikin da na bakin kogi yake ha

damin wanda zai bita da takardarta har dakin uwarta..........”

Sai ya bude kofar, hawaye na tsiyaya daga idanunsa ya ce,

“Kafin in bita da takardar har dakin uwarta.......ke ga taki a gaban taki uwar. Ki je ki komawa mai kudi tsohon mijinki, amma ni ban

i da kudin da kike zato.

Ni ma’aikaci ne kawai wanda zai iya ciyar da Sakinah kadai, ki je na sake ki saki uku! Ko a yanzu haila kike, babu jinina a tare da ke.

Cutar da kika yi min kika kika rabani da mai kaunata kika hadani da iyayena ki je na yafe mik

i”.

Ya juya ya fita ya barsu tsuru-tsuru an rasa mai karfin gwiwar yin wani motsin kirki a tsakaninsu.

Ya dawo da takarda cikin ambulan ya dora mata a kan cinya ya juya ya fita yana cewa.

“Ina da bukatar muhallina, don haka na baki kwana daya ko allurar

ki kada in gani a gidana. Idan hakan ta faru to za ki kwashe su a waje. Na gaya miki na kara gaya miki, kwana daya rak na baki ki bani muhallina”.

Ya fita yana hawaye ya nufi gidan Hajiya. Yadda ya shigo ma Hajiya Laila sai da gabanta ya fadi.

Ya zauna c

ikin kujera idanuwanshi jazur, jijiyoyin kansa sun fito rado-rado, ya dafe kanshi da hannuwa bibbiyu hawayenshi na zuba.

Ta ce, “Kai lafiya? Ko wani ya mutu?”

Ya girgiza kai, ya ce, “Ki yafeni Hajiya......tabbas duk wanda ya ki bin mahaifiyarshi yana tar

e da nadama......”

Ya kwashe duk abin da kunnuwanshi suka jiye mishi tsakanin Farida da mahaifiyarta ya fada mata. Da kuma matakin da ya dauka. Ta ce, “Kash!

Ka yi mummunan saki wanda Allah ba ya so. Sannan saurin saki ba dabi’a ce mai kyau ba.

Ni din

nan ba abin da ban yiwa mahaifinka ba,don kada ya kara aure, don haka don anyi maka ba zai zamo abin mamaki ba, tunda an ce duk abin da ka yi, sai an yi maka, ko a yiwa naka.

Amma yanzu na gane kuskurena, na tuba ga Allah na nemi afuwar mahaifinka, kuma y

a yi afuwa a gareni.

Sannan don ta taba yin aure ai ba wani abu bane, tunda ba cikin shege ta yi ba. Sannan akasarin mata da suke bin wannan hanyar don soyayyar da suke yiwa mazajensu ne ta yadda har basa son wata ta rabe su......”

Ya girgiza kai ya ce,

“Duk soyayyar da aka ginata bisa karya da yaudara Hajiya ba soyayyar gaskiya ba ce, don wanda ke son wani da sharri, shi da alheri, to zuciyarshi ba mai kyau ba ce.

Farida ta sire min Hajiya, don ba sona take ba, kanta kawai take so da amfanin kanta. Ba z

an kuma amince mata ba, domin a da na yarda da ita, nayi mata shaidar alheri, amma ashe ZUCIYAR MUTUM….BIRNIN SA! Ba zan kuma iya ci gaba da zama da ita ba.

Ina da kishi Hajiya, ba zan iya sake hada jiki da sauran wani ba. Ta je ta koma gidan mijinta, dam

a tausayinta ne ya ribace ni da tunanin soyayyar da take yi min ce ta hanata yin aure. Don haka tunda ita mayaudariya ce, to ta je ta ci gaba da yaudarar wasu ba ni ba”.

Hajiya ta girgiza kai ta ce, “Allah shi kyauta”.

Ya ci gaba da zama bai tashi ba, ya

na so Hajiya ta yi mishi zancen Sakinah, amma ba ta yi ba. Ya kara sunkuyar da kai ya ce,

“Don Allah Hajiya ki taimake ni ku dawo min da Sakinah........Daddy da Abban Sakinah sun ki saurarata.

Wallahi Hajiya bani da wani nufi a kan Sakinah sai na soyayy

a, amana da alheri........illa na samu kaina cikin gudun bacin ran Farida da tsoronta. Hajiya a yanzu Allah ya yaye min, ji nake kamar an sauke min wasu kaya masu nauyi daga kaina”.

Hararar shi Hajiya ta yi, kafin ta yi murmushi ta ce, “Sanda kuke kulla m

ata mugun nufi kai da matar da kake son ka tuna dani? Sai yanzu da ta kwabe maka za ka san dani? To babu ruwana, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Cewa nake ka san inda take, sai ka je can ka nemo ta”.

Kamar ya yi kuka ya ce, “Don Allah don Annabi

Hajiya ki yi hakuri, kuskure ne babu wanda ya wuce shi. Na kuma amsa cewa na yi kuskuren, na tuba na bi Allah na biki...........don Allah Hajiyata”.

Abin ki da UWA, nan da nan zuciyarta ta soma sanyi, ganin Abdulhakim yau yana yi mata kuka da girmanshi

da komai, abin da ba ta taba gani ba a girmansa.

Sannan Abdulhakim din shi kadai Allah ya bata duk fadin duniyar nan, kaunar da ta ke mishi ba kadan ba ce. Sai dai ya bata mata rai ba kadan ba, tunda ya batawa Sakinarta.

Ya sauka daga kujerar ya kama ka

fafunta yana kuka sosai. Ba ta san sanda ta kai hannunta tana share mai hawaye ba.

Ta ce, “Ya isa haka Abdulhakim, Sakinah da Abbanta basa nan suna kasar Libya wajen mahaifiyarta. Ban san kuma ranar da za su dawo ba, ka je ka nemi afuwar Daddy in ya ga da

ma sai ya baka adires ka same su a can ko ya rakaka tunda ya san inda suke”.

Ranshi ya yi sanyi, tunda a qalla Hajiya ta yafe mishi. Sai dai yana tsoron karon shi da Daddy.

Kwanan shi uku yana bin Daddy da magiya da ban hakuri kamin ya samu Daddyn ya sau

ko, amma ya yi masa fada sosai, ya kuma hada da nasiha.

Sannan shi ma bai ji dadin sakin rashin tausayi da ya yiwa Farida ba. Duk Abdulhakim ya karba ya kuma ba da hakuri, sannan ne Daddyn ya ce ya soma yi musu shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login