Showing 21001 words to 24000 words out of 237425 words

Chapter 8 - ZAKI COMPLETE

shanye ba ko suga. Sauran ragowar kudin na fito da su ina kargawa da na hada sai na ga ba su kai ma dubu uku ba gaba daya dubu biyu ne da dari hudu da naira talatin, haka na hada kudin guri daya, na kurawa

Lukman ido ina ta kallonsa yana shan koko duk da kasancewar hankalina a gurinsa ya ke ba. Bayan ya gama na dauki wainar da ragowar canjin mu doshi asibitin ni da shi ina tafiya ina jin kamar ana turani gabana sai faduwa yake. Lokacin da muka isa asibitin s

ai masu gadin ward din suka hana mu shiga, wai ba a zuwa ganin marar lafiya sai da yamma haka dokar asibitin ta ke.

“Ba ganinta na zo ba, abinci na kawo mata kuma ni nake jinyar ta”

Na fada cikin muryarta ta gajiyayyu mutane marasa galihu.

“To ba

ri likitoci su fito sai ki shiga”

Na koma gefe na tsaya kamar yadda na tararda wasu mutanen a tsaye, ina nan zaman jiran likitonci su fito wata Nurse ta fito daga dakin tana tambayar mai jinyar Asma'u Ummaru.

“Ga ni nan”

Na fada da dan kuzarina.

“Shigo ciki ana nemanki”

Na bi bayanta kamar yadda ta umarta Lukman kuma ya biyo sai securiting ya rike shi a nan ya fasa masa ihu kamar zai tashi kunnuwansa a dole ya sake shi ya biyo bayana.

Kusan likito ci hudu ne tsaye akanta ta farka har sun

tashe ta ya dan jingina da gadon tana kallonsu bakinta ya bushe sosai har fatar bakinta ta fara kankara kamar wace ta shekara ba ta sha ruwa ba.

“Ke kike jinyarta?”

Daya daga cikin likitocin ya tmabaya yana kallona, wata kila gani yake kamar na yi

karama ko kuma kyauwo na yake kallo oho.

“Eh ni ce wani abun ne?”

“Babu wani babba sai ke?”

“Bata da kowa sai ni, ni ma kuma ba ni da kowa sai ita”

“Ina hoton da na rubuta miki jiya kin yi?”

Sai da yai maganar na iya gane daya daga cikin lik

itocin wanda ya karbe mu ne jiya da muka zo.

“Ban yi ba, sai yau zan je na yi”

“To kije ki yi, yana da kyau a kara tabbatarwa, abu na biyu kuma karki kuskura bata komai ta ci drip din da aka saka mata ba zai bari ta ji yunwa ba, ba za ta ci komai ba

sai an yi mata hoton an kara tabbatarwa”

“To na gode”

Na fada cike da sanyin murya, sannan dayan ya miko min wata farar takarda.

“A siyo mata wadannan magungunnan”

“To”

Na fada bayan na karba, sannan na zauna a kujera ina hawaye, su kuma s

uka nufi wata marar lafiyar dake kusa da mu suna dubata.

“Sannu Nana”

Na fada ina jin kuka kamar zai kubuce min, sai tai murmushin karfin hali ta ce.

“Yauwa, Lukman”

Ta mika masa hannu sai yaje da sauri kusa da gadon ya tsaya yana share hawaye

n kukan da be gama ba har yanzu na rokewar da wacan securiting yai masa abun ka da mai tsoron mai uniform.

“Mi akai maki? Kin ci abinci”

“Na sha koko, wacan dan sandan ne ya rike ni wa ba zan shigo ba”

Ya fada yana hawan gadon ya zauna, sai ta ka

lleni.

“Ke kin ci abincin”

Kai kawai na iya gyada mata alamar na ci din, sannan na mike tsaye.

“Ina zaki je Ataa?”

Ta tambaya da yaren buzanci, ni kuma na bata amsa da hausa.

“Zuwa zan yi na tambaya kudin hoton da maganin na ji ko nawa ne”

“Kar ma kije tun da kin san ba kudi da mu ba”

“Ba ki sani ba ko kudin ba shi da yawa, kara dai na tambaya na ji, idan da yawa sosai sai mu hakura”

“To Allah yasa ba bu yawa, akwai ragowar kudi da yawa a hannu hannunki?”

“Eh akwai”

Duk wanna

n maganar da yaren buzanci mu kai sannan na mike tsaye na fita jiki babu kwari, sai da na tsaya bakin kofar na fadawa security cewar zan dawo kuma ni ce ta dazun mai jinyar marar lafiya gudun kar ya sake hana ni shiga idan na dawo. Wannan karon ban tambayi

kowa ba na nufin gurin hoton sai suka rubuta min kudin hoton a jikin takardar dubu takwas da dari biyu wai babban hoto ba ne wanda za a ga duka sassan jikinta a jikin hoton. Sannan na doshi pharmacy na mika musu takardar suka duba suka rubuta min kudin ma

ganin shi ma dubu biyar da yan kai, dukan ya tashi kusan dubu goma sha dubu ba dari uku, ji nai kamar na dora hannuna saman kai na kurma ihu, sai dai idan nai ihun wa zai taimake ni wa zai tausaya min har ya kawo min a gaji, a halin da na ke a yanzu ni kai

na tsoron taimakon na ke duk wanda zai yi kare ni da zimmar taimako matukar ba ni na nema ba, na yana da wahala na iya amincewa da shi. Tafiya na ke kaina a kasa idona na zubar da ruwan hawaye, jin na ke kamar fuskata za ta taba kasa saboda maso min da til

e din da nake takawa ake ina ganinsa kusa da ni.

Kallon da na ga mutane na min ne yasa na share hawayen na daga kaina sama har na iso ward din na shiga, yadda na bar Nana haka na sameta Lukman na kusa da ita tana ta mata firar mafarkin da yai.

“Kudin

na da yawa ko?”

Ta fada tun kan ji ta ji domin yanayin fuskata ya nuna hakan.

“Su na da yawa amman za mu iya samu idan muka yi bara, sai na hada da wandanda suke hannuna”

“Ataa kudin da za muke samu a bara ba su da wani yawan da za mu iya siyen m

agani”

“Zan yi kokarin na samo su cikin sati biyu, ni da Lukman za mu yi In-Sha-Allah za mu samu kuma za ki samu lafiya Nana”

“Ko dai mu koma asibitin wacan likitan?”

“Aa ba sai mun koma ba, ba kuma za mu koma ba har a bada”

Na fada cike da zaf

in rai.

“Amman ya taimaka mana ai”

“Eh ya taimaka mana ya ceto ranki daga saran da maciji yai miki, sai dai yanzu tiyatar da yai miki duk ita ce ta ja mana wannan matsalar”

“Cewa sukai wani abu ya samu tiyatar ne?”

“Aa cewa sukao maganin da ki

ka sha ba shi ya kamata koli sha ba wai likitan be kware sosai ba”

A take naga hankalinta ya tashi, har fuskarta ta kara boyewa, nasan da na fada mata gaskiyar cewar kodarta aka cire wata kila zan iya rasata ma a nan take. Matsawa nai kusa da ita ina ko

karin kwantar mata da hankali.

“Nana ki kwantar da hankalinki zan samu kudi zan biya a baki magani, kuma za ki warke za ki tashi, domin sun ce idan aka ba ki maganin za ki iya jin sauki a take”

Hawayen idonta ta share tana sauke ajiyar zuciya tare da

saka dayan hannunta ta dafe gefen hakarkarinta.

“Nawa ne kudin maganin?”

“Dubu takwas ne kuma akwai ragowar dubu biyar a hannuna, kin ga dubu uku kawai za mu samo”

Na mata karya saboda hankalinta ya kwanta. sai ta lumshe ido hawaye suka sauko ma

ta, ashe zubar hawayen mahaifiya yana da zafi da daraja a idon 'ya'yanta, domin a take na ji duk wani kuka nawa da na ke kokarin tarewa ya tafi sai na nemi rashin kuzarin na rasa, wani karfi da shaukin neman mafitar inda zan tsayarda da zubar hawayenta ya

cika ni. Mikewa nai tsaye na juya da zimmar tafiya sai na ji Lukman ya kira ni.

“Ataa zan biki ni ma zan yi baran”

Hannuna mika masa ya mikon nasa na rika muka tafi daga ward din zuciyata cike da karsashi.

Babban titin Gawon Nama muka fara yin

baran, ganin ďan abun da muka samu ba mai yawa ba, yasa na ja hannunsa muka nufi titin gadar Alu ganin can din kamar ya fi manyan motoci, misalin karfe daya muka isa gurin bani da agogon da zai tabbatar min da hakan, sai dai ganin yadda rana ta soma budewa

tana yin zafi yasa na fahimci hakan, gashi kuma wasu masallatan har sun fara kiran sallah karfe daya. Muna tafiya Lukman na ta bata fuska da alama ya gaji da tafiyar da muke a kafa, daga ni har shi sai gumi muke na wahala.

Muna isa na nufi gurin wasu

motocin shi kuma ya doshi wasu yana mika musu hannu, ba zan iya fadar abunda ya faru ba, iyakar abunda na sani an saki traffic motocin sun fara wucewa sai kuma na jiyo ihun Lukman da dukan karfinsa sai kuma na ji kaurar karafuna. Juyo nai a firgice ina ka

llon mutane da ke nufar gurin da sauri, wani irin kara nai da muryar da ban taba sanin ina da irinta ba, na saki kudin da ke hannuna na n ruga a guje ina haniniya kamar wani doki...

ALIYU POV.



Yana zaune sitting rooms dinsa yana duba wasu ta

kardu da Nasir ya kawo masa tun daga Abuja domin ya saka hannu.

“A nan ma kai za ka wakilce ni Nasir, ba zan iya barin Matata a nan na tafi saboda aikina ba”

“Amman miyasa ba zaka dauke ga kuje can gaba daya, ai zaka iya kula da ita a can din ma”

Shiru yai few minutes kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yai maganar cike da gundira kamar wanda ya shekara yana magana da wani.

“Yeah ita ce ta ki ta yarda wai ta fi son kusa da Familyn ta har sai ta ji sauki sosai sannan ta koma”

“Amman ai zaka i

ya convince dinta ta yarda ta bika”

Aliyu be sake ce masa komai ba, wayarsa da ke aljihu tai kara alamar sako, fiddo wayar yai ya duba.

_Na shirya kuma ina son ruwa_

Cikin sauri ya saka hannu ya mike tsaye yana kallon Nasir.

“Matata tana da

muhimmanci a gurina i can't choose my work over her, kar ka sake min irin wannan maganar”

Yana fadar hakan ya jefar da takardun saman center table din dake tsakanin shi da Nasir din ya bi ta kofar ciki ya fito ta baban falon. Kai tsaye freezer ya nufa y

a dauko robar ruwa ba mai sanyi sosai ba da cup ya nufi upstairs. Tana zaune bakin gado ta cancanda ado kamar wacce zata je gurin biki sa kanshim turare take.

“Princess you look cute”

Ya fada yana kokarin aje ruwan kasa tare da kai hancinsa ya shimsh

ina gefen wuyanta.

“Kun kare meeting din?”

Ya gyada mata kai yana zuba ruwan a kofa.

“Nasir ya tafi?”

Ya daga kafadunsa alamar be sani ba, sannan ya kai mata ruwan a baki, kadan ta sha ta kawar da kai.

“Mu tafi yanzu”

Ta riga shi mikewa

tsaye kamin shi ma ya mike ya riko hannunta suka sauko downstairs. Kadan kadan take tafiya kamar mai tausayin kasa har suka isa gaban motar ya bude mata ta shiga, ganin babu motar Nasir na tabbar masa da cewar ya fice. Front seat ta shiga shi kuma yaja mo

tar tun kan ya juyo da motar mai gadin ya bude masa gate. Kai tsaye Family house dinsu Rahama ya fara isa ya aje, sai suka bude motar suka fito tare, tana gaba yana bayanta har suka shiga cikin falon yadda ta tararda fuskokin my siblings dinta ta san ba la

fiya ba.

“Miya faru na ga fuskokinku a haka?”

Ta fada cike da faduwar gaba, tana kokarin zama kusa da kanwarta Razinatu.

“Wallahi one of those big shopping mall din Daddy da ke kano ya kone, ya ma tafi can tun da safe shi da Mommy”

“Innalilla

hi wa'inna ilaihirraji'u”

“Saboda wannan tashin hankalin na ki yace kar a fada miki baya son ranki ya bace”

Cewar Razinatu sannan ta shiga sahun yan'uwanta da ke mikawa Aliyu gaisuwa, shi kuma gaba daya hankalinsa yana kan Rahma ganin kamar ta tashi

hankalinta sosai.

“Dear”

“I'm okay, idan ka je ka ce ina gaishe da Momy kuma na mata naganar mai aikin”

Kai kawai ya gyada mata sannan ya juya ya fice wani shan kamshi. Yana shiga motarsa ya dauki hanyar family house dinsu daman yana jin cikinsa b

abu nauyi.

Ko da ya shiga falon ya tarar Momy na tattara littafan da jikokinta suka watsar wato kanenen Aliyu da akaiwa aure suka haihu.

“Momy barka da safe”

“Safe yanzu 12:13pm?”

Ta fada tana kallon katon agogo dake falon. Shi ma kallon tsad

adden agogo hannunsa yai kana ya zauna yana fadin.

“Ban san ta yi ba, gaske na ji cikina ba nauyi”

“Matarka bata nan?”

“Tare muka fito da ita na aje ta gidansu”

Momy ta cigaba da tara books din ba tare da ta kara cewa komai ba, shi kuma yana t

a kallo yanayinta.

“Anything Momy?”

Sai ta kalleshi.

“No nothing kawai ina tunani ya kamata ace ka ci abinci ne kamin ka fito”

“Momy yadda kike tunanin Rahma fa ba irin waennan 'ya'yan talakawa ba ne, duk wani aiki mai nauyi Rahma ba za ta iya

ba, ko da can ma balle yanzu, kuma dacan Rahma tun da ta tashi a gidansu ba ta aikin komai bayan hutu saboda ciwon kidney din da take”

“Kuma bata iya zuwa gidan sukukanta ta gaishe su ba ko? Gidansu kawai ta sani sai gidan kawaye sai fita waje idan ta

gaji da kasar”

Ya shafa kansa yana ta neman kalmomin da zai hada ya fahimtar da mahaifiyarsa ko wacece Rahma.

“Yana da wahala ka ga kafar Rahma a gidan nan sai idan wani abun ake muhimmi, shin bata san zuwa gida sukurukai gaishesu yana da muhimmanci

ba? Ko ta dauka Fulani ce Real Mother dinka? Bata taba fada mata cewar ni na haife ka ba? Ko kuma tana ganin kamar bana jin zafin abun ne? Idan zaku zo hutu daga Abuja wani lokacin har ku kuma ba zata tako kafarta gidan nan ba, sai idan za ku tafi shi ma

idan kuna tare,, balle kuma ta dauko wani abu ta kawo min ko ta aiko min, ba dan ina da bukata ba, amman kowa yana son kyautatawa”

Momy ta fada mishi with serious face. Mikewa yai tsaye ya nufi dinning ba tare da kalma daya ta sake fitowa daga bakinsa b

a sai dai yadda yaga fuskar mahaifiyarsa ta cikinsa yasa shi jin babu dadi be taba daukar abun nan da Rahma take wani abu ba, a ganinsa Rahma ta riga ta saba da rayuwar turai ne, ita kuma Momy ta kasa hakan, ba kamar Mama Fulani ba da bata taba damuwa da s

higa safgar Rahma ko da kuwa zata taka ta ta wuce ba dan komai ba sai dan tana ganin daga Rahma har ubanta ba su kai matsayin da zata iya kallonsu ba, domin ita bata huldu da duk wani mai kudin da baya isa amsa sunansa a birnin Abuja.

____________

Assalamu Alaikum.

Kwana biyu ban yi posting ba hakan ya faru ne saboda rashin lafiyar Kakata, amman yanzu Alhamdulillah, In-Sha-Allah posting babu kama hannun yaro.

And ina son nai amfani da wannan damar na sanar da ku cewar da zarar mun kai page 1

2 za mu tsayar da Free pages, hakan na nufi sai mutum ya biya sannam ya samu cigaban labarin, daman na fada tun a ZABIN RAI cewar littafin ZAKI na kudi ne, wadanda suka sani sun sani domin na fada, and ina yin littafi free, wanda zai zo bayan shi na kudi,

kamar dai yadda RAI BIYU ya zo free HAFSATU MANGA (yarinyar K'auye) na kudi, haka ma ZABIN RAI free ZAKI na kudi.

Ga wanda suke son fara biya tun yanzu za su iya turo 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot t

a wannan number 08036126660, 'yan nijar za ku tura 500f na line orange ko zain ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Paid Group.

Thanks

🙏🏻

https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K I*

By Khadeej

a Candy

1





0





Kamar wata mahaukaciya haka na rika ratsa mutane ina cusa kaina har na karasa inda yake, ihu yake ta yi yana rike da jafarsa yana jiran sunana.

“Wayyo Allah Ataa kafana wayyo ni kafana”

Babu jini a kafar amman yadda yake ihu

cikin magagi ya fahimtar da ni irin ciwon da kafar take masa, ga gefen kansa sai jini yake yana ta wani jujjuya ido kamar zai shude.

“Ai wallahi Allah ya kara mutanen ba su da godiyar Allah, kullum cikin bara, da sun hango mota har sauri suke su mikawa

mutane hannu, yara kanana an koya musu bara”

Shine abunda mafi akasin mutanen da suke gurin suke fada, masu ganin tausayinsa kadan domin sauran ta'alaka abun ne da rashin wadatar zuci irin na mu, na raba a titi da kaskantarta kai.

“Jama'a ku taimak

a min kar ya mutu”

Shine abunda ya iya fada cikin kuka, sai daya daga cikin mutanen da ke tsaye ya zo ya dauke shi ya saka a mota wanda na ke kyautata zaton shi ya kade shi. Gidan baya ya bude min na shiga gurin da Lukman yake sannan ya bude mazaunin di

reba ya zauna na fisgi motar muka doshi specialist hospital wato asibitin daji. Muka isa aka wuce da shi layin yan hadari ni kuma na bi bayansu hankalina a tashe, sai da suka fada min cewar na je na karbo kati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login