Showing 48001 words to 51000 words out of 237425 words

Chapter 17 - ZAKI COMPLETE

dai ya saka a masa, but this time around yana jin kamar da kansa yake bukatar yin gudun kar wani yai masa fahimta baibai.

  Sai da ya hango wani tafe kusa da motarsa sannna

n ya sauke gilashin motar ya bude baki kamar baya son magana ya ce.

“Malam ina masu gidan nan?”

Mutumen da aka tambaya ya tsaya daidai gilashin motar Aliyu yana kallonsa ya ce.

“Mai ainahin gidan kake tambaya?”

Aliyu yai shiru na yan mintuna

kamar ba zai sake cewa komai ba.

“Wata fulanin yarinya na ke tambaya”

“Oh Ataa buzuwa ga inda suka koma can, gidan na shiga kwanar akwai wani karamin gida ba sosai ba, ka tambaya suna can”

Mutumen na gama yi ma Aliyu kwatan gidan da ke nesa da wa

nnan, Aliyu ya daga gilashin motarsa ba tare da yai ma mutumen godiya ba, ba kuma tare da ya sake cewa komai ba. Har mutumen ya ji haushin bata lokacinsa da yai yana masa bayani. Inda mutunen ya kwatanta masa ya nufa amman ya ki ya shiga kwanar ya tsaya ya

na hangon gidan da yake sa ran shine mutumen yake nufi. Idan ma ya ganta mi zai ce mata? Shi ya fi tsaya masa a rai, yasa ba zai iya bata hakuri ba, and ba zai iya tsayawa yi mata bayani ba, then miye na neman inda take har ya nemi ganinta.

‘No idan na

ganta da ido na tabbatar tana nan zan saka wani ya zo yai mata bayani, ba ni da hannu a ciki’

Zuciyarsa ta raya masa, gamsuwa da wannan yasa shi shiga kwana ya tsaya daidai kofar gidan, babu wanda zai aika ciki and wa zai ce a sallamo masa ma idan ya a

ika din? He decided ya danna horn idan an fito fine idan ba a fito ba kuma ya kama gabansa. Sau biyu ya danna kan yai na uku Farida ta leko ganinta yasa shi sauke gilashin motar yana aika mata da wani kallo. Tabbatar da kofar gidansu ake horn din yasa ta k

oma ta saka Hijab dinta ta fito ta nufo inda yake fake da Motarsa yana kallon kofar gidan na su.

“Ina wuni?”

Ya gyada mata kai alamar ya amsa gaisuwar gaisuwa sannan ya motsa bakinsa kadan ya ce.

“Wata buzuwa na ke nema ance suna nan”

Gaban F

arida ya fadi, jin cewar Ataa yake nema, gashi daman daga ganinsa ba zai yi mutumci ba, abunda ya fara zuwa a ranta mi Ataa tai masa da ya zo nemanta, mi zai mata? Miyasa yake nema? Duk a lokaci daya tai ma kanta wannan tambayar.

“Sun tashi daga nan”

Ya sake kallonta kasa da sama ba tare da yace mata komai ta shiga masa bayani domin itama kanta tana jin kamar zai gano karyarta ne.

“Eh mai wacan gidan ne ya ce sai sun tashi, saboda an fada masa maciji ya sari maman Ataa, da aka kaita asibiti suka d

awo nan shine ya sa aka watsar da bukkarsu aka koresu ya zagaye gidansa, sai suka dawo nan shekaranjiyar nan suka koma Kaduna”

“Ba su gida ne?”

“Ba su da gida daman bukka ce suke kafawa da mutumen ya koresu suka zauna nan na kwana biyu sai kuma sheka

ranjiya suka koma Kaduna”

“Kaduna wane unguwa?”

“Na'am...”

Tai shiru tana ta tunanin unguwar da zata fada domin ko a sokoto ba ko wace unguwa ta sani ba balle kuma a Kaduna da bata taba zuwa ba.

“Rijiyar Zaki... ”

Ya sake kallonta da kyau g

ashi fuskarnan tashi babu annuri duk sai tsoro ya kara kama ta.

“Aa ba can ba unguwar mai malala... ”

“Malali?”

Ya gyara mata jin kamar ba ta fada daidai ba.

“Eh eh can fa, kusa da wani gida mai jan gini zaka ga bukkarsu a gurin”

Hannunsa

ya saka ya dauko katinsa da ke cikin motar ya jefara kasa.

“Ga kati nan idan kin samu labarin gaskiyar inda take ki aika min sako ta number, ko kuma ki tura min number ta”

Dukawa tai ta dauki katin tana fadin.

“Su da ke neman abunda za su ci ina

ma zata samu waya, amman miyasa kake nemanta ta maka wani abun ne?”

Ko ba ita ba be ji zai amsawa kowa wannan tambayar balle kuma ita da yake gani ita da banza duka daya. Gilashin motarsa ya tayar ya soma driving a hankali ya bar a gurin tsaye tana kall

onsa har ta daina hangosa.

   Daga Clapperto road ya dauki hanyar arkilla wato family house dinsu wajen Momy. Yanzu kan ya gane dalilin daya kai Ataa asibiti, wato maciji ya tsari mahaifiyarta a can ne Doc Asim ya ganta ya cire mata kodar, amman abunda ya

fi tsaya masa a rai zancen bukkar nan, how on earth za ace akwai mutumen da be da gidansa kansa, even ma ace mutum be da gidan kansa ai akwai gidajen haya da zaka iya biyan kudi ka zauna, amman ya za ace a bukka suke zama, samun kansa ya kasa yarda da abu

nda yarinyar nan ta fada masa. A daidai gate din gidansu ya tsaya ya danna horn sau daya kan kace kwabo aka bude masa gate din ya shiga, a harabar gidan ya faka motarsa ya fiddo wayarsa ya kira Doc Asim, ringing daya ya picking a tunanin Doc Asim zai masa

maganar ciwon Rahma ne ya ce ya tashi ko wani abun dabam amman a mamakinsa sai ya ji ya aika masa da wata tambayar ta dabam.

“Yarinyar da ka cirewa mhaifiyarta koda miya kawo ta asibitin ka?”

“Maciji ya tsari mahaifiyarta, suka zo bata da kudin maga

ni ta ji ana zancen koda ta ce zata siyar”

“Ba siyarwa tai ba Asim, cirewa tai da karfin tsiya, da siyar tai yi kudin da zaka bata za su isheta tai rayuwa na wani lokaci”

“Ina shaidar siyar da ita da tai, kuma be kamata wannan ya dame ka ba, kai dai

ka ce kana son koda kuma an samo maka ba an wuce guri ba”

“Da na ce ka kawo min ban ce ka zalinci wata ba ai, maciji ya sari mamanta sai ki amfani da wannan damar ka yaudare ta ko? Mahaifiyarta tana raye ko ta mutu”

“Ba ni da masaniya yanzu”

Aliy

u ya kashe wayar tare da bude motar ya fito, yana tuna lokacin da yake tare da kanwarsa Humaira har take mikawa Ataa hannu ta ce ta bata wayarta da ta dauka. Be samu kowa a falonsu ba, kai tsaye nufi dakin Momy da yake hangowa a bude, yana shiga ya sameta

tana gyaran gadonta, da sallama ya shiga ya zauna a kujear da ke facing din gadonta.

“Momy yau ke kike gyaran gado da kanki?”

“To yau duk da wuri suka fita, kuma har yanzu ba su dawo ba”

“Ai ba kullum za su rika aiki ba, su ma suna bukatar hutu, d

a dai kin samu mai aiki ai su ma sai su hutu”

Zaunawa Momy tai tana kallonsa.

“Shi gyaran gado shara wanke wanke girki har wani aiki ne? Idan ba su koya a gida ba so kake su je su yi ma mazajensu irin na matarka? Ai ba kowa ne namiji ne irin ka ba”

Yayi murmushi.

“Momy ita ma fa saboda ciwo ne, bata saba da wahala ba”

“Kula da gida da miji shine wahala? Wasu na can Allah kadai ya san abunda suke kamin su samu su ci ma, wasu ba su kaita ba amman suna can sun iya kula da miji, kai yanzu baka

san dadi mata ba sai ka samu mai kula da kai”

“Rahma ma tana kula da ni Momy, ke ce ba ki gane ba”

Tabe baki Momy tai

“Dazu mun yi waya da Fulani ashe taje dubai har ta dawo ban sani ba, ta kirani tana ta min fada wai na dauke mata yaro”

“Eh t

a kirana kwanan baya tace min zata je dubai ashe tafiyar ba mai dadiwa ba ce, ai mun kusa zuwa Abuja Rahma ma ta fara min maganar”

“Ya dai kamata kan ka koma gurin aikinka, kuma kasan Fulani ba son take kai nisa da ita ba”

“Zan koma”

Sai yai shiru

for some minutes sannan ya kalli Momy ya ce

“Momy wai ashe akwai mutanen da basa da gidajen zama har sun kashe bukka? I find it so hard to believe”

“Ban fahimta ba, wa ya fada maka?”

“Mamy yarinyar nan da na ke fada miki, wai ashe gidan da take z

aune gidan baban Rahma ne, sai maciji ya sareta da ya samu labari sai ya koreta sanadin hakan aka kai mahaifiyar asibiti ina jin a can ne Doc Asim ya cire mata kodar aka sakawa Rahma, wai can din bukka suke kafawa su zauna”

“Dan wajen Fulani ina ka samu

labarin nan?”

Momy ta tambaya jikinta a sanyeye. Sai yai shiru kamar baya son fadawa Momy cewar ya je nemanta ne.

“Just tell me i want to help her, ina zan samu ganin yarinyar nan? An zalince da yawa, tana neman gurin zama ace kuma an yi ma mahaifi

yarta haka, mahaifiyar ma tana da rai ko ta mutu? Kuma ace mutumen da ya koreta

a gidan macijin ya tsareta a gidan an dasawa yarsa kodar mahaifiyarta, yarinyar nan ba zata taba mantawa da ku ba Dan wajen Fulani kun cucece ta”

Momy ta fada hawaye na sauk

o mata, zuciyarta ta cika da tausayin Ataa duk kuwa da kasancewar bata taba ganinta ba ko sau daya. Aliyu ya baro kujerar da yake zaune ya zauna kusa da Momy.

“Momy trust me, Wallahi ba da sanina akai mata haka ba, duk laifin Doc Asim ne, nima ta ba ni

dan tausayi....”

Momy ta kalleshi.

“Da? Dan tausayi fa ka ce Dan wajen Fulani, sai ka ce ba musulmi ba, irin wannan yarinyar ai kamata yai ma a kwato mata hakkinta”

“Gurin wa?”

Ya fada yana kallon Momy. Sai ta share hawayen da suka zubo mata

ta ce.

“Seriously yarinyar nan ta ba ni tausayi, yarinyar da take irin wannan rayuwar sai kuma a sake jefata a wata rayuwar ta wahala, ku kuna cikin farinciki ita an saka ta a kunci”

Ya busar da iskar bakinsa, ba dan tausayinta yake ji kamar yadda y

a ce wa Momy ba, tausayinta ne gaba daya ya cika masa zuciya, be taba jin tausayin wata halitta mai sunan dan'adam ba kamar yadda ya ji yana tausayin Ataa a yau, and the most annoying part is be san inda take ba, waya sani ko sanadin hakan ta kara shiga wa

ni halin.

A unguwar yai sallah la'asar sannan ya nufo gidansa, yana ta sake saken zuwa kaduna daga can ya bi ta Abuja ya gaishe da Mama Fulani, sai dai daya tuna da cewar idan ma yaje din be san mi zai ce mata ba sai duk wani karfin guiwa na shi ya zub

e daga ya yanke shawarar samun wani ya bincika masa a can Kaduna din.

ATAA POV.

Ina zaune a inda Maman Salma ta tafi ta bar ni ban tashi ba su kuma ba su kula da ni ba, ina zaune a guri har na iya gane anyi sallah azahar ta hanyar agogon falon

daya nuna karfe 2. Ban san wa zan yi ma magana ba cewar ina son nai sallah ba, domin ban ga fuskar kowa a cikinsu ba, duka yan matan ko wacce ji take da kanta dan ko kallo ban ishe su ba, bana jin cewar idan nai musu magana za su amsa min, ina zaune a guri

n ina ta rokon Allah ya kawo min mafita sai ga Inteesar ta shigo sanye da uniform din Islamiya tana kallon inda na ke.

“Ke Ammy na kiranki”

Ta fada min sai kuma ta nufi Anty Maryam tana fadin.

“Anty Maryam makaranta zanje yanzu ba kudin na siyo

miki tuwon madara”

Ni dai ban jira na ji abunda Anty Maryam din zata fada mata ba, na mike tsaye na nufi kofa na fita da sauri kamar zan fadi. Hanyar da naga Maman Salma ta bi farkon zuwan mu na bi na shiga part din Ammy da sallama, sai ta amsa min da f

ar'arta kamar dazun har hakoranta biyu na makka na bayyana, na sake gaisheta ina risinawa kasa.

“Lafiya kalau ya ma sunanki?”

“Aisha amman Ataa ake kirana”

“Masha-Allah ashe Mamana ce, fatar dai kin iya yankan allayahu ko?”

“Na iya”

“Da kya

u to shiga kitchen gashi can sai ki yanka min ki wanke kinji ko?”

“To amman ban yi sallah ba”

Sai ta nuna min bandakin da ke falon.

“Shiga can ki yi alwala”

Na nufi inda ta nuna min, a lokacin da na shiga sai na samu komai tsaf kamar ba a taba

shiga bandakin ba, a kasa nai alwala domin na hango akwai hanyar ruwa a gurin sannan na fito na shimfida dankwalina kusa da kofar bandakin nai sallah, sannan na nufi kitchen ina shiga na samu allayahu a kwando na dauka na gyara na saka wuka na yanka kanan

an sannan na wanke mata na aje kamar yadda ta bukata na fito daga kitchen din.

“Na kare”

“Yauwa sannu ko, za ki iya tafiya”

Na juyo ina ta jin kamar nai zamana a part dinta ko ba komai zan fi sakewa fiye da part din Mama Fulani da ba su san daraj

ar mutane ba. Haka na dawo part din cikin rashin jindadi da na dawo ban samu kowa a falon ba sai tv, a inda na zauna dazun na sake zama sai na raba da kujera saboda na jidadin jinginawa, haka na zauna a gurin har la'asar ba a bani abinci rana ba, da akai l

a'asar ne na unkura zan tashi sai na ji an turo kofar falon an shigo, waigowar da zan yi sai na ga Muhseen, murmushi ya sakar min ya karasa inda take nake yana fadin.

“Tun da na ganki na ke ta tunanin inda na san fuskar nan take, sai yanzu na tuna da n

a taba ganinki asibitin uduth ko? Kin tuna?”

Na dan yi shiru alamar tunani sannan na gyada masa kai alamar na tuna.

“Good girl, ashe zan sake ganinki, kin ci abinci?”

Na girgiza masa kai alamar ban ci ba.

“To kin yi sallah?”

Nan ma kan na g

irgiza masa sai yai murmushi.

“Ba ki magana ne hala?”

Na yi shiru ban ce masa komai ba, na yi kasa da kaina.

“Za ki sha wahala idan kika ce kunyata za ki ji, ga toilet can je ki yi alwala sai ki zo ki ci abinci”

Ina nufar inda ya nuna min sai

Mama Fulani dake saukowa ta daka min tsawa.

“Karki kuskura shiga toilet din nan, yarana su shiga ke ki shiga akan me?”

Tsayawa nai cak ina kallonta kamar yadda shi ma yake kallonta.

“Sallah za ta yi fa Mama”

“Ko mi za tai taje can a tab din

garden ta yi karta shiga mana toilet”

Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya kalleni ya ce.

“Idan kin fita daga falon nan za ki ga wani gurin ai kin san Garden ko?”

Na gyada kai.

“To can za ki je”

Na juya na fice daga dakin ina hangen ya

dda Mama Fulani take watsa masa harara da alama bata jindadin yadda yake min magana ne. Fitowa nai daga part din na nufi garden din, ina shiga na samu kaina a cikin wani irin katon guri mai shuke shuke kala kala ga wani bangare an ware anyi pool mai zubar

da ruwa gwanin sha'awa. Inda na hango fanfo na nufa na kunna daya nai alwala na shimfida dan kwalina kamar dazun nai sallah, da nai sallah sai na yi zamana a gurin ina ta kalle-kalle kamar an ce na juyo sai na hango mutum ta windows mai gilass yana kallona

, kasa nai da kaina ina jin tsarguwa da kallon wata kila ma ya dauki tsawon lokaci yana kallo ban sani ba. Tasbihi na shiga yi da hannuna ina tasbihi da na gaji na tashi na koma part din dan na fara jin yunwa sosai, ina ko shiga na samu su sukansu a dinnin

g suna cin abincin, a inda na zauna dazun na sake zama na labe bayan kujera.

“Yar kyakkyawa zo ki karba”

Muryar Ya Muhseen ce hakan yasa ni lekowa sai yai kirana da hannu, ba musu na tashi na karasa inda suke sai ya miko min plate din abinci cike da

nama.

“Muhseen you know me well bana son haka, bana son wani ya ci abinci da kwannon da muke ci”

Mama Fulani ta fada tana kashe ido.

“Yunwa take ji”

“Dan tana jin yunwa sai ta ci abincin a plate din ka? What nonsense is this? Ke tara dankwal

inki ki zube, kamin a duba miki wani gurin”

Mai nema sai hakuri, a haka na cire dankwalin kaina na aje akasa sannan na karbi abinci na zube a dankwalina yana ta kallona cikin yanayin da ke nuna be jidadin hakan ba, na dauka na fito daga falon gaba daya

na koma garden na zauna na ci abuna sai da na koshi sannan na bude fanfan ko na sha ruwa na wanke dankwali na shanya. Ina gurin wani matashin saurayi dan kazo na zo ya same ni a gurin yana fadin.

“Ke zo a nuna miki gurin kwananki”

Tasowa nai na biyo

shi yana gaba ina biye har muka isa gurin motocin gidan, wani tsohon gareji ya bude ya nuna min shi.

“Nan za ki rika kwana”

“To na gode”

Sannan ya juya ya tafi ni kuma na zauna a gurin, ina ta kallon yadda yai datti, ba a dauki lokaci ba sai gash

i ya dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login